← Book details Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun tuni yayi mata wuri na musamman arayuwa gaba dayansu birgeni sukeyi kuma yusuf yana son hawwa fiye da tunanin mai karatu haka itama hawwa anata haukan na kuriciya kawai yan uwan taka ne, cikin karfin hali mami tace my own son ina son kazama namiji tsayayye bana son ka kara zubar da hawayenka akan matarka wadda itace zabinka bazan so inga mace tana sanya yarona kuka ba gsky bazan lamunta ba sbd haka kada in kara ganin haka my son.cikin yanayin damuwa ya amsa da to mami insha Allahu na bari amma mami ina son hawwa kowa ma ya yasani amma ummah kullum nuna mani take zata iya rabani da hawwa kuma ni a tunanina babu wanda ya dace da ita kamar ni indai har tana son kwanciyar hankalin mu ni gsky bazan iya hkra da ita ba itace mace ta farko dana ji ina kauna tun ban san cewa sonta nakeyi ba sbd haka ina ftn zama da ita arayuwata na har abada.

Kallon ikon Allah umar yakeyi masa tare da tausaya abokin nasa don ya daina bashi mamaki tausayi yake bashi wanda tun tuni ya fada tarkon son hawwa amma yanayi da irin taurin kai irin na abokin nasa yasa yakasa tantance hakan, duba da yanda yanmata ke bibiyarsa amma yana avoiding dinsu lallai so daban ne Allah bamu masoyan gasky Amin.mami ce ta ka tse mas ushirun su wanda kowa da abunda yake kitsawa karka damu yusuf ummanka tafi kowa son zamanka da hawwa don na tabbatar babu wanda zata sallama ma kowa hawwa idan ba kai ba don haka ka kwantar da hankalinka babu wata matsala insha Allahu umar ya nisa "yace hakane mami nima abunda nake nuna masa abi komi a hankali haka dai suka ci gaba da maganganunsu da mami da cewar sun bar mata komi tayi masu jagora daga karshe suka tashi suka nufi part din yusuf da yake mallakinsa ne a gidan.

Sbd shima dan gidan ne suna shiga ko ina a gyare tsab ga kamshi yana tashi ko ina na kusuwar dakin sbd mami ba daga baya ba wurin tsabta koda yusuf ba zaune yake ba amma kullum cikin gyaran shi take ko ta gyara da kanta ko kuma su fatima su gyara sbd tace a koda yaushe yana iya shigowa suna shiga umar ya wuce bedroom bai tsaya yin komai ba ya fada toleit yayi wanka yana fitowa kwanciya yayi akan gadon dakin don ya gaji bai dade kwance ba bacci yayi gaba da shi.shi ko yusuf dama bai shiga ba falo ya tsaya ya zauna kan kujera sai yanzu ya tuna cewa ya kashe masu wayoyinsu cikin hanzari ya yasa hannunshi aljihun suit dinshi ya dauko wayoyin ya kunna don yasan rigima na can sunayi ita da umma kuka kam ya tabbatar ta sha shi har sai ta ba umma haushi kuma sai yaji ba dadi bai kyauta ba bari ya kunna wayar ya kirata ko kara zolayarta yayi

Yanayin dalling din no ta bugu biyu aka daga amma yayi mamaki idan dai har itace bazata daga ba har sai ta katsaye ya sake kira kafin ta dauka indai tana fushi dashi sallamar nabila ta katse masa tunani cikin fargaba nabila ta gaishe shi tace bacci takeyi yaya cikin damuwa yace bacci nabila?ki fada mani gsky fa yasake tmbyrta?cikin tsoro nabila ta baiyyana mashi komi duk abunda ya faru tace yanzu haka tunda abun ya faru batayi ma kowa mgn.cikin tashin hankali yace wasa nake mata fa?yanzu ina ummah ya tmby ta?umma tana part dinta taje ta dauko wani abu cikin hanzari yace to kada ki fada mata munyi waya ma insha Allahu i am my way to katsina.nabila ta amsa da to yaya itama hawwa kada ki sanar da ita daga haka ya kashe wayar yana dana sanin abunda ya aikata "nabila ta sauke ajiyar zuciya taji dadin hakan ko ba komi yar uwarta zata warware ta samu sauki indai yaya ya dawo na tabbatar zatayi kwanan farin ciki batare da damuwa bedroom din ya shiga yasamu umar har ya fara bacci cikin damuwa ya tashe shi tare da sanar masa katsina zasu koma sbd hawwa ba lfy cikin damuwa umar yace littel ba lfy me yasameta shima ya tambya cikin rudewa yana kokarin tashi.sai alkcn ne yake fada masa abunda ya aikata.cikin fushi umar yace walhi yusuf baka da tausayi saida ka kara sanya mata wata damuwa wai kai wane irin mutum ne?kullum a irin damuwar sanya ta ciki to ni gsky bazan yarda ba arinka yin wannan dani ba.

