← Book details Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta kuma bashi amsa an sake bugun ƙofar “Ma can i come in?”

Sakin hannayen junansu sukayi Al’ameen yayi saurin nufan ƙofa ita kuma Kausar ta koma kan kujera ta zauna

Yina buɗe mata ƙofa yayi maza ya fice

Wani irin kallon tuhuma July ta bishi dashi kafin ta shigo office din gabaɗaya

“My friend Baki gota lokaci why now? Kin kara mana minti sha biyar akan talatin ɗin da kika bamu duk muna zaman jira...”
[3/10, 3:07 PM] Chu_chu👻💩: Page C
My house boy📚

At the meeting round

Kausar good presentation take badawa tana cire main main point din abunda sauran ma'aikatan suke tattaunawa at her presence ,el'ameen yina zaune a ta gefen ta itakuwa tana tsaye tana bayani ,gabadaya dakin anyi shiru ita ake saurare ,gabaɗaya burgesa yaji tanayi don haka yakai hannu ya ɗan taɓa gefen hip ɗin ta da ya fidda shape mai ɗaukan hankali ,saida yakai hannu ya taba wajen sannan ya ankara da shirmen da ya buga . Da sauri ya janye hannunsa yina kautar da fuska .
Kausar ba haƙuri dakatawa da magana tayi ta duƙa cikin murya ƙasa ƙasa tace “Me yasa ka taɓeni....ehemm meyasa ka taɓani?”

“It was a mistake” harara ta banka masa gamida cewa mistake?”
Oga AD da ya gaji da watching drama ɗinsu katsesu yayi da cewa “Hey what's going on?”

El’ameen kautar da fuska yayi yina washe baki “Eh sir dama na tuna mata ne game da wani point da ta manta bata faɗa ba ”

“Oh I'll like to hear that faɗa mana” tsuru tsuru dukkansu sukayi da ido sabd dai babu abun faɗi,July kuwa tafi kowa fusata a wajen saboda ta gane irin shishigewa Kausar da El'ameen yakeyi yana da manufa na soyayya gashi ma har sun fara nunawa a cikin jama'a.

“Uhmm ehhh watoo dammmaaaa” gabadaya fashewa akayi da dariya jin yanda ya daburce ya rasa mai zai fada don yayi saving dinsu kuma ya gasgata kansa .

Mr Ad ba karamin yaro bane ya rigada ya ranfosu don haka bai ja da tsayi ba ya kawo karshen meeting din tunda brain boxes din nashi sun tafi wani duniya bazaa taba kawo abu mai nagarta a zaman ba.

Da ɗaya da biyu kowa ya fita ya bar Kausar da El'ameen a dakin tana nan tsaye a kansa ,tana ganin an watse ta fara magana

“El’ameen kake ko wane? Nagode da taimako na da kayi a baya,amma hakan ba zai zama dalilin da zaka ringa taɓa mun jiki a kowani lokaci ba,mind you jail is real ! So becareful

Yes bana manta alheri ko ya Yike ,saboda haka tashi muje zan fita dakai shopping muje ka sauya wardrob dinka atleast ka samu sababbin sutura...Inajin shine kadai hanyar da zan taimaki samartakanka😏”

Miƙewa yayi ya ɗan tafa hannu gamida sakin wani killing murmushi “Hakan yayi kyau wowww😘”

Sai kuma ya ɗaure fuska yazo ya ɗan dafa kafaɗarta yina saka idonsa a ƙwarar idonta ,sosai ya sauke muryarsa kamar mai raɗa kar wani ya ji su

“Bazan iya fita dake ba😏” sattt ya sace Mata gwuiwa don haka ta tsaya galaala tana kallonsa ,saida yayi taku hudu sannan ya waigo ya kalleta yina dage mata hannu

“Parameters ... remember?” yayi waje abunsa yina wani irin tafiya na gadara

Dafe kai tayi da sauri ta zauna akan kujera ta ɗan saki ƙara “Y na? Yayi gaskiya fa Ni boss ɗinsa ce bai kamata in fita dashi ba”

July tana ganin ya fita ita kuma ta yi maza ta shigo

“Babe whatsup?”

