← Book details Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Jamilu yaja Kujerar dake facing ta Anwar ya zauna A hankali Anwar ya ɗago kanshi ya zubawa Alhaji jamilu idanu bai ɗauke idanunshi ba har seda ya ɗaga wayar ya kira Chief staff officer tare da Chief Information officer da kuma Chief marketing officer gaba ɗaya manyan Masu muƙaman kamfanin sun halarci zama a cikin Office ɗin Anwar.

Ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo Alhaji jamilu ne kaɗai zai iya haifar sa amman sauran masu manyan muƙaman basu fi sa'annin shi a haife ba.

"Ko wannen ku idan ya rasa kujerar sa ina nufin idan ya rasa hanyar samun abincin sa ina ga zai shiga hankalin sa ta yaya Kuna Cikin kamfanin nan Kuɗi su dinga ɓata ko mu loda kaya a manyan Motocinmu zuwa wani gari ace motar ta faɗi an sace kaya driver na asibi mai yake kawo haka?"
Ya tsaida idanunshi akan chief information officer kafin yace "Kaine kake da Lasisin ganin dukkan abin da yake faruwa acikin wannan kamfani ta cikin na'urorin dake office ɗinka, sannan alhakin ta yaya har kuɗi masu yawa suka salwanta babu sanin ka?" sannan ya kalli chief marketing officer tare da cewa "Kaikuma kaine mai lasisin kula da ƴan kasuwar dake shige da fice acikin wannan kamfani ta yaya har aka fitar da kuɗi ba tare da saninka ba bayan lasisin Kula da al'amuran kasuwancin wannan kamfani yana hannun ka?" ya Kuma kallon chief staff officer yana ce masa "Babu yadda za'ai ayi wani babban cinikayya acikin kamfanin nan batare da saninka ba sabida kaike da Kujerar shugaban ma'aikatan kamfanin nan baki ɗaya dole komai za'ai seda sanin ka sabida Duk wani staff ɗin kamfanin nan a ƙasan ka yake" yayi shuru tare da ɗaukar Gorar ruwa ya Kora "Alhaji Jamilu Financial Officer ni kaina in zan taɓa kuɗi seda izininka sanin dukkan wani tracking na kuɗin kamfanin nan yana wajan ka mai yasa har waɗancan Kuɗin da suka fita yau kimanin sati Biyu wanda yayi daidai da kwana na Biyar a Dubai suka fita wanda ni ban sani ba don ban signing shigowar wasu kaya ba bare ace an fitar dasu Duk ƙarshen wata nake Turawa Abba komai yana sanin Shigowar Kuɗin sa da fitar su da kuma albashin Ma'aikatan sa wannan karon Kuɗin da suka salwanta sunfi na kowane wata yawa duk da ba genaral total mukai ba wannan duk ƙarshen shekara Muke yi.

Alhaji jamilu ya kasa magana haka sauran ma Anwar ya kuma kallon Chief information Officer yace "Lallai lallai ka tabbatar ka nemo yadda kuɗinnan suka fita da lokacin su da komai haka kai ma Alhaji jamilu Tabbas ka tabbatar ka kawon cikakkiyar Hujjar da kasa hannu har kuɗaɗan nan suka fita batare da sanina ba Chief staff zaka iya komawa kai da Chief Marketing zan ƙara kiran ku"

Daga haka ya tashi yabar su a wajan ya shiga cikin resting room Jakar computers ɗinshi da keyn motar shi se wayoyin shi daya ɗauka Ya fito da sauri sectaren shi ya zo ya amshi kayan seda ya raka shi har wajan adana Motoci Inda motar shi take ya buɗe masa ya shiga Ciki ya zauna a driver seat sannan yakai masa kayan sa back seat sukai sallama Anwar Yaja Motar a nutse ya nufi ƙaton Bakin gate ɗin kamfanin wanda Securties suka cika wajan ɗaga wa Anwar Hannu suke batare daya Ɗago ya kalle suba ya danna hancin Motar shi yabar harabar Kamfanin Gudu yake Lokacin Yamma tayi sosai a ƙofar Gidan mahaifin shi Alhaji sule kurfi dake Unguwar Rijiyar zaki layin Muhalli Yayi parking ɗin Motar shi yana danna Horn masu gadi suka wangale masa gate Ɗin ya shiga cikin harabar Gidan ya adana motar shi bai ko tsaya ɗaukar komai ba dan hatta wayar shi ma A motar ya bari haka ya Nufi Part ɗin shi a hankali ya faɗa saman Gadon shi ya kifa cikin sa zuciyar shi babu daɗi sam wannan tasa tunda Abban shi ya Damƙa masa Dukiyar shi yayi bankwana da Nutsuwar shi Tarin damuwa da Ƙunci ne suka ƙara taruwa acikin zuciyar shi..........
*YANKAN ƘAUNA..I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *008*

