← Book details Yar Aiki Return Part 1 Complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Yar Aiki Return Part 1 Complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........karasawa sukayi inda yike suna fuskantar juna amma sun kwau da kawunansu"Assalamu Alaiqum?
"wa'alaikumu salam.wata zazzakar muryar daya doki kunnesune yasasu dago kaii.caraff suka hada ido da nazeem!!!,gaban feenart ne yayi mumunar faduwa wanda seda ta girgiza.ganin nazeem dake mugun kama da jalil,danba hasken da hacin da jalil yafishi ba muryarsu daya amma jalil yafisa sanyi murya da seta rantse jalil ne ke tsaye agabanta.allah me iko.haka yakasance abarayin juwairiyya mamakin kamannisa da jalil ne yacikata,kodayake ba'a ja da ikon Allah,Allah me ikoo!.
Ganin mamaki kwance a fuskarsune yasa nazeem gyaran murya sanan yace"nasan kuna mamakin ganina ko?
Basu ce masa komai ba se na mujiya dasuka zuba masa.cigaba yayi da magana"sunana Nazeem,sunan mahaifina Alkasim mahaifina shine managing director na NNPC dake nan garin,Wanda nasan ko bakusanshi a idoba kunajinsa a gidan t.v radio ko jaridu.ni kadai Allah yabawa iyayena,bayan ni basu kara haihuwa har yanzuh.nayi karatuna a Oxford university inda nakaranci law.yanzuh haka nazama babban lawyer.sorry fah ina ta cikaki dasuru ban fadamiki ya'akayi nasanki ba kuma har nakawo kaina gidanku.
Murmushin karfin hali feenart tayi amma batace komai baa.juwairiyya dake tsaye tawuce gurin da'aka ijiye rubber chair dake dan nesa dasu tazauna jiran feenart.
Cigaba yayi da fadin"Ranar dana fara ganin wata kyakyawar halitta wace nike fatan tazama matata kuma uwar yayana shine inadawo daga gurin aiki motata tadan samu matsala adede university din dakuke zuwa nafito dan duba menene yafaru tayatace ta yi faci bansan yaxanyi ba hakan yasa nafara kiran abokina bayan mungama wayane,naganki kun fito da sis ki fuskarki kawai nasamu damar gani nan take naji sonki da kaunarki sun kamani lokaci guda,babu abinda nike inbanda kallonki,inan a tsaye har kuka wuce da motarku,bandena kallon motarku ba har seda ta bacemun.tun lokacin nike fah mah da dakon sonki har illa yau,every second every minute se kin fadomin a rai,da wanan kyakyawan fuskan naki nike kwana nike tashi,ina fatan allah ya kara hadamu,segashi dazu kun futa shine nabiyoku abaya.dafatan zaki amince dani danallah.yakarasa maganarsa murya araunane!!
[12/7, 8:11 PM] Real Farhana: Cikin zazzakar muryarta me seta zuciyan masoya tace"toh nazeem nagode dawanan matsayin da kabani.
Hanunsa yadaura akan lips dinsa have"shhh,don't repeat it again.amma kin amince dani kuwa?.pls karkice A'ah,dan wallahi zan iya mutuwa,kitemaka mun.
Shuru tayi kafin tace"shikenan I will think about it insha Allah.
"Owk sleep with it in your mind,it will come to u directly.
"Owkk.batakuma cewa komai ba.
Shiko shuru yayi yina kallonta.hakan yasata durkusar da kanta.can kuma setace"zan shiga ciki inadan wani aiki nee.
[12/7, 8:43 PM] Real Farhana: "Wanan wani aiki ne ze katse hirar masoya?
Tama rasa mexatace sekuma tace"Assignment nike ne.
"Eeyya,toh amma baki fadamin komai akanki ba.
"Toh mekake so nafada maka.
"Just tell me more about yourself.ko sunanki mah fah bansanibaa?
"Owk sunana Nafeesat Umar,I lost my parent seens I was a child.mahaifan juwairiyya ne ke rike dani wanda suka maidani tamkar yar dasuka Haifa a cikinsu.yanxuh ina 100level ne ina karantan business. Dana daya Hashim amma muna kiransa farhan.I mean ni bazawarace.
Kallonta yayi yakuma kallo yace"k
Allah sarki allah yaji kansu,kayyyy bazan taba yarda kin taba aure ba koda kuwa duk jikina kunne ne.
"Hmm,Aameen.ban taba aure ba,amma kuma ni bazawarace!!
"Baki taba aure ba kuma ke bazawarace?
"Ehh.
"Pls abar chapter nan.ynxuh zakije kiyi assignment dinne?
"Ehh,se anjima koh.
"Ehh yafada yina kara jingina da motarsa haryanzuh hanunsa na rungume akan kirjinsa.
