← Book details Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Yaron Gidana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[3/10, 3:07 PM] Chu_chu👻💩: Paid Page A
MY HOUSE BOY

Kausar daga wajen aiki kuwa cigaba da damunta da kira suka yi wannan dalilin yasa momy tursasa mata ɗaga wayan
Don haka a handsfree tasa wayar gamida ajiyesa akan bed

“Hello ”
“How are you Kausar?” jin Muryar ogan aikinta ya sata ƙasa da kai kaɗan.

“I'm fine good morning sir”

“Ehmmm...ahhhh...wato dama akan wannan work ɗin ne da kika turo assistant ɗinki dashi jiya,gaskiya ya fita yanda akeso saidai muna buƙatar ƙarin haske,babu ke babu assistant ɗinki duk baku zo ba kuma baku sanar ba”

Sosai abun yayi shocking dinta wato el’ameen maisheta bahuwa yayi ko yaya? Ta yaya zatakai dare tana sabunta aikin da an rigada an submitting ɗinsa?

“Miss Kausar are u on?”

“Yes sir,sorry sir gani nan zuwa”

“Ok take care” Kashe wayar tayi ta miƙe jiki a sanyaye “Momy bari inje suna nema na”

“Better” ta bata amsa gamida miƙewa ,har ta kai ƙofa ta dakata “Kafin ki fita Kisha paracetamol naga kamar kina tare da headache”

“To momy” ta amsa cikin jin daɗin kular da yau ta ɗan samu,dukda binne ƙasar zuciyarta zullumine fal, duba da tunanin in momy ta Kira Anty hafsat tace Bata zo ba mai zai faru? Tambayar da za'a soma mata ina ta kwana? Ita kuwa wani amsa zata bada don ta wanke kanta?

***
Tana shiga ɗakin meeting ɗin da sauri ,duk kowa ya haɗu ita ake jira,don haka saida ta bada haƙuri sannan ta samu permanent seat dinta da ta saba zama duk in za ayi irin wannan congregation din ta zauna . Kallonta A.D yayi zai magana sai ga El’ameen ya turo ƙofa ya shigo

“Mr El’ameen why are you and your boss late today?”

Dam gabanta ya fadi ,ina ƙasa yau ya buɗe ta shige? Kausar ta kasa ɗagowa ta haɗa ido dashi

Bending yayi kamar zai ruku’un sallah “I apologize sir”

“Get seated ,kamar yanda kuka gani the meeting was already on progress...My kausar ko zaki ɗan kara mana haske akan graph ɗin da kikayi plotting harma da su pie chart din da kika fitar a discussion of finding ɗinki?”

Natsuwa Kausar tayi sosai cikin zurfafa tunani ,itadai tasan batayi wani abu da yayi shige da maths/Statistics ba a cikin aikinta saidai in ɗan na iyan ne (Tana nufin El’ameen)

Gyaran murya tayi saboda yanda kunya ya haifar mata da shaƙewar sa “Referred to my assistant i knw he can handle them...Yasan komai na aikin”

“Oh really? Mr El’ameen elaborate plz. Zoka ƙara buɗaɗa mana lissafin”

El’ameen wanda tunda ya ga Kausar cikin ƙoshin lafiya wani daɗi ya kashesa a wajen saida yaji an kira sunansa sannan yayi gigif ya tafi gaban white board ya ɗauki maker ya buɗe soft copy ɗin aiki akai highlighting ɗin sa kowa yina gani sannan ya fara masu bayani ta hanyar fidda wasu misalan a jikin allo ,tamkar dai malami na koyar da ɗalibansa

“Yanzu kunga misali a demography dinmu da muka fitar idan misali muna bukatar ribar miliyon saba’in ne a duk kilo meter 400 na titinmu ,zamu yanke faɗin titin da ɗigo 0.5 👌 0.5 kadai fa mind you,so a kaidan lissafi munsan duk abunda baikai daya ba sufuri ne ,don haka ɗan abunda kuka cire bazai ɓata aikin ba ,so idan muka lissafa ɗigo 0.5 × 400 abinda ya bamu sai muyi converting ɗinsa to kilometers duk amsar da ya bada ,sai mu lissafa kudin wannan distance ɗin shine silent ribarku Wanda baya cikin lissafi....To yanzu lissafin da nayi idan har an bisa a haka za kuyi generating riba five hundred million Naira”

Tsit ɗakin tattaunawan yayi saboda dai tun a lissafin ya kwance ma wasunsu hadda sai tsiraru irinsu Kausar da Sir A.D ke biye dashi har ya ƙare bayaninsa.

