← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sweetie kazauna gida gurin mummy Mana idan zamu dawo I promise to buy ice cream for you my boy.

Maqe kafa'da yayi Yana Shirin yin kuka tajuyo takalli anty fannah sbd baita6a cewa saiya bitaba idan zata fita yafi yiwa anty fannah haka.

Riqosa anty fannah tayi ya fashe da kuka tareda fa'duwa qasa Yana Shure Shure.

Kamo hannunsa shanty tayi tareda tayardashi ta 'daukesa takalli Nana tace,

Jeki 'dauko hijab dinki muje ki riqesa.

Da gudu Nana ta 'dauko Dan akwaita dason yawa da wasa Dan akwai sauran 'dabi'un qauye atareda ita.

Tunda suka fito tayi tsit gabanta na fa'duwa hakanan taji hankalinta na tashi
Shanty dake driving ta juyo ta'dan kalleta tace,

Whats wrong eshaah?...sunan datafi kiranta dashi kenan.

I just don't know but I'm having some strange feelings.

Ba komai eshaah just relax okay.

Wata qatuwar shopping complex suka Parker suka fito tareda shiga.

Mahmud dake hannun Nana riqe Yana hango 6angaren kayan wasa yayi can da gudu Yana cewa Nana,, yeeyyyy catch me if you can.,
Binsa tayida gudu dai lokacinda idanuwan ayshah suka sauka kan qatuwar plasma tv dake gurin,,,
Fuskar Deen ce bayyane jikin tv 'din cikin taron dubban jama'a fatarsa kawai ta Isa ta nuna tsananin hutu da kwanciyar hankinda yake ciki tareda farin ciki.,

Bodyguards taga sunata faman kakkaresa masu 'daukar hoto da Yan jarida Sai rige rige suke yaci wani irin ado cikin dark blue shadda da maiqonta kawai ya bayyana tsananin tsadarta....

Kai Amma wlh yau nataya shaikh nuraddeen auren dayayi Dan kuwa Yana matuqar tausayi da taimakon addini Dan kuwa shika'dai ne matashin babban shaikh damuke taqama dashi a qasashen qetare..

Hmmmnn kaidai jabir Bari wlh ni Yana matuqar burgeni daya za6i zamowa babban masani akan addini maimakon wani aikin Kuma qarin abin burgewa shine dayazo gida Nigeria ya za6i Mata ya aura.....

'dauke Kai tayi tana qoqarin danne abinda yake taso Mata Amma tuni wani wawan jiri ya 'dibeta shanty tayi saurin tareta kafin tayi magana saiga Nana a guje hankali tashe kamar zautacciya tace,

Anty anty wasu sun 'dauke Mahmud sun gudu dashi a mota.

Wat'"shanty tace da qarfi tareda sakin ayshah da itama tuni ta girgije ta kwasa waje da gudu suka bita tareda sauran ma'aikatan Amma Ina suna fita motar na barin gurin.
Kawai Sai ganin sukayi ayshah ta yanke jiki ta fa'di.

Mamuh??

_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*30*

*_gskia I really appreciate_*😍
*_masoyan taura biyu_*💋

Zaune take gaban mum Banda tsayayar hawaye ba abinda take sbd duk duniya batajin zata iya abinda mum 'din tace na cewar ta cire muh'd cikin ranta sbd tasan ba abune Mai yiyuwa ba,

Cikin baqin ciki da damuwa mum 'din tace,

I will never forgive that horrible ninja lady for wat she has done to my family,,
The family I build with so much love,
She distroy everything for me,,,,

Cikin hawaye Khadija (Davina) tace,

Mum please stop blaming ayshah sbd mu muka dama muka za6i rayuwar datafi, rayuwa Mai 'dorewa ta gobe a qiyama,,

Tashi mum 'din tayi jiki a sanyaye sbd gabaki 'daya yanxu Bata iya zaman mintuna da 'yayanta sbd zancen addininsu dasuke yimata akoda yaushe.

Cikin sallama yashigo qayataccen palon Yana tashin qamshin turaren Arabian oud cikin farar tsadaddiyar jallabiya fara blue Sai Kyau da hasken fatarsa ya da'da bayyana.