Walhi kuma wannan izzar dake bisa kanka garaka sauketa ka tarairayi abunda tuntuni shine zabinka to kana ji kana gani zakayi asara ka daina ganina kowa yana bayanka haka umar ya gama shiri ya yana bambamin fada shidai yusuf bai kara cewa komi ba tunda dai yasan bai kyauta ba umar nagama sanya kayansa yace ma yusuf bani wayata mika mashi yayi batare da yayi mgn ba yace daga yau kada ka kara yi mani irin haka yanzu ummah cewa zatayi hada baki mukayi yana gama fadin haka ya fita yusuf tashi yayi yabi bayansa ya rufe part din aranshi ya ce dole in lallabaka umar suna fitowa part din mami suka shiga suka sameta a falo ita da fatima da ta dawo daga skul kenan cikin kulawa tace a'a har angama hutawar ne mami ta tmby su.ta cigaba da cewa dama yanzu ummi take tmbyr big bros nace kuna ciki kuna hutawa ban ma san yanzu zaku fito ba ko ta karashe mgn tana dariya.umar ne yayi saurin cewa mami wani aiki ne ya taso mana yanzu ake neman mu a company baki zamuyi shine muke son juyawa insha Allahu yusuf baiyi zaton abunda umar zaice kenan ba kallonsa kawai yakeyi ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da hamdala tunda dai umar bai tona masa asiriba wurin mami fatima ce ta gaishe su tare da cewa nidai banji dadi ba walhi cikin damuwa ta kara she mgn

Umar yarinyar tana birge sa sai yaji ba dadi sbd tana da hankali kuma shu yawancin zuwan shi kaduna don yazo ya ganta ne shima yaso ace ya kwana amma wannan guy din ya rusa komi amma ba komi yasamu lkc ya dawo ya ganta ya fadi cikin ransa.mami ce tace idan banda abunki ummi ai zuwan su ba matsala bane ko yaushe zaki iya ganinsu a haka dai sukayi sallama suka rako su har bakin mota mami ta bada sako akawo ma ummah saida suka fita get din gidan ne suka koma ciki mami ta fahiimci dawamuwa a wurin yusuf sbd tasan waye yusuf?

To haka nan zan makale ko ajikin tayar motar yusuf ne nima in bishi katsina gidan ummah don nasan akwai rigima kwance mai zuwa ya biyoni🚕

🥰🥰🥰🥰🥰 masha Allah takuce sa'ar mataaaa ina gdy gareku readers ngd sosai da kulawarku.🤝

TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘

By sa'adatu Bello [email protected]!

Page 14

.......koda suka kama hanya babu mai mgn cikin su kowa da nasa tunanin arai umar tuki yakeyi amma zuciyarsa fal da tausayin dan uwansa kuma amininsa gsky ne yusuf yana tsananin son littel amma ya kamata ya nuna mata ita ce abokiyar rayuwarsa ta har abada amma ba komi zai kara ankarar da shi batare da wata matsalaba, yusuf kuwa irin tashin hankalin da zai tarar yake tunanin fuskanta a haka har suka kusa shiga katsina wajan karfe 8:30 na dare suka shiga cikin katsina umar ne yace to kadai tanaji amsar da zaka ba ummah ko?batare da ya kalli yusuf ba yayi mgn "haba frnd ai bani da wata amsa wacce ta wuce in bata hkr sbd koma me xance mata ba yarda zatayi dani ba " umar yasake kallonsa yace ni kasan ma babbar damuwata?a'a yusuf ya bashi amsa "to walhi marin da tayi ma littel umar ya fada tare da daukar abun da muhimmanci wanda nidai a tarihin rayuwata ban taba ganin haka ba tsakanin ummah da diyarta amma gashi kayi abunda har haka ta faru tsakaninsu kaga ko dole ummah taji haushinka sosai yusuf duk da ummah itace mahaifiyarka walhi bazai hana ta hukunta ka ba akan yarinyar nan tunda ummah mace ce mai son gsky da rikon amana haka Abba shima kasan kaifi daya ne don haka ina mai shawartar ka da idan Allah ya baka hawwa kada ka jawo wani abunda zaizo yazamar maku matsala sbd ita dai hawwa kai ne zaka dorata akan turbar duk abunda kake so wanda dama tun yarintar ta kaine idonta don haka plss ka amshita amatsayin makauniya kaine idonta abunda yasa kaji ina fada maka haka nayi imanin jamila da mahaifiyarta bazasu barku ba amma ya kamata ka daura damarar yaki dasu tsakaninka da iyalinka.
Chapter 6 · 0% Book details