Sashe 12
Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tarar da gayu suka yi a wajen sun gaji da had'uwa, kowanne ka gani yana wane wannan.Kowa ji yake da kansa, wajen yayi kyau sosai, kowa ka gani da abokiyar watsewarsa, an ware music ana ta taka rawa.Suna shiga wajen gayu suka shiga ihu da sowa da tafi.Haka dai aka ci gaba da cashewa a wajen birthday d'in, wasu na rawa wasu na manne da 'yan matansu suna ta shashancinsu.
Kwance yake kan faffad'an gadonsa ya kasa bacci, yana rufe idonsa fuskarta yayin da suka had'a ido ke masa gizo.Lokaci guda soyayyar yarinyar ta mamaye zuciyata da jikinsa gaba d'aya, har bai san yarda zai sarrafa ta ba.Fatansa dai Allah ya sa zuciyarta ba mallakin wani ba ce, ce dan zuciyarsa zata iya mutuwa murus idan hakan ya kasance...
Fatinku ce 😘😍
*🅱️RILLIANT WRITE RS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 59 - 60
Daren ranar kam kwana yayi ba baccin kirki tunaninta ya cunkushe masa zuciya.Wata iriyar zazzafar soyayyarta yake ji a zuciyarsa, wacce bai tab'a sanin yarda take a zuci ba, bai tab'a sanin ciwon da take wa mutum a zuci ba, sai a sannan rana da ya had'u da macen da ya tabbatar idan bai mallake ta ba sai ya shiga matsala, ciwon san ta bazai tab'a warkewa ba a zuciyarsa ba.Tun da yake soyayya da mata iri iri bai tab'a sanin ma menene soyayyar ba, sai yau ya san ainihin abin da ake nufi da so, lokacin da ciwon so yayi masa kamun kazar kuku.Ba shakka Allah maji rok'on bayinsa ya amsa masa rok'onsa, shi yasa ya k'addara had'uwarsu tare da dasa masa zazzafar kaunar ta cikin zuciyarsa lokaci d'aya.
Washe gari bai tashi ba sai wajejen tara saura kasancewar sai bayan ya dawo daga sallar Asubahi wani samu damar yin bacci.Da hanzari ya mik'e yana salati cikin sauri yaje yayi wanka dan daman Allah Allah yake gari ya waye yaje ya samu mahaifansa ya sanar da su da ya samu matar aure.Yana fitowa ya shirya cikin wata shadda ruwan kwai wacce tayi masa k'yau ba na wasa ba, ya fito ya nufi b'angaren mahaifansa.Tarar da su yayi zaune kan dining table suna breakfast.Gaida su yayi ta amsa masa cike da kulawa, shi kuwa mahaifinsa ba yabo ba fallasa ya amsa masa.Ba dan ya so ba ya ja d'aya cikin kujerun dining ya zauna, ji yayi baya sha'awar cin komai, dan ya san bazata tab'a lamunta ya fita ba alhalin bai cin komai ba.Ruwan tea kawai ya had'a ba tare da ya sa madara ba.
"Badai ruwan shayi kawai zaka sha ba ?", ta fad'i haka ganin ya tea kawai ya had'a yana sha.
Langawab'e kansa yayi kamar zaiyi kuka yace, "Dan Allah kar ki ce sai na ci wani abu, shayin kawai ya ishe ni".
"Naji amma ka daure ka ci ko yaya ne ka ji my son", ta fad'i haka cike da tsantsar kulawa.
Wainar kwai da plaintain ta zuba masa cikin plate ta ajiye gabansa tana cewa, "yi sauri ki cin ye duka ka ga ban sa maka da yawa ba", badan ya so ba baya san k'ara yi mata musu ya soma ci, d'an tsakura kawai yayi yace ya k'oshi.Dad d'insa kuwa ko uffan bai k'ara cewa ba tun da ya amsa gaisuwarsa, ya ci gaba da breakfast d'insa, ko ta kansa bai k'ara bi ba.