ƙirjinsa ne ya soma ciwo ga wani irin zafi da yake yi masa tun yana iya Numfashi har fitar Numfashin Nasa ma tazo ta gagara a hankali Numfashin sa yake ɗauke wa kafin ya faɗo daga saman gadon tim baya Numfashi A wannan Lokacin bashi da Bambanci da gawa dama haka Yake yi Duk Lokacin da Ciwon zuciyar sa ya tayar masa wani irin baƙin Gudan Jinine ke fitowa daga cikin Hancin sa Adaidai wannan Lokacin Khalid ya shigo Gidan dawowar shi daga Office kenan kasancewar yana ɗaya daga cikin masu kula da Branch ɗin Alhaji dake kasuwar sabon gari Har Khalid zai shiga Part Ɗinsu wajan Innah domin yace tayi Musu Dambu kafin su dawo sanin Anwar Yana masifar son Dambun Shinkafa seya fasa ya tsaya a compound ɗin gidan tare da Fito da wayar shi yana kiran Number Ɗin Anwar wanda seda Khalid yayi masa Five Misscalls amman Anwar bai ɗauka ba A fili Khalid yaja tsaki tare da shafa sumar kanshi yana cewa.
"Wannan Bahagon Mutumin ina ya saka wayar shi Oho! Jin ana kiran sallah Khalid ya Nufi Bakin Jerin famfunan dake Compound yayi alwala ya shiga masallaci Bayan sun idar da sallar ya Nufi Part Ɗin su har ya ƙarasa Falon Innah yana Kiran Numbers ɗin Anwar Amman baki ɗayan su ba'a ɗauka ba zama Khalid yayi Rahma Autar Innah tana Kunna kallo ganin shi ta dakata tana masa sannu da zuwa.

"Ina innah Anwar ya shigo nan kuwa?" Rahma tace "A,a bai zoba Inna kuma tana É—aki tana sallah" Daga haka tabar wajan sanin idan Manyan yayin nasu suna Falon basa zama su aciki.

Khalid se kiran Numbers Ɗin Anwar yake suna shiga amman har Lokacin bai ɗauka ba se duk yaji babu daɗi sabida da zarar sun dawo daga Office to suna tare Muddin ba Ƙasar Anwar ya bari ba, Ko shi in yaje Lagos ko wata jahar kai kaya.

A haka Innah ta fito tana Murmushi "A,a naga Hassan ban ga Hussainin ba ina Muhammad ÆŠin?" Inna ta faÉ—a tana zama a saman Kujera Khalid cikin rashin walwala yace mata "Tunda nazo nake Neman Layi kanshi amman bai É—auka ba Duk hankalina ya tashi Innah Ina Malam?" Innah ta ÆŠan sauya fuska cikin halin damuwa tace "Malam yana É—akin sa yana karatun alkur'ani wai nan Saifullahi ko Fatihu yake Jira su dawo daga shago su kaishi Aski amman ya kamata ka binciki halin da Anwar yake ciki sabida kasan yana da matsala wadda bama fatan tashin ta"

Khalid tashi yayi tsaye tare da cewa inna bara ya leƙa part Ɗin Anwar ɗin Ko yana ciki Cikin sanyin Jiki Innah tace "To Allah yasa dai lafiya Kona Biyoka?" Khalid ya ɗan kalleta sanin matsayin Anwar a wajanta Ko shi data Haifa bata Nuna masa Soyayya kamar wadda take nuna wa Anwar "Inna ta Anwar Ki kwantar da hankalin ki Innah bari naje yanzu zan dawo" Inna har bakin Ƙofa ta bi Khalid wanda seda taga ya nufi part Ɗin Anwar Sannan ta koma ciki Khalid yana Jan Handle ɗin Ƙofar Bedroom ɗin Anwar yaji ta buɗe ya shiga ciki ɗakin akwai Duhu sosai wayar shi yasan ya ya lalubi swich ɗin ɗakin haske ya bayyana tarwai wanda Idanun Khalid suka ci karo da Anwar a ƙasa wanwar kamar gawa da gudu Khalid ya saki wayar ya nufi wajan shi gaba ɗaya ya tattaro Shi Jikinsa yana Jijjigashi "Anwar! Anwar tashi mana yaushe Ka faɗi ciwon kane ya tashi garin yaya?" Duk Khalid ya shiga jera tambayar kamar Anwar yana Jinsa bayan shi tuni yayi nisa acikin suman da yayi.
Chapter 7 · 0% Book details