← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayshah kuwa Banda kuka Babu abinda take Dan kuwa ko hannunta Bata iya 'dagawa.

Daqyar yasamu ya daidaito numfashinsa ya jawota jikinsa ya rungume cikin wani mugun sonta dake qara hudasa yafara lallashinta.

Wahallalen bacci da zazza6ine suka dauketa ya sauko gadon ahankali tareda kunna wayarsa yakira shaikh yayi masa bayanin yanda zaiyi wankan janaba ya fa'da toilet yayo wanka yadawo bakin gadon yazauna gadinta sonta da tausayinta na shigarsa.

Lokacinda ta farka bacci ya 'daukesa a gurin ta saki wani sabon kuka zuciyarta na karyewa ga mugun zazza6in datakeji.

Kukantane ya tadashi ya tashi da sauri ya zauna kusada ita tareda juwota yafara lallashinta kaman zaiyi kukan shima.

Daqyar yasamu tayi wanka ya dawo da ita sukayi sallar azahar da ake Kira.

Abu kaman wasa saigasu da kwana uku a gurin Dan tuni soyayya tayi tasirin shagaltar dasu suka Sha amarcinsu ba damuwar komai.

Yau tunda ta tashi gabanta ke fa'duwa sbd motarsu da aka gama gyarawa Kuma ayau 'din zasu koma gida.

Tsaye take gaban mirror 'daure da towel tayi zuru cikin tunani ya duqo tareda rungumota ta baya ya 'dora kanshi saman wuyanta a kasalance yace,

My love..

Juyowa tayi ta kallesa ya hure Mata ido tareda kissing idon bayan ta lumshe yace,

Baby let's stay here I don't want to go back.

Shigewa jikinsa tayi ta kwantarda Kai a sanyaye tace,

No Deen let's go home.

Kanta dake jiqe da ruwan wankan tsarkin datayi ya shafa Yana cewa,

Ok but I will take you to a saloon to dry this hair first.

Bata basa amsaba sbd bakinta daya cafke da nasa Yana kallon eyes dinta data lumshe...Nan yaqara shagaltar dasu Saida suka Kuma making love kafin sukai wanka a gaggauce suka fito.

Driving yake Amma hannunsa 'daya na riqeda nata harsuka iso cikin gari..

Tana ganin ya Kama hanyar anguwarsu hawayen datake riqewa suka 6alle Mata yayi saurin yin parking ya jawota jikinsa.

Sun 'dan Jima ahaka kafin tayi qarfin halin janyewa tace,

Yatafi zata qarasa da qafa Dan batason yashiga anguwar Dan koba'a fa'daba tasan fitina nacan qasa tana jiransu musamman mashi da komai zai iya faruwa dashi idan yashiga anguwar Yan gidansu suka ganshi.

Kallonta yayi cikin damuwa yace,

No ayeeshah I will drop you home.

Riqe hannunsa tayi cikin karyar da kai tace,

Please deen don't be stubborn now.

Badan yasoba ya yarda ta yabarta ta tafi bayan ya miqa Mata wayarsa 'daya Dan yariqa waya da ita Amma taqi karba.

Saida yaga tashige konar layin gidansu ya iya barin gurin ya nufi gida.

Tun kafin ta qaraso abbakar dake zaune qofar gida tareda Ahmad ya hangota yayi saurin sake kallawa yaga ita 'dince ya Kira sunanta da 'dan qarfi nansu Ahmad suka lura da ita.

Umar dake taredasu baba a Palo Yana yimusu bayanin haryanzu ba wani bayani daga 'yan sanda Sai sukaji ankira sunanta bai qarashe abinda yake fa'daba ya fito da sauri daidai lokacinda tashigo gidan Nan kowa yafito cikeda fargabar yanayin dazasu ganta Amma ga mamakinsu Sai sukaganta lafiya qalau dansu a tunaninsu tanacan suna azabtarda ita kaman yanda akayiwa su baba.

Durqushe tayi gabansu baba malam Banda kuka babu abinda takeyi musamman yanda taga duk sun yamutse sbd tunani da fargabar halinda take ciki.

Saidata sukaga kukan yaqi tsayawa baba malam ya kalleta murya a karye yace,

Ayshah kidaina kukan haka ya Isa kije ciki abata abinci ta huta anjima zanyi magana da ita Kuma Kar Wanda ya tambayeta komai.