Mik'ewa yayi bayan ya kammala yana cewa, "ni zan fita dan ina da appointment k'arfe goma", yana fad'in haka ya nufi hanyar fita ba tare da ya tankawa Abdul da ke cewa Allah ya kiyaye hanya, yi yayi kamar bai ji ba.Tashi tayi ta bi bayansa dan yi masa rakiya kamar yarda ta saba kullum.
Tarar da shi tayi hannunsa tallafe da hab'arsa bayan ta dawo daga rakiyar tasa.Janye hannun tayi tace, "bana ce kar ka sake ka sa damuwa cikin zuciyarka ba ?"
Wata naunauyan ajiyar zuciya ya sauke yace, "dole na damu dan naga alama har yanzu bai sauko daga fushi da yake da ni", ya fad'i haka cike da tsantsar damuwa
Numfashi ta ja bayan ta gama sauraran sa tace, "ba komai ya sa ya daina sakar maka fuska ba sai dan ka shiga taitayin ka ka d'au maganarsa da mihimmanci, kai dai kayi k'ok'arin yin yarda ya ce kafin lokacin da ya ba ka".
Wani gwauron numfashi ya ja yace, "wallahi na d'auki maganarsa da matuk'ar mihammanci, shi yasa Allah ya taimake ni ya had'a ni da matar aurena jiya, daman ina da niyyar in sanar da ku idan muka kammala breakfast".
Murmushi tayi cike da tsantsar farin ciki tace, "Alhamdullilahi madalla wacece wannan mai sa'a da tayi nasarar rikita zuciyar santalelen son d'ina lokaci d'aya", ta fad'i haka cikin barkwanci.
Sa hannayensa yayi ya rufe fuskarsa yace, "har ki sa naji kunya mummy".
Dariya ta sa tana cewa, "aî gaskiya na fad'a, my son santatalen k'yakyawa san kowa k'in wanda ya rasa", tana fad'in haka shi ma ya sa dariya.
"To ina sauraran ka ba ni amsar tambayata", ta fad'i haka bayan ta tsagaita dariyar da take.
"K'awar little ce jiya ta zo gidan wajenta na gan ta".
"Au ka ce k'awar k'anwarka ce ma, ka ga kenan komai zai zo cikin sauk'i, insha Allah idan dad d'in ya dawo zan sanar da shi, Allah dai ya tabbatar da alkairi", ta fad'i haka cike da tsantsar farin ciki.
"Ameen summa Ameen, bari na tashi na tafi lokaci na ja, sai na dawo mum", yana fad'in haka ya mik'e tsaye.Allah ya kiyaye hanya tayi masa, yana amsawa ya nufi hanyar fita zuciyarsa fal da farin cikin komai zai daidaita tsakaninsa da dad d'insa, alak'arsu ta dawo tamkar da...
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers)
*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 61 - 62
Zaune yake a k'asaitaccen Office d'insa da tulin takardu gabansa ya kasa tabuka komai ba, saboda tunaninta da yayi kanai kanai a zuciyarsa, yana jin san ta na k'ara bin duk jijiyoyin jikinsa, a d'an ganin ta da yayi jiya ta tafi da imaninsa, ji yayi bai da muradi da ya wuce ya k'ara d'ora idanunsa akanta.Nan take ya tuna da Fadila 'yar uncle Hassan da ke Kaduna ce wato twin brother d'in Mamy, da ta mace kan san sa bata da wani buri da ya wuce ta mallake shi a matsayin mijin aure.Tunawa yayi da yanayin fuskarta lokacin da ya furta bazai iya auran ta ba, ta kalle shi ta rik'e kanta da hannu hawaye na zuba daga idanunta.Bai damu ba dan bai san soyayya ba a lokacin, bai san abin da take ji a zuciyarta ba sai yanzu ya san dalilin da ya sa Fadila ta kama kanta da hannu biyu.
