← Book details Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karo aka ci tsakanin Khalid da Hanan wanda bata Kula shiba Inna tabi Hanan da kallo haka suka É—unguma zuwa É—akin Anwar wanda Jin alamun shigowar su yayi saurin share hawayen shi.

"Oh Ni Æ´asu bawa dai ba abakin Komai yake ba Ni Baraka Jibi yadda Muhammadu ya koma Lokaci É—aya sannu kaji Muhammad Anwar"

Inna ta faÉ—a tana zama a kusa da shi kansa ya É—auka ya É—ora a saman kafaÉ—un Innah a jikinta ne yake Jin ÆŠumi na uwa.

"Khalid bai gaya maka dalilin ciwon nashi ba ko?" cewar Inna Khalid daya ke ɓallo magani tare da ɗaukar Gorar ruwa ya nufo wajan su yace wa Inna "Wallahi innah ban sani ba Allah dai ya bashi lafiya kawai" daga haka ya ɗago kan Anwar ya damƙa masa maganin a tafin hannun shi.

Anwar ya ɓata Fuska kamar wani ƙaramin yaro sabida a rayuwa baya ƙaunar magani tun yana yaro haka yake kuma gashi har an girma bai daina ƙin maganin ba.

"Ka daure ka sha ana shan magani ne ba don daÉ—i ba se don A warke daga ciwo" cewar inna.

A wajanta yake samun irin wannan kula da tarairaya kwanciyar shi ya gyara a saman kafaɗunta seda Innah tai da gaske sannan yasha maganin yana ta ɓata Fuska yana yatsina baki kamar zai dawo da maganin.

A hankali Muryar shi a dashe kamar mai cutar Mura yace wa Innah.

"Ni dai zan bar kamfanin Abba Innah dama kece kike bani haƙuri a kullum idan nazo miki da ƙorafin barin kamfanin shi"

Innah da Khalid suka kalli Juna dama Khalid ya raya hakan aranshi yasan musabbabin ciwon Anwar baze rasa nasaba da Ɓacin ran daya ke fuskanta daga wajan Abban shi ba.

"A kuya ce a daji Ta haifi ƴaƴa goma se Kuraye da zakuna suka zagaye wannan akuyar suna farautar ta, to akuyar ta rasa yadda za tai sabida tana son ko wanne acikin ƴaƴanta Kuma tana son rayuwarta Kuma idan ta gudu tabar ƴaƴanta cinye su waɗannan kurayen da zaku nan zasuyi sannan In ta zauna Tace ƴaƴanta su tafi waɗannan Kurayen da zakunan ba zasu barta ba Kenan Ko wanne acikin akuya da ƴaƴanta suna da Buƙatar Junan su sabida haka kawai sai akuya ta Fara kokawa da waɗannan namun dajin Tana gazawa se ƴaƴanta suka soma taya ta har suka cimma nasarar Kuɓuta amman fa seda suka ci wahala"

Cewar inna tana Kallon cikin ƙwayar idanun Anwar wanda bai fahimci mai take Nufi da wannan maganganu nata ba Katse shirun nasu ta kuma yi tare da cewa "To ina nufin barin ka kamfanin Alhaji kamar ka bawa mugaye da azzalumai damar handama da babakere ne acikin Dukiyar mahaifin ka dama abin da suke so kenan shiyasa suka shirya maka wannan Tuggun"

Anwar ya É—age kafaÉ—a tare da cewa.

"Innah su kwashe mana kowa da arziƙin sa yazo Nifa inna bada ban abba yana dakatar dani ba ga Khalid nan da tuni na jima da barin ƙasar nan nayi tafiya ta Duniya na jingine kaina tunda bani da kowa"

Inna taÉ—an harare shi.

"Kada ka kuma faɗin haka, kana da Allah da Manzon shi, Sannan kana da mahaifin ka wanda yake matiƙar Buƙatar ka a kusa dashi Anwar kana da Basira wadda take taimakon Dukiyar mahaifin ka, Ba komai bane yasa ake Shirya maka wannan gadar zaren face ganin kana da ƙwaƙwalwar gano dukkan macutan cikin kamfanin ku, Ka saka a ranka wannan Dukiya bata kowa bace se taka sabida Alhaji Kai kaɗai ya mallaka ɗa namiji a duniya don haka ka jajurce wajan Haɓɓaka dukiyar mahaifin ka Don Kaine nan gaba zaka moreta"

Anwar cikin rashin damuwa yace.
"Nifa innah Dukiyar Abbah bata gabana shiyasa da Iya selary ɗina nake rayuwata wallahi Inna ficikar Abba ban taɓa fitar wa ba ga Khalid nan Duk abin da nake da Kuɗina nake yadda kowane ma'aikaci yake masa Hidima ya biyashi nima haka ne amman by mistake aka samu matsala Abba yana rufe idanun shi ya nuna kamar bashi ya haife ni ba da bani da matsala dashi amman tunda ya ɗorani a kan dukiyar shi nake samun matsaloli da Abba yanzu har takai A gaban kowa ma faɗa yake mini Ni kuma bana son zargi a rayuwata"

Anwar ya faɗa cikin ɓacin rai.

