← Book details Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna yin parking hawwa ta fito ta bude masu gidan shi kuma umar ya kama yusuf suka shiga ciki yakai shi har part din hawwa sannan ya nuna ma hawwa yanda maganin yake sannan yace shi zai koma sai da safe dare yayi sosai "yusuf yace bros ngd Allah yabar zumunci." ba komi umar yace Allah ya baka lfy sai na dawo da safen haka sukayi ban kwana hawwa ta biyo shi ta rufe gidan shi kuma ya shiga mota ya nufi gida cike da takaici aransa.

.......jamila ko na fita bata zame ko ina ba sai gidansu tana shiga tayi parking ta fito ta shiga cikin gidan bata zame ko ina ba sai part din hjy mariya tana shiga ta sameta sai hada mata magungunan takeyi cikin tashin hankali tace mummy na fasa masa kai.cikin tsoro tace"garin yaya jamila!zakiyi wannan danyen aikin?walhi mummy hanani fitowa yayi shine nima na aikata hakan, "kash!amma ke banza ce to yanzu ai kin lalata komi sai ki zauna mu nemi mafita zuwa safe, " ai dole mummy daddy dai bashi nan ko?don shima yanzu naga kamar ya fara bin bayansu Abban yusuf."ke don Allah kyale shi can da munafurcin su kije ki kwanta bashi gari "to mum ngd.

Hawwa na dawowa wurin yusuf ta zauna tace" yaya bari in hada maka tea kasha kafin kasha magani ko, ta tmbye shi cikin damuwa tausayinta nae fal aranshi yarinya karama amma ana sanya mata damuwa da yawa why ya tmby a zuciyarsa, azahiri kuma murmushi yayi yace"duk yanda kike so sweet heat zanyi, murmushi tayi tace to hak ya kamata tashi tayi ta wuce kitchen ta sanya mashi ruwan zafi tare da warming din kazar da suka zo dashi don su duka babu wanda yaci komi in banda cinye juna da sukayi wanda yasa har jamila tayi masu wannan rashin mutunci.

Haka tayi komi ta dawo ta zauna kusa dashi tana bashi tea din yana sha ita kuma tana ci kadan don ita kanta komi ya fita aranta amma bata so taga yanada damuwa aransa ita dai fatan ta Allah ya bashi lfy kafin tace komi.bayan ta gama ne ta taimaka mashi ya shiga bathroom yayi wanka tare suka gama komi suka fito haka ta shirya shi cikin kayan baccinsa saida ta tabbatar ya kwanta sannan itama ta hau bisa gadon ta kwanta tare da rungume shi ta baya juyowa yayi yana mamakin yanda ta canza duk wannan kunyar ta ta ta cireta shima murmushin jin dadi yayi ya kara rungume abinsa ko ba komi ya samu natsuwa aransa.sai muce Asuba ta gari masoyan juna🤩

......washegari da safe bayan sun gama komi ta bashi magani suna zaune a falo tayi pillow da cinyarsa shi kuma yana wasa da kalabar dake kanta shi kansa wani dadi yakeji aransa yanda yaga bata damu da abunda ya faru ba bare ta tmbye sa me ya faru tsakaninsa da matarsa.ba zato taji yace"littel amma ina ftn babu wanda yasan me ya faru ina nufin su umma.dariya tayi tace"babu wanda yasani, "gud house wife haka ake so mace ta rinka rike sirrin cikin gidanta kuma kada ki damu da abinda jamila takeyi with time kinji ko?" Naji yayana kuma insha Allahu zanyi yanda kace"Allah yayi maki Albarka "Amin dear ta amsa masa tare da kara shigewa jikinsa.

Basu dade ba umar ya shigo duba shi hawwa bayan sun gaisa ne ta tashi taje ta kawo ma shi lemu da ruwa.yusuf ne yace" frnd ina so ka rakani in maido da jamila.cikin razana umar ya mike tsaye yana nuna shi d ya tsa zaiyi mgn sukaji faduwar tiren da hawwa ta dauko da lemu da glass cup din data dauko suka fadi kasa suka fashe sbd jin furucin da hawwa taji yusuf yayi na zuwa dawo da jamila.gaba daya suka juya tare da ganin hawwa bata tsaya ba sauraren komi ba ta juya da gudu tana kuka!!!😨

Masha Allah kuyi hkr na rashin jina kwana biyu walhi na zama busy ne amma duk da haka zaku rinka jina akai kai iluv u fans 💋
Din Tun Ina Karama ina maku ftn Alkairi irin sosai din nan 🥰🥰🥰

Mu hadu a next page takuce sa'ar mataaaa🌹🌹💞🤝

*TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘*

By sa'adatu Bello saadatu99gmail.com!

©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...

Page 27

........tana shiga d'aki tasa key ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yusuf binta yayi a kidime yana kiran sunanta amma yana isa kofar yaji ta sanya key, komawa yayi wurin umar wanda tunda yazama kamar an dasa shi sbd mamaki ya zama kamar status.