Rik'e kansa kamar yarda Fadilan tayi, ya samu kansa da fad'in, "na ga ta kaina ni Abdul, Allah na rok'e ka ka sa ta aminta da ni, ka sa mata tsantsar sona cikin zuciyarta, kamar yarda ka sa nata cikin zuciyata farat d'aya", ya fad'i haka cike da tausayin kansa.Wayarsa ya d'auka ya kira lambar Zainab.
"Kina School ne ina san ganin ki ?", ya tambaye ta bayan sun gaisa.
"Eh bros ina School yanzun nan muka fito daga exams", ta ba shi amsa da fad'in haka.
"Ok zan zo na same ki a can yanzun nan", yana fad'in haka ya katse wayar.Cikin nauyin jiki ya tashi ya fita daga Office d'insa zuwa harabar Companyn ya ja motarsa ya nufi Bayero University (B.U.K).
Suna zaune k'ark'ashin wata bishiya suna hira akan exams d'in da suka fito, ya shigo makarantar parking d'in had'add'iyar motarsa yayi gabansu, nan fa idanun d'aliba mata da maza da ke harabar makaranta suka dawo kan motar wacce ke ta zuba walk'iya.Sai da ya shafe mintina yana kallon Humaira cike da tsantsar so da kauna da ke motar ba'a ganin wanda ke ciki sai shi ya ga mutum.Wata ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke lokacin da Zainab ta d'an k'wank'wasa k'ofar motar, kana ya fito daga motar.Kan Humaira na k'asa ta gaida shi cike da girmamawa, amsawa yayi fuskar d'auke da wani k'ayatattan murmushi.
Mik'ewa tayi bayan sun gama gaisawa ta kalli Zainab tace, "Ina zuwa besty", tana fad'in haka tayi saurin barin wajen, tayi haka ne dan ta ba su waje su gana.
Gyaran murya Zainab tayi ganin yarda ya bi bayanta da wani irin kallo sai lumlumshe idanunsa yake, jiki a sanyaye ya juyo ya kalle ta yana sosa k'eya.
"Bros da alama fa ka mato fa, wannan kallo haka",, ta fad'i haka cike da zolaya.
"Aikuwa kamar ki san tuni na mato wallahi", yana fad'in haka suka sa dariya.
Gimtse dariyar yayi yace, "Serious da gaske nake na mato kan besty d'inki, lokaci d'aya ta sace min zuciya san ta ya hana ni sukuni, a dalilin haka nace ina san ganin ki, ina san yanzu ki fad'a min komai game da ita, ina sauraran ki".
Cike da tsantsar farin ciki tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha dan murna tace, "amma bros baka ji yarda dad'i ya ziyarci zuciyata ba, dan besty akwai da hak'uri da ladabi, ta san mutuncin kanta da na mutane, bros ina mai tabbatar maka idan har ka mallaki besty a matsayin matar aure, to ina maka albishir da samu mace *WAYAYYA* mai tarbiyya insha Allah bazaka yi nadamar auren ta ba".
Murmushi yayi yace, "daman tun da na gan ta na fahimci akwai nutsuwa a tare da ita, yanzu ina san ki zo kiyiwa su dad bayani kamar yarda kika min, dan a nemo min aurenta a gidansu, dan bana san a ja lokaci ban mallake ta ba fatana dai kar ya kasance akwai maganar wani akanta, ko dai na jira dawowar ta na fallasa mata abin da ke zuciyata game da ita"
"Kar ka damu bros ka yi tafiyar ki ka bar komai a hannunsa, kuma insha Allah ba maganar kowa akanta", ta fad'i haka tana jinjina san bestyn d'inta da ya kamu da shi farat d'aya.
"Yauwa little 'yar k'anwata 'yar luk'uta kiyi iyakar k'ok'arinki ganin ki kafa gwamnatin bros d'inki cikin zuciyarta".
Zumb'uro bakinta tayi tace, "na ma fasa tun da kace min 'yar lukuta".