← Book details Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ɗan ɓacin rai ta juyo gareshi zata yi masa magana, Yay saurin hanata furta maganar ta hanyar Rungumeta ta baya yana zuba mata dukkan Nauyin shi Kokawa suka shiga yi acikin Motar hankalin Saadatu yayi Mugun tashi.

Sai da tayi da gaske sannan ta iya Rabashi da Jikinta sai faman Nishin azaba take Ranta a tsananin ɓace ta kalle shi da Manyan idanunta waɗanda suka Sauya launin su zuwa jajir.
"Dama haka halin ka yake? mai yasa kayi min haka daman dan ka lalata min rayuwata ka rabo ni da Gidan dana ke sa ran samun halak É—ina?"
Sai hawaye! shaaa suka soma ambaliya a saman fuskarta.

Dafe kanshi yayi yana Ƙoƙarin saita Nutsuwar shi a hankali ya zira Hannu Cikin Aljihunshi ya ciro kuɗi masu yawa wanda bai ma san adadin suba ya kama hannunta ya damƙa mata gaba ɗaya ya kasa magana.
Watso mai da KuÉ—in tayi Jikinsa.
"Allah ya kiyaye na amshi KuÉ—in ka ko zan rasa komai bazan iya amsar KuÉ—in kaba Kuma sai Allah ya saka Min abin da kayi Mini"
Daga haka ta fita daga cikin Motar tana wani irin Kuka mai tsuma rai da zuciya.

A guje ta faÉ—a Gidan ko sallama bata iya yiba

Da kuka ta shiga É—akin su Ummi na sallah Ummi tana idar da sallar ko addu'a bata tsaya yiba ta Juyo tana tambayar sa'adatu.
"Lafiya kika shigo da kuka! menene mai ya faru?"
Ummi ta faɗi maganar a firgice ganin yadda saadatu take Gursheƙen Kuka!

Baffa yana bakin dakalin Ƙofar Gida yana kallon sanda motar ta sauke saadatu har zuwa sanda saadatu ta fito daga cikin Motar Murje idanunshi yayi yana kuma Buɗesu tabbas saadatu ce ta fito daga Motar Jikin Baffa har tsuma yake wajan takewa saadatu baya zuwa Cikin Gidan daga tsakar Gida ya soma ƙwala mata kira.

"Saadatu! saadatu!! fito nan Munafukar Allah, yau Allah ya tona miki asiri dama na jima ina zargin ki yau dai Abin Ɓoye ya fito Fili"

Saadatu daga cikin É—aki ta Matse Ummi jikinta sai rawa yake tana tsiyayar hawaye!
Ummi ta ɗago tana kallon Yadda saadatu take kuka! adaidai nan Baffa ya ƙaraso gaban Ƙofar ɗakin yana Bugawa da ƙarfi yana kuma nanata Kiran sunan saadatu.

"Idan baki Fito waje ba zan tona Miki asiri a cikin unguwa kowa yaji"
Da sauri Ummi ta kama hannun saadatu suka fito tsakar Gidan.

Suka zube a gaban Baffa.

"Dama ni na jima ina zarginku to yau na ga komai da idanuna saadatu ashe ba wanke wanke da shara kika jeba ashe yawon iskanci kika je uban waye ya sauke ki a mota?"
Ya faɗa cikin ƙaraji.

Wanda faÉ—in maganar tashi tayi daidai da sanda Abbati ya shigo gidan Umma dasu Jamila kuma suka fito daga cikin É—aki.

Yowa kanta baffa yayi kamar zai daketa yana kuma tambayarta.
Toshe bakinta tayi tana wani irin kuka!
"Ba magana nake Miki ba uban waye ya sauke ki a mota? wato mu zaku mai da marasa tunani Kin tafi wajan namiji ya kwana dake, Shine zaki fake da tafiya wajan aiki"
Kuka saadah take sosai a wannan karon.
"Wallahi Allah Baffa Babu wani Iskanci dana je É—an gidan ne yace na dawo Gida na cigaba da Kula da Hajiya wallahi Iya gaskiyata kenan Kuma shine ya kawo ni har nan"
Baffa yayi wata irin dariya.
"Bayan ya gama lalata dake Ko? babu wanda zaku rainawa hankali kawai kawaliya ce tai Miki Hanya kika je kikai kwana biyu kika dawo Gida To bari Kiji ba agidana wannan abun Kunyar ba wallahi bazan É—auka ba sabida haka tun wuri Ku haÉ—a ina ku ina ku Kubar Min gidana danni ba zakuja Min zagi a cikin Unguwa ba"

