← Book details Wani Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 11

Sashe 9

Wani Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

akan ta dawo gida.fadeela ce mai cewa sameera kiyi haquri ki koma.duk abinda ya faru ga bawa Allah ya riga ya kaddara zai faru dashi. Sameera ta yarda ta biyo mu misalin karfe 3:20pm muka iso zariya.kannai su adnan suma sun nuna farin cikin su sosai da suka ga sameera.washe gari kamar yadda na saba zuwa gaida ummana da dady na naga sameera.tachi wata uwar kwalliya tsayawa kawai nayi ina kallon ta.data fahimchi ina kallo sannan tazo ta duqa ta gaidani sannan ta rokeni gafara na yafe mata akan maganganun data fadi man.na che mata ai babu komai. Allah ya yafe mana baki daya.nan har nake to nan ta nace saura yanzuh ma ki gudu.sai tayi wani murmushi tace kaji yayana da wata magana..mukai wasa da dariya na shiga falo na gaida su dady. Bayan na gaisa dasu. sai dady yake ceman my son inaso zanyi wata magana da kai.bai gama rufe bakin saba sai naji wayata na kururuwa. Da alama wani ne ke kirana.ina dubawa naga polina ce kawar manasa.ke kirana.ina amsa kiran akace munan asibiti manasa ta haihuwa ta sami budurwa.kayi sauri kazo ka biya kudi za'a salla Alhamdulillah nace.to ganin tafe.na fada masu dady cewa manasa ta haihu suma sunyi farin ciki ummace tace bari na dauko hijabi na mu tafi tare. Ina zuwa falo na fadi ma sameera cewa manasa ta haihu tayi man murna dayi ma jaririyayar addua Allah rayata.amman naga alama sameera na cikin damuwa amman bata nuna man ba.muna zuwa asibiti na biya kudi muka dawo gida nayi ma jaririya huduba. Na sa mata suna sameeeeera. Nayi dana sanin fadi ma manasa sunan jaririyaR bayan nayi ma ta huduba.nace ma. manasa sameera na sa ma ta suna.tace baka isa ba wallahy dole ka chanza mata huduba.wallahy da kasa ma yar"ta sunan wannan jakar yarinyar gwanda ta mutu na huta. lokacin ne na tsinke manasa da mari ina ce mata na lura ke mahaukaciya ce to bari kije wannan sunan shi nayi niyyar sama yar"ta yanzuh tunda kin haihu ni daidai dake ne.na fice daga dakinta na barta tana sharar kuka. Lokacin da naje daki na naji jaririyar tana ta kuka.amman manasa taki daukar ta sai uban kuka take. Na leko nace mata manasa kiji tsoron Allah wannan jaririyar bata son komai ba amman kina zalintarta.lokachin ne ta dauke ta ba bata mama. Sannan nace mata idan ta gama da ita zamuyi wata magana da ita. Tana gama bata mama jaririyar tayi barchi sai tazo daki na ta sameni.na fara bata labarin sameeera tunda farko har karshe. Da Alama manasa taji tausayin sameera lokacin da na gama bata labarin naga manasa tana share hawaye ta rokeni gafara na yafe mata laifunkan data yiman. sannan tace tanason taga sameera.na kira sameera tazo gidana tayi ma manasa barka.zata tafi manasa tace ta tsaya. manasa taba sameera haquri akan abinda ya faru.suka yafe ma juna.da daddare ina kwance manasa tazo dakina taceman mijina inaso na rokeka wata Alfarma don Allah ka auri sameera. Wallahy nayi ma alkawarin zamu zaune lafiya da ita. Nayi farin ciki kwarai da manasa tace na auri.sameera safiya nayi naje gaida su dady kamar yadda na saba. sannan na fadi mai abinda manasa tace.shima yayi farin ciki sosai.yace daman ranar da matar ka ta haihu maganar da nake so nayi ma kenan.sai aka kiraka. Amman yanxuh bazan yanke hukunchi ba sai naji daga sameera idan zata aureka. Dady ne yasa umma ta tambayi sameera idan tana sona.tana tambayar tache eh tana sona kumah zata aure ni.bayan sati 1 da haihuwar manasa Akayi suna.aka sa ma yarinyar sameera......... Sameera tayi farin ciki da taji sunan ta nasa ma yar"ta.sameera ta suwo kaya masu yawa ta kawo ma takwararta. Bayan anyi suna kowa ya watse. Aka sa mana ranar aure nida sameera.lokachin da akasa yayi akashe shagali aka kawo sameera gida.na tara su nayi masu nasiha akan su zauna lafiya.nace ke sameera kece karama kiyi ma manasa biyayya.ke kuma manasa ki wa Allah ku zauna lafiya kada wani ya zalinchin wani. Haka suka zaune lafiya. sameera aunty take ce ma manasa.bayan shekara 1 da "yan watanni sameera ta haifa man yaro namiji.na saka masa sunan dady na SULAIMAN amman Abba ake kiransa.gaskiyaba karamin farinci nayi ba da naga mata na suna zaune lafiya babu rigima babu tashin hankali. Muka chi gaba da rayuwa mai inganci muka manta da abun ya faru A baya. KARSHEN LABARIN KENAN WANI DARASI KUKA SAMA GAME DA WANNAN LABARIN? Kuma wani korafi zakuyi game da wannan labarin domin mu gyara, zaku iya fata tanan ko kuma ku turo mun da sakon ku ta nomber ta 07033020404 Admin
Chapter 9 · 0% Book details