← Book details Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 41 - 42

A hankali ya sake ta kana ya ja ta suka zauna, sa hannu yayi cikin aljihun rigarsa ya ciro wayarsa.Mahaifinsa yayi kira ya sanar da shi rasuwar.

"Innalillahi wa'innailahir raji'un", Mahaifin nasa ya ta maimaitawa, kana ya ci gaba da cewa, "Allahu Akbar, kullun nafsin za'ikatul maut, Allah ya jikan ta yayi mata rahama ya sa ta huta, ya sa Aljannarsa makomarta", ya fad'i haka cike da jimami.

"Ameen summa Ameen Abba".

"Zan yi kiran Abbanka (wato Mahaifin marigayiyar) na sanar da shi ba sai kayi kiran sa ba"

"To Abba ", ya fad'i haka cikin girmamawa.Suna katse wayar yayi kiran k'anin nasa.

Zaune suke a had'ad'an falonsu suna yiwa twins d'insu dariya kan musun da suke tun da suka ji haihuwar yayarsu, cikin nishad'i da annushuwa cike da tsantsar farin ciki.

Abbansu ne ya tsagaita dariyar da yake tare da gyaran murya, dukkansu shiru suka yi suka maida hankalinsu gare shi", haba my cute twins naga duk kamanninku d'aya, menene na musu akan da wanda baby yake kama daga cikinku"

"Haba Abba ni fa na san da ni yake kama, dan na fi ta kama da Yaya", Hussaini ya fad'i haka cike da hak'ik'ancewa.

"To shine aka ce maka da shi babyn yake kama, to ni na ga ma dukkaninku kamanninku d'aya, to menene kuma na musun", Ummansu ta fad'i haka cikin dariya.

"Haka ne kuwa Umma, ni fa Umma Allah Allah nake gari ya waye mu tafi Kano lafiya (da ke su a Kaduna suke da zama), nayi tozali da my cute baby", Hassana ta fad'i haka cike tsantsar farin ciki.Wayar Abbansu da tayi ringing ce ta katse hirar tasu, da sauri ya d'auka ganin sunan wanda ke yawo kan screen d'in wayar.

Shiru ne ya biyo baya bayan sun gama gaisawa."Yaya ya naji ka yi shiru", ya fad'i haka jin ya d'au mintina bai ce komai ba".

Wani gwauron numfashi ya ja yace, "dama ina san nayi maka wata tambaye wacce nake so ka ba ni amsa".

"Ina sauraran ka Yaya insha Allahu idan na sani zan fad'a maka".

"Kai ne wani ya ba ka aron kaya to sai ya zo karb'an kayansa, zaka ba shi ko zaka hana shi ?"

"Haba dai Yaya zan ba shi man tun na san ba nawa ba ne"

"To haka nake so ku yi tawakkali ku rungumi k'addara, Allah da ya ba ku Zainab ya karb'i abarsa, Allah dai ya bamu hak'uri da juriyar rashin ta", yana fad'i haka ya katse wayar cike da jimami, zuciyarsa cike da tsantsar tausayin d'an uwa, dan ya san irin matsanancin kaunar da suke yiwa 'yar tasu.

Shi kuwa rintse idanunsa yayi ba sai nanata "innalillahi wa'innailahir raji'un yake.Cike da tsoro matsananci da fargaba dukkansu suka yi riga rigen tambayar sa, "Me ya faru ?"

Cike da daurewa yana k'ok'arin matse hawayen da ke san zubo masa ya sanar da su, bayan ya nusar da su tare da yi musu nasiha mai ratsa zuciya, akan su yi tawakkali.Ai yana gama fad'a twins suka zube kasa suna kuka, su kuwa iyayen nasu wasu zafafan hawayen suka shiga zubarwa.Cike da juriya dan shi ma k'arfin hali kawai yake, ya rik'o su zuwa jikinsa ya shiga rarrashin su.Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru.