Da sauri saadatu ta kama ƙafafun Baffa tana wani irin kuka!
"Baffa iya gaskiyata kenan Wallahi bai min komai ba in ƙarya nake kazo Muje Gidan ka tambaye shi"
Wani irin naushi abbati yakai mata babu ji babu gani yahau dukanta Ummi ta rungume saadatu wanda ya haÉ—e su gaba É—aya yana duka har wata tsuma yake.

"Mu zaku wulaƙanta? dama ni Jikina ya bani ba alkairi ne ya fitar dake daga gidannan ba ashe yawon Iskancin ki kika tafi to yau saina Illataki na lalata duk wata Kafa da namiji zai gani ajikinki har yayi sha'awa" Cewar Abbati yana dukan su Umma dariya take Ɓoyewa tana furta.
"Abbati kai mata a hankali fa kar Cikin nata ya zube bafa a dukan mai Juna biyu"
Duk da saadatu tana cikin Jin raÉ—aÉ—in Dukan da yake mata sai da ta juyo ta dubi Umma saboda raÉ—aÉ—in Maganar Umma yafi Dukan yi mata zafi!

Babu irin Cin zarafin da Baffa bai Musu ba Kuma babu wanda ya ƙwace su daga dukan abbati har seda ya gaji dan kanshi sannan ya soma Kumfar baki yana balbalin bala'i Ummi ce ta janye sa'adatu suka shiga ɗaki Lokacin saadatu Ko hannunta bata iya ɗagawa Kuka kam tayi shi harta Godewa Allah taja wa Anwar Allah ya isa tafi Cikin Carbi ta la'ance shi har babu adadi don shine Silar Jefata Cikin wannan matsala a haka sum sum dashi kamar na Allah.

"Saadatu Meye dalilin ki na baro Gidan aikin sannan na kasa Gasgata gaskiyar maganganun Baffa shin waye ya kawo ki acikin Mota?"
Cewar Ummi.

"Kema zargina kike kema ba zaki Min Uzirin ba shikenan Ni kawai gwara na mutu na huta"
Sai ta soma yin wani Irin tari wanda ya ɗagawa Ummi hankali Duk taurin zuciyar Ummi kuka take na ganin Halin da ƴar uwarta ta shiga Hajiya dake kwance itama kukan take ganin Saadatu bata yin Motsi yasa Ummi fita don neman ɗaukin mutan gidan nasu amman Duk ihun da take babu wanda ya Kulata Ganin wankin Hula na neman kaita dare yasa ta fita Gidan Aunty Murja Wadda ta biyo Ummi zuwa gidan babu yadda Saadatu take Haka suka ɗagata Mijin Aunty murja ya ɗauko Motar shi suka sakata aciki wani Ƙaramin asibiti dake kan titin Rijiyar zaki suka kaita Nurses suka amshe ta da gaggawa Suka shigar da ita ɗakin duba marasa lafiya.

Jingine kanshi yayi a jikin Sitiyarin Motar yakai Minti Goma a wajan kafin ya tayar da Motar tashi yabar Layin Cikin kasala yake Driving zuwa Gida gaba ɗaya kanshi ya Kulle Har ya ƙarasa Gida ya Fita daga Mota Ya shiga part Ɗin shi bai gama dawowa daidai ba wani Irin Yanayi ke Fisgarshi bai ɗauka zai kamu da wuri haka ba.

Tun ranar daya soma ganinta a part Ɗinshi da yamma Da alamun ɓatan kai tayi ta shigo masa, Yaji gabanshi ya faɗi bai son soba sabida bai taɓa Yiba amman yana Jin lamarin ta mai girma acikin zuciyar shi bai damu da ƙasƙancin taba shi dai yafi damuwa da tarbiya.

