← Book details Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Wayayyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A gaskiya ni ma son ina ma ina bayanta akan wannan maganar, dole ne ka nemo matar aure ka yi aure", dad d'insa saukowarsa kenan daga upstairs ya fad'i haka.

Sunkuyar da kansa yayi yana share zufa, zuciyarsa a cunkushe dan shi bai tashi yin aure yanzu ba.

K'arasowa yayi ya zauna ya kalle shi fuskarsa a d'aure yace, "na ba ka nan da wata d'aya ka kawo min wacce ka aura, idan kana san ci gaba da zama lafiya da ni da ganin walwalata, fakat na gama magana", yana fad'i haka ya tashi ya haura sama ba tare da ya saurari abin da zai ce ba.

"Ka ga ni dad d'inka ma baya bayanka, dan haka kayi k'ok'arin bin umarninsa".

"To amma dan Allah ki rok'e shi ya k'ara min lokaci kan lokacin da ya fad'a", ya fad'i haka a marairaice.

"Kar ka damu yanzu nan zanje na rarrashe shi insha Allah zai k'ara maka", tana fad'in haka ta tashi ta haura sama.Zuciyarsa a cunkushe ya tashi ya fice daga falon.

*Waye Abdul*

Muje zuwa next page d'in.

Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 29 - 30

AbdulHakeem Ibrahim Ahmad shine cikakken sunansa, mahaifinsa minister ne, amma ya sauka yanzu haka kasuwanci yake yi, hamshak'in d'an kasuwa ne, wanda ake damawa da shi a harkar kasuwanci a dukkan k'asar nan gaba d'aya.Matansa biyu, Hajiya Khadija uwargida sai kuma Hajiya Zainab, wacce ta rasu bayan ta haifi Abdul.

Marigayiya Zainab ita ce ta haifi Abdul, washe garin haihuwarsa ta rasu bayan ta dank'awa Hajiya Khadija shi k tace ta bar mata shi halak malak ko bayan ranta kar ta sake ya san ba ita ta haife shi ba, dan ta san zata rik'e shi amana tare da ba shi ingantacciyar tarbiyya.A daren ranan ta amsa kiran mahaliccinta (Allahu Akbar, kullun nafsin za'ikatul maut, Allah ya kyautata namu zuwan, ya kuma sa mu cika da imani, Ameen summa Ameen).Mutuwarta ta matuk'ar tab'a Hajiya Khadija, dan ta tabbatar ta rasa abokiyar zama tagari, tsawon zamansu ba'a tab'a jin kansu ba suna zamansu lafiya tare da fahimtar juna gwanin sha'awa, dan dukkanninsu *wayayyun mata* ne, masu halin kwarai wad'anda suka san rayuwa.Sam ba k'yashi ko bak'in ciki, ba kishin hauka irin na wad'ansu ballagazazzun mata masu rasa imaninsu saboda kishin banzansu (kalubale gare mu 'yan uwa mata, mu yi koyi da ummuhatil Muminina wato matan Annabin rahama (S.A.W), wajen yin halatacciyar kishi, mu daina haramtacciyar kishi mai sa ku saki hanya, daga baya kuma ya kai ku gidan nadama, Allah ya sa mu dace ya kuma ganar da mu gaskiya, Ameen).

Haka ta raina shi ta kuma dama ita Allah bai ba ta haihuwaba, hasalima saboda rashin haihuwarta danginsa suka masa akan ya k'ara aure ko ya samu haihuwa.Badan ya so ba suka aura masa Zainab wacce take cousin d'insa, mahaifinsa da nata uwa d'aya uba d'aya, dan ba dama yayi musu da su.Hajiya Khadija ce kasancewata *wayayyar mace* mai aji wacce ta san ta kan rayuwa, sam bata nuna damuwarta ba, ta saki ranta sam bata nuna alamun kishi ko haushi ba, hakan ba k'aramin k'ima da daraja ya jawo mata wajen danginsa har da shi kansa maigidan.Bayan auren amarya ta tare a gidan, sukayi zamansu lafiya kasancewa ita ma Zainab akwai hankali ga nutsuwa da sanin ya kamata...

Pls kuyi manage da wannan, luv u all my fans.

Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*Dedicated to u dear sister Hafsat Arab (Mimsqueen), ina taya ki murnar kammala book d'inki *NAILA ('Yar baiwa), Allah ya ba ki ladar fad'akarwa ya kuma yafe miki kurakuren da kikayi a ciki, ina yin ki dear irin sosai d'in nan ❤️❤️👍*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 31 - 32

Haka suka ci gaba da rayuwa hankalinsu kwance kansu a had'e, tare suke girki ko da ba girkin d'ayansu bane, 'yan aiki ne ke yi musu sauran aikace - aikacen gida.Rayuwa suke mai cike da burgewa, babu wanda zai kalle su yace kishiyoyi ne, saboda yarda suka had'e kai suke zamansu lafiya cike da fahimtar juna.Shi kuwa maigidan har wani k'iba ya k'ara da cikar kamala to ya samu nutsuwa, kullum cikin godiya yake ga Allah da ya azurta da shi da mata nagari masu biyayya da sanin ya kamata.A lokacin Allah yake ta k'ara bud'a masa ta kowanne fanni, a kuma lokacin ya samu nasarar zama minister, ya kuma samu shahara sosai.

