Sashe 9
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ci gaba da cewa, "ni a ganina ka bar ya tafi kasar wajen, na san abin da kake gudu kana tsoran kar ya je can tarbiyyarsa ta gurb'ata, kayi hak'uri ka bar shi ya tafi mu dage da addu'a insha Allah ba abin da zai faru sai alheri.
Wani dogon numfashi yaja yace, "to shi kenan na amince Allah ya sa hakan shi ya fi alkairi".
Da sauri ta rungumo shi zuwa gare ta cike da farin ciki ta kank'ame shi tace, "Ameen summa Ameen, na gode sosai da ka fahimce ni".
Shi ma k'ara kank'ame ta tayi a k'irjinsa yace, "kar ki damu uwargidanta matar kwarai, kin fi k'arfin haka a wajena", yana fad'in haka ya d'ora lips d'insa kan nata, daga nan fa labarin ya sha bambam suka lula duniyar ma'aurata.
Washe gari farin ciki sosai Abdul yayi da suka sanar da shi.Nasiha sosai suka yi masa akan yayi abin da ya kai sa wato karatu.Haka dai aka shirya masa ta tafi tare da abokan nasa classmates d'insa, daman su suka kwad'aita masa fita wajen karatu.
A can ne fa suka lalace idonsu ya bud'e da neman mata.Da farko shi Abdul sam bai bi ra'ayinsu ba, dan yana kan nasihar da iyayensa suka yi masa, amma da yake yana tare da tantirai gogaggun 'yan bariki, sai da suka yi galaba akansa, ta hanyar sa shayar da shi maganin tada sha'awa masu k'arfi kullum ba tare da saninsa ba.Dalilin haka shi ma ya zamo manemin mata har ya zamo masa jiki.Cikin wannan halin suka had'a masters suka dawo gida Nigeria.
A b'oye yake neman mata sam bai bari iyayensa sun sani ba, can gidansa da Abbansa ya mallaka masa yake kai matan.Kwatsam Abbansa ya bijiro masa da maganar aure, wanda shi a lokacin bai ga macen da yake so ya aura ba.Haka ya d'au lokaci ba tare da ya samu mafita ba, shi kuma Abban nasa bai k'ara bijiro masa da maganar ba, ganin haka ya shiriritar da magana.Ganin har watanni sun shud'e bai kawo musu matar aure, ya sa ba shi lokaci ko kuma ya ba shi zab'insa...
Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 47 - 48
*Ci gaban labarin*
B'angarensa ya nufa ya bud'e k'ofar falon ya shige jagwab ya zube kan two seater yana maida numfashi.Tagumi ya zube fuskarsa d'auke da tsantsar damuwa, yayi iyakar tunaninsa bai gano mafita ba, bai san wacce yarinya ya dace ya aura ba, yana da 'yan mata da basu da adadi, amma bazai iya tantance guda d'aya wacce zai ce yana yi mata hak'ik'anin so ba son sha'awa ba, so na gaskiya na aure, ko Latifa da suka had'u shekaran jiya a wajen birthday d'in abokinsa ita ma sha'awar ta kawai yake ji bai jin wani san ta cikin zuciyarsa.
Wayarsa ce ta kama k'ara, d'auka yayi dan ya kashe, ganin wacce ke kiran sa ya fasa, yayi picking.
"To ga ni nan zuwa yanzun nan", ya fad'i haka muryarsa a matuk'ar sanyaye bayan ya gama sauraran wanda yayi kiran nasa.
B'angaren mahaifan nasa ya koma, zaune ya tarar da su a falon.Fuskar mahaifinsa ba alamar wasa ya kalle shi bayan ya zauna a gabansu kansa a sunkuye yace ya yarda ya ba shi nan da wata biyu
ya nemo matar aure.Rok'on sa ya shiga yi da ya k'ara masa wata d'aya dan yayi nazarin matar da ya dace ya aura.
Harara ya zabga masa yace, "kai!, shiga hankalinka, ni bazan k'ara dad'a maka wani lokacin ba, na ba ka nan da wata biyu ka nemo yarinya 'yar mutunci ka aura, idan ka d'auki maganata da mihimmanci ke nan, idan ba ka d'auka ba zaka gane kuskurenka", yana fad'in haka ya mik'e ya haura sama, ya bar shi zaune cikin damuwa.
A damuwance ta kalle shi cike da tsantsar kulawa ta shiga nusar da shi tana cewa ya bi umarnin mahaifinsa yayi yarda yace kafin lokacin da ya ba shi, ya kuma fauwalawa Allah komai, shine zaiyi masa zab'in mafi alkairi."Yanzu ka tashi ka je kayi alwala kar ka rasa jam'i", ta fad'i haka jin an fara kiraye kirayen Sallar Magrib.Jikinsa a matuk'ar sanyaye ya tashi ya fice daga falon.
Pls kuyi manage da wannan, uzururruka ne sukayi min yawa shi yasa kuka ji ni shiru kwana biyu, luv u all my fans.

*Wannan page naku ne Ummu Auwal da Hassanan Maska (Asmeenat Zeeyan fans grp), I really appreciate ur love and cares 😍*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 49 - 50
A damuwance ce ya koma b'angarensa jikinsa a sanyaye ya d'ora alwala ya tafi masallaci, ana tayar da Sallah ya isa.Sai da aka yi Sallar Isha'i suka bar masallaci kamar yarda kullum suka saba shi da mahaifinsa.Yana fita daga masallacin bai zarce ko'ina ba sai gidan Mamy wato gwaggonsa Hussaina.Da isarsa yayi knocking gate d'in gidan, bud'e masa maigadi yayi ya shiga bayan ya tambaye shi waye ya fad'a masa.
