← Book details Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

El'ameen cikin barci yaji alamun gudu ana iface iface a falonsa ,da gudu ya fito dashi sai gajeran wando ,ai kuwa surayya tana ganinshi taje da gudu ta rukunkume bayansa “Wayyo ya El'ameen zata nakasta Ni...wallahi ba da nufin sharri nazo gidan nan ba invitation card din bikina na kawo maku”

Habawa kausar wani malolon kishine ya takureta yanda surayya ta lale mata jikin miji ba kaya a jikinsa ,wani dulalo ido tayi kamar me aljanu ,nunfashinta ya fara fita sama sama kamar zai dauke

“Zo ki fita....surayyya zan...za...hannn(ta soma nishi tana dafe kirji) surayya zan kasheki in Baki bar jikin mijina ba”

Ɓanbare surayya yayi a jikinta ya nufi kausar da gudu yana kiran sunanta “Sweet meye haka kinsan bake kadai ba ne meyasa zaki biye mata ”

Ai surayya na ganin ya riketa sun zube akan kafet ya rungume ta akan cinyarsa yina hura mata iskar bakinsa ta kwashi jaka da takalmin ta da gudu ta fice ,tana ayyanawa a ranta yanda kausar zatayi mata jina_jina taci biki da farfasashen jiki

Saida ta dangana da gate kana ta tsaya tana hutawa ta kira wayar driver yazo ya dauke ta zancen zucinta. Ne ya fito sarari .
“Waikkkk ai bansan wannan mahaukaciya bace ba,lallai zata iya kisa ,zaifimun sauki kar in Kara zuwa masu gida kafin su sabautani a banza ,kuma goyon bayanta za ayi ace Ni naje masu gida,bare nayi kaurin suna a dangi itakuma ana sonta amaryace a cikinsu ...”

Driver ƙunshe dariya ya dinga yi yina Satan kallonta ta mirror a ransa yina ma Allah godiya da surayya ta samu mai cin ƙaniyarta.

#Oum Aphnan
#Yaron gida na.
09065990265
[3/10, 3:09 PM] Chu_chu👻💩: END ... Inshallah🫰

Bayan shekaru 5

Alhmdllh komai ya baka kuka wataran zai baka dariya....Hausawas😉Karin maganar uwar aphnanuwan ya fita daidai kuwa?....Lolz
Hakane ya kasance a cikin rayuwar gidan Kausar da El'ameen Rayuwar Aure mai tsafta ,Nagartattun Iyali abun birgewa,Zaman lafiya mai ɗaurewa,Girmamawa gami da martabawa ,a gefe guda kuma sassanyar soyayya mai tsayawa a zuciya su suke cigaba da wanzuwa a wannan gidan.
Tafi tafi dai El'ameen da kausar shekarunsu biyar da aure da ribar diyoyi guda uku mata biyu namiji daya ,kausar tuni ta zubar da makamar yakin raina miji ta yarda tabbas komin kankantan namiji yafi karfin mace ,zai iya dealing da ita a......kun ma dai gane kawai🤣
Elameen ya zama cikakken namiji ya tara gargasa ya aje teɓa ya zama nagartaccen miji Kuma kamilallen uba,Kausar kam kullum tana packaging abunta ɗas ɗas tana cin sisinta,ta riƙe gaba ta riƙe baya El'ameen attention dinsa baya kan kowa sai Madam dinsa,bazaka taba bata shekarunta ba ,In kuwa suka fita shopping da kyawawan yaransu da mijinta ,ko sukaje biki kowa sha'awarsa yake Kallon farko zakace ita da _Mine boo_ dinta sun dace.

***
Yau sukayi anniversary dinsu na cika shekaru biyar dinsu ,anci ansha anyi hotuna sun amsa gift kamar na hauka ,haka maids dinta suka cike wani empty room da yike gefen ɗakin yaranta da kyaututtukan jama'a ta barsu sai in ta natsu zasu bude a tsanake . Kowa ya watse ta shige Toilet ta ɗan zuba turaren wankan ta masu daɗin ƙamshi kala kala ,ta ɗan diga turaren bint Sudan kaɗan ,don ƙara mata soyayya a zuciyar El'ameen ,wankanta takeyi amma jifa jifa rayuwar tagayyarar ƙawayenta su lateefat yina faɗo mata a rai ,hawayene ya fara tsatsafo mata a ido ,ba arziki ta dauraye kumfar jikinta ta fito Toilet ɗin ,ɗaure da towel , El'ameen da shigowarsa kenan yaji motsinta a toilet ya dakata ta fito yina duba hotunan da Camera man ɗin ya turo masu just now.

Fuskarta ba walwala ta fito ,ta nufi dressing mirror ta na shafa turare ko lura dashi batayi ba,ajiye wayar yayi a hankali ya saɗaɗa bayanta ya rungume ta yakai hannunsa ya rufe mata ido da tafukan hannunsa ,wani wawan ajiyar zuciya ta saki ,a hankali ta mika hannunta taɗan shafa bayan hannunsa kana a sanyaye tace “Mine boo😘” wani hustle kiss ya sakin mata a gefen wuya kana ya sauke hannunsa a fuskarsa “Happy wedding anniversary my whole world”

Juyo da jikinta tayi gaba-daya tana kallonsa fuskarta ba walwala ta fara masa magana kamar zatayi kuka
“Nagode Allah da ya bani sadaukin miji kamar ka...i thank you God for given me a joy giver ,my everlasting hubby ,Boo bansan da wani baki zan furta tarin godiyata da yabona a gare ka ba ,ka bani so ka bani farin ciki sannan ka bani kulawa,bada dun ka tsare mun mutunci na ba da ynz na zama irinsu lateefat da school momy dina gayican sunyi ma turawa laifi a Cyprus an wuce dasu gidan yari fitowa nan da 25yrs kaga fitowarsu na me rabone....Boo I'm so so worry”

Rungumota yayi sosai yana shafa bayanta a hankali “Is alright here ,uhum ....Ni ma ai ina alfahari da Matana ko ba haka ba? So don't allow that mood to spoil our night plz I need you ...Ki Shiru kinji ,ke kamilalliyace koda na aureki ban sameki a ballagaje ba ,wannan kiman zan cigaba da ganinki da shi har tsawon lumfashina na ƙarshe ,Ina sonki ina sonki rahatyl ƙalb”

Kwantar da kanta tayi a kafaɗarsa tana sakin ajiyar zuciya wani kan wani ,lallai El'ameen shine likitan zuciyarta da ɗan kalmomi ya wanke duk ciwo da mikin da take ta yawo dashi tun rana da ta samu bakar labarin ,amma ta kowani fuska su suka ja ma kansu .

“Nagode mijina ,nima ina mahaukacin sonka sadaukin zuciyata”

Ɗagota yayi suna fuskantar juna ,fadada fuskarta tayi da Murmushi

Cikin wani irin salo ya kashe mata ido guda “Oya prove it...i need some sugar ,ki jika mun aiki a daren nan ki sani kukan dadi ki tuno mun da first night dinmu...Amma yau anyu exchange kece angon nine amaryasss😁”

Tammat bi hamdullah
Barkanmu da shan ruwa duk wanda mukayi azumin yau tare dashi ,plz ya kukaji rana😟 Gsky xan huta fa,kamar ma Ulcerna zai tashine😰😂
I'll miss you guyz Ina sonku sosai.....bye😘

Taku har kullum
Uwar Aphnanuwa
Mu hade a sabon littafina
*HARIJIN NAMIJI* (BASTARD BITCH)

Thurs 9_March_2023
Chapter 17 · 0% Book details