Sashe 11
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*Ku yi hak'uri da rashin posting kwana biyu, luv u all my fans*
*This page is for u namesake Fatima Tijjani, ina taya ki murnar kammala book d'inki mai cike da darussa, Allah ya k'ara basira da hazak'a takwara 🥰🥰🥰👍*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 55 - 56
Cikin wani salo irin na nisa a iskanci da lalacewa suke latsa juna, suna sumbatar ko'ina a jikin juna duk sun fice daga cikin hayyacinsu, baka ji komai cikin motar sai nishi da gurnaninsu.
Cike da shak'iyanci Fahad da ke tuk'i ya kalli Ruky yace, "da alama dukkansu sunyi missing d'in juna, bari na k'arawa motar mai mu samu mu kai da wuri, dan ni ma a matuk'ar matse nake", ya fad'i haka yana k'anne mata ido.Bai bari tayi magana yayiwa motar wani irin fisga, ya shiga sharara wani irin mahaukacin gudu.Nan take ba shiri suka dawo cikin hayyacinsu dan mahaukacin fisgar da yayiwa motar.
"Haba Man ya zaka katse mana jin dad'inmu, wallahi kai mugun d'an buk'ulu ne, ina tsaka da jin dad'ina amma kai d'an air ne wallahi kuma d'an bak'in ciki", Hisham ya fad'i haka cike da takaicin katse musu hanzari da yayi suna tsaka da jin dad'insu hakawai.Dukkansu ban da shi dariya irin tasu ta 'yan duniya suka fashe da shi.
"Ai daman da gangan nayi haka, dan baku kad'ai ne ke san dad'i, ku bi kun damu mutane da nishi da gurnani, shine nace bari nayi maganinku", Fahad ya fad'i haka cikin dariya, bai jira ba abin da zai ce ba ya ci gaba da sharara mahaukacin gudu.
Harara ya zabga masa yace, "ai daman na san da biyu kayi haka, d'an bak'in ciki kawai", dukkansu dariya suka suka k'yalk'yale da shi.Basu jima sosai kan hanya ba suka isa Abuja, direct gidan abokin nasu suka zarce.Tarar da falon gidan suka yi cike da samari da 'yan mata suna ta shan giya da lalata iri iri , zama suka yi bayan sun gama gaisuwarsu irin ta gogaggun 'yan duniya suma suka shiga holewarsu da Hisham na manne da Latifa suka tashi suka shige bedroom, da shigarsu ya shiga yi mata wani irin salo wanda ya kashe mata jiki, nan take ta biye masa ta shiga mai da masa martani.
Wayarta da ta bari a falo ne ta hau ringing ba kaukautawa.Fahad ne ya d'auki wayar ya kashe gabad'aya ganin ba'a daina kira ba.Shi ma tashi yayi suka shige d'aya bedroom d'in shi da Ruky, abokin nasu sai shak'iyanci yake yi musu yana zolayar su akan daga zuwansu ko hutawa basuyi ba zasu hau yin harka.
La'asar sakaliya ta gama shirinta cikin atamfa mai kyau ruwan hoda da ratsin fari, d'inkin riga da zani, d'inkin ya karb'e ta matuk'a.Yalwataccen mayafi ruwan atamfar ta yafa, ta zura takalmi da jaka suma ruwan atamfar, ta fita dan yiwa Momi sallama.
Zaune ta tarar da ita tana da waya a hannunta tana k'ok'arin yin kira, da sauri tayi mata alama da hannu da ta fita.Murmushi tayi wanda da gani na yak'e ne ta fice daga falon.
