← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 27

Sashe 22

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukane yaci qarfinta tayi shiru zuciyarta na tsananin zafi da qunar halinda take ciki...

Da sauri ta miqe sbd kukanta daya fara sauti Dan karta tadashi Wanda ita Bata saniba duk abinda take fa'da yanaji
Jikinsa yayi matuqar sanyi Dan baita6a tunanin haka take sonsaba Sai yanxu,
After what all happened she really wants to give his love a chance...

Rintse idanuwansa yayi jijiyoyin kansa na tashi tausayinta da sonta na shigarsa lokaci 'daya musamman yanda yakejin 'dacin rabata 'da 'danta da akayi lokaci 'daya kenan wanine ya 'dauke mahmud yakawo Masa ba itace takaisa da kantaba.

I'm the reason for all her pains and sorrows,
I've been acting to harsh towards her,
I've insulted her for no reason,

Rintse idanu yayi zafin abubuwan na shigarsa kamar yayi kuka,
Ayshah kukanki yazo qarshe insha Allah..
From tomorrow i will give you your full right as a lovely respected first wife.

Har akayi asuba idonsa biyu cikin tsananin tunani Nan take Sai kansa yafara wani mummunan ciwo Wanda baita6a irinsa ba musamman yanda kaman tunaninsa ke neman dawowa da qarfi out of control.

Da qayar ya iya fitowa yaje masallacin gidansa sallar asuba.

Akan idon siyama ya fito hawayen datake dannewa suka silalo Mata kenan dai agurin ayshar ya kwana.

Daga masallaci part 'dinsa ya wuce Kai tsaye ya kwanta sbd har time 'din jiyake kaman kansa zai buga Dan har wani jiri ya ke gani.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_[7/29, 8:55 AM] ‪+234 703 233 7874‬: *_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*29*

Arikice shanty takamota tana girgixata da qarfi cikin tashin hankali Amma ba alamar ko numfashi atareda ita bare tasakaran zata motsa.,,

Kallon Nana dake risgar kuka cikin tashin hankali tayi tace,

Kamomin ita maza,
Mota suka sakata cikin mota aguje ta Isa specialist da ita kafin takira anty fannah tafa'da Mata abinda ke faruwa.

Sumane kawai anty fannah batayiba Jin mummunan zancen cikin qoqarin danne kukanta tace gatanan qarasowa asibitin,
Tana kashe wayar tasaki kuka ahankali jikinta na matuqar rawa Dan tasan rashin ganin Mahmud barazanace ga kwanciyar hankali da dadda'dar rayuwarsu musamman ayshah datasan zaucewama zatayi.

Kodata isa asibitin ayshahn ta farko Banda hauka Babu abinda take musu Sai ririqeta akeyi tana ganin anty fannah tasaki wani irin kuka Mai qarfi tareda fadawa jikinta tana cewa,

Anty fannah Mahmud 'dina,,,,I can't live without my son,,,,, Mahmud is my life,,,my Mahmud.....

Kukane yaci qarfinta ta rintse idanuwa tana rerosa da qarfi..

Anty fannah da shanty ma duk kukan suke Nana kuwa ita ko magana ba'ayi.

Police sukaje suka bada report tareda zube maqudan ku'di Nan da Nan suka 'dau bayanai suka fara nemansa cikin gaggawa.

Gida suka koma Amma ayshah ko Zama kasayi tayi ta zari mukullin mota ta Fice da sauri suka bita Nan suka fara yawo cikin gari lungu da saqo suna nemansa ganin dare yafarayi ba alamar ganinsa yasa ayshah qara rikicewa Banda kukan tashin hankali Babu abinda takeyi,,

Daqyar suka samu suka tirsasata suka dawo gida cikin dare..

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun safe suna yawo Amma ba alamar nasara suna dawowa gida wani mugun zazza6i ya rufeta sbd kuka da rashin cin abinci danko ruwa su anty sunyi sunyi Amma Sam ko kallon abinci tason yi Banda kuka ba abinda take iyayi.

Police sunyi iya yinsu har tsawon sati biyu ba wani bayani Sai kawai suka aje case 'din gefe,,,

Duk inda hankalin anty fannah da shanty yake ya matuqar tashi sbd halinda ayshah ke ciki Dan kuwa sosai ciwo ya kwantar da ita tayi wata irin muguwar Rama ta yamutse ta Fice hayyacinta sbd komaima sabo yadawo Mata ciwon rabuwa da iyayenta Dana 6atan 'danta da yanda rayuwarta ta ta6ar6are duk komai ya taru ya zautata.