"Kaga irin abunda nake nuna maka Yusuf, yanzu ace kai bazaka iya hkr da Jamila ba sbd sun gama dakai sun maida ka wani wawa sbd da Allah kanayi ma yarinyar nan adalci kuwa?gsky Yusuf zan fidda hannuna akan wannan badakala taku don bazai yiwu ba kullum problem's yaki karewa tsakaninku kai kuma kullum kalmarka bata wuce revenge zakayi taking ba kuma har yanzu kaki gamawa da al'amarin ba."

"Umar kasan bazan boye maka komi ba arayuwata ba to walhi ban taba son Jamila koda da second daya ne idan ba don asiri ba kuma gaba d'aya mun san haka to Jamila tayi mani abubuwa da yawa arayuwa infact ma ince maka ban taba samun mutumin da ya musguna mani ba arayuwa irin Jamila idan har na rabu da Jamila salun alun to gsky banyi abunda ya dace ba,amma ina so in nuna ma jamila ita bata isa ba arayuwa duk abunda take takama da shi ina so in raba ta dashi in nuna mata ita bata isa ba kuma bazata iya samun digo araina ba na soyayyarta kuma ina so duniya tayi mata kunci, ina so in azabtar da rayuwarta har sai ta wulakanta sannan inyi mata mai gaba daya zan dasa mata ciwo a zuciyarta wanda har ta mutu bazata daina jin sa ba,amma hakan bazata samu ba har sai mun zama clothenings da ita don haka ina so ku bani lkc ku fahimce ni babu komi araina intentionally nayi mgnr nan dama ina so Hawwa taji don inga reaction dinta kuma nagani zanyi handle din komi"ya kara she mgn yana kallon umar sosai.

.......ajiyar zuciya Umar ya sauke tare da jinjina kai alamar gamsuwa,"to amma Yusuf taya ita Hawwa zata tabbatar ba sonta kake ba?"

" Yes ina so Hawwa ta kwaci kanta wurin Jamila tacire tsoron da takeyi mata arai kamar yadda Nabila ta bata shawara kuma naga ta dau hanyar yin hakan, kuma ina so ita Jamila tasan Hawwa ita kadaice macen da nake so a zuciyata duk da ta kasa gane hakan har yanzu zan bita akan asirinta na ta siri har sai nakai inada zamu fara game din daga nan zata fadi kasa warwars daga ita har uwarta."

"to shikenan amma u have very careful about her"insha Allahu frnd ama ba yau ba kaje ka lallashi littel"

"hmm walhi Umar tunda ta kulle daki bazata saurareni yanzu ba"

"to yanzu kasan ya zamuyi?"

"Ban sani ba umar."

"Nabila zan kira tace mata zata zo yanzu na tabbatar bazata cigaba da fushin ba har kasamu ka fahimtar da ita komi cikin hikima."

"gud idea frnd."

Koda Umar ya kira Nabila ya fadi mata ga abunda yake so tayi ta amsa da to kuma bata kawo komi aranta ba sannan yace mata bai so abarta ita kadaine tunda zasu fita da Yusuf ne, koda Nabila ta fada ma Umma sakon Umar na zuwanta gidan Hawwa bata hanata ba don itama tasan Hawwa tana bukatar wani kusa da ita tunda jiya ta koma Umma tace ma Nabila," idan kin shirya ki tafi a motar Hawwa sbd abar mata abunta can nasan ai kun kusa komawa skul?"

"haka ne Umma zan tafi da ita dama key din yana hannuna."

"to shikenan agaisheta amma kada kiyi dare, Umar ya maido ki gida."

"to umma ngd" kiran Hawwa tayi kamar yadda Umar yace ta sanar mata zuwanta Hawwa tana da son boye tsakaninta da Yusuf shiyasa koda Nabila ta kirata bata daga ba saida ta saita kanta sosai sannan ta kirata kuma ita kanta Nabila bata fahimci komi ba.

Suna gama samun mafita Umar yace su fita kada ma tasame su haka suka fito shi Yusuf ga plistar agoshi gidan su Umar suka wuce direct suka nufi sashin Umar batare da sun yarda Ammi ta gansu ba bare ta tmby me yasamu Yusuf din.

Ita ko Jamila tana gida gabanta na faduwa tana tunanin ya zatayi idan kuma an samu wata matsala tsakaninsu amma tayi mamakin yanda har yanzu bataji wani feed back ba kuma tayi tunanin ko Hawwa zata fadi ma Umar komi kuma shima tasan daya sani da yanzu yazo yayi mata hauka amma bari takara sauraren su iyaka kawai tace masu bada niyya tayi ba tsautsayine kawai tana wannan tunanin ne Mummy ta shigo dakin suka ci gaba da kullawa suna kwance wa.

Nabila data zo wurin Hawwa bata fahimci komi ba don bata son daga dawowarta tace ga matsala tana so ta fahimci abunda Yusuf yake nufi da zaman su, haka suka sha firarsu kamar bata da wata damuwa koda Nabila ta tmby ta aunty Jamila cewa tayi ta fita hospital tunda ta na tunanin kamar afternoon takeyi haka suka bar mgnr batare da tunanin komi ba azuciyar Nabila.
Chapter 16 · 0% Book details