Babu laifi taci jarrabawar shi, sabida yana Gudun sharrin mata tunda akwai tabo acikin zuciyar shi bai ɗauka zai kamu cikin sauƙi ba sai dai Tun ranar daya ganta ya kasa sukuni ya kasa Nutsuwa ita kaɗai yake kalla acikin Idanunshi.

Yayi saurin kauda ita ne daga Cikin Gidansu sabida kar ayi amfani da ƙarfin Ta azuciyar shi a cutar da Shi sabida Yana jin baze Taɓa Jure kawaici akanta ba, ita ce mace ta biyu data ji tausayin shi bayan innah ita ce mace ta biyu data kare Lafiyar shi sanda za'a cutar dashi Tabbas Lamarinta mai girma ne a gare shi.

Lumshe ido yayi yana Neman yafiyar Allah na rungumar da yayi mata wanda ba don komai yayi mata hakan ba sai don ya ƙara gwadata akan wankin ido ko itan ta kasance acikin jeri ƴammata masu wankakken idanu sai dai kashh bai samu nasara akanta ba sai ma ƙarin Tashin hankali daya gani kwance a cikin ƙwayar Idanunta hakan ya bayyana masa tsantsar kamun kanta.

Kama lips ɗinshi yayi yana Tsotsa Jinshi yake a wata irin Duniya ta daban yana jinta a ranshi amman yana Jin nauyin furta mata kalmar da zata haɗa zuƙatansu waje ɗaya sabida yana ganin kamar har yanzu akwai sauran Lokaci.

Mirginawa yayi tare da matse ƙaramin Pillown dake gaban shi yana sakin sassanyan Numfashi da ƙyar ya tashi yayo sallar Isha'i wata irin kewa yake Ji acikin zuciyar shi da gangar Jikin shi kwanciya ya kuma yi babu Jimawa bacci mai daɗi wanda ya jima bai samu ba ya ɗauke shi.

Washe gari bai yarda sun haÉ—u da Abba ba sabida Tun jiya yake ganin Kiran abba amman yayi Buris sabida yasan baze wuce maganar Alhaji Jamilu bace.

Ayyukan shi ya cigaba dayi acikin Office koda ya kammala Komai da yamma ya fito daga Office yana driving yana sakin Murmushi wanda tunda ya tashi a safiyar yau Fuskarshi ke cike da Wannan Murmushi wanda ya nuna zahirin farin Cikin da yake Ciki.

Hanyar Gidansu Mami ya nufa sunan daya sa mata kenan Sanye yake Cikin farar shadda ƙal wadda Kallo ɗaya zaka yi wa shaddar ka gane zahirin tsadarta.

A ƙofar Gidan su yayi parking ya fito daga Cikin Motar ya jingina ajikinta yana neman yaron da zai aika ya kira masa ita.

Ummi da Aunty Murja a wajan saadatu suka kwana wadda zazzaɓi mai zafi ya rufeta fuskarta duk ta fashe Ba yadda Aunty Murja batai da Ummi akan ta tafi gida ba amman taƙi data takura mata ma sai ta saka mata Kuka dole mijin Aunty Murja yace to ta kwana da ummi.

Washe gari da Zazzaɓin saadatu ta kuma tashi, sai amai take ruwa aka saka mata bacci ya ɗebe ta wajan rana Aunty Murja ta koma gida ta Yo Musu Girki bayan ta dawo Ummi ta tafi sabida ta ɗauko kayan su ta kuma gyara Hajiya don har Lokacin Saadatu bata farka ba.
Sabida allurar baccin da aka zuba mata acikin ruwan.
Ummi ta kammala Komai ta gyara Hajiya sai da akai la'asar sannan ta fito daga Gida.
Wanda tana fitowa Anwar yaɗan zuba mata ido ganin yanayin su da saadah yasa ya ƙarasa Wajanta Ummi da Anwar ya cika mata ido da sauri ta Rissuna tana gaishe dashi ya amsa yana tambayarta Ina Saadatu Dan Allah kozata Kira masa Ita.
Chapter 19 · 0% Book details