Jinjina kai sir A.D yayi cike da gamsuwa “Hmmmm.... Brilliant” ya yi magana yana ƙwarara masa gwuiwa gamida yabonsa

Ɗan murmusawa El'ameen yayi “Nagode sir”

Waigawa A.D yayi gamida kallon Kausar “Yaya zamu iya samun ƙarin wani abu a wajenku gobe da zai ƙara ma wannan aikin armashi?” lumshe ido Kausar tayi “InshaAllah sir”

Clapping Hannunsa yayi👏 cikin murna “Ynzu mun kawo ƙarshen meeting din nan kowa ya koma bakin aikinsa”

Hargitsewa wajen yayi da ƙaran motsa kujeru kowa ya mike tsaye har saida A.D ya fice duk ba wanda ya motsa,sannan itama kausar ta mike

Gabaɗaya sauran ma'aikatan kallonsu sukayi “Gaskiya aikinku yayi kyau sosai” El’ameen arhan dariya murmushi yayi masu “Mun gode”

Jan ƙafa Kausar tayi zata dawo gaban allon don haka El’ameen da sauri ya kautar mata da takardun gabanta ,caɓe baki tayi cikin gatsali tace “That was a good presentation”

Washe baki yayi kamar bai fahimci da gatsali ta masa magana ba “Thank You boss”

Ko kallonsa bata kuma yi ba,taje gaban allon ta tsaya “Hey guys kunji dai abunda ogana ya bukata a wajena mu kawo wani abu da zai ƙara ma aikin mu armashi...don haka za muyi sharing idea ,wake da ta cewa?”

July ta fara ɗaga hannu“me zai hana a saka fitulun tsakiyar hanya ?” caɓe baki Kausar tayi

“Noooo”

Balƙis uwar kararrafi “Ok a zuba flower side by side da tsakiyar titin ”

“Thank You amma bamunzo decorating gida bane...any?....any?”

Shiru kowa yayi kowa na tsoron magana a gwasalesa

“Come on guys kuyi magana mana kuna kawo sillies”

Gyaran murya El’ameen yayi “A fitar da flyover a duk wani titi da Yike da mahaɗa da zai kai titin wani gari zuwa wani...”

Ƙyam Kausar ta dakata da motsi ta ɗan taune ƙasar biro ɗin ta tana ɗan juya ƙwarar idonta cikin tunani

“Its good but it sound barbaric😏...akwai wanda zai taimaka masa da gyara?”

Sake ɗaga hannu El’ameen ɗin yayi “Tom a yalwata duk wani City da flyover atleast 6 da manyan round about”

Gabaɗaya ɗakin taron hargowa suka farayi na tabbatar da abinda ya fadan yayi daidai kuma zai burge

Kallon bilƙis tayi “Me kika ce?”

“Nace ne hakan da ya fadi yayi tsari mai kyau kuma zai bada shaawa”

“Eh ya fadi daidai amma har yanzu akwai ɗan gyara nace ,inaso kowa ya ringa amfani da kansa wajen yin tunani wisely ba kwaikwayon ra'ayin wani ba,don haka na bar maku wannan a matsayin assignment,kowa yayi tunani zan dawo nan da minti talatin” tana Gama magana ta bubbuge folders dinta ta hadasu waje ɗaya tazo ta raɓe ta wuce ta barsu suna dambe da ƙwaƙwalwa su ' wajen tunanin yanda zasu fitar da titi mai kyau da nagarta.
[3/10, 3:07 PM] Chu_chu👻💩: Paid Page B
My house boy
Kausar kam tana komawa office ɗinta damuwa ya dawo mata sabuwa fill all those traumas Suka sake dawowa kwanyarta

“Shikenan yaron nan ya rainani ,ya ganni ina timɓelen maye ,ƙila ma nayi masa kiss,Ga fitsarin kwance da nayi masa,a ɗaki ba dole ya raina Ni ba,na koresa a aiki ya dawo ,yana mun shiga hanci da ƙudundune duk saboda yina taƙama yaga gadon barci na????”

