← Book details Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunshi da suka soma sauya launin kalar su sabida baccin daya fara kamasu ya buɗe ya jefasu Kan ƴar ƙaramar wayar dake Bedside drawer kafin ya miƙa hannunshi ya ɗauko wayar ya tsirawa Number Idanu UMMINA da babban baƙi aka rubuta wayar ta katse still Wani kiran ya shigo ya ɗaga kanshi yana kallon ɗan ƙaramin Agogon dake Jikin gadon shi ta hasken sleeping lamp ɗin daya bari Ba wani dare ne yayi ba amman da yake Lokacin Sanyi ne yasa garin yayi shuru sosai Musamman Cikin Gidan da ƙafafun Ma'aikatan dake Hidimar kaiwa da kawowa tai saurin ɗaukewa.

Ƙara wayar tayi  Massage ne ya shigo.
"Sa'adah ki É—auka mana zan baki labarin Baffa"
Abin da kawai aka rubuto Kenan Gaban shi ya faɗi ya tsirawa saƙon Idanu Yana maimaita Sunan acikin zuciyarshi wanda Girma da Ƙimar sunan baze faɗu a bakin shiba Sa'adah ya Kuma nanata wa acikin ranshi yaɗan cije laɓɓansa yana sakin Iska ta cikin su.
Kira ya kuma shigowa da sauri kamar wanda ake bawa Umarni ya ɗaga wayar ya kara a saman Kunnen shi da ɗan ƙarfi Muryar mace ke sauka cikin Dodon kunnen shi wadda bata tsaya taji maganar wanda take wayar dashi ba bare su gaisa kawai magana take sakaka babu stop.
"Sa'adah ina ta kewarki Hajiya taci abincin da kika bamu harda naman sai dai Baffa yayi Cin Mutunci sosai har yana cewa in Allah ya yarda sai Kin kwaso abin Kunya Yaya Kamalu ma yazo ya gama zage zagen sa harda cewa a nuna masa Wadda ta kawoki aikin sai rufe Ƙofa nai sabida yana ƙoƙarin dukana amman dai yau tashin hankalin sa yafi na Kullum Sa'adah ko zaki haƙura Ki dawo Gida don ita kanta Hajiya Tunda Muka Fito take hawaye har na koma Hawayen take sai da na rarrasheta gashi bata da bakin magana"
Sai da takai aya a maganar sannan tace.
"Wai ni kam kin zama kurma ne sa'adah ina ta magana kin mini banza?"
Da sauri Anwar ya kashe wayar gaba ɗaya ya juya ya kwanta sai dai baccin yaƙi zuwa idanunshi kamar farko dama shi matsalar shi kenan In yana bacci aka tashe shi to da wuya in zai koma ta sauƙi Dire ƙafafun shi yayi a ƙasa ya kunna hasken ɗakin ya janyo system ɗin shi ya ɗora saman Cinyar shi ya kunna ya shiga tura saƙonnin Office har wajan 11yana aiki da ita kafin ya kammala ya aje Fita yayi daga bedroom Ɗinshi zuwa Falo yana duba tea flask ko zai samu ruwan zafi aciki sai dai babu Kuma yadda yake Jin sanyin nan sosai in bai Using da ɗan ruwan Ɗumi acikin shiba tabbas akwai damuwa Zira slippers yayi ya fita zuwa cikin Gida a dining ya zauna yana dudduba Tea flask ko zai samu duk wanda ya duba wayam yaja tsaki kaɗan Hanan ce ta fito daga Bedroom Ɗinta sanye Cikin Riga da wando na Bacci Cotton sai ɗan ƙaramin Hijab data ɗoro akai yunwa take Ji kamar taci Babu tana Isa gaban  dining ta sauke ajiyar zuciya Ganin Ya Anwar zaune ya sunkuyar da kanshi kamar mai Tunanin wani abu ayyanawa tai dama ace sunyi aure suna zaune acikin Gidan sune.

"Yaya"
Ta faÉ—a.
Da sauri ya É—ago idanunshi da har Lokacin kalar su bata dawo daidai ba yaÉ—an HaÉ—e ranshi.
"Baki iya sallama ba?"
Taɗan tura baki kaɗan kamar wata Ƴar Baby.
"Kayi haƙuri bazan kuma ba"
Ƙoƙarin Tashi yake da sauri ta dafe hannunshi ta hanyar ɗora nata akai wani matsiyacin kallo daya watsa mata ne yasa tai saurin sauke nata hannun.
"Ammmm yaya dama dama" ta faɗa tana Ƙifta ido.
Ya saki Huci mai zafi kafin ya silale ya zauna a saman kujerar daining É—in.
"Please bring me a cup of tea now" a hankali.
Shi kanshi bai san maganar ta fito daga bakin shiba da sauri ta bar wajan tana shiga kitchen ta ɗauraye tukunya a cikin sink ta zuba ruwa cikin tukunyar tare da sugar wanda bata san adadin yawan shiba ta Kunna cookergas Minti Biyu ya tafaso ta Juyo masa a Cup ta Fito ko Tea spoon bata saka aciki ba gaba ɗaya jikinta ya ɗaukanta da ta burgeshi Yana turiri ya amsa yana Ƙoƙarin kaiwa cikin bakin shi sabida yafi son yaji shayi na Ƙona mai baki yana ratsa masa Jikinshi Kurɓa ɗaya ya furzar dashi yana kallonta ta kwa zuba masa ido kamar zata haɗiye Shi.
"Ke wace irin Sakarai ce kamar ki baki Iya dafa tea ba?" ya faɗa yana ɗan zaro mata idanunshi kaɗan Ƙwalƙwal Idanunta yayi gaba ɗaya Jikinta yayi sanyi Faɗa ya dinga yi mata hawaye yana bin Kuncinta dama shi abin faɗa baya yi masa wahala musamman gareta sabida tace tana son shi a yadda ta Lura kenan.