Juwairiyya tayiwa allama da tazo,tasowa tayi takaroso.
Nazeem ya ciro wata katuwar bakar ledda a cikin motarsa yamika mata,Kai ta girgixa alamun a'ah.
"Shedan ne kawai ke maida hanun kyauta baya.pls ki amsa.
Amsa tayi hade da cewa"nagode.
Sallama sukayi da juwairiyya itama feenart hakan.harsun fara tafiya yace"heartbeat.
Cakk ta tsaya,bece komai ba.jin yayi shurune yasata jiyo wa ahankali.
"Ki cigaba da irrin tafiyar dakike tana seta zuciya.yafada yina nuna zuciyarsa da dan yatsa.
Murmushi kawai tayi hade da juyawa tayi tafiyarta.
Sedaya ga bacewarsu sanan yashiga motarsa yafice daga gidan.
[12/7, 9:15 PM] Real Farhana: A falo suka tarar da mum itakadai da alama farhan barci yayi juwairiyya ce ta gudu ta fada jikin mom tana murmushi tace"mom wlhyy Bestie tasamu miji kinganshine haddade ga ilmi,kyakyawa gashi lawyer.
Murmushi mom tayi irrin nasu na manya.sanan tace"danallah,ke zo kiban labari tafada tana nunamata kusa da ita.
Cikin jin kunya ta zauna gefen mom.
"Toh inaji me yace miki?
Cikin jin kunya feenart ta labartawa mom komai.cikin farin ciki mom tace nasan mahaifinsa ay abokin dad ne,wlhyy yinada mutumci kuma ba karamin me kudi bane.kinsan me nikeso dake karki Kara masa maganan ke bazawarace ni dakaina Zan masa magana amma fah ba yanzuh ba sekin gama yabawa da halinsa.
"Toh mom yarda kikace haka za'ayi.amma matsalar shine,suna mugun kama da jalil amma a iya sanina jalil beda wani kani shima naxeem yace shi kadaine a gurin iyayensa.
"Ehh kinsan ikon allah.sekiga ba ku hadda komai da mutumba se kiga kuna fuzgar kamanni.
"Ehh mom.zancenki dalma.fdin juwairiyya.tana kokarin bude bakar ledan dasuka shigo dashii.
Gabadaya hankalinsune ya karkata izuwa ledar.wani Dan madedecin box tafito dashi,budewa tafarayi.envelope ne aciki.dawani karamun kite.envelope din ta bude abinda ke cikine taciro,kudine yan dari Dari bandir daya irgawa tayi 5k ne.kallon juna sukayi sanan ta fara karanta wasika nafarko a bayane kamar haka: _HEARTBEAT U ARE MY LUV MY HAPPINESS,PLS DON'T IGNORE ME,I CAN LIVE WITHOUT U_
Sako nabiyu kuwa abinda aka rubuta shine: _INDE HAR KIN AMINCE DANI INASON KISA ABINDA KE CIKIN KITE DINAN GOBE SHINE ZE NUNAMIN KIN AMINCE DANI,PLS DON'T REFUSE TO PUT IT_
"Kashhhh wanan ya iya love,juwairiyya tafada tana murmushii.
"Mom ce tace sosai mah.ay ni inawa feenart sha'awar gidanan saboda mutuncinsuu.
"Nima haka wlhy,baride inbude kite dinan muga.bude kite din dazatayii,zobene me shegen kyau da tsada aciki se wani daukar ido yike.
Fitowa dashi juwairiyya tayi tace"wowww,mom danallah kalli.kamarma goald ne.
Amsa mummy tayi"tabass wanan goald ne.gashi me tsadanee.amma hidimar nan batayi yawa ba zuwana farko.
"Aah mom bawani yawa gyara wasanshi yike,wanan yina nuna mana ne ze iya kulla da ita koda tashiga gidanshii.
"Ehh kuma da gaskiyarkii.feenart amshi zobenan kisa...........
~*pls kuyi hakuri da wanan wlhy lamarin maranta se asilo*~
_By_
*REAL FARHANA*
[12/10, 2:37 PM] Real Farhana:
*'YAR AIKI*

~*love and romantic story*~

*STORY AND WRITTEN BY*
*FATEEMARH XAHRA EEDREES(REAL FARHANA)*
```Fellow me on whattpad@Eedreesfateemarh```
*FARINJINI WRITERS ASSO.........
~masu comment ina godiya,but pls adunka dagewa anayii~
*53-54*
.............kallon mom tayi tace "mom kinagani babu matsala?
"babu wani mtsl saboda nasan iyayen yaron masu haline zema iyamiki abunda yafi hakan kinga shima yinada aiki.
