Sashe 2
Tun Ina Qarama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama naga yayi akujerarsa ya fiddo wayarsa naga ya nemo wata no yana kira yana karawa akunnensa naji yace na iso ina office kasameni, banji mai akce ba saidai kawai naji yace ok sai kazo ya ajiye wayar ya fara duba file din dake ajiye kan table din sa, ba don yana jin dadin aikin ba sbd damuwace fal azuciyarsa.
.....jamila ta gama shirinta tsab na zuwa hospital wurin aikinta, saida tagama ta fito ta wuce sashen maigidan amma abun mamaki rufe ta ganshi hanyar fita tayi tafito daga cikin gidan tayi harabar gidan wajan parking amma bata ga motar shi ba.tsaki tayi tace to koma dai baya kwana gidan ne?ta dage kafadarta alamar ko oho" tace nasan yana wurin mayyar nan amma zanyi maganin shi mts yana can kamar wani rakumi yana bibiyarta.kwaf tayi ta nufi wurin motar ta ta sa key ta bude ta shiga tayi rivos ta nufi get mal isah na ganinta ta wangale mata get tazo daidai fita ta sauke gils, "mal yace barka da fitowa hjy " cikin isa da jiji dakai tace barka dai yaushe mai gidan nan yafita ta jefo mashi tmbyr?"yace ai hjy zaikai awa biyu da fita batace komi ba ta rufe gilas din ta ja motarta ta fice rai bace, tunani takeyi yau sati guda kenan abunda yakeyi mata kenan, kuma in ya dawo baya yarda su hadu cikin yanayin damuwa ta furta:yusuf Bashir kankiya ka tabka babban kuskure!!!
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing 🤪🤪🤪 takuce sa'ar mataaaa 🤝
TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘
By sa'adatu Bello [email protected]!
Page 6
.......Tunda umma ta daga dakina na tashi na shiga toleit na kara wanke fuskata na fito na tsaya gaban mirrow na dan gyara fuskata wadda dama bawani make up nakeyi mata ba.sbd dai dai gwargwado ni farace kuma ina da kyauna daidai missali Allah yayi mani hallita mai kyau sbd haka kullum nake kallon kaina ina gode ma Allah Alhmdulillah.
Ban canza shigata ba amma na dauki hijabi na sanya a maimakon gyalen dana sanya.sbd dama gaskiya idan zanyi driving to bana sanya gyale saidai hijabi dama don tare dashine nake wannan shigar, duk da shima baya son inayi don yusuf yanada kishi ba tun yanzu ba nasan hakan.tun kafin muyi aure yana hanani ire_iren wannan shigar.
Ina da lucture karfe 2:00 shiyasa nayi kokarin fita in shiga skul kafin lkcn ko don in dan rage ma kaina damuwar dake zuciyata.bude jakata nayi na dauko key din motata na rike ahannu na, nafito na rufe dakina na nufi dakin umma don banganta a falo ba, ina zuwa na murda kofar dakin tare da sallama na shiga.tana zaune tana waya na shiga sai naji tace ina zuwa mami zan kiraki bari in sallami diyata.kawai naga ta kashe wayar tare da amsa sallamata"tace hawwa har kin shirya tafiya zakiyi?na amsa da eh ummatah.ta sake kallona tace wai yauma kina azumin ne?nace inayi tace to yaushe zaki dawo?nace ummatah sai karfe 5:00 tace to Allah yabada sa'a adawo lfy.don Allah a kula nace insha Allahu.na juyo zan fita ta taso ta biyoni a baya tana cewa wace motar zaki hau?ina murmushi nace ummah tawa zan hau, tace to shikenan Allah ya tsare na amsa da Ameen, sai da ta rakoni
....har bakin motata na shiga da Addu'a abakina na waigo nace umma bye itama ta daga mani hannu tace bye bye adawo lfy, haka nayi ma motata key a lkcn har baba mai gadi ya bude mani get na isa bakin get din zan fita na sauke gilas dina na gaishe shi, shikuma yana yi mani Allah ya kiyaye haka na fita gidanmu na dauki hanyar skul ina tafiya cikin natsuwa da taka tsan tsan a hanya na kunna kira ar Ahamed suleman ina saurare ina jin wata natuwa na zo mani.kuma ina tunanin maganganun ummatah wanda sune fal araina.ina neman mafita awurin Allah.sbd ban san kowa ba sai yusuf babu wanda na saba da shi acikin dangi kamar shi haka awaje ma babu shi kadaine abun alfaharina kuma tamkar jinin jikina.wasu hawaye masu zafi suka zubo mani, ummatah idan kika rabani da shi wazan jawo arayuwatah TUN INA KARAMA.nake son shi tun ban san menene so ba tunanina yan uwanta ka ne ashe kaunace mai tsanani tsakaninmu dawannan tunanin na isa skul daidai get din skul din mu na UMARU MUSA YAR'ADU'A UNIVERSITY dake cikin garin katsina haka nasa sighnal din motata na shiga cikin skul din na nemi wurin da mukeyin parking na parka motata na fito na kulle na wuce block din class din mu inada nasa zamuyi lucture.