Anty fannah ma tuni kwanciyar hankali yayi Mata qaura duk ta rame sbd ganin yanda ayshan takoma kamar Wadda tayi shekaru cikin ciwo,,

Sunyi yawon asibitota harsun gaji Amma Babu wani sauqi..

Wata biyu da 6atan mahmud ciwo ya kwantar da ayshah suka kwanta asibiti jinya..

Zaune take bakin gadon 'dakin datake cikin mummunan yanayi Dan ko gani sosai batayi yanzu sbd kuka dayafara cinye Mata lafiyar Ido.

Daqyar shanty dake zaune ta lalla6ata takamota suka fito wajen 'dakin kota 'dan sake maimakon ciki Banda ajiyar zuciyan kuka ba abinda take Dan yanxuma kukan bai zuwa saidai na zuci dayafi ciwo.

Wata kyakkyawar lady ce ta nufo aminity word 'din cikin shiga ta alfarma ta dogon hijab maroon har qasa daya matuqar qayata kalar fatarta hannuwanta sunci adon Jan lalle hakama qafafuwanta wasu matsiyatan heels ne duk da hijab ne ajikinta,

Murmushi fuskarta ke bayyanawa har haqoranta na 'dan bayyana ta qaraso gurin wasu Mata dake zaune kan qatuwar dadduma suna fira daganinsu kasan gidan masu tsananin arxiki suka fito.

Cikin farin ciki suka tarbeta tareda 'yan rakiyanta guda biyu dake bayanta,
Kujera aka 'dauko Mata da sauri aka aje Mata ta zauna cikin sakewar fuska takalli dattijuwar ciki tace,

Haj babba Ina wuni,,

Lpia klau *_siyama_* ya gida ya nuraddeen da jama'a.

Murmushi tasaki cikin Jin da'din tambayar mijinta da akayi tace,

Alhamdulillah hajiya ya mama da jiki?

Taji sauqi Dan muna sakaran sallama yau ko gobe insha Allah.

Allah yasa su sallameku yau Dan inason nayi fira da mama kafin gobe mu wuce sbd yanada wani taron manyan malamai dazasuyi a Madina insha Allah.

Ok Allah ya taimaka ai gskia nuraddeen Yana qoqari Dan wlh samun irinsa acikin sa'anninsa zaiyi wuya ta yanda yake yiwa addini yaqi da hidima duk da dai ba acikinsa yatasoba mudai saidai muce Allah yasakawa Wanda yayi jahadin musuluntar dashi,ke Kuma Allah yabaku Zama lpia da zuria Mai albarka.

Amin""""tace cikin farin ciki da Jin da'din anyabi farin cikinta ma'ana mijinta.

Ayshah datun zuwan matar taji zuciyarta na Mata nauyin ganinta ta rintse ido Amma Jin abinda suka fa'da yatabbar Mata dako matar wace,.

Jitayi tana qoqarin ha'diye wani Abu daya tsaya maqoshinta Yana neman danne numfashinta ta miqe da qyar tabar gurin zuciyarta na gaf da bugawa..

Ganin yanayinta yasa shanty saurin Kiran nurses tareda Dr Nan suka fara qoqarin dubata sbd numfashinta dake sama sama kaman zai fita...

Wani qarfine da mummunan 6acin Rai suka taso Mata ta fusge hannunta da ake qaqarin zubawa ruwan allura ta cannula.

Riqota shanty tayi cikin tsoron sabon yanayin data ganta ta girgixa Sai kawai ta fashe da wani irin kuka Mai tafasa zuciya.

Sanyi jikin shanty yayi ta zauna kusada ita tareda dafata cikin sanyin murya tace,

Ayshah Dan Allah kiyi hkr ki rungumi qaddarar Allah har zuwa lokacinda Allah zai iyakance miki..

