← Book details Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin ga har zan tafi mum bata dawo ba idan ta dawo ki gaida ta ki ce Mamy ma na gaida ta", Zainab ta fad'i haka da fitowarsu tsakar gidan.

"Zata ji insha Allah", tana fad'in suka fice daga gidan.

Ranta fari kal ta dawo daga rakiyar ta, wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, wani irin dad'i da sanyi ke ratsa zuciyarta.Da shigarta d'aki ta fad'a kan gado tana lumshe ido.Tun ranar da suka had'u soyayyarsa ta sa ta a gaba take wahalar da zuciyarta, rok'on Allah ta shiga yi da ya sa shi ma ya kamu da san ta, dan yarda soyayyarsa ta mamaye zuciyarta farar d'aya, tabbas zata shiga damuwa idan ya kasance so maso wani take.Ba shakka kamar yarda Zainab ta fad'a aji kawai take san jan, dan so tana san sa.Wani irin dad'i ne ke ratsa ta godiya kawai take ga Allah, zuciyata cike da nishad'i cikin wani yanayi na jin dad'i...
*https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/ WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 67 - 68

Zainab na isa gida bayan tayi parking ta fito daga mota, wayarta da ke cikin handbag d'inta ta hau ringing.Ba ta tare da ta tsaya d'agawa ba ta nufi k'ofar falon gidan.Zama tayi kan two seater d'in da ke falon ta ciro wayar da ke faman ringing daga cikin handbag d'inta, ta dubi sunan wanda ya bayyana akan screen d'in wayar, murmushi tayi ganin wanda ke kiran ta kana ta d'aga wayar.

"Ina kika shiga ne ina ta kiran ki baki d'aga ba ?", tana d'agawa aka tambaye ta daga can d'ayan b'angaren.

"Afuwan bros ina parking kiranka ya shigo, shi ne na bari sai da na shiga falo"

"Ok to yaya kin isar da sak'ona kuwa ?", ya k'ara tambayar ta.

"Eh dawowata kenan daga gidansu dan ban samu damar sanar da ita a Makaranta ba ".

"Yauwa shi yasa nake ji da ke da fatan dai na dace", ya fad'i haka zuciyarsa cike da fargabar abin da zai fito daga bakinta.

"Ka bari idan ka zo zan sanar da kai yarda muka yi da ita",

"Ga ni nan tafe yanzun nan", yana fad'in haka ya katse wayar bai jira abin da zata ce ba.Ita kuwa yana katse ta k'yalk'yale da dariya dan ya matuk'ar ba ta dariya jin yarda ya rud'e.

"Ikon Allah me ya faru kike dariya ke kad'ai ?", Mamy da fitowarta kenan daga kitchen.

"Bros ne ya ban dariya Mamy ", ta fad'i haka cikin dariya.

"Ke kuwa dariyar me ya ba ki ?".Tsagaita dariyar tayi ta fad'a mata yarda suka yi da shi a waya ta k'are da cewa, "rud'ewar da yayi ne ya ban dariya ",tana fad'in haka ta k'ara sa dariya.

Murmushi mai sauti Mamy ta saki tace, "yanzu rud'ewar da yayi ne kike yiwa dariya, to kamar a kunnensa sai na fad'a mas...".

"Ba sai kin fad'a min ba Mamy na ji komai", Abdul da ke tsaye bakin k'ofar falon ya katse ta tun kafin ta kai ga kammala abin da tayi niyyar fad'a.Su duka juyowa suka yi suna kallon sa.

Zainab ce tayi saurin cewa, "la!, bros ka ce har ka iso, lallai su bros an k...", bata kai ga k'arasawa ba tayi gum da bakinta dan wani irin harara da taga yake zabga mata.

K'arasawa yayi cikin falon inda take zaune ya kama kunnenta yace, "na ga alama yanzu ki zamar da ni kamar sa'anki, to daga yau idan kika k'ara yi min dariya bulala zanyi miki", ya fad'a tare d'an murd'e kunnen nata.

"Wayyo Mamy kin ga shi ko", ta fad'i haka tana cuno bakinta cike da shagwab'a.

"A'a ni ba ruwa tsakaninku ne kin ga tashina ma zan je na dubo girkin da nake", Mamy ta fad'a tana dariya, tana dariya ta tashi ta shiga kitchen.

Kallon sa tayi tana cuno bakinta tace, "to na fasa ma fad'a maka yarda muka yi da ita".

Da sauri ya rik'o hannayenta yace, "dan Allah kiyi hak'uri duk cikin wasa ne fa, kin ji 'yar siririyar k'anwata", yana fad'in haka suka sa dariya.

"Na k'i wayon", ta fad'a tana nok'e kafad'arta bayan sun tsagaita dariyar .

"Please lil sis kiyi hak'uri ki fad'a min kin ji 'yar siririyar k'anwata", ya fad'i haka yana langwab'e kansa.Dariya ta sa ganin yarda ya langwab'e kai.

Kwashe komai tayi ta fad'a masa bayan sun dakatar da dariyar ta k'are da cewa, "ka kwantar da hankalinka bros insha Allah ita ma tana san ka zata amince da Kai, dan na ga alama haka tarada ita".

Saki d'an murmushin jin dad'i yayi yace, "Allah ya amshi addu'arki".

"Ameen summa Ameen", Mamy wacce fitowarta daga kitchen kenan d'auke da tray d'in abinci ta furta haka.Da sauri Zainab ta tashi ta je ta karb'e tray d'in daga hannunta ta nufi dining.