Amsan zoben tayi tasa a yatsarta bakaramun kyau yayi mata ba.
**************
Cikin farin ciki ya isa gida zuciyarshi fess,dan yason feenart ta amince masa,daga ganin yarinyar bata da matsala,Allah sarki marainiyar Allah,amma metake nufi da ita bazawarace kuma harda da daya,sanan tace bata taba aure ba,zancen yafarasa sa tunani tunani hakan yasa yakwara dazance,killan kora da hali take son yimasa.kodaya isa gida afalo ya tayar da Abba da aunty suna hira shiga yayi da sallama abakinsa,fuska asake suka amsa masa,gaishesu yayi duk suka amsa,dad ne yace"Aaah son zauna anan.zama yayi kusa da Abban nashi."daga ina hakan?
Aunty ce tayi caraff tace"ay daga gidan surukanmu yike.
Murmushi dad yayi"ahhh Alhamdulillah,yasunan surikar tamu?
Dan Sosa kai nazeem yayi kafin yace"Nafeesat!
"Allah sarki suna me dadi.
Aunty ce tace"toh yaushe za'a kawo mana ita mugaisa.
"Kwanan insha allah.
Haka sukaita fira Wanda duk Rabin firan na feenart ne.
**************
Kwance yake akan gado kanshi na kallon siln,yarasa me ke masa dadi duniyar gabadaya juyamai take,Ashe haka duniya take inkana cikin jin dadi Seka dauka kafi kowa jindadinta,inko tajuya maka baya sekaga kamar tafiii tsanarkaa.
Tunanin baya yikeyi yarda yike cikin jindadi ga sahibarsa akusa dashi,amma yanxuh tayi masa nisa,abayane yace"Ya Allah kahadani da burin zuciyata muradina,ko da so dayane nagyara kuskurena na baya.nasan na cuceta na zalumceta wanda ina mutu da wanan kaya me nauyi,inada yakinin ko kamshin aljana bazanji ba......,kukane yaci karfinsa yakasa karasawa.
Hajiya data dade da shigowa ta girgiza kai hade da goge kwallar data zubo mata.duk ita tajawa danta wanan abin Allah yayafe mata.cikin tausayin dan nata dake ratsata ta ko ina,ta janyosa jikinta tana lallashinsa hade da bubuga masa baya tana fada masa kalamai masu sanyaya zuciya.......
*BAYAN WATA HUDU*
Ayanxuh soyayya me karfice tsakanin feenart da nazeem,basu 30minutes basuji muryan juna ba,inko suna waya sesuyi 1hr basusan sunyiba,kullin se nazeem yaje gidansu tadi.hatta dad yasan da nazeem saboda Abba yaje ya tambaya masa izini,feenart sunje sun gaisar da aunty duk kallon sani sukewa junna amma sun mance inda suka San juna hakan yasasu share maganar.
Mom tafadawa nazeem raping din feenart da'akayi allah sarki tausayin feenart yamugun kamashi kuma nan take yaji wani zazzafar sonta da kaunarsa ya shigesa.shima yasanar da iyayensa sukace ai babu mtsl inde yinason abarsa ahakan angama,duk weekend se nazeem yafita da Farhan bakaramun siyayya yikewa Farhan ba hakan yakara farantawa feenart rai da dankwam kaunarsa a ranta.
Nazeem ne kwance akan kujera yina waya da jalil nan jalil ke sanar dashi zuwansa ranar friday murna yashiga yi.bayan sun kammala wayanne yasanar da aunty dadi aunty tafaraji jin zataga danta.
*Ranar Friday*
Nazeem ne yaje taro jalil a airport,yafi 5mnt awajan.can yahango jalil nasakowa...
Sanye yake cikin polo shirt,white in colour,se trouser black in colour,Rolex watch ne daure a tsintsiyar hanunsa kyawawan idonsa ya rufesu da bakin glass.tafiya yike cikin takunsa ne cike da yanga da kasaita wanda ya jawo hankaluwan matan dake wanjan.hango nazeem yayi yina masa weaving gurinsa ya nufa....
Rungume juna sukayi"You are welcome bro.
"Tnz.
"How was the trip?
"Alhmdllh..
Mota suka shiga,wanda tuni driver yasamasa kaynsa a boot,hiran yaushe gamo kawai sukeyi.nan nazeem yashiga basa labarin feenart dinsa,amma besanar da shi fyadan da'aka mata dan yadauki wanan a matsayin tonan asiri.
"Wai danallah bakabari naje gida nahuta ba kawai ka isheni dawata sahibarka.ni ko sunanta ma bansaniba???
_By_
*REAL FARHANA*
[12/12, 10:17 PM] Real Farhana:
*'YAR AIKI*
Chapter 14 · 0% Book details