← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wawan Mari ayshah tasakar Bata batareda tayi tsammaniba takuma tureta tareda fitowa daga palon ta qwala Kiran Mai aikin dakeda suna Fatima.

Da sauri fatimar ta iso jikinta na rawa ayshah ta kalleta fuska a 'daure tace,

Wuce maza ki kwaso kayan Nan ki aje duk aikin dakike Kona waye ki wankemin su now..

Fitowa siyama tayi cikin zafin Rai da zafin Marin datasha ta kalli fatima ta daka Mata tsawa tuni jikin yarinyar ya'dau rawa sbd ganin tana tsaka...

Kallon siyama ayshah tayi cikin takaici kafin ta juyo takalli Fatima Sai kawai takama hannun fatimar tajata zuwa part 'din Deen.

Da sauri siyama tabi bayansu tana Kiran sunan fatimar a fusace,

Zaune yake a palon Yana waya sanye yakeda qananan Kaya sai wani qyallin kyau fatarsa take Sai ganinta yayi gabansa ba zato,.

Kayan dake jikinta yafara kallo tunda sama har qasa ya dan tsuke fuska sbd fa'duwar da gabansa yayi,,,

Maida kallonsa kan siyama dake cika tana batsewa yayi hankali kwance yace,

Ya akayi ne?

Cikin 'dage gira ayshah tace,

Nizaka kalla Dan nice zanyi magana,

Kan tv ya maida fuskarsa Yana cewa,

Then speak.

Cikin takaici tace,

Wannan me aikin waye yake biyanta agidan Nan?

Kallonta yayi cikin mamaki da takaici yace,

Idan baniba kece kike biyanta?

Just answer the question bance ka fadamin maganaba.

Yana kuma maida kallonsa ga tv yace,

Nine nake biyanta,.

Nikuma menene sunan matsayina agidan Nan?

Mata"""""yafada Kai tsaye batareda ya juyo ya kalletaba sbd yagano Sarai masifa takeji shikuma bazai iyaba yanxu.

To hakan ne gud for nothing matarka takasa ganewa sbd she's insane so just tell her karta Kuma shiga harkana daga yau sbd next time I won't be nice like this...ok..

Juyawa tayi tabar gurin yabita da kallon mamaki baki asake harta fice kafin yamaido kallonsa kan siyama cikin 'daure fuska yace,

karki Kuma tsokanota Cox she's nothing but trouble so idan bazaki iya tsayawa gurinki ba harsaikin je neman fa'da to karkiga laifina akan irin hukuncin dazan riqayi.

Miqewa yayi yashige bedroom dinsa yabarta tsaye kamar zatayi bindiga sbd baqin ciki da takaici.

Itakuwa tana komawa fatima ta kwashi kayan tafice dasu jiki na rawa ita kuwa kasa Zama tayi a palon ma tashige bedroom 'dinta ta kwanta.

Bayan two days da faruwar haka ta fito part 'dinta tana Shan waqar single ladies ta Beyonce a wayarta ta nufi 'dakin Khadija dake kusada part 'din siyama.

Siyama dake zaune balcony 'dinta tana gyaran farce tahangota Nan take taji duk annurin zuciyarta ya gushe sbd ganin baiwar kyawu da diri da ayshan takedashi,,

Gefen Deen takalla taga Yana zaune shima a balcony 'dinsa Yana karatu ga dukkan alama shibaima lurada itaba hankalinsa nakan abinda yake karantawa,

Saurin tasowa tayi sbd Sam batason mijinta yaga ayshan ahaka,

Gabanta Tasha tareda jifanta da wani wulaqantancen kallo tundaga sama har qasa kafin tace,

Kindaisan Nan ba gidan gala bane dazaki ringa shigarda kikaga dama idanma kina tunanin 'daukar hankalin mijina ne then you're wasting your time sbd mijina bashida sha'awa akan matan bariki hasalima kallon maza yake musu ba Mata ba so just go back inside and change kafin ki Kuma fitowa.

Kashe wayarta tayi tareda sakata cikin aljihun jins 'din dake jikinta ta kalli siyamar taga kishi qarara bayyane cikin idanuwanta cikin ranta tace,

Lallai ma wannan matar tacika Yar rainin wayo nida nakeda mijin tun farko na danne abinda nakeji shine zata kawo min rainin hankali lallai kuwa Zan daidaita Mata sahu na koya Mata hankali.