Kallon su yayi idanunsa jajir cikin taushin murya yace, "ku yi shiru kukan ya isa haka kar wanda ya k'ara, addu'a take buk'ata gare mu", cikin dauriya ya fad'i haka dan shi ma ji yake kamar ya rushe da kukan.A daren kam ba wanda ya rintsa daga cikinsu, raba dare suka yi suna nema mata gafara wajen Ubangiji (S.W.T).Washe gari k'arfe shida daidai suka yi sammakon zuwa Kano.

Tafiyar awa biyu ne ya kawo su Kano, tarar da gidan suka yi cike da jama'a 'yan uwa da abokan arziki, dan kafin safiya labarin rasuwar ya gama kewaye gari, har an had'a ta.Haka dai aka mik'a ta makwancinta na gaskiya bayan sun yi mata addu'ar sallama kark'ashin rakiyar d'imbin al'ummar musulmai...

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 43 - 44

Zaune take a falo tare da d'imbin 'yan uwa da abokan arziki cikin alhini da jimamin wannan rashin da suka yi.Mahaifiyar marigayiyar ita ma na zaune tana k'ok'arin b'oye tashin hankalin da damuwar da take ciki, ta girgiza kwarai da gaske, ba k'aramin k'ok'ari tayi ba wajen danne firgici da razanin da ta shiga.Ita ma Khadija haka yake wajenta, lokacin da ta ga an fito da ita za'a kai ta makwancinta na gaskiya.Hussaina kuwa kasa b'oye nata tayi, sai da ta rushe da kuka tana cewa, "wayyo shi kenan Aunty ta tafi ta bar ni bazan k'ara ganin ta ba, way...", Ummanta ce tayi saurin rufe bakinta da hannunta tana girgiza mata kai tace, "ambatan Allah ne ya kamata ya fito daga bakinki ba wannan furucin ba, addu'a ya kamata kiyi mata ba kuka ba, dan ita mamaci ke buk'ata", ci gaba da rarrashin ta tayi tana tunatar da ita ayoyi da hadisai na tawakkali da hak'uri.

Kallon su Khadija take cike da tausayi mai tsanani, ko shakka babu dole Hussaina ce tayi kukan, sun shak'u matuk'a suna kaunar junansu sosai, su kad'ai Allah ya bawa iyayensu, Marigayiyar ita ce ta fari sai su twins d'in.Tun tasowarsu take musu wani irin kulawa da tattali har kawo girmansu, tana matuk'ar ji da su tamkar tsoka d'aya a miya, sam bata san abin da zai tab'a su, tabbas wannan ya isa dalili mai k'arfi da zai sa tayi kuka mai yawan gaske na rashin 'yar uwa Yayarsu mai tsananin kaunar su.

A cikin kwanakin bakwan da aka yi ana amsar ta'aziyya, kullum gidan cike yake da jama'a.A kwana bakwan mahaifan marigayiyar suka koma amma ban da Hussaina, Khadija ce ta nemi alfarmar da su bar ta har ayi arba'i, nan take suka amince jin ta suke tamkar d'iyarsu Zainab.Ita kuwa Hussaina taji dad'in haka sosai, dan sam bata san tayi nesa da AbdulHakeem (sunan da aka sakawa babyn).

A ranar arba'in da suka zo suka so komawa tare da ita, amma ganin ta shiga tsantsar damuwa suka ce ta zauna ta taya Auntynta rainon babynsu.Nan take wani irin farin ciki ya kama ta, nan take damuwar tata ta gushe, jin bazata yi nesa da babynta ba, wanda ta d'auki san duniya ta d'ora masa, sam bata san tayi nesa da shi.