.....yusuf bai gama duba file din dake gabansa ba aka buga kofar office din shi batare daya daga kansa ba yace yes come in, umar ne ya bude kofar tare da sallama ya isa inda yusuf yake zaune ya mika mashi hannu suka gaisa.sannan ya nemi wuri ya zauna yace wlhi compaming din kayan nan ne tsaya yi amma komi normal in sha Allahu.yusuf yace ba ok ba damuwa umar yasake kallon yusuf yace frnd naga kamar you not feeling okey?yusuf ya dan ya mutsa fuska cike da damuwa .yace walhi umar umma bazata taba yarda dani ba.
Kullum cikin tada mani hankali take wai dole saina sakar mata diya kumani umar walhi bana iya daukar hannuna in yi saki kokuma in furta da bakina wai in saki hawwa tare da nuna kanshi ya girgizawa kamar zaiyi kuka yace frnd ican't umar zuciyata zafi take duk ranar da ummah tayi ikirarin rabani da hawwa.
Tunda ya fara magana yaji abokin nashi ya bashi tausayi, karo na farko kenan tunda matsala ta faru tsakanin shi da hawwa ya tausaya masa.sbd shi kanshi haushin shi yakeji sbd bai kyauta ba duk da yasan ba laifinsa bane to amma sbd me bazai dauki tsatsauran mataki ba yana gani ana cutar dashi amma ya kasa magana.umar ya nisa yace agky frnd bazan boye maka ba dolene ummah tayi maka haka sbd kayi kuskuren da sai munyi da gske zamu gyara shi, kuma walhi kada kasake ayi nasarar rabaka da hawwa kayi duk abunda zakayi ka tabbatar hawwa ta dawo gareka.shine abunda zamuyi, "yusuf yasake runtse idanuwan shi ya kara tura kujera baya ya kwanta yayi blance yace umar ita kanta hawwa ta canza mani maganar ummah ita take amfani da ita yau karara na hango tsanata a idanuwanta.
....cikin damuwa umar ya taso ya dafa kafadarsa yace kayi hkr frnd insha Allahu komi zaiyi daidai kuma hawwa zata dawo gareke da yardar Allah karka damu.umar ya koma ya zauna yace frnd kasan wani abu?cikin yanayin damuwa ya girgiza masa kai alamar a'a ya cigaba da cewa to dazun jamila tazo wurina cikin tashin hankali ya dago kanshi ya kalli abokin nasahi ido cikin ido yace what?jamila!
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing 🤪🤪🤪 takuce sa'ar mataaaa🤝
TUN INA KARAMA 👭🌹🌹🌹💞💝💝💘
By sa'adatu Bello [email protected]!
Page 7
ASALIN LABARIN:
.......waye yusuf Bashir mado kankiya?Alh Bashir mado kankiya haifafan cikin garin kankiya ne dake jahar katsina Alh bashir su hudu ne wurin mahaifinsu.Alh bashir shine babba a cikin su da shi da kanin sa Alh bello sai kanwar su hjy mariya dakuma autar su rabi atu.sun taso cikin jin dadi da walwala ta rayuwa, sakamakon mahaifinsu yana da ilimi na addini dana zamani yasa yazama wayayye kuma gashi yana amfani da iliminsa wurin iya mu amula da mutane.sannan ga tarin dukiya Allah ya hore masa, yana kasuwancin shi cikin ilimi da gogewa ta rayuwa.matar shi daya hjy hauwa'u wadda itace mahaifiyar su Alh bashir.sunyi auren soyayya da Alh mado itama yar cikin garin kankiya ce.sunyi zama na soyayya da Alh mado wanda har Allah ya azurta su da haihuwar yara guda hudu, shima Alh bashir koda yake dan boko to ya biyo baban shi wurin son business sosai don tunda ya taso ya gama karatunsa na degree akan business ne yayi karatu har master's din shi.
Shi kuma Alh bello gsky yafi karfi a govment sbd yanzu haka shine commissioner na manoma watau agric.ita kuma hjy mariya sakamakon mijinta mai haline yana da tarin dukiya sosai shiyasa ita bata aiki sai kawai ta fada harkar kasuwanci, tana fita dubai tana kawo kaya sosai.sai Rabi'atu wadda itama tayi aure amma tana aiki da ma'ikatar lfy ta kano.gaba dayansu kowa yana da rufin asiri daidai gwargwado sbd Alh moda koda yake da kudi bai yarda ya bar yaranshi ba babu ilimin addini dana zamani ba.bayan rasuwar maifinsu ne Alh mado Alh bashir ya koma katsina da zama a inada ya auri diyar aminin babansu Alh garba mai dala.wadda dama suna soyayya dashi wadda hakan yasa iyayensu sukayi masu alkawarin auren junan su kuma Allah ya kaddara.shikuma Alh bashir dalilin dayasa ya koma katsina da zama sbd duk harkokin mahaifin shi suna can to koda y rasu sai ya tattara gaba daya ya koma da zama.yaso ya tafi da mahaifiyasu amma ta nuna mashi tafi son zamanta anan kankiya cikin danginta haka nan ya hakura badon ranshi yaso ba.amma duk satin dunya yana zuwa ya kwana biyu wurin mahaifiyarsa saidai idan baya kasar.kuma yana zuwa da matarsa hjy khadija wadda mace ce mai karamci da nuna kulawa ga yan uwan mijinta shiyasa ta shiga ran kowa na family dinsu Alh bashir .ita kanta hjy hauwa'u tana kaunar sirikar tata sosai bata son taji ance ga laifinta.shikuma Alh bashir ganin yanda take kula da mahaifiyarsa da yan uwansa yasa yake kara ganin darajarta da kimarta.