Sashe 7
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin wannan yanayin ya taya ta suka kammala girkin cikin k'ank'anin lokaci.Wanka suka je suka yi bayan sun gama, cikin zumud'i suka shirya sun k'agu su je suyi tozali da baby da kuma mahaifiyarsa tare da fatan tarar da su cikin k'oshin lafiya.Fitowa suka yi zuwa harabar gidan bayan sun gama shiryawa dan komawa asibiti, hannunta rik'e da basket d'in abinci, shi kuma rik'e da kayan da suka san mai jegon zata bukata.Direba wanda ke zaune inda ya bar su suna hira, yayi saurin tashi ya tarbe su ya amshe kayan daga hannunsu, ya nufi parking space da su ya bud'e mota ya sa su a ciki, kana ya bud'e wajan zaman direba ya zauna, ganin suna isowa suka shiga bayan motar, tada motar yayi suka fice daga harabar gidan bayan maigadi ya wangale mu gate d'in gidan.
Suna isa asibiti suka fito suka shiga ciki bayan sun sallami direban akan ya koma gida zasu yi kiran sa ba sai yayi jiran su ba.Arba suka yi da likitan ya fito daga d'akin da take.Da sauri suka k'araso wajensa.
"Ta farka kuma bata tare da wata matsala", likita ya fad'i haka cike da fara'a, da k'arasowarsu wajensa.
"Alhamdullilahi mun godewa Allah", suka fad'i haka a tare zuciyarsu cike da tsantsar farin ciki.
"Yanzu zaku iya shiga wajenta, Allah ya k'ara musu lafiya, ya kuma raya babyn , ya albarkanci rayuwarsa".
"Ameen summa Ameen likita mun gode sosai", suka amsa masa a tare. kana suka shiga d'akin.
Suna shiga suka had'a ido da ita, dan idanunta na kan k'ofar d'akin.Cike da wani irin tsantsar farin ciki suka k'araso bakin gadon, ita kuwa kallon su kawai take fuskarta d'auke da murmushi.
"Sannu k'anwata Allah ya k'ara miki lafiya ke da babynmu, ya raya mana shi kan sunna", ta fad'i haka bayan ta rik'o hannunta cike da tsantsar kulawa.
Fad'ad'a murmushin da take yi tayi kana tace, "yauwa Auntyna", dubanta ta kai gare shi ji shi ma yana yi mata sannu fuskarsa d'auke da wani irin k'ayatattan murmurshi, amsa masa tayi ita ma fuskarta d'auke da murmushi.
Jaririn da ke kwance cikin gadon jarirai ne ya callara kuka, riga rigan d'aukan sa suka yi, ita tayi nasarar d'aukar sa, tsam- tsam ta rungume shi, tana jin wani irin matsanancin kaunar sa a zuciyar sa, shi kuwa tana d'aukan sa yayi shiru.
"Da alama fa kayi mana wayo dan ya fi kama da kai", ta fad'i haka cike da zolaya.
"Ai haka ne daman k'yaun d'a ya gaji mahaifinsa, ko ba haka ba ne ?
Gyad'a kanta tayi tace, "eh haka ne, amma fa ya fi ka k'yau".dukkansu murmusawa suka yi .
Taimaka mata tayi ta tashi ta zauna dan ta shayar da babyn.Bayan ta gama ba shi ta kamo hannunta tamke cikin nata kana tace, "Aunty kin ga wannan babyn na dank'a miki shi naki ne halak malak har abada, ba shi da uwa bayan ke ko bayan raina k...", da sauri ta sa hannu ta rufe bakinta tana girgiza kanta tace, "kar ki ce haka insha Allah tare zamu raini babynmu , dan haka ki bar cewa haka kin ji k'anwata", ta fad'i haka jikinta a matuk'ar sanyaye.
Cikin mutuwar jiki da alama shi ma maganarta ya shige shi yace, "ku bar maganar ki tashi ki taimaka mata taje ta wanko fuskarta, ta samo ta abinci", yana fad'in haka ya sa hannu ya karb'i babyn.