Haka dai zamanta ya ci gaba da kasancewa a gidan, suna nuna masa wani irin kulawa da tattali, tana dawowa daga school rainonsa ke dawo hannunta, sam bata san abin da zai tab'a shi.Haka suka ci gaba da rayuwa tare, tana matuk'a girmama Khadija ta d'auke ta tamkar marigayiyaYayarta, kamar yarda ita ma ta d'auke ta tamkar k'anwata.Kullum cikin yiwa Marigayiyar addu'a suke, tare da sauke mata Alqur'ani mai girma duk shekara.Shi kuwa gina masallaci yayi da niyyar ya zama Sadakatul Jariya gare ta, Khadija ce ta ba shi shawarar haka (Allah na rok'e ka had'a mu da kishiya mai k'yakkyawar zuciya irin ta Khadija, Ameen summa Ameen).

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*This page is for u my Suruka Mugirat Musa marubuciyar LAHANI, Allah ya k'ara basira da d'aukaka, ina yin ki my Suruka irin sosai d'in nan 🥰😍👍*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 45 - 46

Haka rayuwarsu ta ci gaba da kasancewa suna tattali da ririta shi, hakan bai lalata shi ba, domin yaro ne mai hankali gami da nutsuwa.Haka ya girma a cikin wannan ingantacciyar rayuwa, yana samun cikakkiyar kulawa daga kowannensu, duk abin da yake muddin abin ya dace sai sun nema a ba shi, duk da ririta shi da suke bai sa sun sangarta shi ba, suna k'ok'arin kwab'ar sa a duk lokacin da yayi abin da bai dace ba.

Yana da shekara goma a duniya, Allah buwayi gagara misali, mai yin komai a duk lokacin da ya so, ya bawa Hajiya Khadija juna biyu.Sadak'a da salloli suka rink'a yi na godiya, haka ma Hussaina (wacce tuni tayi aure, aminin Daddyn Abdul take aure har da d'anta d'aya) da duk dangi tare da masoyansu su taya su farin ciki.Cikin na da wata tara ta haifo sankaceceyar 'yarta k'yakkyawar gaske, sak marigayiya Zainab, shi kuwa Abdul cike yake da murnar an haifo masa baby ya samu k'anwa.Ranar suna babyn ta ci sunan marigayiya wato Zainab, wanda hakan zab'in Khadija ne.Hakan ya matuk'ar farantawa Hussaina da iyayenta rai, suka k'ara ganin k'ima da mutuncinta.Wani irin so da tattali babyn take samu daga wajen Abdul da Hussaina da kuma sauran dangi musamman iyayen marigayiya, dake ba wani nisa tsananinsu hasalima a unguwa d'aya suke, wajen kullum sai Hussain ta zo ganin babyn, tana matuk'ar tattalin ta tare da nuna mata zallar kauna, sam bata san ta ji kukanta.

Watanni sun gushe, shekaru sun tafi, Abdul ya kai shekaru goma sha takwas, ita kuma Zainab wacce suke kira da little shekara rta takwas, tuni little ta saba da Hussaina wacce suke kira da Mamy sun shak'u da ita sosai, tun tana zuwa gidanta tayi kwana biyu har ta kai ta koma can da zama,haka Hajiya Khadija ta had'o mata dukkanin kayayyakinta ta rik'e su tare da d'anta, lokacin shekararsa goma sha hud'u.

Lokacin ya gama Secondary ya nacewa Abbansa shi ya fi san ya fita waje yayi karatunsa na Jami'a.Hak'uri ya ba shi akan ya fi san yayi karatunsa anan dan baya san yayi nesa da shi.Bayan sun tashi daga falon da daddare, Mummy wato Hajiya Khadija bayan sun koma d'aki, sun yi komai kamar kullum kafin sun kwanta, ta kalle shi tace, "ni kam Abban Abdul ina san muyi magana kan karatun Abdul ", tana fad'in haka tayi shiru tana sauraran abin da yace.

"Ina sauraran ki ya kuma kika yi shiru", ya fad'i haka jin tayi shiru.
Chapter 8 · 0% Book details