Wasu lafiyayyun hawaye suka fara mata sintiri a kunci “Duk ke kika jamun Raudha wlh duk kece”

El’ameen yina cikin ɗakin taron kawai wata zuciya ta bashi Kausar !!
Zumbur ta miƙe ya nufi office dinta ,tana cikin rizgar kuka sai jin shigowarsa tayi ,aikuwa zabura tayi a falon office din nata zata shige na can ciki shima da sauri yabi bayanta ,buɗe ƙofar tayi ta fada office din kafin ta maida kofar tasa makulli ya turo ya shigo gabaɗaya.

Wani tsawa ta doka masa “Wai meye?”

Cikin zafin murya yace “Kinsan kuwa so nawa na kiraki a waya? Kausar kinƙi ki daga wayata ,na damu dake Kausar” ya mika hannu ya kamo hannunta ,wani warce hannun tayi da karfi gamida daka masa tsawa “Stop it!!! Me kake so a wajena kuma?”

Cikin dakakkiyar murya irin na namijin duniya ba tsoro ba shayi ba fara'a ,ya soma mata magana ido cikin ido “Inaso da fari ki daina mun kallo irin na baƙon halitta a rayuwarki...Inaso ki tsaya muyi magana akan laluranki”

“Bana so ka rabu dani and work out from my office” taui masa cikin fushi da kwarmato.

“No Kausar You need a shoulder”

“Alameen bana buƙatar kafaɗun yada zango , indai kafadun da zai zama na tausayawa ne a gareni”

“Ƙarya kike yi,ba wani dan adam da baya bukatar abokin shawara ,ƙaryane” yanda yake mata magana cikin hargagi shi ya bata mamaki har ta farajin ɗan tsoronsa ashe ya iya masifa haka yake kwantar mata dakai kamar na gari?

“Alamin yayi maka kyau,wato saboda daren jiya ka kwanta dani ka lallatseni shiyasa ka rainani...”

Dafe kansa yayi ya yarfe hannuwarsa a iska “haba Kausar ki fahimceni mana Ni ba magana nike akan Sex ba,and beside ban maki komai ba.....I love You....I really do like you.... Ina matuƙar ƙaunarki kausar.....Ki dubeki kina da ƙwazo , kin iya ado gaki da kwarjini kina da zarrah above all gaki da Izzah mai firgita zukatan maza su susuce su kasa yi maki musu kinsan duk kina da wainnan nagartan?” ya tambayeta yina daɗa matsowa har gabanta yakai hannu ya dafa kafaɗarta ,jikinta yayi sanyi laƙwas ta kasa motsa ko ɗan yatsanta

Ɗan sunkuyawa yayi da fuskarsa a daidai nata har sunajin sautin hawa da ɗaukan numfashinsu

“You too dame gorgeous ...Kausar plzzzzz ki daina koro na a inda kike ki bari muyi maganar damuwar nan a tare ”

Ya ƙare magana yina kai hannunsa gadon bayanta a hankali a hankali har ya haɗe hannayensa ya ƙanƙamesu ,cikin wani irin slow motion jikinsu ya ringa matsowa wa junansu kamar ansa masu mayen ƙarfe har ta kwanta a faffaɗan ƙirjinsa ta haɗe hannuwanta ta baya sukayi ma juna wani kyakyawar runguma .

shikuma ya ɗaura gemunsa a kan Kausar ɗin yina shararar da wani irin hawaye da baisan na ko menene ba.

Cikin murya mai rawa tace “Wannan shine dalilin da yasa bana soyayya ,Alamin I hate dating”

***
Knocking din da sukaji anayi daga ƙofane yasa El'ameen janyeta a hankali daga jikinsa yana jan hanci yina ƙoƙarin share hawayen fuskarsa saidai tuni jan idanuwarsa ya tona masa asiri.

Kausar haɗe hannayensu waje guda tayi tana kallonsa shima ɗin ita yake kallo

Girgiza masa kai ta shigayi alamar ya bar kuka

“Me yasakika tsani soyayya wannan mummunar shawara ne zuciyarki ta baki”
Chapter 1 · 0% Book details