Kallon sa Mamy tayi bayan ta zauna tace masa kar ya damu zata je wajen su dad d'insa su tattauna akan maganar, za'a je a nemo masa izinin zuwa wajenta su gana su fahimci juna tukun, ya so daga baya sai ayi maganar aure.Tashi tayi tace zataje tayi wanka, tana gamawa zata je wajen nasu suyi maganar.Shi ma tashi yayi ya fice daga falon zuciyarsa cike da fatan samun dacewa, Zainab kuwa tana ajiye tray d'in kan dining ta shige d'akinta...
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 69 - 70

Dad d'insa na dawowa bayan yayi wanka ya huta ta zayyana masa komai ta k'are da cewa, "yanzu abin da ya saura shine gidansu za'a je a gabatar da musu da cewa, d'anmu ya ga 'yarsu yana so muna nema masa auranta, dan kar ya kasance akwai maganar wani akanta".

Gyad'a kai yayi cike da gamsuwa yace, "tabbas haka ya kamata ayi, nayi farin ciki sosai dan kwarai nake son ganin Abdul ya aje iyal...", Sallamar da Mamy tayi ne ya sa ya katse maganar, a tare suka amsa mata.

Bayan sun gaisa ta bayyana musu maganar da ta kawo ta.Wayarsa ya d'auka yayi kiran wansa wanda suke uba d'aya ya sanar da shi komai, cewa yayi ga shi zuwa gida yanzu.Bai wani jima ba ya iso, nan suka taru suka tattauna kan maganar, suka yanke shawarar gobe insha Allah zasu je gidan.Washe garin ranar kawu Sani wato wan dad da maigidan Mamy kuma aminin dad suka je gidan bisa jagorancin direban gidan Mamy.

Daidai k'ofar gidan yayi parking suka fito.Yaro suka aika da yayi musu sallama da maigidan.Bai dad'e ba ya fito yace ga shi nan fitowa.

Jim kad'an da fitowar yaron ya fito, basu hannu yayi suka yi musabaha.Bud'e musu d'akin da yake sauke bak'i yayi suka shiga.Fita yayi bayan sun zauna tare da cewa yana zuwa.Humaira ce ta shigo d'akin bayan tayi sallama sun amsa mata, d'auke da tray ta yafa babban mayafi kan atamfar da ke jikinta.K'anta na kasa cikin girmamawa ta gaida su, ajiye tray d'in tayi a gabansu ta tsiyaya musu ruwa cikin cups ta mik'awa kowannensu cike da nutsuwa.Tana mik'a musu ta tashi ta fice daga d'akin.

"Da alama munyi sa'ar suruka", kawu Sani ya fad'i haka da fitarta cikin jin dad'i.Yana rufe baki Abba yayi sallama ya shigo d'aki.

"Dan Allah kuyi hak'uri na bar ku kuna jira", Abba ya fad'i haka bayan ya zauna.

"Ba komai kar ka damu", kawu Sani ya fad'i haka murmushi d'auke a fuskarsa.

Gyara zama kawu Sani yayi ya sanar da shi abin da ke tafe da su tare da yi masa gamsashen bayanin kan zuri'arsu ya k'ara da cewa, "ba ma san a ja wani dogon lokaci, idan ba maganar wani akanta".

Gyad'a kai yayi bayan ta gama sauraran bayaninsa cike da gamsuwa yace, "tabbas ba maganar kowa akanta, yana damar zuwa su ga juna, idan ta amince tana san sa shi kenan Allah dai ya tabbatar da alkairi", dukkansu suka amsa da Ameen Ameen.

Kawu Sani ne ya fiddo kud'i daga aljihun rigarsa ya ajiye gaban Abba.K'arewa kud'in kallo yace, "a'a na gode sosai, kuyi hak'uri bazan karb'i kud'in nan ba".

Alhaji Ahmad ne wato maigidan Mamy yayi saurin cewa, "haba dai idan kayi haka sai mu ga kamar ba mu samu karb'uwa ba ne ", badan ya so ba ya amince ya d'auki kud'in.Sallama suka yi cike da ganin dattakon juna suka tashi suka fice tare dan yi musu rakiya...
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*Afuwan da ji na shiru kwana biyu, luv u all my fans 😘😍*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 71 - 72

Yana dawowa daga rakiyar su yayi kiran ta ya zaunar da ita ya bayyana mata komai ya k'are da cewa, "ni dai na ba shi izinin zuwa wajenki ku gana da juna, dan kwarai na yaba da dattakon magabatansa", shiru yayi yana sauraran abin da zata ce.

Kanta a sunkuye tace, "Abba ai ni ban da abin da zai ce, tun da ka amince ni ma na amince da ya zo d'in", tana rufe baki ummanta ta shigo falon ba tare da tayi sallama ba, wuce su tayi ko kallan inda suke bata yi ta shiga bedroom d'inta.

Girgiza kansa Abba yayi cike da takaicin halin matar tasa, ace mace bata komai sai gantali, idan ta fita tun safe sai fad'uwar rana zata dawo, hakan na matuk'ar yi masa ciwo a zuciya, amma babu yarda zai yi, yana k'arfin halin yi mata magana zata hayyak'o masa, bai sa me yasa ba ya ke shakkar ta, baya iya maida mata magana ba.

Murya a sanyaye cikin yanayin damuwa Humaira tace, "Abba dan Allah ka daina sanya damuwa a zuciyarka, wani ciwon zai iya kama ka, tabbas kowana bawa akwai ta inda Allah ke jarabta shi, ka fawwalawa Allah komai shi ne zai yi maka maganin komai".

Naunauyan ajiyar zuciya ya sauke yace, "tabbas haka ne na yarda da cewa nawa jarabtar kenan, kar ki damu tuni na daina sa damuwa cikin zuciyata, a kullum addu'a nake Allah ya shirya ta ya ganar da ita gaskiya".Muryarta a raunane tace "Ameen Abba".
Chapter 14 · 0% Book details