← Book details Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalid ya bishi da kallo Anwar bai da magana amman idan ya yanko maka wata maganar se ka cika da mamakin shi.
"To Mijin Æ´ar lukuta Allah ya ba ka"
Ɗage gira yayi bai cewa Khalid komai ba yabar wajan Direct part Ɗinsu ya nufa Ya nemi Guri a saman dining ya zauna Yana ƙoƙarin haɗa Coffee Wayar shi ta hau Ringing Innah Ce sanar dashi tayi ta masa faten dankali Da sauri ya tashi yabar Coffee ɗin yana Ƙoƙarin Fita Mama ta fito daga Ɓangaren Bedroom ɗinta da alamun Part Ɗin Abba zata shiga sanin Ya dawo ɗazu da yamma kano.

"A,a Yaya ina zaka kuma baka shafa coffee ba naga kamar shi ka haɗa?" cewar mama, ba tare daya kalli direction na wajan da take ba yace "Ehh na haɗa kuma inna tamin tayin fate" daga haka ya Nufi fita daga part Ɗin ta bishi da wani Mugun kallo tama kasa magana tai ƙwafa! ta nufi Part Ɗin Abbah.

Zaune ta tarar da Abba yana kallon Sunna tv a hankali ta ƙarasa wajan shi ta zauna a kusa dashi.
"Barka da zuwa Ranka ya daÉ—e yaya hanya?" Abba ya kamo hannunta wanda ya sha jan lalle yana murzawa.
"Hajiya shafa'atu Mowar mata yaya hidima da yarana da fatan na same ku lafiya amman wannan Ƙunshi yayi wa Farar fatar ki kyau" Ya faɗa still yana matsa hannun ta wanda yake a cikin nasa.
"Dan kai nayi Alhaji Allah dai ya barmu tare" ta faɗa tana kwanciya a saman kafaɗun sa wanda in ka kalle su sai kace matasa ne ƴan shekaru ƙalilan Cikin kwanto da iya kirsa tace.

"Nayi maka maganar zuwan Husna har yanzu baka bani amsa ba Ya kamata kace wani abu mana sabida ta shiga watan haihuwa ko yanzu aka ce mana ta haihu ba zamu yi Musu ba ta yaya zata haihu a dawa babu kowa nata"
Mama ta faÉ—a cikin Nutsuwa.
"Shafa'atu ba komai yasa kika ji nayi shuru ba ya kamata abar wannan yarinyar ta haihu a ɗakin Mijinta duka duka yaushe akai mata auren ma amman Mijinta ya kawon ƙararta na ƙazanta yafi sau Goma sabida haka kawo ta gida ma wata sangartar ce gaskiya abarta a ɗakin ta kawai"

Mama ta ɓata fuska.
"A,a nida nasa aka gyara É—akin dake kusa da nawa hatta kayan baby na siyi komai Dan Allah Alhaji karka hana zuwan nan Please"
Ta wani haɗe hannu waje ɗaya tana roƙon shi.
Yayi murmushi"wato rigimarki tana da yawa Shafa tunda kina son hakan Allah ya kawo ta lafiya" Yana faÉ—ar haka kuma ya É—auki wayar shi.
"Kazo ina son ganin ka inda hali ma kazo mini da shaidar dawo mini da kuÉ—aÉ—e na daka Fitar"
Daga haka ya katse wayar.

Mama ta wani marairai ce tana kallon Abba "Haba Alhaji Abin da kake wa Anwar Baya dace wa kamar ba mahaifin shiba, Nifa karka jamini zargi ace nike shiga tsakanin ka da ɗanka dama naga take taken matar Gidan can dan ɗazu ma da bai da lafiya dana je wallahi Khalid hanani yayi na ganshi yanzu ma kamar abin arziƙi yazo nan zai ci abinci Baraka tai Kiran shi ya fasa ya tafi can" mama a siyasance ta kawowa Abba ƙarar su Innah Murmushi Abbah yayi.
"Rabu da Shi dasu Baraka Kinji Ya riga ya saba dasu ne Kinsan ita ta yaye shi"
Mama bata so Abba yace haka ba se tai dariyar yaƙe ta kuma lanƙwasa kanta.
"Ina nemar wa É—ana afuwar ka dan Allah karka tuhume shi akan wannan KuÉ—i'
Abba ya kalleta "Idan ban tuhumi Muhammad ba Jamilu zan tuhuma wanda shi nake tare da shi tun kafin Muhammad yayi ƙwari?"
Mama taÉ—an sosa kai.
"Ni ba nufi na haka ba sabida bawai Yaya Jamilu dan yaya na bane Nina san baze taɓa cin amanar kaba Allah ya huci zuciyarka ai yaranne se Addu'a damma shi Anwar Komai nasa yana Ɓoyewa wasu kuwa da zaka ga In suka ƙi yin auren suna aje matan banza a waje ai yawanci Kuɗin su a wajan mata yake tafiya" ta faɗa tana Murmushi wanda ta faɗi hakanne Don ta ƙara jefawa Abba zargin yaron nashi aran shi Amman ba zaka taɓa gane da wace siga ta faɗi maganar ba sabida tsantsar Kirsar ta.

