Sashe 1
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{Home of exceptional and magnificent writers}}
*🧕WAYAYYIYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*Dukkan yabo godiya sun tabbata ga Ubangiji mad'aukakin Sarki,tsira da aminci su tabbata Shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W) tare da Ahalinsa da Sahabbansa.Alhamdulillahi da ya k'ara ba ni damar rubuta wannan littafi, Allah ya sa na rubuta abin da zai amfanar da Al'umma, ya kuma yafe min kurakuren da zanyi a ciki, Ameen summa Ameen*
*Jinjina gare ku hazik'ai kuma jajirtaccun marubutan Brilliant writers, shafi na farko sadauk'arwa ne gare ku, Allah ya k'ara had'a kanmu iya wuya ana tare 🤝*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 1 - 2
Wata dalalleliyar motar ce k'iorar picanto tayi parking bakin wani madaidaicin gida da misalin k'arfe sha biyun dare.Ak'alla motar tayi mintina talatin a fake, sannan wata k'yakk'yawar budurwa ta fito daga motar.Bata damu ba ko a jikinta dan ta shiga gidansu a irin wannan lokacin, tana layi ta shiga gidan ta rufe k'ofa ba kowa a tsakar gidan, d'akinsu ita da k'anwarta ta fad'a.
Tana shiga d'akin k'anwarta Humaira ta dube ta cike da takaici tace, "haba Anty Latifa sai yanzu kika dawo ?".
Hararar ta tayi cikin fushi tace, "Eh sai yanzu na dawo, ina ruwanki ?".
Cikin takaici ta k'ara ce mata "uhum lallai kam ba ruwana amma hakan da kika ce bazai hana in ci gaba da tunatarwar da bakya so ba".
Jin tayi shiru bata k'ara cewa komai ba ta ci gaba da cewa, "ba mutuncinmu ba ne ki maza na zuwa a manyan motoci suna d'aukar ki fita yawo, baza ki dawo ba sai tsakar dare.Duka wad'anda suke rud'ar ki suna lalata miki rayuwa babu wanda zai yarda ya aure ki, ni wallahi duk macen da take biyewa namiji yana lalata da ita, kallon wauta da rashin wayewa nake mata, in ban da wauta ya zaki biyewa wanda kika san ba auran ki zai yi ba, jikinki kawai yake so..."
Cikin tsananin fusata Latifa ta d'aga mata tace, "ya ishe ki haka, har ke zaki ce wani bai waye ba, ke da kike babbar kidahuma, dan ki ja bakinki kiyi shiru kafin in fasa miki baki yanzu".
Murmushi tayi cike da takaici tace, "ba mace wayayya sai wacce ta tsare dokokin Allah, babu wayewar da ta fi ta addini.Duk macen da take tallar surorin jikinta ga wasu mazan wanda ba muharramanta ba tabbas bata san ciwon kanta ba, duk wanda bai san ciwon kansa ba shine bagidaje sam ba wayewa tare da shi.Dan Allah Anty Latifa kiji tsoran Allah ki daina wannan rayuwa, sam ba riba ko kad'an cikinsa sai fad'uwa tare da tarin nadama".
Wani dogon tsaki taja ba tare da tanka mata ta cire kayanta tayi wanka, ta sa kayan bacci ta yi kwanciyarta ta hau chatting kamar kullum, sai ta kusan kwana tana Online.
Ita kuwa Humaira girgiza kanta kawai tayi cike da tsantsar takaici, tare da yiwa Yayar tata fatan shiriya a zuciyarta...
Sai naga ruwan comments, zan ci gaba da suburbud'o muku typing 😎
Fatinku ce 😘😍
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}
*🧕WAYAYYIYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
Bonjour
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 3 - 4
Washe gari sai wajejen k'arfe goma sha d'aya safe Latifa ta tashi saboda kwanan rashin bacci.Da k'yar ta k'ok'arta ta tashi tayi sallar Asuba ta koma ta ci gaba da baccinta. Tana tashi tayi wanka ta tsuke cikin pink d'in riga da wando, ta tufke gashin kanta da ya sha kitson attached ya sauka har gadon bayanta.
Fita tayi zuwa babban falon gidan, mahaifinta kad'ai ta tarar a falon da yake kwana biyu baya jina dad'in jikinsa shi yasa baya fita.Dan tsabar rashin tarbiyya wucewa tayi zata shiga d'akin mahaifiyarta ba tare da ta gaishe shi ba.Kiran ta yayi, juyawa tayi ba tare da ta amsa ba, fuskarta a tsuke ta k'arasa gabansa ta d'an rissina tace, "ga ni".
Girgiza kansa yayi cike da takaici ya fara magana da cewa, "yanzu kina ganin irin rayuwar da kika zab'arwa kanki kuwa zai haifar miki d'a mai ido ?, jiya k'arfe nawa kika dawo ?
Shiru tayi bata ce masa komai ba, shi kuma ci gaba da cewa yayi, "ina sane sarai k'arfe goma sha biyun dare kika dawo, wace irin rayuwa kike Haka ta cutar kai ?, ki daina biyewa mahaifiyarki da ke d'ora ki kan muguwar rayuwa, wacce ba inda zata kai ki sai gidan nadama, dan haka ki guji abin da zai sa ki da na sani, dan yana da matuk'ar ciwo a zuciya.Idan aure kike so ki fidda miji kiyi aurenki ya fiye miki wannan yawon da kike".
Jin sa kawai Latifa amma ko kusa bata ga abin da d'auka amaganganunsa ba. Maganar dai d'aya ce ta rabu da shak'atawar da take, wanda sam ita ba zata iya dainawa.