"Aunty ki bari zan iya shiga da kaina"
"A'a ki bari na taimaka miki", tana fad'in haka ta kama ta taimaka mata ta shiga band'akin, ita kuma ta tsaya bakin band'akin tana jiran fitowarta...
Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 37 - 38
Tsawon lokaci ta d'auka tana jiran ta amma bata fito ba, kara kunnanta jikin k'ofar band'akin, da sauri ta bud'e k'ofar tare da cusa kanta cikin band'akin, jin wani irin numfafashi na fitowa daga band'akin.
"Innalillahi wa'innailahir raji'un!" abin da ya fito daga bakinta Kenan da shigarta band'akin.A gigice ta k'arasa inda take yashe a kasan band'akin rik'e da cikinta sai murk'urkusawa take duk ta fice hayyacinta.Tsugunawa tayi gabanta ta sa hannu ta tallafo kanta zuciyarta cike da tsantsar tausayin tace, "subhanallahi cikinki ne ko, bari naje inyi kiran likita". tana fad'in haka da sauri ta tashi ta fice daga band'akin.
A k'ofar d'akin suka yi kacib'is da shi maigidan nasu da kuma likitan, domin yana jin ta furta "innalillahi wa'innaillahir raji'un"!, a gigice shi ma ya tashi a rud'e ya shiga band'akin.A matuk'ar rud'e ya juya dan kiran likita ganin halin da take ciki.
"Yauwa ku zo ga halin da take ciki, ayi sauri a bata taimakon gaggawa", ta fad'i haka a rud'e.
"Ku kwantar da hankalinki insha Allah zata samu lafiya", likatan ya fad'i haka kana ya juya ya kalli nurses da ke tsaye bayansu yace "ku shiga ku fito da ita", yana fad'i haka suka shiga band'akin.
Taimakon gaggawa suka shiga bata bayan an fito da ita daga band'akin, dan a sume nurses d'in suka fito da ita.Kimanin awanni hud'u suka d'auka, kafin da k'yar kafin su samu numfashinta ya dawo, su kuwa suna waje suna jiran abin da zai je ya dawo, addu'a kawai suke yi a ransu Allah ya ba ta lafiya, zuciyarsu cike take da tsantsar tausayin ta.
Dukkansu a tsorace suka tambayi lokacin da ya fito daga d'akin da cewa, "likita yaya dai jikin nata ?"
"Ku yi hak'uri kuma kwantar da hankalinku an shawo kan matsalar ta dawo hayyacinta, ita ce ma tace tana san ganin ku, amma ku kiyaye dan tana buk'atar hutu, don dai yanzu ta matsa ne da son ganin ku ne ".
"Kar ka damu insha Allah zamu kiyaye likita "suna fad'in haka suka shiga cikin d'akin.
Ba k'aramin tashi hankalinsu yayi ba ganin lokaci d'aya ta fice daga hayyacinta, dukkansu hawaye suka shiga zubarwa zuciyarsu cike da tsantsar tausayin ta.
Rik'o hannunta Khadija hawayen tausayin ta na kwaranya kan kuncinta, tace, "sannu k'anwata Allah ya ba ki lafiya".
"Yauwa Auntyna", tana fad'i haka kana jin muryarta zaka san tana jin jiki, f
tana sakar mata murmushi.
K'ara dad'a tamke hannunta tayi cikin nata tace, "Aunty ke 'yar uwa ce mai so na da gaskiya, sam baki rik'e ni a matsayin kishiya ba, tamkar k'anwarki da kuka fito ciki d'aya kika d'auke ni, tabbas samu abokiyar zama irinki a wannan zamanin sai an tona", d'an tsayawa tayi kana ta ci gaba da cewa, "Aunty na dank'a miki babynmu na mallaka miki shi, dan na san ko bayan raina zaki rik'e shi amana, dan yarda nake ji a jikina da k'yar idan z...", da sauri ta sa hannu ta rufe bakinta tana girgiza Kanta hawaye na zuba daga idanunta.