Kallo 'daya mum tayi Masa ta 'dauke Kai ta nufi hanyar bedroom 'dinta yayi saurin Shan gabanta tareda riqo hannunta fuskarsa 'dauke da wani lallausan murmushi yace,

My sweet mum please don't stop ignoring me like this,,
I love you so very much mum so will you please stop ignoring me mum,,

Kallonsa tayi tayi son 'danta da kewarsa na 'dawainiya da ita ta rintse ido tareda juyawa zatabar gurin..

Granny,,,,

Cak ta tsaya tareda sakin tareda juyowa Nan take tasaki fuska kamar ba itaba da gudu ya qaraso gurinta ta 'daukesa sama duk da yaqara girma sosai tace,

I miss you so much my beautiful boy..

Kumatunta yaja cikin dariya kamar yanda taja nasa yace,

I miss you too granny but I won't stay with you today since you're angry with my daddy.

Bedroom 'dinta ta nufa dashi tana cewa,

Your daddy is a stubborn man he doesn't care for me now....

Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka 'dan bayyana sbd yasan mum ta sauko sosai sbd tsananin sonda takewa mahmud Amma yakasa gane meyasa ta tsani ko sunan uwar Mahmud 'din afada.

Juyowa yayi gefen Khadija dayar kolacin take zaune tana kuka ahankali ya zauna a sofa Yana kallonta yace,

Menene Kuma Khadija?

Ahankali tace,

Shaikh just pray for me sbd naji ajikina nice Zan biya dukkanin haqqin ayshah da aka zalunta Dan kuwa tun yanxu nafara ganin ishara Kuma na tabbatarda duk inda ayshah take Bata cikin kwanciyar hankali tunda Bata tareda iyayenta da 'danta duk sbd soyayya.,,,,

Katseta yayi cikin 'dan yamutse fuska yace,

Karki ha'da kanki da ita sbd ita itace ta za6i kawo 'danta dantayi rayuwar dataga dama afterall tasan inda nake tunda harta kawomin 'dana so inda tanada niyyar Zama Dani da tuni ta bayyana kanta Amma she chooses to stay away and wani gefen zuciyana is telling me we are better without each other.....

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta tana girgixa Kai cikin kuka tace,

Shaikh kaiba butulu bane karkayi butulci da raharamarda Allah yayi maka ta musulunci ta dalilinta,
Shaikh kome ayshah tazama arayuwa Kaine sanadi,
Koda yake basai nafada ba Zaku gani akaina duk da banjiba banganiba Amma haqqi zai sauka akaina.

Miqewa yayi batareda yakuma tanka zancentaba yace,

Maganar zuwana Nigeria ne yataso sbd gobe Zan wuce insha Allah if you're still interested in coming with us ki shirya.

Wucewa yayi yabarta farin ciki na ratsa zuciyarta najin maganar zuwansu Nigeria zataje taga muh'd dinta.

Washe gari shida matarsa siyama da 'dansu mahmud tareda Khadija suka diro Nigeria suka baro mum cikin 'dibbin damuwar ganin gabaki 'daya yayanta yanxu kamar ba nataba nantafara tunanin mezai Hana tabi nasu addinin matuqar familynsu zai qara Zama Happy family kamar da.

A qaton lafiyayyan gidansa dake asokoro suka sauka Wanda Nan aka qaro securities agidan
Siyama hankalinta ya qara kwantawa Dan dama tafison zamansu a Nigeria akan can Paris 'din,,

Babbar damuwa da tashin hankalinda take ciki shine rashin haihuwarta har yanxu,,
Tayita yimasa compain akan hakan Amma bai damu ba sbd ganin mahmud dayake jinsa cikin jinin jikinsa Dan ba qaramin so yakewa yaronba.
Hakan yasa gabaki 'daya hankalinta ya tashi dason haihuwa sbd batason Koda wasa yayi tunanin maido karuwarsa tada Dan ita Bata 'dauketa matarsaba saidai karuwa Dan bataga dalilin ha'da shimfida da kafiriba tunda alokacin yanada sauran dabiar kafirai ataredashi.