Murmushi tasaki na rainin wayo tace,

Kina tunanin inada abinda zanyi da wancan mijin naki?
Banda abinyi dashi Amma Zan nuna Miki Koda na lalace ahaka shi yanada abinyi Dani idanma bayada Zan nuna Miki mijinki baida tabbas.

Kallon kanta tayi taga dogon pencil jeans ne blue daya matse 'yan cinyoyinta sosai red top Mara hannu Sai 'yar jacket Mara nauyi data 'dora akai ko 'dankwali Babu akanta,

Murmushin mugunta tasaki tareda kashe Mata ido 'days ta nuna Deen da idanu tace,

Just wait and watch...

Jacket 'din jikinta ta zare tabar taciki ta nufi gurinsa tana zare ribbon 'din data 'daure kanta dashi.

Saidata Kusa Isa gurinsa ta tasaki qara tareda qarasawa gurinsa da sauri tana ihu...

'dagowa yayi da sauri tareda miqewa tsaye kafin yayi wani motsi ta shige jikinsa ta cukuikuye tana ihun Kiran scorpion.

A tsorace ya 'dago da ita daga jikinsa Amma Sai qara shigewa jikinsa take tana ihun kuka kamar da gaske....

Rintse idanuwansa yayi kansa na sarawa sbd hoton ranar da irin haka tafaru a tsakaninsu can baya ya dawo masa.

Girgixasa tana sakin kukan qarya yayi saurin 'dagota cikin kasala Yana kallon cikin idanuwanta wasu abubuwa na qoqarin dawo masa yace,

Calm down ayshah ba wani scorpion anan.,,,

'dagowa tayi ta kallesa sbd Jin kasalalliyar muryar dayayi magana da ita tace,

Akwai scorpion anan'''""" ta fa'da cikin shagwa6a tana nuna cikin rigarta,.

Hannuwansa dake riqe da ita ya 'daga 'daya ya nufi cikin rigar ahankali jikinsa na tsananta mutuwa.

Gefen siyama dake daskare cikin tsananin mamaki da takaici tareda baqin ciki ta kalla tasakar Mata wani mugun murmushin mugunta Jin hannunsa ya sauka cikin rigarta yasa tayi saurin zamewa tana ha'de fuska Amma ganin siyama ta nufosu a zuciye saitayi saurin komawa jikinsa tana cewa,

Ba anan yakamata acire scorpion 'dinba we need some privacy.

Hakanan yakasa Musa Mata ta jasa suka shige part 'dinsa ta turo qoafar da qafarta sukabar siyama tsaye sake da baki jiri na neman zubarda ita.

Suna shiga ta fixge jikinta tareda harararsa tana qarasawa tsakiyar palon ta kwanta a 'daya daga royal kushins dake palon ta canxa Tasha zuwa boomtv.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_[7/29, 5:22 PM] prince_s_square: *_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*33*

Qarfe bakwai na safe motar muh'd tashigo harabar gidan badan yasoba sbd tun ranarda Deen yamaido ayshah gidan ya yafe gidan gabaki sbd zuciyarsa bazata ta6a iya 'daukar ganin ayshah da waninsa ba.,
Amma yau dolece sbd tun jiya mum ke Kiran Deen Bata samunsa shine takirashi ta sanardashi mutuwar Finn cikin tsananin kuka da tashin hankali gashi daddynsu tuni Yakoma Madina da Zama saidai yakan ziyarceta time to time.,
Ga Deen da Khadija basanan tayi kuka harta gaji shine ta yanke shawara ta sallami duka masu aikinta da zarah Mai kulada mahmud tayo Nigeria gurin 'yayanta danta gaji da muguwar rayuwar ka'daicin datake ciki tana buqatar 'yayanta atareda ita Koda hakan na nufin saita musulunta infact she's ready to become Muslim kamar mijinta da yaranta musamman ma Mahmud shiyasa tana dirowa qasar takira muh'd yazo ya 'dauketa.

Bu'de qofa yayi yafito riqeda mahmud ya zagayo ya bu'de Mata qofar ta fito tun anan jikinta yayi mugun sanyi sbd ganin baiwa da 'daukakar da Allah yayiwa 'danta ta hanyar musulunci.

