← Book details Wani Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 11

Sashe 10

Wani Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..........CIKIN DARE { Part 12 }........... Rahul yayi
matukar mamaki da Sameera ta zageshi A guje
ya Debi motarsa Izuwa gida Yana shiga gida Sai
Hajiya tace Rahul Ya kashigo gidannan ranka
A6ace meyasa meka? Rahul yayi shuru Hankalin
Hajiya ya tashi Ta kara cewa Rahul Don Allah
kafada man Waya 6ata maka rai? Rahul cikin
fushi yake cewa Hajiya Wai Hajiya yanzu kamar
Sameera Ita Ce zata zageni a tsakiyar Kasuwa
Hajiya tace Sameeran Ce tazageka? Yace Eh
Hajiya! Hajiya Tace kaje ka dakko wayar Redio
Idan tadawo kai mata Kafirin duka Rahul yaje ya
samu Wayar Redio Manasa ma Itama tasamo
wayar Redio Wai harda ita za'a daka Sameera
saboda tazagar mata Yayanta, A falo suke tsaye
suna jiranta Manasa da tadawo gida tana zuwa
harabar Gidan Taji gabanta yana fadi, Kamar
tajuya ta fita gidan amma hakanan ta tashiga
gidan Tana zuwa falo Manasa tayi saurin kulle
kofar falon Sameera ta zaro Ido Tace Manasa
Lafiya? Manasa ta wanketa da mari Rahul yacire
hijabin dake jikin Sameera kukaci gaba da
dukanta Sai da sukaimata ti6is Suka far fasa
Mata jiki Ko ina ajikinta ya fashe Fuskarta Ce
kawai batayi komai ba Saboda itama tana rife
fuskar Sameera tayi kuka kamar ranta ya fita
Bayan sun gama bugunta 3 Awos Bata iya tashi
Sameera da rarrafe takai dakinta Jikinta gaba
daya duk bakarfi Kankace haka ciwon kai mai
karfi Ya kamata zazza6i Idonta biyu Ita kanta
Tana tausaya wa kanta Gari nawayewa Rahul ya
shigo yacewa Sameera Ke Ga kayana can dana
Manasa Dana Hajiya Ki wanke Mana Kitabbatar
da kin wanke su kafin Mu dawo daga Jos Cikin
sauri Sameera ta Amsa Saboda gudun bugu, Yaja
tsaki ya fita, CIKIN DAREN bacci yaki yuwuwa
man Saboda tunanin Sameera Shin tunanin
danakeyi Wane hali Sameera take ciki kuma Ina
take Ammsar Dana kasa Samu kenan, Gari na
wayewa nayi wanka Nadau Key din motata Naje
gidan su Dady Ina zuwa nagaida momy na da
Abba Sannan Nasanar dasu Yadda mukayi da
Abban Manasa nacewa naturo Magabata na da
ayi Maganar Aurena da manasa Dady yayi farin
ciki Itama mahaifiya ta Buda bakin Momy Sai
tace dannan Wlh harga Allah naso ka Auri
Sameera Allah nedai bai nufaba yanzu nata Raye
ko bata Raye Wallahu A alamu Sai dady yace
man yaushe Iyayen Manasa sukace katuro
mahaifan ka Sai nace mai Dady 2week suka Ce
Dady yace Allah ubangiji ya kaimu lokacin Momy
tace Ameen, Jingine nake ajikin motata a kofar
super market din dake Tudun wada Zaria Tunanin
Sameera ya hanani walwala da Kwanciyar hankali
Ni Sai naga kamar 6atar Sameera batazana Ce ga
Rayuwa ta Ina tsaye nayi tagumi Sai ga wata
kyakykyawar Yarinya taci kwalliya Tazo tasameni
tayi man Sallama, Salamu alaika? Na6ata rai
nace mata Wa'alaiki salamu, Sai tace naga
Malam naga kamar kana cikin damuwa kozan
tayaka fira? Sai nasha kunu Na daure fuska Nace
mata Dan Allah malama kirabu dani kona Ce maki
Ina Son mutun yataya ni fira ne? 6ace man
dagani ko kuma nayi maki wula kanci, Sai tayi
murmushi tace Allah ya baka hakuri Sai munsake
haduwa Natabbata idan kadaina fushi to zaka
saurare ni Saboda ni kyakykyawa Ce, Sai nayi