Tana fita ta samu adaidaita sahu ta fad'a masa inda zai kai ta, ta hau bayan ya fad'a mata adadin kud'in da zata biya.Har bakin gate d'in gidansu k'awar tata ya kai ta ta fito ta sallame shi.Daidai lokacin wata had'add'iyar mota ta iso gate d'in gidan, maigadin na jin horn d'in motar ya bud'e gate d'in, mamallakin motar ya danna hancin motar harabar gidan, Yana shiga ita ma ta shiga bayan sun gaisa da maigadin dan daman ya san ta.Tana shiga mammallakin motar ya fito bayan ya gama yin parking, carab idanunsu suka had'u da juna, cike da tsantsar kunya ta gaishe da shi kana ta shige. cikin gidan.Bin bayanta yayi da kallo, yana jin wani abu na tsirga masa a zuciyarsa, wanda bai tab'a jin makamancinsa ba, wani gwauran numfashi ya ja ya shige ciki.
Durjar ta Hisham ya shiga yi dan yayi missing d'inta sosai, sai sumbatun dad'i yake.Ya jigatar da ita sosai har ta kai ta gaji ta hankad'e shi tace, "Kai ka rabu da ni haka na gaji".
Dariya ya k'yalk'yale da shi yace, "to naji zo muje muyi wanka tare".
"A'a na k'i wayon, kowa yayi wankansa d...", bai bari ta k'arasa ba ya sure ta sai band'aki, sai dariya yake.Badan ta so ba ya k'ara wani round d'in a band'akin, kana sukayi wanka suka fito.
Falo suka fito bayan sun gama wajen abokanan shashancinsu, sai shan giya da lalata iri iri suke.Suna zama Latifa ta d'auki wayarta ta gan ta a kashe, kunnawa tayi dan Allah Allah take tayi kiran mominta taji abin da ake ciki, aikuwa tana kunnawa kiran momin nata na shigowa.
Kallon Hisham tayi tace, "Momi na kirana zan je na amsa mata", tana fad'in haka ta tashi ta shige bedroom.
Tana shiga ta d'aga wayar, tana d'agawa mominta tayi saurin cewa, "duk inda kike kiyi shiru dawowa gida yanzun nan, kar ki b'ata lokaci".
"A gaskiya hakan bazai yiwu ba dan ina Abuja, ya ake ciki mom da fatan dai an samu nasara"
Cike da tsantsar mamaki tace, "Abuja fa kika ce ?".
"Eh tabbas ina Abuja Mom, Hisham nayiwa rakiya".
"To ai da kin jira dawowata ga shi kin sa nayi wahalar banza, dan kin riga da k'etare sharad'in da boka ya ba mu".
"Mom wana sharad'i ne ?", ta tambaye ta a rud'e.Kwashe duk yarda suka yi da boka ta fad'a mata.
"Momi shi kenan daman Ruky tace idan muka dawo zata raka ni wajen wani bokanta", ta fad'i haka cikin yanayin damuwa.
"To yaushe zaku dawo ?"
"Gobe ko jibi zamu dawo".
"Ok Allah ya dawo da ku lafiya", tana fad'i haka suka katse wayar.Tana d'aga kanta suka had'a ido da Hisham tsaye k'ofar d'akin yana kallon ta...
Fatinku ce 😘😍
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 57 - 58
Dam zuciyarta ta buga cike take da fargabar kar dai ace ya ji hirarsu, amma dan tsabar iya makirci ta maze, cike da rangwad'a cikin tafiyar da ta san zai d'imauta shi cike da barikanci ta k'araso inda yake tsaye.Bakinta ta kai daidai kunnensa ta wani kashe cike da kissa da kisisina irin ta gogaggun mata da suka iya kashe zuciyar maza tace, "kai honey wannan kallon fa kamar yau ka fara ganina ?"
Kallon sa da take masa mai tsuma zuciya yasa ya kasa fad'in abin da yayi niyyar fad'a, jikinsa na k'yarma yayi mata wata runguma wacce saura kad'an ta shid'e, kamar mayuwancin zaki ya shiga mammatsa ko'ina a jikinta yana sumbatar ko'ina, jikinsa na tsuma ya d'auke ta sai kan gado, dan ji yayi bazai tab'a samun nutsuwa da kwanciya hankali ba sai ya je gare ta ya biya buk'atarsa.
