Sashe 13
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Langawab'e kansa yayi yace, "dan Allah yi hak'uri na daina ce miki 'yar lukuta, kin ji 'yar k'anwata 'yar siririya", yana fad'a haka suka k'yalk'yale da dariya.
"Bari na koma Office yanzu kam hankalina ya d'an kwanta, fatana dai Allah ya sa ta aminta da ni".
"Insha Allah zata aminta da kai bros kar ka damu", sallama sukayi akan sai had'u a gida kamar yarda suka tsara, kana ya shiga motarsa ya ja bar harabar makaranta yana jin wani irin dad'i had'i da farin ciki a zuciyarsa.
A b'angaren su Latifa kuwa haka suka ci gaba da cashewa wajen birthday d'in, samari da 'yan mata sai tirka rawa suke, yayin da wasu ke zaune kan kujeru manne da juna suna shashancinsu, wasu kuwa kayan maye iri iri ne gabansu suna k'orawa.Sha biyu da rabi daidai Mr Dj ya bada announcement lokaci ne na yanka cake, kowa ya tsagaita abin da yake.Tare da budurwarsa suka k'araso manne da juna inda birthday cake d'in yake, wak'ar happy birthday sai tashi a wajen.Bayan Mr Dj yayi k'irga d'aya zuwa uku, da sauri budurwar tayi masa wata irin runguma ta baya, ta zuro hannunta ta d'auki 'yar wuk'ar da ake yanke cake d'in da ita, ta sa a hannunsa ta d'ora nata hannun akan nasa suka yanka cake d'in, suka ciyar da juna, sowa da ihu gayun da ke wajen suka sa, dan yarda suka ciyar da juna ya matuk'ar burge su.
Cashewa samari da 'yan mata suka ci gaba da yi, aka ci gaba da tikar rawa.Su Latifa ma ba'a bar su a baya ba, Hisham ya kama waist d'inta da hannu biyu suka hau rawa mai d'aukan hankali, nan kallo ya koma kansu, nan gayu suka shiga tafa musu ana sowa.Sai wajejen k'arfe d'aya da rabin dare aka tashi daga birthday d'in, a maimakon a nemi hanyar komawa gida, a'a yawancinsu kama d'aki suka yi suka shige ciki da 'yan matansu, suma su Latifa ba'a bar su a baya ba, kama d'aki sukayi suka shige ciki...
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 63 - 64
Bai dad'e da tafiya ba ta dawo fuskarta sam ba walwala, kana ganin ta zaka san ranta a matuk'ar b'ace yake.
Duban ta Zainab da alamun damuwa a fuskarta tace, "besty lafiya kuwa na gan ki cikin wannan yanayin ?"
Wani dogon tsaki ta ja cike da takaici tace, "Ashe Dr Balarabe haka halinsa yake ban sani ba".
Duban ta Zainab tayi tana zaro ido tace, "me ya faru ?, me yayi miki ?".
Wani gwauron numfashi ta ja kana tace, "baya ce na zo na same shi a Office d'insa ba, to daga can nake yanzu, lallai kai dai ka ga mutum kawai, tabbas na yarda mutum mugun ice besty", daidai nan lokacin komawa yayi, tashi suka yi suka bi sauran d'alibai suka koma class.
A wajen suka k'ara zama bayan su gama fito.Kallon ta Zainab tayi bayan su zauna tace, "kiyi sauri ki fad'a min dan ki sa ni cikin fargaba kafin direba ya zo".
Cike da tsantsar takaici bayan ta ja wani dogon numfashi ta ci gaba da cewa, "ina zama ya tashi daga inda yake zaune ya dawo ya zauna kusa da ni tare da zubo min mayun idanunsa, zabura nayi na tashi tsaye tare da ce mata sir me ye haka kuma.Lumshe idanu yayi ya bud'e kana yace min wai tun da ya gan ni ya kwad'aitu da ni, in amince masa komai nake so zai mallaka min, yana so na sosai a ransa, in dai har zan rink'a ba shi had'in kai, shi kuma yayi min alk'awarin duk abin da nake so kowacce irin buk'ata ce, shi dai fatansa na yarda da shi.Mutuwar tsaye kawai nayi zuciyata cike da tsantsar mamaki na k'asa ce masa komai, mik'ewa yayi ban ankara ba ya rungumo ni jikinsa, wata k'ara na saki gami da fizgewa a fusace na juyo nace masa daman haka halinsa yake, to ni Humaira na fi k'arfin abin da yake nufi da ni, sam bana cikin irin d'alibai da kake zato, dan haka kar k'ara gigin tab'a jikina", ina fad'in haka na juya na fice daga Office d'in raina ya kai k'ololuwar tashi, ina ji yana ta kirana amma nayi biris da shi nayi ficewata".
Flddo ido Zainab tayi cike da tsantsar mamaki tace, "lallai d'an adam mai wuyan gane hali, sam a haka bazaka d'auka haka halinsa yake ba, ashe a fili yake Musa a zuciya kuwa Fir'auna, Allah dai ya shirya masu hali irin nasa ya ganar da su gaskiya, ya kuma kare ki daga mugun nufinsa".
"Ameen summa Ameen".
"Kin ga direban ma ya iso", Zainab ta fad'i haka daidai lokacin da direban yayi parking gabansu.
"Maganar da kike zaki fad'a min sai gobe kenan".
"Eh sai gobe na fad'a miki duk da na so na fad'a miki yanzu".
"Ok Allah ya kai mu goben", tana fad'in haka suka tashi suka shiga motar, direba ya ja suka fice daga harabar makarantar.