tsaki Naja motata izuwa gida, Ranar da Su Dady
suka shirya zasu Bauchi zuwa kar6o aure na
Sameera ji tayi gabanta nafadi kamar wani Abu
zai sameta Su dady suka isa Bauchi Amma su
Kansu sunji ajikinsu kamar zasu ga Sameera a
bauchi Saboda suna isa Bauchi tunanin Sameera
ne kawai ke yawo a zuciyar su, Ita kanta
Sameera Baccin data danyi na mintoci Har
mafalki tayi wai sun hadu dasu dady Da mom da
kuma ni Lokacin Da muka isa harabar gidan su
Manasa Kowanne Acikinmu gabanshi bugawa
yake Muna Isa Falon Kawai Sai naga,,,,,, mu hadu
a part 13 anjima
n gidan su
Manasa Sai Mukaga Manasa Tafito ban daki Sai
kunya ta kamata A guje tatafi dakinta Sai nacewa
dady Wannan Wadda taruga Itace Manasa Sai
dady yayi dariya Hajiya Ce taje tacewa Sameera
Kada tasake Tafito Kicin din indai tasan bata
gama Abincin ba Sameera ta Amsa dato Muna
zaune Sai ga Abban Manasa ya shigo suka gaisa
da Mahaifana ni kuma Natashi natafi dakin
Manasa A wannan zuwan da mukai gidan su Su
Manasa Shine Aka gama Komai har sukasa Ranar
Aurena da Manasa Wata daya ne akasa Saboda
Dady Yana so yatashi kasar England Har Muka
gama komai Muka tafi Sameera batasan Abinda
ya faru ba Sai bayan wuce Sameera ta gama girki
Sannan tasamu damar fitowa Daga kicin tana
zuwa falo Sai taji Ana Maganar Dame dame ya
kamata ayi A daurin Auren Manasa Da
Muhammad Abdulhadi Sai taji gabanta ya fadi
har tanayiwa Manasa murnar Saranta da akayi
Manasa Cikin Fushi ta iya Amsawa Saboda
tatsani Manasa sosai Sameera ahankali cikin
kasala ta tatafi Dakinta Tana zuwa dakinta
tazauna tayi tagumi Sai Taji sallamar Wani yaro
An aiko shi ya kirata, Yana shigowa Inda Manasa
take Yace mata Sameera kizo ana kiranki Awaje
Sai tasha kunu Tace wake kirana?.Sai yaron yace
Wani mutimine Tana cikin fadin haka Sai Ga
hajiya tashigo Dakin tana fadin Dan ubanki kitashi
kije Abokin Rahul ne yake kiranki Idan baki jeba
Rahul Zaici Ubanki kuwa, Sameera da sauri
tatashi tatafi Saboda Tsoron Rahul datake yi,
Tana zuwa gum matashin dake kiranta Mai suna
Bala Sai tayi mai Sallama Sai ya amsa mata tare
dayin murmushi Sai tace malam Don girman allah
karabu dani wllh akwai Wanda make so Buda
bakin Bala Sayyace Waye kike so Sai tace
Inarunka dole Sai kaji sunansa? Sai yace a'a
Amma don girman allah Kitai maka kifada Man
Sai tace mai Sunansa Abdul-ahad Sai bala ya
zaro ido yace Wanda zai auri Manasar Shine kike
so? Sameera tace don Allah karufaman Asiri wlh
bashi bane Wannan nanine daban kuma Ai anayin
suna Iri daya Sai yace Hakane Amma wlh Koki
bar garinnan konace wa Rahul Saurayin Manasa
Shikike so, A guje Sameera ta shige gida Saboda
taji bala yace zai gayawa Rahul shiyasa Sameera
tayanke Shawar Barin gidan Sameera tana zuwa
daret tana nufa Dakinta Ta Hado kayanta Duka
Tasa acikin Leda Sai da ta fahimci falon Bakowa
Sannan Tayo waje da gudu .Sai mai gadi ya
tareta yace Mata Sameera Nasan kina Shan
Wuya acikin gidannan Garama ki gudu Ni kuma
zan taya ki da Addu'a Sameera a tsorace tace
mai Nagode tafita da gudu Ashe Bala wasa yake
mata Shikanshi baya jin dadin dukan da Rahul
yake mata, Sameera Tana zuwa tasha Tasamu
wani mai kudi Taroshi alfarma daya tai maka