Har kasa ta durk'usa ta gaida da Mamy da tarar zaune a falo cike da ladabi.Cike da fara'a fuskarta a washe ta amsa mata tare da cewa, "Lale marhabin da Humaira yau ke ce a gidan namu, yaya su Ummanki ?"
"Suna nan lafiya kalau Mamy ", ta amsa mata kanta a sunkuye cike da girmamawa.
"Masha Allah haka ake so, mutuniyar taki na cikin d'akinta tana shiryawa zasu fita ita da yayanta, ki shiga ki same ta".
"To Mamy", tana fad'in haka ta tashi cike da nutsuwa ta shiga d'akin.Bin bayanta da kallo Mamy tayi tana jinjina hankali da nutsuwarta a zuciyarta.
Sallama d'auke a bakinta ta shiga d'akin.Doka wani uban tsalle Zainab dake gaban dressing mirror tana kwalliya tayi cike da farin ciki ta tare ta rungume ta tana cewa, "oyoyo sannu da zuwa, baka ji yarda dad'i ya ziyarci zuciyata ba".
Murmushi mai sauti Humaira tayi tace, "to sake ni kar ki yada ni kin san ni ban da k'arfinki".tana fad'in haka suka sa dariya.
Bayan sun tsagaita dariyar Zainab tace, "bari naje na kawo miki abin motsa baki", tana fad'in haka ta fice daga d'akin.
Tana shiga d'akin ya shigo falon bayan sun gaisa yake tambayar ta Zainab, tace tana d'aki ita da k'awarta da ta kawo mata ziyara.Dai dai lokacin ta fito tana ganin sa tace, "bros ashe ka zo, ga shi kuma nayi babbar bak'uwa yaya kenan ko zamu bari sai gobe".
"Ta fito mu tafi tare man ai ba wani dad'ewa zamu yi ba", ya tsinci kansa da fad'in haka.
"Haba dai kawai ku bari sai gobe shi ya fi", Mamy ta fad'i ta fad'i haka
"To Mamy Allah ya kai mu goben lafiya"
"Ameen summa Ameen".
Bayan ta kai mata abin motsa baki ta d'an tab'a suka hau hirar jarrabawar da suke da ita gobe insha Allah a school.Zumbur ta tashi lokacin da ta kai dubanta ga agogon da ke manne a bangon d'akin.Tsuke fuska Zainab tayi tace, "ba dai tafiya zaki yi ba".
"Eh tafiya zan yi duba agogo ki gani yamma tayi sosai, ya kamata na tafi yanzu", ta fad'a tana gyaran mayafi ta.
"To shi Kenan zo mu je ku gaisa da yayana da nake ba ki labarinsa yana falo".
"To mu je ", tana fad'in haka suka fice daga d'akin
Zaune yake shi kad'ai a falon dan bada jimawa ba Mamy ta tashi ta haura sama, hankalinsa duk na kan k'ofar d'akin Zainab.Sassayan ajiyar zuciya yayi lokacin da ya ga fitowarsu.
"Bros ga aminiyata ku gaisa", Zainab ta fad'i haka.
D'ago kansa yayi daidai lokacin da ita ta d'ago nata kan, karaf sai suka had'a ido, dukkansu gabansu ne yayi mugun fad'uwa.Da sauri suka maida kansu k'asa.Kansu a sunkuye suka gaisa cike da girmamawa.
Suna gama gaisawa Mamy ta sauko daga sama, suka yi sallama tayi mata kyautar kud'i tace ta sayi kayan cosmetics, da k'yar ta karb'a sai da ta nuna mata b'acin ranta, direban gidan ta sa ya kai gida.
Wanka suka shiga tare bayan buk'atar zuciyarsu ta biya, suka fito suka hau shirin tafiya birthday d'in abokin nasu wanda za'a yi a Sharaton, lokacin k'arfe sha d'ayan dare.Suna gamawa suka fito suka nufi Sharaton shi da abokin nasu tare da budurwarsa, daman su kad'ai suka rage su da su Fahad da Ruky, duk sauran abokan watsewarsu tuni suka tafi.