Zainab na komawa gida ta zayyanawa Mamy komai.Kwarai Mamy tayi murna da farin ciki dan ta san Humaira da k'yawawan halayenta.
"Ba sai kin je ba an jima zan je na samu yaya mu tattauna akan maganar", Mamy ta fad'i haka cike da tsantsar farin ciki.
"To Mamy ni kuma zan iya zuwa gidansu yanzu ?", ta tambaye ta tana mai neman izinin ta.
"Eh zaki iya zuwa ki gaida min da mutanen gidan nasu".
"To Mamy zasu ji insha Allah", tana fad'in haka ta tashi ta shige d'akinta dan shiryawa...
*Pls kuyi manage da wannan, kwana biyu ina da uzurori ne, luv u all my fans 😘😍*
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*Inayiwa d'aukacin al'ummar Musulmai barka da Sallah, Allah ya maimaita mana ya nuna mana na bad'in bad'ad'a, aci nama sannu sannu fans dan tsaro ba tsoro ba 😂🤣🤣*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 65 - 66
Bata jima ba ta fito daman mayafi kawai ta shiga ta d'auka da handbag.Sallama tayiwa Mamy ta fita.Tana fita harabar gidan direba da ke zaune kusa da maigadi yayi saurin tashi da nufin ya kai ta, ta tare shi da cewa ya bari zata yi driving da kanta, ta isa inda motar ke fake ta shiga ta ja ta bar harabar gidan, shi kuma ya koma ya zauna kusa da maigadi suka ci gaba da hirar da suke.
Daidai k'ofar gidan tayi parking ta fito ta k'wank'wasa k'ofar da ke rufe, ta d'an d'auki lokaci tana k'wank'wasa k'ofar ba tare da an zo an bud'e ba, jimawa can taji muryar Humaira na cewa waye ?, amsa tayi da cewa ni ce besty, tana jin haka tayi saurin bud'ewa.
"Dan Allah besty kiyi hak'uri wanka nake yi, fitowata kenan kuma ba kowa a gidan kaya kawai na zura na zo na bud'e miki", Humaira tayi saurin fad'in haka lokacin da idanunta suka d'oru kan na Zainab.
Murmushi Zainab tayi tace, "kar ki damu besty ba komai wallahi", ita ma murmushi tayi ta kama hannunta suka shiga cikin gidan, suka shiga d'akinsu ita da Latifa.
Sai bayan sun zauna ta kalle ta sosai tace, "besty na dawo na fad'a miki maganar da nace zan fad'a miki ne, wato ba komai ba ne Yayana ne ya mato akanki, shine ya tuntub'e ni nace ya bari zanyi miki magana, yanzu ina san in ji ta bakinki, ke ma kin mato ne, ko da yake da alama ke ma kin mato dan na san yayana ba daga baya ba", ta fad'i haka cikin zolaya.
Fiddo idanunta tayi tace, "tab!, waya fad'i miki haka ?".
Girgiza kanta tayi tace, "a'a ba wanda ya fad'a min, amma ai labarin zuciya a tambayi fuska, ina lura da yanayinki lokacin da na ce ya mato akanki har da lumlumshe idanu saboda dad'in da ya mamaye zuciyarki"
"Hmmm!, to gaskiya fuskar tawa bata ba ki ainihin labarin da ke cikin zuciyata ba".
Maka mata hararaa tayi cikin wasa tace, "yarinya kar ki ce zaki ja mana aji fa, dan na san aji kawai kika ja mana amma tuni kika mato akanmu".
Girgiza kanta ta shiga yi tana cewa, "ba aji nake ja muku ba".
"To besty dan Allah yanzu mu aje wasa a gefe ki fad'a min gaskiyar abin da ke zuciyarki game da shi".
Ajiyar zuciya ta ja tace, "ki ban d'an lokaci zanyi tunani akai
Kallon ta tayi fuskarta na nuna rashin jin dad'i tace, "to amma dan Allah kar ki ja lokaci, dan a watan nan ake ce ayi komai", tana fad'in haka ta mik'e ta rataya jakarta tana cewa, "ni zan tafi insha Allah zai fad'a masa dan ni 'yar aike ce", juyawa tayi da nufin fita, da sauri Humaira ta kamo hannu rausayar da kanta tayi tace, "dan Allah kiyi hak'uri besty na san baki ji dad'in maganata ba, ba wai ina k'in Yayanmu bane, ina san dai nayi shawara ne tukun".
Juyowa tayi ta harare ta cikin wasa tace, "kya ce haka mana saboda nace bros ya mato akanki ne zaki wani ja mana aji, har da cewa wai sai kinyi tunani akai, a zatona ko albarkacina kya amince masa".
Murmushi mai sauti tayi tace, "besty badai mita ba, to kiyi hak'uri ki bar mitar haka insha Allah zuwa gobe zan sanar da ke, kin ji besty d'ina".
Wata hararar ta k'ara maka mata tace, "au ni ce mai mita, yo ai gaskiya na fad'a dan na tabbatar ke ma kin riga da kin mato kan bros, amma ina koma zan sanar da shi da ba ki amince ba tun wuri ya nemi wata".
A zabure ta kalle ta tace, "ni fa ban ce haka ba cewa nayi sai nayi tunani tukun".
Zainab bata lokacin da fashe da dariya ba har da rik'e ciki, sai da tayi mai isar ta kana ta kalle ta tace, "hmmm!, su besty ana so ana kaiwa kasuwa", tana fad'in haka dukkansu suka sa dariya.
"Ni zan tafi kuma insha Allah zai sanar da shi abin da kika ce", ta fad'i haka bayan sun tsagaita dariyar.Tare suka flta dan yi mata rakiya.