Tsawon shekaru uku suna zaune amma ko b'atan wata Zainab bata tab'a yi ba.A shekara ta ukun ya biyawa gabad'ayansu kujerar aikin Hajj suka ziyarci d'akin Allah, a can suka dage da rok'on Allah da ya azurta su da haihuwa mai albarka.Allah maji rok'on bayinsa ya amsa rok'on su, basu fi wata uku da dawowa ba, Allah ya bawa Hajiya Zainab ciki.Murna da farin ciki wajen bayin Allah kamar me, suka rink'a sadak'a da salloli suna godewa Allah.

Daga Maigidan har Hajiya Khadija tattalin ta suke yi da ririta ta bata yin aikin komai, saboda bin umarnin likita wanda yace kar su bari tayi aikin wahala cikin zai iya b'arewa.Ba tare da nuna k'yashi ko takaici ba Hajiya Khadija ta d'auki ragamar yin duk hidimar gidan, kullum cikin sanya mata albarka yake, tare k'ara ganin k'imarta, da kuma wani irin so da kaunar ta yake k'ara bin dukkan jijiyoyin jikinsa, ta k'ara siye zuciyarsa.Tabbas samu mace ta kwarai mai zuciya irin tata a yanzu sai an tona, wacce ta san hakk'in aure da soyayya, fatansa a kullum Allah ya bata haihuwa ita ma, ta samu d'anta na kanta.

Cikin nada wata tara ta fara nakud'a a wata safiyar Juma'a, cikin gaggawa suka d'auki zuwa asibiti sai fatan saukarta lafiya suke.Tun k'arfen goman safe har wajejen k'arfe ukun rana bata haihu ba, duk ta galab'aita.Ganin haka aka shirya yi mata Cs wanda da k'yar Alhaji Ibrahim ya amince yasa hannu cikin tsantsar tashin hankali.Cikin ikon Allah ana shigar da ita d'akin tiyata ta ja wani nishi sai ga kan d'a ya fito, da sauri likitar yasa hannu ya cire shi tare da godewa Allah.Mik'awa nurses babyn yayi dan su kimtsa shi, ya shiga duba mamar.Taimakon gaggawa ya shiga bata ganin ta sume, da k'yar da taimakon Allah ya samu numfashinta ya dawo.Fita yayi dan ya sanar da su abin da ke faruwa.

Tarar da su zaune jugum jugum cikin tsantsar damuwa, zuciyarsu cike da fargaba.Suna ganin fitowar likitar dukkansu suka sa masa na mujiya zuciyarsa cike da fargabar abin da zai fito daga bakinsa.

Dukkansu wani naunauyan ajiyar zuciya suka sauke bayan ya fad'a musu da ta sauka lafiya ba'a kai ga yi mata Cs ba, amma yanzu ta samu bacci nan da awa biyu zata iya farka insha Allah, dan tana buk'atar hutu.Cike da tsantsar farin ciki suka koma gida dan samar mata abin da zata ci idan ta farka...

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of Freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*Inayiwa d'aukacin al'ummar musulmai barka da Sallah, Allah ya karb'i ibadunmu, ya kuma sa muna cikin 'yantattun bayinsa, Ameen summa Ameen*

*This page is for u 'yan tagwayena Hassan da Hussaini, Allah ya k'aro muku shekaru masu albarka, ya sa ci gaba da yalwar arziki, lafiya da kuma kwanciyar hankali su ta wanzuwa a rayuwarku, Ameen ya rabbi*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 33 - 34

Zuciyarsu fal da tsantsar farin ciki suka isa gida, suna parking ta fito ta shige ciki, shi kuwa tsayawa yayi wajan direban da maigidan gidan da suka tarar zaune suna hira ya sanar da su k'aruwar da ya samu tare da yi musu k'yautar kud'i dan tsananin farin ciki.Barka sukayi cikin suna masu cewa, Allah ya raya kan suna ya albarkanci rayuwar baby, ya kuma kare shi daga sharrin mutum da aljan, ya kuma biya bukatunsa na duniya da lahira cike da farin ciki.Amsa musu yayi cikin walwala cike da jin dad'in addu'arsu.

Tana shiga falon ta cire gyalenta ta shiga kitchen.Tana cikin girki ya shigo amma bata ankara ba, hankalinta duk yana kan girkin da take.

"Duk wannan zumud'in murnar an zama uwa ne".

Fuskarta d'auke da k'ayatattan murmushi ta juyo ta kalle shi, tsaye yake bakin k'ofar kitchen d'in tace, "aikuwa dai duk ita ce, ai ni yau farin cikin da nake ciki baya fad'uwa", ta k'arasa fad'in haka cikin farin ciki mara misaltuwa.

Wani gwauran numfashi ya ja kana k'araso inda take, wani runguma yayi mata yana jin wani irin so da kaunar ta na k'ara ratsa shi, wani irin dad'i ne ke ratsa shi godiya kawai yake ga Allah da ya arzurta da mata tagari *wayayya*, tabbas ya san yayi dace da mace abar alfahari ga duk d'a namiji, tabbas ita k'arshe ce halayenta abin koyi ne.

D'ago fuskarta yayi suka kalli juna cike da tsantsar kaunar juna, lumshe idanunsa cike da shaukin ta yace, "Khadija tabbas ke mace ce abar tak'ama da alfahari ga duk d'a namiji, ni kam a gidan duniya Allah ya gama yi min komai sai dai fatan dacewa a ranar Alk'iyama", amsawa tayi da "Ameen".

"Yanzu bari na taya ki girki mu samu mu koma kan lokaci", ci gaba da girkin dan dama yana taya su girkinsu, suna hirarsu cike da tsantsar so da kauna cikin nishad'i da annushuwa...

Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*

{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}

*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*

*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Page 35 - 36
Chapter 6 · 0% Book details