mata da kudin mota Zuwa Zaria city Mutiminnan
Dubu 10,000 Ya bata Saboda tausaya mata da
yayi Ganin yadda tazo A gigice, Ina zaune Dady
Ya kirani Bayan mungaisa Sayyace man My son
Yau wata daya kenan dagama gidajena na
Kaduna Nawa da naka Don kada Gidan da kake
ciki nasiyar dashi Da Wanda mu muke ciki don
haka gobe kashirya da Sassafe Nasa azo man da
Tirela ta kwashe kayanmu duka Sai naji dadi
amma tsoran danayi Karmu bar gidan kuma yaza
mana Sameera tadawo gidan nemanmu gashi
dady yace kada Wanda ya fada makowa Inda
zamu zauna A Kaduna Gari nawayewa Tirela Tazo
ta kwashe kayanmu duka A wunin muka gama
Kwashe kayanmu Muka koma Kaduna Su dady
Suka zauna A Tudun wada ta Kaduna Ni kuma
Nazauna a Kawo A gidan dazan zauna Nida
Amaryata Sameera, Satinmu Daya da komawa
Sameera Bayan tabar gidan su Rahul Gidan wata
kawarta taje A jos mai suna Fadeela Isma'il Satin
ta ukku A gun Fadeela dayake ta bata duk
Labarin Abunda ya faru da ita Sameera tayi
matukar Tausaya mata Sosai Shiyasa har bata so
Sameera tatafi Watarana tace ma Sameera Ya
kamata muje Zaria Kudaidai ta da Iyayenki da
kuma Baffan Saboda kisamu kiyi Aure kinsan
Yanzu zaman aure shiyafi komai Dadi Lokacin Da
Sameera Sukazo Zaria sukatarar da muntashi
Adaidai wannan Lokacin Ake Daura Aurena Da
Manasa, Sameera tayi kuka sosai Hakanan ta
hakura ta koma Jos sukaci gaba da zama da
Fadeela, Bayan aurena abokai Kowa ya watse
Aduniya banda iyayena Babu Wanda nake son
gani Sai matata Manasa Manasa tana Mani son
Da bata ta6a yiwa wani ba Shekararmu daya da
wata biyu Manasa tasamu Ciki Wanda ya kai
munzalin haihuwa Watarana zani office Manasa
tarakoni Izuwa harabar gidana Sai nashafa mata
cikin ta nace Insha allahu Kafin nadawo Sai dai
naji Anyo man Waya ace kin haihu Sai tayi
nurmushi tace Ameen Sai nasunbaceta na ja
motata nayi gaba,saneera kuwa Sai Alokacin ta
kara wayewa haduwarta da fadeela ta koya mata
Kwalliya Da salon tafiya Kai idan baka san
Sameera ba Sai karantse kace 'yar shugaban
kasace Watarana Sameera taje Super market Sai
ta hadu da Polina Polina tayi matukar far in ciki
da taga Sameera Bayan rungume Polina tace
Sameera wllh Kinyi kyau ko Gomna Ai yaganki
dole ya kyasa Sai polina tace wa Sameera
Kishirya kizo muje Kaduna gun Manasa Wata
kawatace wadda muka hadu a bauchi Jikin
Sameera yayi sanyi Sai taba Polina labarin
Zawanta bauchi Polina tatausaya mata Sai
tacewa Sameera karki damu ai yanzu kinfi karfin
Manasa tata6aki barinma mujinta yaganki Ai kau
Dole shima ya kyasa Sai sukai dariya Sukayan Ke
shawarar Gobe da safe misalin karfe shida zasu
wuce Kaduna Saboda basaso sukwana Sai
Sameera tacewa polina kinsan Inda Manasan Tayi
Aure? polina tace Naje gidansu aka bani Address
Din gidan Ammace man Tana da ciki haihuwa yau
ko gobe Ahaka suka rabu akan gobe zasu hadu
Sai suwuce Kaduna, Gari nawayewa Sukakama
hanyar zuwa Kaduna Misalin karfe Ukku suka Isa
Kaduna Sai kai sa'a sukaga Gidan su manasan
Ananne Sameera taji gabanta nafadi Suna zuwan
falon Manasa Sai Sameera taci karo da Makeken
hotona wanda muka Dauka Da Manasa Ahotan
kamar zanyi magana Hankalin Sameera yayi
muguntashi,
Chapter 10 · 0% Book details