← Book details Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 15

Sashe 10

Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin tarar ta yayi da cewa, "dan Allah daga rana ita yau kar ki k'ara kira na, bana san wani abu ya k'ara had'a mu", yana fad'in haka ya katse wayar ba tare da ya jira abin da zata ce ba.Yana katse wayar yayi blocked lambarta tare da duk lambobin watsatstsun 'yan matansa, kana ya ci gaba da shiryawa...

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 51 - 52

Latifa bin wayarta da ido tayi lokacin da ta fad'i daga hannunta, maganarsa ta matuk'ar rud'a ta, ji tayi zuciyarta kamar zata buga."na shiga uku wallahi bazan iya rabuwa da kai ba har abada", tana fad'in haka ta sunkuya ta d'auki wayar dake yare a kasan d'akin ta k'ara trying d'in lambarsa.Hankalinta tashe ta juya ta fice daga d'akin bazata tab'a samu ba

Ko ta kan Mum d'inta da ke jiran a falonta bata bi ta fice daga gidan, ta bazama neman sa a gidansa tun da bazata same shi a waya ba.Hana ta shiga gidan Maigadi n yayi tare da ce mata ya fita kuma ya gargad'e shi kada ya bari wata mace ta sake shigar masa gida sai da izininsa.

Cike da tsantsar bakin ciki da damuwa ta juya ta bar gidan.Cikin wannan yanayi ta isa gida.Mominta na zauna da waya a hannunta tana k'ok'arin kiran ta, ta shigo ta fad'a jikinta tare da sakin kuka tana fad'in, "wayyo Allah na ga ta kaina Mum".

"Ke lafiya Latifa na gan ki haka ?", me ya same ki ?, a rikice ta jero mata wad'annan magana.Kasa magana tayi sai kuka take.

"Kiyi shiru haka ki fad'a min abin da ya sa ki kuka", tana fad'in haka tayi shiru ta kwashe duk abin da ya faru ta fad'a mata.

"Amman wannan yaron anyi mara mutunci d'an iska banza, shi kenan ya ruguza mana shirinmu", Momi ta fad'i ta fad'i haka a harzuk'e bayan ta gama sauraran ta.

"Momi dan Allah ki taimake ni kar ya rabu ni, idan ya rabu da ni mutuwa zan yi, bazan iya rayuwa babu shi ba".

Bayanta ta shiga bubbugawa tana cewa, "ki kwantar da hankalinki yau ba sai gobe zanje mu koma wajen boka yayi abin da zai sa hankalinsa ya dawo kanki, ya zamo bai da kwanciyar hankali muddin banyi tozali da ke ba, ke dai ki kwantar da hankalinki ina mai tabbatar miki sai ya dawo gare ki ya durk'usa ya ba ki hak'uri, dan haka share hawayenki ki daina kuka"

Wata doguwar ajiyar zuciya ta yi tace, "idan ko kika yi min haka min haka kin gama min komai, dan zuciyarta na bala'in san sa".

"Ke dai ki sha kuruminki ki d'auka tamkar kin gama mallakar sa, sai ya zamo miki tamkar rak'umi da akala, sai kin juya shi kamar yarda ake juya waina, yanzu ki tashi ki je kiyi breakfast d'in da ba ki tsaya kin yi ba, dan zumud'in zuwa wajensa, ni yanzun nan ma zan tashi na tafi, dan sam bana san muyi sanya", tana fad'in haka ta d'auki mayafinta wanda shi da babu duk d'aya ne, ta fice daga falon...

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 53 - 54

Tagumi ta zabga bayan ficewar mominta, sam bazata iya rayuwa babu shi ba, ji take idan ta rasa shi mutuwa zata yi, lokaci d'aya ya rushe soyayyar Hisham (matashin da zuciyarta ke ciwon so fiye da kowanne namiji), nan take ya kafa gwamnatinsa.

Rurin da wayarta keyi ne ya katse mata tunanin da take, kamar bazata d'aga ba, sai ta jure ta d'aga".

"Lafiya kuwa muna ta neman ki a waya bamu samun ki besty ?", tana d'agawa wacce tayi kiran nata tayi mata wannan tambayar.

"Maganar bata waya ba ce besty, ki zo ki same ni a gida, mayi maganar", ta fad'i haka cikin yanayin damuwa.

"Ok ga ni nan yanzun nan kuwa", tana fad'in haka suka katse wayar.

Ba'a jima sosai ba ta shigo falon ba ko sallama, cikin lalatar shiga kanta ya sha attachement, kana ganin ta ka ga gogaggiyar 'yar bariki wacce idonta suka bud'e a harkar.Tana tsaye kanta kallon ta kawai take ganin sam bata ankara da shigowarta ba, dan tsabar nisan da tayi a fannin soyayya, kamar akansa ta fara sanin d'a namiji.

Zama tayi kusa da ita ta zuba mata ido ganin har yanzu bata farga ba, karkad'a 'yan yatsunta tayi kusa da fuskarta, firgigit tayi tare da sauke tagumin da tayi tana cewa, "yaushe kika zo ?", a sanyaye tayi maganar kamar ba bestynta ba, wacce indai zasu ga juna a guje da ihu zasu rungumi juna suna murna.

"Kin dilmiya tunani ta yaya zaki san lokacin da na zo, besty wai me ke damun ki haka, tun jiya Hisham ke neman ki a waya yana san ganin ki baya samun ki, shi ne ya zo ya same ni yana tambaya ta abin da ke faruwa da ke.Nace masa ban da masaniya, dan ni ma nayi kiran ki ban same ki ba, shine yace mu zo gidanku mu ga ko lafiya, yanzu haka suna waje suna jiran mu zamu yi musu rakiya zuwa Abuja".