Adaidai nan Kuma Anwar ya shigo falon sabida Lokacin Abinci ma zeci yaga wayar Abba ya rufe ya tawo.

Ko zama Anwar bai kai dayi ba yaji Muryar Abbah.

"Ka dawo Mini da kuɗina daga nan zuwa gobe, Sabida ni ban yarda dakai ba Ƙila ma matan banza Kake bi ace shekararka Kusan arba'in a duniya amman bakai aure ba Duk sanda nai maka maganar aure kamar na haɗaka da ajalinka To Ni kuɗina bada ga kwance na same suba seda na tashi nai gogayya da mutane kala kala na tara su ta hanyar halak wallahi seka dawo Mini dasu Mutumin banza daga kai har Khalid Ɗin kunƙi Aure saboda Kunsa shashanci acikin ranku"

Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un itace kalmar da Anwar yake ta nanatawa dan yaji sassauci a zuciyar shi na maganganun da Abban shi ya gaya masa a wannan Lokacin kafin a hankali ya.........*YANKAN ƘAUNA…i littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

​

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *11*

Ya Ɗago shanyayyun idanun shi waɗan da suka rine da zallar ɓacin rai ya dire su A saman fuskar Abbah wata irin damƙa yakai wa center carpet Hannunshi gaba ɗaya ya jiƙe da zufa Shi kan shi Abba yanayin ANWAR ya ɗan firgita shi sabida bai taɓa ganin Yaron nashi a haka ba.

Magana yake son yayi Amman ya kasa Muryar shi ta dashe.

Tashi yayi da sauri Kuma a gaggauce yabar falon.
"Alhaji karka fa.......
"Dakata shafa'atu wannan ba hurimin ki bane koma mai zai same shi ya same shi" da sauri Abbah ya faɗa kuma da sauri ya tashi yabar mata falon ya shige bedroom gaba ɗaya ya rufe kanshi yaƙi bawa Mama damar bin shi.

Da wani irin tsantsar farin ciki ta bar Falon Abbah direct Bedroom ɗinta ta isa tana zuwa ta kulle ƙofar tare da zira Key ajiki.

Ta ɗauki wayarta tana kiran Numbern Alhaji jamilu yayan tane uwa ɗaya uba ɗaya, Shi take bi kuma dukkan wani makirci tare suke ƙullawa don su gina kansu sabida yadda take da ƴaƴa mata gani take nan gaba Anwar ne zai gaje rabin Komai in batai da gaske ba.

"Yaya barka da dare" ta faÉ—a.
Daga nashi ɓarin yace mata.
"Lafiya lau shafa'atu yaya ake ciki ne?"
Ta gyara zama a gefen gado.
"Yaya da alamun fa wannan Lokacin Anwar zai bar mana kamfani, Saboda ban taɓa ganin Yadda ran Alhaji ya ɓaci irin na yau ba dan bana hango soyayyar nan a idanunshi ta Anwar sai tsantsar ƙiyayya da zargi kuma shima kasan Anwar da zuciya kamar Kuturu da wuya ya koma Office"

Alhaji Jamilu yayi wani basaraken Murmushi tare da cewa.
"Ta yaro kyau take bata ƙarko ai yadda nai masa babu yadda za'ai ya iya fita, sabida duk wata Ƙofar da zata nuna akwai saka hannun shi wajan fitar kuɗin ta nuna sabida haka nina san dole ya bar mana kamfanin mu cigaba da cin gashin kammu haka kawai yaro yazo ya zame mana jaraba komai mukai akan Idanunshi"

Dariya take sosai.
"Ai yaya kafin Alhaji ya rasu se na kwashe dukkan dukiyar shi dan Ni mai ƴaƴa mata nice a ƙasa sabida haka shiyasa tun yanzu nake cin kaso na"

Murmushin mugunta yayi.
"Haka ne shafa'atu sabida haka zamu dage damtse" tai Murmushin itama.
"Yaya zan turo account ka turo mini kasona dan kuÉ—in suna da yawa ka É—au kaso É—aya ka bani biyu" ya wani haÉ—e rai.
"Ki bari mana a gama bincike In komai ya daidaita saina baki naki haba kefa akan Kuɗi baki da sauƙi, Ni burina wannan shegen yaron yabar mana waje mu sarara na koma kan Kujerata ai tunda ya sake ya hau saman Kujerar da nake kai wallahi Koda asiri sena sabau tashi"

Dariya take har tana ƙwarewa.
"Yaya kenan kana ganin wannan dutsen zai biyu ta sauƙi? to ban hanaka ba amman zaka kashe kuɗi sosai ni ai tun akan auren Hanan na daina kashe Kuɗi ba inda ban jeba amman Ko gezau shiyasa na shiga tunanin anya ma kuwa shi kaɗai ne ko ga rashin auren sa ma ina ga ba lafiyayye bane  shiyasa yanzu ba boka ba malam kirsa ta kaɗai ta isheni se yadda nai da ubansa"
Chapter 10 · 0% Book details