← Book details Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To fah🤔 yanzu aka fara wasan fa menene burin jamila yaya hawwa zata dauki aurenta da yusuf?wace irin kalubale ke tare da rayuwarsu?to koma me kenan mujira dawowar Abba, ngd da kauna masu biyoni a pc suna nuna mani soyayyarsu da littafina mai suna tun ina karama👭insha Allahu nima ina tare daku don jin dadinku 🌹🌹🌹masha Allah sai mun hadu a next page takuce 🥰🥰🥰 sa'ar mataaaa🤝

TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘

By sa'adatu Bello [email protected]!

Page 12

........( ban san lkcn da hawaye suka zubo mani ba nayi sauri na nasaki labulen na koma wurin drawer na maida ledar da ban san menene ciki ba nace nima bazan bude ba har sai idan ya daina fushi dani haka na shirya cikin doguwar rigata ja mai stone agaban ta na dauki vell dinta na saka powder kawai nasa batare danayi make up ba haka na sanya takalmina simple na fito nasame su su duka gidan suna falo ummah da Asabe da nabila Asabe mai aikinmu ce amma mun dauketa kamar kaka sbd shakuwa dakuma kirkin matar shiyasa ta zama tamkar yar uwa ta jini da yanda ta dauki umma shiyasa umma ta jata ajikinta sosai gani na kowa da murmushi a fuskarsa umma ko cikin ranta cewa tayi masha Allah yayi hallita wurin plss🙏 le ne yusuf ya tashi hankalinsa don hawwa mace ce kyaunta yanzu yake kara fitowa sosai isowa nayi na zauna kusa da ummah na dora kaina bisa kafadarta shi ya dawo da ita tunaninta nace ummatah ina kwana lfy klau ta amsa tare da cewa ya ciwon kan naki ya bar ciwo ko?na amsa da eh ummatah ya bar ciwon kafin mu kara mgn nabila tace ai sai ki tashi kije kiyi break kike ta wani shishigema ummah na dan harareta to yar sa ido.

Dariya su ummah sukayi mana na kalli Asabe nace kakas ina kwana daftn dai kinyi mani kunun gyada kwarai kuwa autar hjy nayi maki , "ummah ta kalleni cikin kulawa tace tashi kije daning kiyi break dinki ke dai dama ya rage na amsa to tare da mikewa tsaye na nufi daning ina zama na zuba abunda zanci na gama na dawo cikinsu hira sukeyi ina jefa nasu baki jefi jefi amma bawai don ina fahimtarsu ba hankalina gaba daya yana wurin yaya yusuf tunda ya saba mani idan har zai fita bai ganni ba to zaiyi mani text " kamar haka sleeping girl in kin tashi ki nemi yayanki yana son jin muryar littel din gidan su.na kanyi dariya in kirashi ya gama tsokanata mu rabu cikin annashuwa sbd yusuf mutum ne mai son tsokana.to amma yau shiru kuma banji ummah tace komi ba.hmm nasan fushi yakeyi dani.amma fa duk mai son hadani da yayana bazan yafe masa ba.

Duk abunda nakeyi nabila na lura dani kuma tana tausaya mani tunda naki yarda da cewa soyayyace tsakanina da yaya yusuf, lkc nata ja naji shirun tayi yawa wajan 11:30 kawai na yanke shawarar yi mashi text haka kuwa akayi"sweet bros don Allah kadaina fushi littel sis dinka plss🙏haka kawai nace masa na tura masa ina gamawa na dora wayata akan kijina na lumshe idanuwa na kamar mai bacci

Dai dai zasu shiga jaji wayar shi yaji alamar shigiwar text ya dauka ya duba sai umar yaga yana murmushi cikin zolaya umar yace littel dince ko?ya jinjina kai alamar eh , umar yayi dariya bai dai ce komi ba.reply ya bata kamar haka.(sorry littel sis ummanki tana sonki da yawa bazata bari in rinka fahimtar dake gsky ba don haka nina tafi kaduna wurin mamita sai Abba ya dawo zan dawo gidanku an good luck all ur best littel imiss u too)idona lumshe kamar mai bacci naji shigowar sako cikin hanzari na bude amma abunda nagani ne yasani mikewa tsaye tare da fadin what!da karfi na fashe da kuka cin ta shin hankali kowa ya ya taso gareni walhi umma kadunanan🤩 bazan zauna ba nima yaya yace ba zai dawoba nima can zan koma ya za'ayi a rabani dashi umma ya zaki barshi yabar gidanmu baki hana shi tafiya ba.tunda na fara magana cikin kuka kowa kallona yakeyi suna ma kasa cewa komi.nabila ce ta matso ta dafani tace wai hawwa me ya farune haka?ki sakeni nabila nima binshi zanyi umma bata sona tunda har ta barshi ya tafi wayyo Allah zan mutu.ran umma yayi mugun baci da jin kalamin dake fitowa daga bakina hankalinta ya tashi wai bata sona yau ita hawwa take fadi ma haka lallai dole ta koya mata hankali don gaba.bata san lkcn da ta daga hannu ba ta dauketa da mari ba ta sake dauke ta da mari akaro na biyu, kowa na wurin saida suka tsorata ni ko wata juwa nagani tana dibana wanna shine tarihin arayuwata wanda umma ta dora hannunta akaina

Ban san lkcn dana daina ganin komi ba saidai jina akayi jim a kasa warwas cikin tashin gaba daya sukayo kaina suna salati umma cikin rudewa ta kamani tana girgizawa cikin rudewa take kiran sunana hawwa ki tashi walhi bazan yafe ma kaina ba idan wani abu yasameki .nabila ma kuka takeyi Asabe ce dabara ta fado mata ta nufi wurin frige ta dako ruwa mai sanyi ta balle gorar ruwan ta watsa mata cikin hukuncin Allah tayi ajiyar zuciya umma tace ma Asabe su kamani su dora ni bisa kujera nabila ta zauna kusa dani umma ta dauko wayarta ta nemi layin amma a kashe ta nemi na umar shima akashe cikin ranta tace lallai yusuf dani kake mgn bazan saurara maka ba.yanda Asabe taga umma cikin damuwa tace"hjy ki kwantar da hankali tunda tasamu bacci data tashi zata warware.