Tsananta kukanta tayi ta 'dago cikin kuka tace,

Shanty na rasa komai duk sbd soyayyar Wanda ba Sona yakeba amfani yakeso kawai yayi Dani,

Shanty rayuwata ta lalace sbd mugun mutumin da yake Kiran kansa da shaikh yanxu,,

Na rasa komai na rasa kowa Banda abinda zan dogara dashi naji qarfin gwiwar qarasa rayuwata.,
Shanty I'm nothing but a loose...
Inama ace zan manta komai nakoma rayuwata ta da,,,inama ace Zan iya ciresa a Raina kwata kwata batareda na tunosa Koda na second 'daya bane,,,,,

Shanty I can't bear this pain anymore,,, it is really hurting...I can't bear it.,,,ji nake gwaramin mutuwa sbd kowa bayasona,,,,
Basa Sona basa buqatana sbd laifi qalilan Kuma naso subani dama na gyara babban kuskuren Dana tafka...
Gashi mahmud 'dina baya taredani duk nasarasa mutanen danake tsananin so da qauna a rayuwa so what is the point of living in misery....

Rufe Mata baki shanty tayi cikin tsananin tausayinta cikin hawaye tace,

You're my best my only friend I can't see you suffering like this I promise you won't feel this pain again,,,you'll be happy again my eshaaa insha Allah..

Bu'de hanbag 'dinta tayi ta 'dauko wasu qwayoyi ta miqawa ayshah tace,

Take this now and I promise you won't feel a thing again...

Kallonta ayshah tayi da jajayen idanuwanta ta kawai da Kai saikuma wata zuciyar ta ingizata ta kar6a Tasha batareda dogon tunaniba sbd kawai buqatarta ta dainajin ra'dadin da ciwon datakeji cikin zuciyarta..

Kanta taji yafara 'dan juyawa ta 'dago takalli shanty saitaga biyu biyu take ganinta Nan ta tashi tana bin 'dakin da kallo Yana juya Mata saitaji abin namata nisha'di Dan kamar a sama take jinta.....

_mugun mafari_,,,

Sannu ahankali saiga ayshah ta warware Ras kamar ba itaba tuni aka sallamesu suka dawo gida duk da anty fannah tayi mamakin ganin sauyin gaggawa daga ayshan Amma saita dangana hakan da adduar datake kwana tanayi Mata.

Ayshah kuwa sabuwar duniyar sha aka shiga Dan kuwa tuni takoma school duk wata mashaya yanxu tare suke zuwa da shanty Wanda Nan take idanuwanta suka qara bu'dewa ta qara zanzarewa Dan yanxu ko Zama gida Basu cika ba kullum suna club suyi nis su lalla6o gida su kwanta,,,,,

Lokuta da dama tana idan tana cikin hayyacinta zaunawa take tayi kuka kamar ranta zai fita sbd ganin mummunar rayuwar data tsinci kanta sanadiyar iyayenta da Deen,,,
Tanason dainawa Amma abin yayi matuqar shiga jikinta Bata iyawa Dan yanxu shiga kowace iri taga dama yitake ta fita sbd abin ba qaramin fara shiga cikin kanta yayiba Dan ita Shan hauka takeyi harsaida shanty tafara Dana sanin sata aharkar.

Anty fannah alamarin duniya ya taru yasata gaba tayi kukan harta gaji Amma ayshah ta zare ko maganarta ba wani jitakeyiba saidai idan abin yasaketa tazo tana kuka tana Bata hakuri.,,,

Tun anty fannah na 'daukar abin da sauqi harta gaji tafara tsanantawa ayshah Amma maimakon sauqi saima ayshah ta qara zarewa danko gida Bata dawowa wataran idan sukayi dare saidai takwana gidansu shanty.

Rama da ciwo yafarasaka anty fannah gaba danko fita office Bata iyayi tayi kuka tayi addua tayi fa'da Amma ba wani sauqi Sai kawai ta tattara kayanta tabar gidan bayan ta rubutawa ayshah wasiqa.

Yau da wuri tadawo Qarfe bakwai parking tayi taga ba motar anty fannah gabanta taji ya'dan fa'di sbd tasan anty fannah batada lpia Bata fita ko'ina tunda da'dewa,

Fitowa tayi riqeda handbag dinta cikin shigar doguwar straight gown ta English wear black Sai blue Vail 'daure akanta da blue designer takalmi masu tudu sosai.,,,

Tayi haske saidai Rama dake tattare da ita dakaga idanuwanta zakayi zargin tana kora qwayoyi sbd a wani lumshe suke.
Chapter 22 · 0% Book details