Tundaga nesa Khadija ta hango mum 'din da gudu ta fito ta rungume mahaifiyarta tareda sakin kuka ahankali sbd tana tsananin tausayin kanta da mum 'dinsu sbd suna cikin tsananin ka'daicin rayuwa musamman yanxu da iyakacinta cikin daki ko gate Deen ya hanata kaiwa bare ta fita.

Lafiyayyen 'dakin Khadija mum tasauka shikuwa muh'd palon Deen yaje ya zauna Yana cigaba da kiransa a waya sbd ko alamar siyama baiganiba bare tafadowa Deen 'din.

Mahmud kuwa da gudu ya nufi bedroom 'din daddynsa Yana kwala Kiran sunansa cikin farin ciki.

'dago Kai yayi daqyar yana ganin Mahmud 'din ya saki murmushin qarfin hali da farin cikin ganin 'dansa ya tashi zaune ya rungumesa.

Assalamualaikum daddy""""yafada Yana tashi daga jikin daddyn nasa tareda miqa Masa 'dan qaramin hannunsa.

Wa'alaikm Salam my boy'""""yafada Yana miqa Masa hannu kafin ya miqe tsaye ya fito dashi Palo Yana ganin muh'd a zaune ya qara sakin fuska tareda miqa Masa hannu suka gaisa ya zauna nan muh'd yafada Masa abinda ke faruwa.

Shiru yayi Yana maimaita innalillahi cikeda tausayin 'dan uwansa sbd ya mutu bai samu arzikin musuluntaba.

Miqewa yayi suka fito suka nufi gurin mum 'din muh'd kuwa noqewa yayi ya tafiyarsa sbd ko ganin Khadija ko ayshah baya son yayi.

Mum na ganinsa ta taso da sauri ta rungumesa tareda sakin kuka ahankali.

Bubbuga bayanta yariqa yi Yana cewa it's ok mum, everything will be fine insha Allah.

Zaunar da ita yayi bakin gado tareda riqo hannayenta biyu yace,

Mum ayshah is here and....

Da sauri ta 'dago ta kallesa yayi shiru taredayin qasa da Kai.

Murmushi tasaki tareda 'dago fuskarsa tace,

I'm happy to hear that sweetheart,,
Your happiness is always my happiness, she won't face anything from me I promise afterall she's my sweet little Mahmud's mother,,,and I'm really sorry for....

Girgixa Mata Kai yayi tareda cewa,

Mother's don't apologise to their children.

I love you my sweet boy.

I love you too mum.

Wayarsa ya fitar ya Danna Kiran siyama don ayi gaggawar shiryawa mum 'din abinci.

Saidata Kusa katsewa ta 'dauka a daqile tayi sallama,,
Shima a qasan maqoshi ya amsa tareda cewa tazo ta gaida mum yanzu a 6angaren Khadija.

Fuska ka 'daure sosai kamar zatayi kuka cikin baqin ciki tace,

Another problem has arrived mitswww.

Abinda Bata saniba shine yaji abinda tafada ransa yayi mummunan 6aci Amma saiya qyale kawai.

Saidata share kusan rabin awa kafin ta iso tashigo fuska ba walwala ta gaida mum 'din.

Baki mum tasaki ganin irin gaisuwar rainin wayo da siyamar tayi Mata Nan take ta 'daure fuska zata yiwa siyamar kaca kaca saita tunoda tayi alqawarin Kama girmanta sbd Deen 'din ta amsa tana qaqalo murmushi Amma cikin zuciyarta tsana da takaicin siyamar ne fal.

Qoqarin juyawa take cikin 'daurewar fuska yace,

Prepare something for mum to eat yanxu.

Danne takaicinta tayi takallesa cikin Ido tace,

Inaga wannan ba aikina bane sbd banice da girki ba idan ka manta jiya agurin tsintacciyar matarka ka kwana.

Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka 'dan bayyana yace,

Yes you're right na mantane you can leave Zan kirata ita tayi.

Haushinsa ne ya qara turnuqeta ta Fice cikin takaici kamar zata daki iska.

Daqyar ta tashi tayi wanka fuskarta duk a kumbure sbd kukan data kwanayi wannan karon doguwar rigace ajikinta Mara hannu ta jawo qaramar hula tasaka duk gashinta a waje sbd Bata kamasaba Kai tsaye 'dakin Khadija ta nufa sbd number shanty takeso ta duba wayarta taga komai ya goge.
Chapter 19 · 0% Book details