Adaidai nan Sa'adah ta fito daga Ɗakin Husna wadda ta gama wanke kayan da Bassam ya ɓata na kashi tana tafe tana yarfe hannunta gab da zatabar falon taji sautin maganganu kamar na namiji tana ɗaga kanta Kuwa idanunsu suka haɗu dana Juna ai tattare Skirt ɗinta tayi zata sa Gudu tana cewa Yana aikin nashi kenan masifa.
"Ke zonan Ke Kuma tashi kibar Min Gurinnan kafin nai Ball dake"
Da Gudu Hanan ta miƙe tana Kuka tana share hawaye sai dai haɗa idanun da sukai da Sa'adah ne yasa Hawayen nata ƙafewa tana Bin sa'adah da kallo wadda ganin Hanan yasa gabanta ya faɗi wannan Ta ɗazun ce wadda ta mareta har tai mata turanci Tsaki Hanan taja Cike da Kishin Sa'adah wadda tun kallonta da ita na farko taji tana Kishin ta sabida kyan ta yayi yawa.

Kafin ta hankaÉ—eta da sauri Sa'adah ta takure a bango tana raba idanunta Yi yayi kamar bai ga abin da Hanan É—in tayi ba.
"I told you to come here, ko zan cinye kine kin wani tsare ni da ido....." sai Kuma yayi shuru Lokacin Hanan takai ga Bedroom É—inta.
Iya ko zan cinyeki ne ta gane da kin tsare ni da ido amman sauran bata fahimta ba.
A hankali take jan ƙafafunta zuwa wajan shi ga falon babu kowa.

Tana zuwa gaban shi Kwarjinin shi ya cika mata Ido zubewa tai jagwab ta zauna agaban shi tana sauke Numfashi.

"Kin iya dafa shayi"
Bai jira mai zata ce masa ba.
"Ki dafa ki kawo Min wannan ɓangaren da kika shigo ɗazu"
Daga hakan yabar falon da sauri.
Sabida yana matiƙar Buƙatar shayin Kuma yasan yanzu Inna tayi bacci bare yace ta dafa masa shi kam bai iya komai ba bare ya dafa da kanshi shiyasa ya zaɓi sabuwar mai aikin da bai san wani aikin take taka maimai agidan ba data dafa masa ganin da yayi kamar zatai tsafta.

Sa'adah tai tagumi Cike da tsoro Hajiya tana gargaɗinsu Da kada su sake su Keɓanta da Namijin daba muharramin suba a duk inda suke su kare Mutuncin su.

Tun kafin Allah ya jarabci Hajiya da lalura take gaya Musu hakan Gaba ɗaya Gidan sunyi bacci kawai sai ta kama hanya tayi ɓangarensa dan bata da Ƙima.
To kuma in bata kai masa ba hakan zai zama laifi dan daga gani Yana da muhimmanci acikin Gidan.
Ajiyar zuciya ta saki domin ko hanyar Kitchen É—in ma bata sani ba.

Sai kawai ta tashi ta Nufi ɓangaren su alwala tayi tai kwanciyarta sai dai Ƙirjinta cike yake da tsoron abin da zaije ya dawo.
"Sa'adatu ki tashi kici abinci naga kin ɓata Lokaci wajan Hajiya Husna"
Da ƙaramin sauti tace.
"Baba na ƙoshi"
Tsaki taÉ—an ja wanda yasa Baba kande tace mata.
"Sai haƙuri Sa'adatu amman kika kwantar dakai zaki ci arziƙi"
Sai ta tashi zaune.
"Baba kande bama wannan ba, Wanine yace wai na dafa masa shayi nakai masa ɓangaren shi Ni bamma sanshi bafa Kuma dare yayi kina kallon ɓangaren babu kowa"
Baba kande tace.
"Waye kar dai Alhaji Ƙarami ne?"
Taɓe baki Sa'adah tayi.
"Wani dai mai faÉ—an tsiya mai ido kamar na Mayu"
Dariya Baba kande tayi.
"Ki rufawa kanki asiri Ki kai shayin nan Alhaji ƙarami ne lallai Yarinya kinzo Gidannan da ƙafar dama Tunda nake ko ruwa bai taɓa cewa na bashi ba Sabida haka maza tashi Muje na Rakaki Kitchen Ki dafa ki miƙa masa Ina wa Muhammad Anwar kyakykyawan zato ba zaki same shi daga cikin lalatattun maza ba In sha Allah yadda kika kai lafiya haka zaki dawo"
Badan taso ba sai dan bata son yiwa baba kande Musu ne.
Taja hijabi ta ɗora saman kayanta tana data sanin Gayawa baba kande maganar suka tafi zuwa babban Kitchen Ɗin Gidan wanda faɗin tsaruwar shima ɓata bakine Wasu Irin sinadaren haɗin shayine daga saudi ake kawosu baba kande ta nuna mata tana tsaye A kan sa'adah ta kammala haɗa shayin wanda dan tsananin Ƙamshi da kayan haɗi har kauri yake da mazarƙwaila aka dafa da zuma bada suga ba ta Juye a wani Dogon Kofi mai ƙananun Ƴaƴa ta ɗora a tray Baba kande ta Nuna mata Part Ɗin Anwar ta Nufi kai masa ciki sai dai Duk Notikan Jikinta sun saki sabida fargaba.........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
Chapter 14 · 0% Book details