← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ikon Allah ba'a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen titi nanta ha'diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar gida suna Shirin fitowa...

Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui Masa Mai kyauba.

Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron wani qaramin gida..

Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare dasuba.

Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi...

Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin 'dinsa ya saitashi ya jefa Masa Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya 'dago lazy eyes 'dinsa dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya batareda yau ya gano gidansuba.

Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.

Azafafe yace,

Uban me kakeyi anan?

Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa'daba..

Mari Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..
Yace,

He said wat are you doing hia you monkey fool.

Kallon Umar 'din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani 'dan Adam Kai tsaye yace,

I came hia to see my love.

Ture sani Umar yayi da qarfi ya shaqo wuyan Nik 'din yace,

Wh...wh..who is your love?

Ayeeshah''''""ya fa'da Kai tsaye ba tsoro a idanuwansa.

Hannu ya dunqule yakaiwa Nik wani mugun duka Saida bakinsa ya fashe.

Wani dattijo ayshah tagani zai wuce tayi saurin Shan gabansa tana hawaye tace,

Baba Dan Allah kaga wasu can suna fa'da Dan Allah ka hanasu karka Bari ayi fitina.

Juyawa yayi ya kalli gurin daidai sun nanna'de rigunansu zasu cire takaicin dukan daakayiwa iyayensu dattijon yayi saurin tarewa tareda matsarda Nik dake tsaye baida alamar motsawa gefe yace,

Haba Kuna 'yayan musulmai 'yayan manyan malamai zakuyi Abu irin na jahilai...
Meyayi zafi haka dabazaku Kira hukuma ba Zaku 'dauki mataki da hannunku...

Fa'da yahau yi musu sosai suka basa hkr tareda barin gurin sbd duk zafin ransu sunada tarbiyar girmama babba sosai Koda basusanshiba.

Juyowa yayi ya kalli Nik yace,

Kaima ka wuce tunda Suma sun tafi..

Juyawa yayi ahankali yabi bayansu duk da baisan abinda mutumin yafadaba...shidai yau alqawarine yayiwa zuciyarsa saiyaganta Dan haka zaibi bayansu saiyaga gidansu..

Daf dazai shiga kwanar yaji anriqo rigarsa ta baya yayi saurin juyowa sukai Ido biyu ta juya yabiyota da sauri Yana Kiran sunanta Amma taqi tsayawa.

Saida takai bakin motarsa ta tsaya tareda juyowa ta kallesa taga yanda goshinsa da bakinsa ke jini ta 'dauke Kai tareda 'daure fuska ta nuna Masa motarsa tace,

Leave...

Da sauri ya kalleta zaiyi magana tace,

Go... please..

Idanuwansa ne suka ciko da hawaye ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah please don't ask me to leave because I can't....

Rintse ido tayi cikin ra'dadin ganin jininsa na zuba ta sake juyar dakai tace,

Please Nik go...
I don't want to lie to myself again..
I don't want to continue believing in a fake dream...
My parents fixed date for my marriage with someone.....

Wani mugun jiri ya 'dibesa dama jurewa kawai yake Dan tuni yakejin jirin jinin dayake fita a goshinsa...

Hawaye taga sun 6alle Masa yayi ya 'dago lazy eyes 'dinsa taga sun canza launi tayi baya ka'dan ba zato taji ya damqo hannunta tana fixge da qarfi yakuma damqota tafara qoqarin qwacewa Amma takasa Dan mugun riqo yayi Mata ita batama ta6a tunanin yanada qarfin dazaiyi Mata wani riqo takasa qwacewa saigashi yabata mamaki..

Da gudu wani Dan sauri dake bakin titin ya isa yafadawasu Umar dake qofar gida suka dungumo a guje daidai lokacinda ya turata mota tana tirjewa yabar gurin da mugun gudu da ita.

iska Umar ya daka da qarfi Yana cewa,

Wlh duk yayi kuskuren ta6ata ko sauke haushi akanta saina nayi ajalinsa.

Gida suka koma suka sanar da iyayensu Nan hankula suka qara tashi suka 'dunguma station don Kai report.