Wata doguwar ajiyar zuciya tayi kana tace, "hmmm!, soyayyar guy d'in da muka had'u da shi a birthday d'in saurayin pinky ke wahalar min da zuciya, ahalin yanzu shi zuciyata ke ciwon so da zumud'in mallaka, amma ya nisanta da ni yanzu ban san yarda zanyi da rayuwata ba muddin bai dawo gare ni ba", tana fad'in haka ta sa kuka.

"Haba besty kar ki ba da ni man, yanzu kan d'a namiji kike asarar hawayenki, kamar ba *wayayyar mace*, ai ni ban ga d'a namijin da zan bari soyayyarsa ta wahalar da ni, tuni zanyi maganin komai, dan ni d'in nan bata wasa ba ce, ni fa duk abin da nasa gaba bana fasawa sai naga bayansa sam bana karaya, yanzu ki daina kukan ki tashi kije ki gyara fuskarki mu tafi kar su gaji da jira, ina mai tabbatar miki idan muka dawo zanyi miki maganin komai, sai ya dawo gare ki yana kuka yana ba ki hak'uri"

"A gaskiya ba inda zan iya zuwa yanzu kuma Momi...".

Bata bari ta k'arasa ba ta tare ta da cewa, "please ki bar komai sai mun dawo, nayi miki alk'awari sai na shiga duk inda zan shiga dan ganin biyan buk'atanki, ke da kiyi sauri ki tashi mu tafi, bamu da lokacin magana yanzu"

"To tashi muje na gyara fuskar tawa", tana fad'in haka suka tashi suka fice daga falon.

Wani gwauron numfashi Humaira ta ja ke da kitchen tana kachaniyar d'ora abincin rana.A kullum cikin yi musu addu'a take da Allah ya ganar da su babu abin da ya gagari Ubangiji (S.W.T), insha Allahu zai amsa mata addu'arta tun da shi maji rok'on bayinsa ne.Cikin yanayin damuwa ta ci gaba da girkin da take, zuciyarta cike da takaicin irin rayuwar gidansu..

*Pls ku ci gaba da manage insha Allah duk lokacin da na samu dama zanyi typing fiye da haka, na gode sosai da kulawarku fans,, Ummu Auwal, Hassanan Maska, Maman Samhat, da duk sauran fans d'ina, luv u all*😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 55 - 56

Sai da ta shiga band'akin ta wanko fuskarta, a gaugauce ta yi make up, suka fice daga d'akin.Tafiya suke cikin taku d'aid'ai cike da yanga kamar suna tausayin k'asar da suke takawa, zo ka ga yarda Fahad (saurayin Ruky wato k'awar Latifa) da ke zaune cikin mota mazaunin di
reba tana ta walk'iya can d'an gaba da gidan ya lalace wajen kallon su.

Waiwayowa yayi ya kalli Hisham wanda ke kishingid'e a gidan baya yace, "Kai mutumina ga gimbiyar nan fa,. lek'a ka ga takun da take.

Ajiyar zuciya mai sanyi yayi bayan ya lek'o suna had'a ido wad'anda k'arasowarsu kenan,
da sauri ya bud'e mata k'ofar motar, tana shiga ya rufe k'ofar tare da zuge gilasan motar.

"Saurara malam dawowa zaka yi nan ka yi tuk'in zamu dawo baya ni da Ruky tausa nake so tayi min", Fahad ya fad'i haka cike da zolaya.

"Please ka yi hak'uri ka bar ni ka bar ni na ji d'umin babyn nan tawa, ka tausaya min nayi missing d'inta sosai kwana biyun da nayi ban ji d'uminta ba", yana fad'in haka jikinsa na tsuma ya shiga kissing d'in ko'ina a jikinta.Biye masa Latifa tayi dan ya san yarda zai k'warewa mace duk iya barikinta, amma sam bai kamo k'afar gwarzonta ba, shi d'in na daban ne a zuciyarta.

K'yalk'yale da dariya irin tasu ta gogaggun 'yan duniya Fahad yayi, ya fisgi motar a guje suka bar wajen.

Mominta bata zarce ko'ina ba sai gidan aminiyarta Hajiya Rabi ta k'are da cewa, "yanzu so nake mu koma wajen bokan yayi abin da zai sa hankalinsa zai dawo kanta, ya zamo baya da kwanciyar hankali har sai ya zo gare ta".

Numfashi Hajiya Rabi ta sauke bayan ta gama sauraran ta tace, "hakan zai yi wuya, ki manta da sharad'in aikin ne amma bari mu gwada sa'armu watak'il idan muka koma mu samu mafita", tana fad'in haka ta tashi suka tafi.

Gurfane suke gaban boka bayan sun gama rattabo masa komai tare da buk'atarsu.Kallon su yayi yana gwalalo idanunsa bayan ya gama surk'ullensa yace, "bazan b'oye muku ba zaiyi wuya asiri yayi tasiri akansa, saboda kaifin addu'ar da ke tare da shi, amma ga wannan ku tabbatar a yau d'in nan ta sa wannan k'wallin sun had'a ido da shi, hakan na faruwa shi kenan buk'atarku zata biya", sa hannu tayi ta karb'a daga hannunsa, suka tashi suka nufi hanyar komawa gida.

Wajejen Sallar La'asar ta dawo gida Humaira kawai ta tarar a gidan, ta gama girki dawowarta take jira, tana san taje gidansu wata aminiyarta wacce tayiwa alk'awarin kawo mata ziyara yau.Neman ta a waya ta shiga yi, amma wayar na ta ringing ba'a d'auka ba.Haka dai tayi ta kiran ta bata d'agawa, daga bisani ma kashe wayar akayi gabad'aya...

Fatinku ce 😘😍
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
Chapter 10 · 0% Book details