Bai tarar da kowa ba a falon zama yayi kan two seater da ke falon ya kama hab'arsa da dukkan hannayensa biyu.Cikin wannan hali Mamy ta zo ta tarar da shi, dafa kafad'arsa tayi tare da d'an girgiza shi ganin ta dad'e tsaye akansa amma bai ankara da wanzuwarta ba
tace, "tunanin me kake yi haka kai kuwa ?"
Firgigit ya d'ago ya kalle ta tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba tare da yace mata komai ba.Kan kujerar da ke facing d'insa taje ta zauna kana ta dube shi tace, "ina sauraran ka, ina san ka fad'i min abin da kike tunani haka".Sai da ya gyara zama sosai sannan ya kwashe komai ya fad'a mata, ya k'ara da cewa, "ni damuwata lokacin da ya bani yayi kad'an, da ya dad'a min wasu watanni shine zanyi nazarin matar da ya dace na aura sosai".
Numfashi ta ja bayan ta gama sauraran sa tace, "a gaskiya ni ma ina bayansa kan wannan maganar, dan ka kai munzalin aure, kayi k'ok'arin nemo matar aure kafin lokacin da ya ba ka ya cika".
Wani gwauran numfashi ya ja kana yace, "na ji kuma insha Allah zan yi yarda kuka ce kafin lokacin".
"Yauwa ko kai fa d'an albarka, Allah ya had'a ka da mace 'yar mutunci nutsatstsiya mai kamun kai", daidai nan Zainab ta fito daga d'akinta, gefe kusa da shi ta zauna tana cewa, "bros shi ne ko ka tambaye ni da ka zo, kuma yau nayi kiran ka yau amma ka k'i d'auka", a shagwab'e ta fad'i haka.
"Afuwan kiyi hak'uri na amshi laifina, kiyi min uzuri bazan k'ala ba kin ji little 'yar lukuta", yana fad'in haka shi da Mamy suka fashe da dariya.
K'ara shagwab'e fuska tayi tana cuno baki tace, "na k'i na hak'ura tun da ka ce min 'yar lukuta", k'ara sa mata dariya suka yi, kukan shagwab'a ta sa musu.
Tsagaita dariyar Abdul yayi ya rik'o hannunta ya shiga aikin rarrashin ta yana cewa, "yi shiru kin ji na daina fad'a miki haka, gobe ki shirya zan zo na Kai ki shopping, ki zab'i duk abin da kike so".
Tashi tayi ta daka wani tsalle yayin da wani dad'i ya ziyarci zuciyarta, cike da farin ciki tace, "kai amma na ji dad'i sosai bros, kamar ko ka san kayan cosmetics d'ina sun k'are ga shi Abba yayi tafiya".
"Kun ga ku bar surutun haka ku tashi mu je mu yi dinner", Mamy na fad'i haka ta tashi ta nufi dining table, daidai nan Faruq (d'an Mamy na fari bayansa ta k'ara haihuwar d'a namiji yana Kaduna gidan kawunsu Hassan, shekararsa d'aya kenan da samun admission a A.B.U Zaria) ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama.
"Daman kana cikin gidan nan tun da nazo ban ji d'uriyar ka ba", Abdul ya fad'i haka bayan su amsa masa sallama.
Cikin zolaya Zainab tace, "ai bros ko yanzu dan yunwa ce ta koro shi da baza ka gan shi ba har ka tafi, ka san acici ne sam baya wasa da cikinsa", ta k'arasa fad'in haka tare da sa dariya, suma dariyar suka sa.
"Eh dai na ji na fi wata dai da ba abin da ta sa gaba sai kwad'ayi, a tambaye ta shan sweet da charcolate kamar wata 'yar yarinya, dan tsabar ita kwad'ayayyiya ce", dukk dariya suka k'ara sawa.Tsayar da dariyar suka yi suka zauna kan dining dan yin dinner.Bai bar gidan ba sai wajejen k'arfe goma bayan sun sha hirarsu ta cike da nishad'i da annushuwa.
Kwance kan faffad'an lafiyayyen gidansa ya kasa rintsawa, tashi yayi ya zauna tare da zuba tagumi.Tabbas ya san abin da yake aikata haramun ne, yayi yayi ya daina ya kasa, ya kamata yayiwa kansa fad'a ya bi umarnin mahaifinsa ya nemo mata yayi aurensa, insha Allah ya d'au niyyar barin sab'awa Allah da yake daga daren yau har zuwa karshen rayuwarsa bazai k'ara komawa zunubin, zai kuma nemi mata 'yar mutunci ya aura, ya bar rakiyar shad'ainun abokanansa wad'anda daman sune silar komai
Jiki a matuk'ar sanyaye ya tashi ya shiga band'aki ya d'ora alwala ya fito.Cire rigar baccin da ke jikinsa yayi yasa farar jallabiya, kana ya tayar da Sallar Nafila.Haka dare ranan yayi ta nafilfili yana rok'on Allah akan ya karb'i tuban sa ya kuma yafe masa zunubansa, ya kuma zab'a masa mata mafi alkairi gare shi.Da Asuba ya so ya makara, a gaugauce ya je ya d'ora alwala ya fita zuwa masallaaci.Yana dawowa ya koma ya kwanta.
Sowar da wayarsa ke yi ne ba kaukautawa ne ya tayar da shi daga baccin da yake, d'aukan wayar yayi ya duba, tsaki kawai yayi ya tashi ya shiga band'aki bayan ya ajiye katse kiran ba tare da ya d'auka.
Yana cikin shiryawa wani kiran ya k'ara shigowa, d'aukan wayar yayi da nufin kashewa, ya fasa ya d'aga,
Yana d'agawa ya ji an sauke ajiyar zuciya tare da cewa, "sai yanzu na ji dad'i a rain..."