July samun waje tayi ta zauna
“Ok fada mun🤗”

Ɗan haɗe gira Kausar tayi “Me kenan?”

“Rannan kun fita da sir El'ameen late evening ya tuka ki a mota daganan all d dramas begun ,me ya faru ne wai?”

Kausar takowa tayi itama ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna “Hmm kina tunanin wani abune tsakani na da yarona? To kar shaidan ya nema wassafa maki abunda babu...idan kinaso kijine, na canja mai aikine saboda wannan yayi masa ƙarfi ,yafi dacewa da yazama driver na ,don haka daga yau ma bazaki sake ganinsa a kamfanin nan ba”

Sosai July ta hango kishi a ƙwarar idon Kausar don haka tace “Ina gargadinki my lady ,wannan ba irin sauran mazan da kika sani bane”

Cikin mamaki ta waigo ta ɗan tsura mata ido kafin ta kauda kai da sauri “Wow i just see that....”

“Zakisha mamaki idan nace maki je was a lady killer😢kassara zuciyar mace yakeyi ta mace a soyayyarsa na yaudara shiyasa duk inda ya soma aiki ake koransa....Plz bana son kema ki zama victim”

“Hmmm na gani fa ,lover boy has a history...yanzu ke Juliana banda kin raina Ni wata tsiya zanci da wannan ƙaramin yaron ,and beside Yaron gidana ne can't you see? Ko Number 14 ɗinki baya aikine?🤔”

“Uhm uhm ki gane fa😄guy din nan yanada wasu irin kwaliti da Yike cusa maka soyayyar sa kafin ka farga shine abinda nikeso ki gane”

Ɗaga mata hannu Kausar tayi tadan kashe mata ido guda gamida murmushi “Ina iya karantar Yaren zuciyarki amma yanzu zan barki ki sarara ...bye😂” ta miƙe ta kwashi laptop dinta da keys ta fice tana murmushin da bata san ko na menene ba
Ni kuwa nace kamar na yaƙin neman zaɓene,kuma ta lura ƙuri'un ta suna sama

Guys ku gane mana ....baku ganin wani abu na moving tsakanin kausar da El'ameen ? Indai na fara hasashe.

Tana shiga office ta hangosa a office ya taƙarƙare yana aiki ,har ta gotashi kuma ta dawo ,kai tsaye ta sa kanta a office ɗin sa ta masa tsaye a kai ,ɗagowa yayi ya kalleta kuma sai yayi maza ya sunkuyar da kai

“Man ! Me kakeyi¿”

“Just some creations”

“In gani” shiru yayi bai motsa ba ,da sauri tazo gabansa ta warce ƙatoton farin carbon papper ɗin ta ɗaga tana ƙarewa zanen da ya fitar kallo

Lambune ya zana mai kyawun gaske sai mace ta kwanta akan rubber grass ɗin da yayi luf luf a ƙasa ,cikin shigar turawa kanta yasha gyara Idanuwarta a lumshe ,gefen kanta glass cup ɗin lemu ne rabin kofi ɗaya ɓangaren kuma laptop

Can wajen ƙafarta kuma ya zana namiji da jallabiya yina rainon wani cute babe da feeding bottle a Hannunsa da ƙatoton kitty bear.

Caɓe baki tayi saboda namijin fuskarsa ya zana ras ,ga yaron lukuti mai kyau ɗan jawur dashi kamar ɗan turawa ,saidai macen ne ansa ƙyalle an kulle mata fuska a zanen so bata gane ko wacece ba.