"Ba'a fushi da mahaifi Anwar ka bishi dukkan abin da yace Ka yarda koda kai É—inne zaka cutu gaba zaka ga amfanin hakan"

Cewar Innah.

"A zahiri yake Nuna yafi yarda dasu Alhaji Jamilu fiye dani Inna mai zanyi da Kuɗin shi ban da Albashina Ina Parsonal Business ɗina wanda yake kawo Mini Kuɗi ga Khalid nan Ban damu da arziƙin da mahaifina keda shiba nawa na kaina nake alfahari dashi wanda na nema da gumina haɗin gwiwa Muke nida wani Babban Mutum acikin kwari Muke kawo Duk wani samfur na lagos lace da Dogayen Riguna daga India muke rabawa Ƴan kasuwa akan sari Tun Muna haɗaka da Mutumin yanzu takai ta kawo Nike bashi ya raba Innah iya waɗannan kaɗai nasan na riƙe zan dogara da kaina bare ma ina da shagunan dogayen Riguna dana zuba yara suke siyar Min acikin kasuwa Nifa wannan Matsayin da Abba ya bani ba ƙaramin takurani yayi ba"

"Ka dai yi haƙuri Muhammadu Kabi mahaifin ka in sha Allah gaba kaine zaka ci riba"
Da ire iren waÉ—annan maganganu Inna ta samu har ya sauka daga fushin nashi Ta shi yayi ya shiga toilet sabida akwai salloli akan shi Innah ta kaÉ—e masa gadon ta fita don ta sama mai abin da zai ci dan tasan tunda dare yayi ba lallai bane yaci dambu sani baya son cin abu mai nauyi idan Dare yayi Khalid shikuma zama yayi a saman sopa yana charting da wayar shi.

Wanka Yayi kafin ya gama ya É—auro alwala ya fito Daga cikin Toilet ÆŠin.

*YANKAN ƘAUNA…I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*10*

Hannunshi riƙe da ɗan ƙaramin tawul yana goge ruwan dake ɗigo masa daga saman kanshi, Cikin nutsuwa kuma a hankali ya ƙarasa gaban dressing mirrow yaja stol ya zauna Body spray ya ɗauka yana fesawa ajikin shi bayan ya kammala ya ɗauki Cream yaɗan shafa sama sama saboda yanayin garin na sanyi dake Busawa Gaban Closet yaje ya ɗauki Ash Jallabiya mai yankakken hannu da sauran tarkace yaɗan kalli Khalid da hankalin shi gaba ɗaya yana kan waya se wani tsadaddan Murmushi yake wanda ze nuna zahirin Nishaɗin da yake samu acikin wayar shi, Anwar Yaja tsaki! mai sauti yana ganin Khalid bai da aikin yi shikam soyayya yana ɗaukar tane a rashin aikin yi Fita yayi Falon shi ya shirya Sannan ya ɗauki sallaya duk yana jin ba daɗi na Missing jam'i da yayi Shinfiɗa ta yayi yana Mai tayar da sallah.

Cikin Nutsuwa da nuna ƙasƙanta kai wajan Allah maɗaukakin sarki Anwar yake addu'a cikin Sujjadar shi Ya jima Yana addu'ar kafin ya ɗago ya yi sallama Bayan kammala dukkan sallolin daya tara sakamakon rashin lafiyar data ɗan kwantar dashi har ta hana shi yabi sallar a kan Lokacin ta Istigfari ya dinga yi kafin ya soma karanto azkar daka ya kammala ya tashi ya Naɗe abin sallar yana mai zama saman One seater yana serching Channel dan ya kamo Mayyar tashi wato tashar kallon ƙwallon Ƙafa Tsaki yaja ganin basu fara wasan ba Khalid ne ya fito daga Bedroom Ɗin Anwar har Lokacin wayar shi na hannun shi Kuma gaba ɗaya hankalin shi yana kan wayar.

"Allah ya baka lafiya amman ni dai ina baka shawara wannan duk ba daidai bane ka zauna kana ɓatawa ƴaƴan Mutane Lokaci Danna san ba Budurwa ɗaya kake kulawa ba, This is not right, stop it"

Anwar ya faÉ—a mashi hakan, Khalid yayi Murmushi tare da cewa Anwar.
No matter how much I tell you how love is, you will not understand it sabida kai har yanzu baka san rayuwa yadda take ba ai soyayya dar ce nake gaya ma in mace ta gaya maka wata maganar ji zakai kana yawo a cikin gajimare dama zaka samu kai wuf da Hanan yadda take mai tar son ka malam ai da ka huta"

Tsaki Anwar yaja yaɗan taɓe baki Kamar baze yi magana ba can Kuma sai ya ce.
"She is not at all the type of woman I love, Sabida bana son siririyar mace In ma zan yi auren kenan, zan auro mace mai Ƙiba yadda nake Bani da jiki ɗinnan ta dinga tare Mini faɗa"
Ya faÉ—a yana Murmushi.
Chapter 9 · 0% Book details