A hankali suka jiyo muryarsa idanunsa jajir dan shi ma kalamanta sun matuk'ar girgiza shi yana cewa, "ban san na k'ara jin haka daga bakinki, ai cuta ba ita ce mutuwa ba, da yardar Allah bazaki mutu yanz...", wani irin tari suka ji ya sark'e ta, sannu suka shiga yi mata cike da tsantsar tausayin ta.Ganin abin ya tsananta ne, Khadija ta tashi a guje ta fice daga d'akin dan kiran likita...
Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BAK'IN DARE da KUNGIYAR ASIRI daga shahararru hazik'an marubuta, Asmeenat Zeeyan da Halimatus Sadiya Muhammad (Leemat), cike suke da ilmantarwa, fad'akarwa da kuma nishad'antarwa, kar ku sake a ba ku labarin daddad'un litattafan nan.Gaba gaba dai brilliant, Allah ya k'ara d'aukaka ku ya kuma k'ara basira 🥰🥰🥰👍👍*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 39 - 40
Bata wani jima ba ta dawo d'akin tare da likitan.Tarar da shi suka yi mutuwar tsaye sai nanata kalmar innalillahi wa'innaillahir raji'in yake, domin tana fita ya ji tana salati, sai kuma ta ja shak'uwa mai k'arfi, shi ke nan rai yayi halinsa, tayi bankwana da duniya, idanunsa sun yi jajir.
Cewa yayi su fita ya duba ta, suna fita ya shiga duba ta sosai duk inda ya kamata ya duba sai da ya duba, jawo mayafin gadon yayi ya rufe fuskarta da shi dan ya tabbatar da rasuwarta cike da jimami.
Jiki a matuk'ar sanyaye ya fita wajensu.Tarar da su yayi zaune sun yi jugum jugum kowa da abin da yake rayawa a zuciyarsa, ita tana fatan samun lafiyarta, shi kuma yana yi mata fatan samun rahama wajen Allah, dan ya tabbatar da Allah yayi mata cikawa.
A tsorace ta mik'e tana tambayar sa "likita yaya jikin nata "
Girgiza kansa yayi tare da sa hannu ya share hawayen da suka soma zubo masa, "abin da nake so da ku shine ku yi tawakkali ga Allah, dan ta riga mu gidan gaskiya, addu'a kawai take buk'ata gare ku".
Ji tayi wasu zafafan hawaye na bin kumatunta, wayyo Allah shi kenan ta tafi ta bar duniya da abin da ke cikinta gaba d'aya.Wani irin kuka mai tsuma zuciya, ta zube a wajen.
Shi kuwa sa hannu yayi ya tayar da ita tsaye tare da rungumo ta jikinsa ya shiga rarrashin ta, shi kuwa likitan barin wajen yayi yana mai zubda hawaye, yana cewa "kiyi shiru ba kuka ya kamata kiyi ba kiji dai abin da likita yace, dan Haka addu'a ya kamata kiyi ba kuka ba".
A hankali ta d'ago kanta tana kallon sa tace, "ai dole nayi kuka, dan na tabbata nayi rashin abokiyar zama nagari mai halin kwarai", tana fad'in haka ta sake sa kuka tare da mayar da kanta kirjinsa.
Bayanta ya shiga bubbugawa ya ci gaba da rarrashin ta yana cewa, "tabbas na san da haka kawai daurewa nake, farin ciki d'aya da kalamatush-shahada ta cika".
"Alhamdullilahi na godewa Allah da ya sa wannan baiwar tasa ta zamo daga cikin bayinsa masu rabauta da rahamarsa, mu ma Allah ya sa mu cika da kalamatush-shahada idan tamu ta zo", ta fad'i haka tana zub da hawayen farin ciki.Shi kuwa amsawa yayi da Ameen summa Ameen...