K'asa k'asa yake yi mata maganar dan kar mahaifiyarta ta ji ta hau yi masa mitar yana takura mata da fad'a kamar ba shi ya haife ta ba, baya san ganin ta cikin walwala.Hakan na matuk'ar ba shi mamaki, mutum da 'yarsa ace ba shi da ikon ya tsawatar mata idan tayi ba daidai ba, sai dai ya sa musu ido suyi yarda suka ga dama, a hak'ik'anin gaskiya hakan nayi masa ciwo sosai, ba yarda zaiyi ne.
Ba tare da ce kala ba ta tashi ta shiga d'akin.Cike da takaici Humaira wacce ta dad'e tsaye bakin kitchen d'in da ke falo ta k'araso hannunta d'auke da ruwa kan tray.Zuba ruwan cikin cup ta rissina cikin girmamawa tace, "Abba ga ruwan da ka ce na kawo maka", amsa yayi daga hannunta yana mai sanya mata albarka da fatan Allah ya bata miji nagari tare da 'ya'ya da zasu zama sanyin idaniya gare ta.Zuciyarta cike da tsantsar kaunar mahaifin nasu tare da jin tausayin sa ta amsa da "Ameen summa Ameen.
Dan Allah ya jarabce shi da samun mata fitinanniya, shi kuma kwata kwata baya san hayaniya, bai d'auki duniya a bakin komai ba, amma sai ga shi Allah ya jarabce da samun mata masifaffiya mai san fitina...
Ku biyo next page d'in dan jin cikakken asalinsu.
More comments more typing.

*Wannan page d'in naku ne Hassan Atk da Hussain Atk, Allah ya saka muku alkairi ya kuma biya muku buk'atunku na duniya da lahira, Ameen summa Ameen*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 5 - 6
Alhaji Umar sani Umar shine cikakken sunan mahaifinsu Latifa, mutum hak'urin gaske, da ace hak'uri yana yiwa mutum yawa, to da shi shi kam hak'urinsa yayi yawa, babu abin da ke d'aga masa hankali cikin lamarin duniya, baya san abin da zai kawo hayaniya da tashin hankali.Haifaffen birnin Kanon dabo ne amma iyayensa 'yan asalin fulanin Yola ne, sha'anin kasuwancin ne ya dawo da su Kano da zama, ba dai dukiya gare shi ba yana da rufin asiri gwargwadon iko.
Babu abin da Alhaji Umar ya fi buk'ata bayan zaman lafiya, yana matuk'ar gudun fitina.Amma kash!, Allah ya had'a shi da jarababbiyar fitinanniyar mata mai san fitina da tashin hankali ga mugun san abin duniya.Aurensu tun saurayi da budurwa, mahaifansu aminan juna ne, su suka had'a auren nasu dan k'ara dankon zumuncin da ke tsakaninsu.Su ma asalinsu fulanin Yola, hasalima mak'otan juna acan Yolan, amintar mahaifan nasu na tun yarinta ne.
Hajiya Karima (sunanta kenan), 'yar kasuwa ce sosai, ta tara dukiya mai yawa.Bayan rasuwar mahaifinta ta samu dukiya mai yawa bayan an raba gado, kasancewar su biyu kad'ai mahaifansu suka haifa ita da Yayanta.A wad'anda suke harkar kasuwancin da su, ta had'u da k'awaye gogaggun 'yan duniya wad'anda suka nuna mata muddin tana san ta zama *wayayyiyar mace* kar ta sake ta d'auki wargi daga mijinta, kar ta sake ta d'auki raini daga gare shi, ta tashi tsaye yanzu kai ya waye, ba'a zama haka.Da taimakon su ta shiga ta fita ta mallake shi, ba shi da ikon cewa komai sai abin da tace, ta zama ita ce maigidan, shi abin da take so ake yi a gidan.
Cikin 'ya'yan biyun da suka haifa wato Latifa da Humaira, Latifa ta fi shiga ranta, dan ita ce mai bin ra'ayinta.Hajiya Karima ta kasance mace mai mugun san abin duniya, duk da yawan dukiya da ke gare ta, tana hangen abin da Latifa zata samo wajen samarinta na watsewa.Bata damu da lalatar da take da kowana namiji ba, in dai zata kawo mata kud'i an gama magana.Bata damu da idanun Latifa suka bud'e ba wajen bin maza ba, ita dai kud'i kawai.
Hakan na matuk'ar tayarwa mahaifinsu hankali, dan yana sane da abin da Latifa take, amma ba shi da ikon yin magana, yanzu nan uwar zata hau shi da masifa kamar ba mijinta ba.Akan dole yake rabuwa da su suke yin abin da suka ga dama.Bata damu ko nawa ne ba zata iya kashewa Latifa wajen kayan kwalisa da suturu masu tsada, dan kawai ta samu samari masu dukiya.Haka dai ya sa musu ido bai isa ya fad'a musu gaskiya ba, in dai duniya ce ga su ga ita, tana jiran wanda bai zo ba bare wanda ke cikinta...

Page 7 - 8
*Cigaban labarin*
Tura k'ofar d'akin mahaifiyarsu Latifa tayi ba tare da tayi sallama ta sa kai ta shiga.Zaune take bakin gado tana waya, kusa da ita Latifa ta zauna sai zumb'uro baki take.
"Mum wai saboda me dad ke san takura min, sam baya san gan ni cikin walwala", Latifa ta fad'i haka bayan ta katse wayar cike da shagwab'a sai cuno baki take.
Wani dogon tsaki taja tace, "ni rasa me yasa dad d'inki ke san takura kullum ba shi da aiki sai takurawa mutane, bar ni da shi zanyi masa magana daga yau daina yi miki fad'a",