Saida ta gama karantar hoton tass sannan ta bushe da dariya

“wow excellent This is a new modern couple designers ....Oh wato kai ga kalar rayuwar da kake hango ma kanka kenan? Ka zama bawan mace ko kyakyawar family dadaɗan halaƙa Hmmm Love one tin tin ” murmushi yayi ya sunkuyar da kai don tabbas ta shigar masa privacy ɗinsa Amma kuma yaji daɗin yanda ta yabo zanen sa

Ba zato yaji ta kausasa muryarsa “Alhaji ka ɗebo wa kanka fake life ,kana wahalar da zuciyar ka da harsashen abinda bazai taba tabbata ba ,don wannan kalar macen da ka zana tafi karfinka”

Muryarsa sosai yayi rauni zuciyarsa ta katse “Yes shiyasa ma na yarda in zama yaronta”

“oh sharraf 🙄......Idan har zaka cigaba da sakawa a ranka wainnan banzayen tunanin a ƙananun shekarunka tayaya zaka iya aikin office? Don haka this is your last chance da zan ce maka bana son sake ganinka a office din nan ,aikin driving shi yafi dacewa dakai sai kayi ta tunanin soyayyar gizo da kokin amma ba anan ba.
Sannan magana ta karshe zan maka Alfarma ta karshe wajen baka masauki a gidana cikin ɗakunan masu yi mana aiki don gaskiya gidan da naga kana rayuwa a ciki na tausaya maka...so mr el’ameen a tashi aje mota a jirani har in Gama aiki banason in sake ganin madigan ƙafarka anan”

Ta juya cikin takun ƙasaita ,ta fara tafiya har takai ƙofa ta waigo ta kallesa

Yina nan yina bin bayanta da kallo yina wani mirmir da ido yina shafa kwantaccen ƙasumbarsa with excited face ☺️

“You heard me?😎”

Da sauri ya mike “Yes boss . Thank you ma I'll be there shortly”

Tsaki taja ta fice.

Oum Aphnan
09065990265
[3/10, 3:08 PM] Chu_chu👻💩: Page D
My house boy

Kausar lokacin tashi nayi haɗo kan kayanta tayi ,ta fito waje ,anan sukaci karo da zarah collègue ɗin ta ne

“Kausar ya aikin dai?”
“Hmm ki bari kawai zarah wlh gajiya nakeyi sosai ,inajin dai zan karɓa lv ne inje vocation ”

“To ba naga an samar maki wani assistant Ba ,dukda kamar bakwa shiri” cabe baki Kausar tayi ba tareda tace mata komai ba ta karba file din hannun zarahn da ta kawo mata da nufin tayi sign ta shiga yin mata sign ɗin a kan hanyan.

“Tell me about him”

A fusace ta juya ta kalli Zahra din “Kar ki cemun kema zuciyarki tana wajen sa , auchhhh abun da ciwo wlhh”

“😄Yana da kyau ,ga zati, ga iya lafazi”

“...mtseww arrogant kuma ba,gwara ki ƙara masa da wannan...kin gane ko guy din yasan farashin kansa ,to so yake ya mulki kowa? Mtsewww shashasha”

“Ke dai kawai baki sonshi ne halan?”

“I dont care much about him...Ina fatan su kawo mun much more efficient assistant ba wannan ba”

“Ke kuwa amma kowa yabonsa yake wajen hazaƙa”

“Amma kuma yina da gajeren tunani ba”

“hajiya gayen nan fa ya haɗu wlh ƙarshene ....ahhhh wayyo Allah walh yana burgeni ” wani kallon banza Kausar tabi zahra dashi a take taji ya fara tsanarta ,daidai nan ya nufo inda suke da shirin tafiya .

Aikuwa zahra ganin yina nugosu ga Kausar tana Binta da wani kallo mai harara harara yasa ta fashe da dariya

Tsaki Kausar taja ta wuce da sauri tabar wajen ,shima ya bi bayanta da sauri ,mota suka shige yau ba uhm ba uhm uhm haka yake driving itakuwa Kallon ƙeyars kawai takeyi tanason ƙwaƙulo muninsa da mutane ke makancewa dashi suke nacin sonsa.

Wayarta ne ya fara ɓurari ,da sauri ta ɗauka gaba-daya ta haukace ganin mai kiran likitanta ne

“Hello Doctor good afternoon”
Chapter 2 · 0% Book details