Kamata su husna sukayi suka nufi ciki da ita kowa da abinda yake saqawa arai.

Da daddare baba malam ya Tara kowa yakirata cikin 'daure fuska yace,

Ayshah,,

Na'am'''tace muryarta Bata fita sosai.

Ayshah kina saneda yau kwana hudu kenan da 6atanki Kuma 'yan uwanki da sauran mutane sunga lokacin da wannan yaron ya 'daukeki?

Eh ''''''tace hawaye na gangaro Mata.

To yanxu inason sanin abinda yafaru bayan nan Dan 'daukar mataki.

Fa'duwa gabanta yahau yi cikin rawar murya zufa na keto Mata tace,

Wani guri yakaini yace su ajeni Kuma bansake ganinsa ba Sai yau Yana zuwa ya daukoni ya dawo dani.

Kallon tsaf yayi Mata yace,

Inane inda yakaiki?

Share zufa tayi tace,

Bansan ko inaneba sbd 'daure idona akayi.

Mata ne yakaiki gurinsu ko maza?

Mata ne""""ta fa'da da sauri.

Kintabbarda gaskiya Kika fa'damin ayshah.

'daga kai tayi hawayen baqin cikin qaryarda tayi suna gangaro mata.

Cikin zafin zuciya da takaici baba alhaji yace,

Wlh Daman ni nasan sunanmu sukeson 6atawa shiyasa ya 'dauketa yakai ya boye yanxu yadawo da ita Dan mutane suyi tunanin anbata Mata rayuwa.

Tabbas hakane baba malam yafada Yana jinjina alamarin cikin ransa Nan kowa zuciyarsa ta yarda da hakan ne suka hau tofa Masa mugayen adduoi.

Umminta da ya Umar kuwa hakanan zuciyarsu takasa aminta da hakan musamman yanda suka lurada yanda fatarta tayi wani fresh Sai glowing take.

Bayan komai ya lafa ummi takira 'dakinta takuma tambayarta harta bu'de baki zata fa'da Mata saiga babanta yashigo ta ha'diye zancen tareda sunkuyar da Kai Nan suka hau yimata nasihar data matuqar sanyaya jikinta ta koma 'dakinsu tana matsar hawaye.

Da daddare ya Umar ya Aiko kiranta Nan taji gabanta ya Fadi sbd tuno yanxu tanada auren wani akanta.
Hakanan ta miqe jiki ba qwari ta tafi.

Polon mama sakina Daman suke fira can ta nufa mamar na 'daki ta shika'dai ne zaune a palon Yana kallon 'yar qaramar tv 'dinta dake kunne ana tafseer.

A darare ta zauna a qasa kaman yanda tasaba saitaga yadawo kusada ita ya zauna suna fuskantar juna.

Da mamaki ta 'dan 'dago ta kallesa ta 'dauke Kai tareda gaidashi a sanyaye.

Amsawa yayi Yana kallon hannuwanta datake wasa dasu yanajin sonta na shigarsa Dan baigane mahimmancinta a rayuwarsaba saidata 6atan Nan yagane samunta shine kwanciyar hankali da cikar burinsa.

Cikin son nuna canzawarsa ya ringa janta da fira Amma saidai ta 'daga ko girgixa Masa Kai.

Hakadai harsuka Dan dauki Time tukuna yabarta ta tafi yanabin bayanta da kallo.

********

Bai Isa gidaba saidaya tsaya wani masallaci yayi sallar magriba da Isha,,

Tunda yayi horn Mai gadi ya bu'de Masa gate yashigo ya hango mum 'dinsa tafe cikin farin ciki da murnar ganinsa sbd tun sunacan yayi wayada ita ya sanarda ita cewan yayi tafiya da friends 'dinsa motansu ta lalace.

Rungumesa tayi cikin Jin dadi tareda cewa,

I missed you so very late my boy.

Cikin kulawa yace,

I love you mum.

I love you too my sweet boy.

Suna shiga Palo Davina ta taso da gudu ta rungume shi tana cewa,

Wow Nik you look fresh.

Dariya mum tayi tareda cewa,

My boy is slowly becoming a big man right?

Murmushi yasaki fuskarsa na bayyanarda annashuwa yace,

Yes mum your boy has finally become a man.

Batareda ta fahimci zancensaba takama hannunsa suka nufi dinning.

Mamuh??