Gudu yake sosai har lokacin idanuwansa basudaina hawayeba jiyake kozai rasa ransa bazai ta6a Bari arabasa da ayshah ba...

Kuka take sosai itama ahankali batareda takalli gefensa.

Fita gari yayi ya qarawa motar gudu tayi saurin kallonsa tareda fashewa da wani sabon kuka zuciyarta na karyewa gabanta na tsananta fa'duwa.

Awa 'daya da rabi saigasu a wani babban gari dabazata iya cewa inane ba.

Anguwar dasuka shiga tasata 'dan sararawa da kukanta Dan lurada kamar anguwar duk malamai ne da almajirai tareda masu 'daukar karatu.

Kallonsa tayi taga fuskarsa tayi jajir sbd azaban ciwon dayakeji akansa hakama jinin dake goshinsa duk ya bushe a fuskarsa...

Wani mugun tausayin kansune yakamata Dan Sai a lokacin ta lurada muguwar ramar dayayi..

Parking yayi tareda juyowa ya kalleta tsowon minti goma murya a sanyaye yace,

Ayeeshah can you please come inside with me..

Goge jajayen idanuwanta dasuka kumbura tayi tareda kallon qofar gidan ta 'daga Masa Kai.

Bu'de motar yayi yafito ya zagayo ya bu'de Mata ta fito jiki ba qwari ga idanuwanta da Bata gani sosai dasu sbd kuka.

Babban palon dake zauren gidan yashiga ga mamakinta saitaji yayi sallama duk da kusan a birkice yayita Saida takusan fa'duwa sbd mamaki...

Babban mutum tagani zaune cikin shigar babban malami Yana karatun wani littafin larabci Yana ganinsa yasaki murmushi tareda amsa masa sallamarsa Yana qara gyara Masa yanda take daidai.

Zama yayi a qasa kusada qafafun malamin tareda fashewa da kuka ahankali....

Subhanallah.....sheik abdallah yace da sauri Yana kallon Nik 'din cikin kulawa yace,

Wat is the matter Muhammad?

Kuka taji itama taji ya qwace Mata sbd sunan dataji ankirasa dashi na Muhammad.

Shiru shaikh abdallah yayi Yana sauraran kukansu na tsawon mintuna kafin Nik ya 'dago manyan lazy eyes 'dinsa ya kalli Ayshah cikin sanyin murya yace,

Ayeeshah....

Bata 'dagoba haka zalika Bata amsa ba har lokacin kuka take..

Ayshah please let get married today...

Sabon kuka tasaki tareda miqewa da sauri zata bar gurin yayi saurin Shan gabanta tareda zubewa qasa ya riqe qafafuwanta..

Gyara murya shaikh yayi tareda Kiran sunanta cikin nutsuwa yace tadawo ta zauna.

Ba musu tadawo a sanyaye tazauna hawayenta na tsananta gudu..

Ayshah ke musulma ce Kuma 'yar malamai Masana addini kamar yanda yanda Muhammad yayimin bayani..

Muhammad yazo Nan kwana biyu dasuka wuce ya bayyanamin komai akan qaunar dakukewa juna Kuma aranar ya kar6i musulunci ya kar6i kalmar shahada Kuma daga ranar kullum saiyazo Nan garin koyan abinda ya danganci addinin musulunci...
Amma bai za6i sunaba yace kece Zaki za6a Masa suna Kuma ya tabbarminda qalubalen da fitinar dake gudanuwa a tsakanin gidajenku Dan haka ya bayyana buqatarsa tason a na 'daura muku aure Dan shika'dai ne zai kawo qarshen fitinar dake tasowa..

Girgixa Kai tahau yi tana cigaba da kuka duk da zuciyarta cike take da muguwar soyayarsa musamman yanzu dataji ya musulunta...Amma bazata yarda suyi aure yanxu ba Saida yardar iyayensu.

Matsowa yayi gabanta a susuce yace,

Please ayeeshah say yes,,,I promise I won't do anything to you until everything is right... please ayeeshah I beg you in the name of Allah...

Rintse idanuwa tayi hawaye nacigaba da xubo Mata ta miqe tsaye tareda juya Masa baya dan matuqar taci gaba da sauraransa zuciyarta na daf da karyewa...