Umma tace Allah yasa Amin suka amsa gaba daya shi kam yusuf yana gama tura mata text din ya kashe wayar shi cikin hikima ya amshi wayar umar shima ya kasheta batare da umar ya fahimta ba.koda suka shiga kaduna basu tsaya ko ina ba sai unguwar sarki gidan mami suna zuwa saka makon suma yan gidan ne mai gadi ya bude masu get suka shiga sukayi parking gaba daya suka fito daga mota suka nufi cikin gidan, mami na kichen taji kamar muryar yusuf na sallama cikin sauri ta fito zuwa falo tana shiga ta gansu zaune cikin fara'a tace aaa bakin nan kun iya bazata daga ina haka cikin jin dadi yusuf ya ce mami daga gida umar yace mami dan lelenki ne yace ya sai yaga maminshi.nima yana raina nan ta zauna suka gaisa cikin girmamawa tare da tmbyr yan gida.bayan sun gama gaisawane yusuf yace mami coffe za a bani tace to ba matsala bari in hada maku kalaci kafin in gama abincin rana dama nasan wanan tafiyar ai bakuyi break ba umar yace ai mami bai bari ba mun yi break tana dariya ta tashi ta nufi kichen ta hada masu komi ta dawo daning ta shirya masu.bayan su gama ne suka dawo wurin inda take zaune umar yace mami da dawata mgn muka zo maki mami tace haba koda naji to ina saurarenku ya akayi?umar ya gaya mata komi yusuf kansa na kasa don kunyar mami yaji sosai

Mami tace ba damuwa barima in kira Alh ku kwantar da hankalinku komi zaiyi daidai insha Allahu.mami ta daga waya ta kira Abba bugu daya ya dauka mami ta gaishe shi cikin girmamawa sannan yace maryam lfy dai ko?cikin girmamawa tace yaya lfy klau dama wata yar alfarma nake nema wurinka game da yarona yusuf takarashe mgn cikin dariya cikin kulawa yace kamar me fa ki fadi ba abunda zai gagara ai in sha Allahu .nan mami ta zaiyyana mashi komi cikin fahimta kuma ya fahimce ta tare dayi mata alkawarin next week zai dawo daga malesiya in ya dawo za'ayi komi agama insha Allahu ta gaya ma yusuf yafara shirye shirye shi ma da yan uwanta aba kowa hakkinsa, mami tace ngd yaya Allah ya kara girma ya amsa da Amin sukayi sallama.

Bazan fasa gdy ba gareku masoyan wannan littafi nawa na tun ina karama ina jin dadin yanda kuke nuna mani kauna nima ina yinku irin sosai da sosai din nan🤩

Masha Allah takuce 🥰🥰🥰sa'ar mataaaaa🌹🌹🌹🤝

TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘

By sa'adatu Bello [email protected]!

Page 13

........Bayan mami ta ajiye waya ta daga kai ta kalli yusuf wanda tunda ta fara waya da Abba yake kallonta zuciyarsa cike da fargaba"mami ce ta katse masu shirun da cewa to yusuf ina fatan dai iyakar matsakar kenan ko?kuma kunji yadda mukayi da Alh ko?to kawai abunda ya kamata kawai kaje ka fara shiri tunda kaga komi yazo cikin sauki in sha Allahu ni daga ban garena banida matsala kuma babu abunda zai gagara kuma idan kana neman wata shawara ko gudunmawa ko kuma wani abunda ya shige maka duhu to kofa a bude to kofa a bude take don ni ba surikarka bace bare kace zakaji kunyata ni uwace diya ba tawa bace ba ga uwarta can itace surikarka wadda naga alama sai kayi da gaske zaka rabata da abunta ta karashe maganar tana dariya cikin zolaya tunda ta lura ya fara nuna mata surutaka ita kuma tafi son yazama free da ita.

Cikin jin dadin maganganun mami gaba dayansu sukayi murmushi umar yace mami godiya muke Allah ya kara girma yasa kifi haka mami gaba daya suka amsa da Amin, yusuf tashi yayi yaje har gaban mami inda take zaune ya durkusa ya dora hannuwansa kan gwiwarta tare da kwantar da kansa yana jin wani irin son mami a ransa tare da kaunarta a ransa yadda take nuna masa karamci bashi da bakin gode mata sai yanzu yake jin kulu-kulun dake cikin zuciyarsa yake fashewa hawayen farin ciki ne kawai ke zuba daga idanuwansa yana jin wani rahama na sauka aransa mami kasa cewa komi tayi sai ma daga masa kai tayi tana share masa hawayen dake zuba daga idanuwansa tana jin wani tausayin sa da kaunar sa tana kara shiga cikin ranta tana ganin soyayya amma soyayyar yusuf da hawwa
Chapter 5 · 0% Book details