_dont forget to follow, vote and comment_
[7/18, 10:01 PM] ‪+234 803 314 9202‬: *_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_??
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*24*

Da daddare dukkaninsu kasa bacci sukayi musamman mashi Sai juyi yake kewar matarsa na shigarsa,
itama anata 6angaren lafewa tayi Dan Kar juyin yayi yawa ayi zargin wani Abu.

Washe da asuba cikin 'dakinsa yayi sallarsa Yakoma ya kwanta gari na waye saiga mum da Bible 'dinta tafara jero Masa adduointa yanaji ya lafe kamar maiyin bacci sbd jiyake kaman tana watsa Masa ruwan zafi a kunnuwa.

Tana gamawa ta tadashi tareda kallonsa cikin kulawa tace yatashi ya shirya lokacin zuwa makaranta nayi.

Lumshe fararen lazy eyes 'dinsa yayi yanajin tsananin buqatar son ganin ayshah ya sauko daga gadon ahankali tareda miqewa ya fa'da toilet.

Duk iya zagayen dazaiyi yayi a makaranta da anguwar Amma baiga ko alamar ganinta ba haka ya lalla6a Yakoma gida a wahalce zuciyarsa ba da'di.

Itama dai Kam sukuku ta wuni ba wata walwala gashi ko maganar zuwa makaranta ba Wanda yayi Mata.

Abu kamar wasa saigasu har tsawon sati Basu ga junaba ita Sam anhata fita yanzu shikuma Yayi yawon yayi neman Amma Babu alamarta.

Sati na biyu kenan da yanxu Kuma zuwa lokacin daga shi har ita kowa danginsa sun gano Yana cikin damuwa ita tayi wata irin Rama shikuma rigis ya kwanta ciwo.

Zaune take tana kallon yanda su husna ke Shirin fita zuwa gidan anty Amina a sanyaye ta bu'de baki tace,

Wai sauri da 'dokin me kukeyi na zuwa gida musamman make husna.

Asma'u dake saka hijab tace,

Fa'da Mata zamuyi tazo taga kayan lefen da ya Umar ya ha'da miki.

Duk da batada wani kuzari a jikinta batasan sanda ta tashi zaune ba ta kalli asma'un da kyar tana ha'diye yawu tace,

Lefen me?

Kallon rainin wayo asma'un ta jefeta dashi kafin tace,

Na aurenku Wanda za'ayi Nanda sati biyu.

Hawayen datake dannewa ne suka 6alle Mata tayi saurin juya musu baya kuka na qwace Mata.

Binta da kallo sukayi basuce Kuma cemata komaiba suka fice.

Bayan gadonsu tashige tafara rero kuka cikin tashin hankali tareda rashin sanin abinyi.

Kamar daga sama saiga nuratu tashigo 'dakin tana ganin halinda take ciki ta qaraso gurinta da sauri tana kallon yanda idanuwanta sukai mugun kumburi.

Kasa tambayarta dalilin kukan tayi cikin sanyin murya tace,

Anty ayshah ummi ce tace nazo nace Miki ki shirya mutafi gidan anty Amina muma sbd duk yau zasuso ganin kayan aurenki gwara ki 'dan fita.

Kallon nuratu tayi da jajayen idanuwanta kamar zatace Bata son fita Koda tsakar gidan ne saita tuna tana tsananin buqatar ganinsa Dan sanin abinyi.

Wanke fuskarta tayi tareda canxa hijab tafito..

Gidan nasu Ashe tuni yafara cika da 'yan uwansu dake garin Sai murna da farin ciki suke.

Kanta a sunkuye tayita gaidasu harsuka fito gidan.

Tunda suka fito take tunanin hanyarda zatabi tagansa suyi magana.

Daf dazasu Isa unguwarsu anty amina kamar daga sama saita hango Davina sun fito wani qaton mall itada mum da Finn..

Rarraba idanu tahauyi kozata gansa Amma Bata gansa ba.

Dakatarda Mai napep 'din dasuke ciki tayi tareda cewa yabi bayan motarsu mum 'din.

A gate suka tsaya tareda miqawa Mai gadi ledojin dasuka siyo suka Kuma barin layin gurin batareda sun shiga gidaba.

Fitowa napep tayi ta matso kusada maigadi dake qoqarin shiga ciki yakai saqon ta qaraso da 'dan sauri tace,

Please is Deen inside.... sorry I mean Nik.
Chapter 12 · 0% Book details