Sake zubewa qasa yay ya riqe qafafuwanta Yana fidda sautin kuka ahankali jikinsa har rawa yake sbd wani mugun zazza6ine ke cin jikinsa Amma bayaji alokacin.

Jin kuka yake sosai zuciyarta takasa controlling kanta ta durqusa da sauri gabansa itama tana tsananta kukanta.

'dagowa yayi fuska jajir ya bu'de baki daqyar yace,

Ayeeshah please.....

'daga Masa Kai tayi da sauri cikin tsananin sonsa da tausayinsa..

Thank you... thank you...yafada cikin farin ciki tareda juyowa gefen shaikh saiyaga baya palon...fita yayi da sauri kaman zai Fadi yakirowosa Yana kallon tsakiyar idanuwanta yace,

Shaikh she accepted... please get us married today...

Kallon ayshah shaikh yayi ta sunkuyar dakai yace,

Allah yabaki ladar wannan jahadin ayshah,,Kuma Allah ya kawo haske a rayuwar aurenku yakuma shirya iyayenku sanadin wannan auren..

Amin tace axuciyar na bugawa very fast..

Kallon Nik dake faman murmushi yayi yace,

I will send her inside now you'll see her after the fatiha...

Ok...yace Yana kallonta cikin farin ciki..

Wait shaikh let her choose a name for me..

Kallonta sukayi su duka Dan sauraron sunanda zata fa'da ahankali cikin sanyin murya tace,

*_DEEN_*....._*NURADEEN*_....

wani lazy smiling ya aiketa dashi yanabin bayanta databi shaikh cikin gida da sauri.

*_ZUCIYA MUGUN NAMA_*......

Cikin qanqanin lokaci layin ya 'dan cika da malamai da 'dalibai tareda masu zuwa 'daukar karatu aka shaida 'daurin auren _NURADEEN DA AYSHAH_...Akan sadaki naira dubu hamsin Wanda shaikh ne yabiya sbd qaunar NURADEEN da Allah yasaka Masa aransa tun ranar daya fara zuwa gurinsa..

Tunda babban 'dan shaikh yashigo ya sanarda an 'daura auren taji hankalinta ya tsananta tashi wani sabon kuka yazo Mata ta sake cusa kanta cikin qafafunta tana yi.

Uwar gidan shaikh 'dince ta ringa rarrashinta tana jero Mata nasihu akan tabbas Bata kyautawa iyayentaba Amma tunda jahadine tayi Allah bazai Bari ta wulaqantaba insha allah...Dan ba'asan iya Wanda zai musulunta ba sanadiyar auren.

Awa 'daya da gama 'daurin auren shaikh ya Aiko kiranta tashiga pilonsa da sallama a qasan maqoshi sbd muryarta data shaqe sbd kuka..

Nasiha yayi Mata sosai Mai matuqar shiga jiki kafin yace taje Deen na waje yana jiranta zai maidata gida.

Tana fitowa idanuwansu suka ha'du Nan take taji jikinta yakuma sanyi gefe 'daya wahalalliyar soyayarsa na 'dawainiya da ita.

Shikuwa ji yake tabbas Babu abinda yakai musulunci da'di tunda ya mallaka Masa ayeeshansa.

Ya zagayo Yana rintse ido sbd mugun zazza6i da rawar sanyi da jikinsa keyi...
Bu'de Mata motar yayi tashiga asanyaye kafin shima yashiga suka bar gurin...

Ko anguwar Basu fitaba yaji jikinsa na neman rikicewa ya 'dan saci kallon gefenta yaga kanta a sunkuye ya tattaro 'dan kuzarinsa Dan yasamu yakaita gida kafin ciwon ya kwantardashi..

Dashi dishi yafara gani saura qiris yadaki wata babbar mota yayi saurin take burki....

'dagowa tayi a 'dan tsorace saitaga jikinsa na rawa sosai idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa duk sun yanko...

A rikice takira sunansa hawaye na gangaro Mata...

Kallonta yayi kaman zaiyi kuka yace,
Chapter 8 · 0% Book details