********
Wani qaton babban hotel daya amsa sunansa na manyan mutane,

Acikinsa akwai manyan halls na alfarma dan meetings ko taron manyan mutane.,

Hakama akwai club na 'yayan manya dake cikin gurin Wanda ya tsaru ya ha'du ba kadanba.,,

Zaune take cikin club 'din tayi crossing legs tana sanye da wata designer English gown red datayi masifar yimata kyau sbd kwantawar datayi ajikinta Sai wani siririn black scarf Mai adon red data 'daure gashinta gefe dashi Wanda duk Rabin gashinta a waje yake sbd tsawonsa Sai hakan ya qara Mata kyau,,

Abuge take banda lumshe idanu ba abinda take shanty dake zaune gefenta waya take tana kur6a ruwan qwayoyi ahankali tana lumshe ido,,,

Wani kyakkyawan saurayine ya qaraso gurinsu cikin qasaita na kasancewarsa 'dan senator ya kalli Ayshah dako kallo bai ishetaba yace,

Eshaah my love look at me please,,,,look wat your love has done to m..

Banza tayi dashi tareda 'daka cup 'din dake gabanta ta shanye zuciyarta na tafasa taji Bata dainajin qunar zuciyarba ta 'daga wani cup 'din takai bakinta yayi saurin Kai hannunsa zai riqe cup 'din ta miqe tsaye ta 'daga hannu ta sharara Masa wani lafiyayyan Mari Nan take 'yan koransa sukayo kanta kafin suyi wani yunqurin takuma yanka Masa wani Marin Nan take guri ya kaure da hayaniyar fa'da sbd wani 'dan governor dayake matuqar son ayshan ya shiga fadan dama yanajin haushin Abbas 'din sbd yanason ayshah Nan suka hau fa'da harda fasa kwalabe.

Shanty datafi ayshah qarfin jini Dan yanada wuya ta bugu duk abinda Tasha kuwa,
Kamo hannun ayshar tayi suka fito harabar hotel 'din inda Nan take gurin yacika sbd fadan Nan yadawo.

Fixge hannunta tayi cikin maye tace,

Let go of me shanty,,,I'm not done,,,let me teach the bastard a lesson...

Fitowarsa kenan daga meeting 'din dasukayi agurin yayi mamakin ganin mutane agurin tunda ko hayaniya ba'ayi sosai agurin.

Kamar a mafarki idanuwanta suka sauka akansa ta lumshesu tasake bu'dewa sai kawai tasaki dariya Mai qarfi cikin tsananin maye tareda nunasa tace,

There he is,,,,the one and only Niklaus Aiden,
The greatest cheat so far...

Kanta securities dinsa sukayo sbd tuni gurin yayi tsit kallo Yakoma kansu ganin tana qoqarin 6atawa shaikh suna cikin bainar jama'a Amma Abbas yayi saurin Shan gabansu cikin rashin mutunci yace,,,,.

Karku fara ta6amin babe okay...

Dariya takuma saki tareda nunasa cikin maye tareda kallon shanty da juyayun idanuwanta tace,

Look at him shanty my sweet friend,,,
He is the father of my poor son Mahmud...

He is nothing but a cheat,,,,he uses me and run away like a,,,,, like a,,,
Yesssss like a mosquito..hahhhhhhh

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa gashi tuni yafara ganin hasken cameras na tashi ana 'dauka koba'a fa'daba ya tabbatarda itace ayshah uwar 'dansa,,,

Kanta securities sukayo tayi saurin zillewa tana dariya ta isa gabansa takallesa from head cikin dariya ta ta6a Masa tana cewa,

Wow Mama's boy yatara muscles bayan yasha duka agunsu ummmmnnn Yama sunansa,,,,,yesss ya Umar the great heartless parson of the universe,,,,look shanty everyone look"""""tafada tana qoqarin Kai hannunta kan damutsansa cikin tsananin 6acin Rai da baqin ciki ya watsa Mata Marin dayasa Rabin mayen dake tareda ita sakinta ya fa'da mota da qarfi driver yaja sukabar gurin wasu na tir da halinsa na 6oye da yau tsohuwar karuwarsa ta tona..

Ita kuwa baqin ciki takaici da danasani ne suka shigeta na abinda tayi cikin mayen shanty tajata sukabar gurin..
Chapter 17 · 0% Book details