← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta up and down yayi Yana mamakin dagon hijabinta dake Jan qasa Amma wai nik take nema.

Yes,,,yace Mata Yana jiran Mai zata Kuma cewa tace,

Please I wanna see him... I'm his school mate.

'dan nazari yayi Amma gudun laifi gurin oga Nik 'din saiya ce tashigo yakaita.

Matsawa tayi jikin napep 'din ta kalli nuratu dake kallon ikon Allah tace,

Nuratu kije gidan anty zainab karkije gidan anty amina zan same acan Zan fa'dawa wata qawatane maganar aurena Dan taje.

Badan ta yardaba ta 'daga kai sukabar gurin da Mai napep itakuma da sauri tabi bayan Mai gadin Dan tasamu tayi magana da wuri ta fito kafin su mum su dawo.

Qaton qyataccen palon gidan yashiga da ita tareda nuna Mata kujera ya qwalawa Deborah Mai aikin gidan Kira ta fito da sauri ya miqa Mata ledojin hannunsa tareda cemata taje sama tafadawa Nik yanada baquwa.

Kallon ayshah tayi cikeda mamakin ganin Mai hijab a gidansu.

Sama ta hau tayita knocking can qasan maqoshi yace,

What?

Murya na rawa tace,

Sir one lady is here to see you.

Tsaki yasaki sbd baita6a kawowa arai ayshah zata iya zuwa gidanba yanxu.

Korota yayi ta sauko takalli ayshan tace yace bayason adamesa.

Kallon Deborah ayshah tayi idonta na cikowa da hawaye tace,

Please go and tell him it's ayshah.

Kamar bazata komaba saita koma ai tana ta6a qofar ya daka Mata wata gigitacciyar tsawa a rikice ta juyo saitaga ayshan bayanta.

Tura qofar 'dakin ayshah tayi tashiga ya Ciro kansa a fusace zai fara zuba masifa idanuwansa suka sauka cikin nata baisan sanda ya zaburo da qarfi ba yayo gurinta yayi Mata wata kyakkyawar runguma itama sake shigewa jikinsa tayi tana qara qanqamesa.

Deborah na ganin haka tayi saurin barin gurin zuciyarta na mamakin ayshan.

Sun Jima ahaka kafin ya jata suka zauna bakin gado ya riqo hannuwanta Yana kallon face 'dinta a kasalance yace,

I missed you so badly my love.. please don't ignore me like this again.

Kasa magana tayi ta lafe cikin jikinsa tanajin nutsuwa na da farin ciki na shigarta na ganinsa.

'dagowa yayi ya kalli face 'dinta Yana shafowa yace,

You look so pale my love..

Fuskarsa ta kalla tace,

You don't look good too.

Matsoda fuskarta yayi kusada tasa Yana kallon cikin idonta yace,

What do you expect to see my love,,,,I'm nothing without you ayeeshah.,
I can't imagine my life without you in it...

Sake shigewa jikinsa tayi hawaye na taruwa cikin idanuwanta na tausayin kansu Dan ko ita tasan Rashi agunta babban qalubalene ga rayuwarta.

'dago fuskarta yayi cikin kulawa yace,

My love is everything ok?... I mean you here..

Gabanta ne ya Fadi da abinda zata fa'da Masa ta zame jikinta tareda miqewa tsaye kanta a qasa tace,

Deen...Sai kuma tayi shiru.

Miqewa yayi ya Kuma kamota ya zaunar da ita kan cinyarsa tareda zare dogon hijabinta ya aje ya kalleta da kyau yaga ta qara wani irin fresh fatarta Sai glowing take Sai 'yar ramar datayi..

shafo wuyanta yayi har zuwa qirjinta ta riqe hannunsa ya kalleta da lazy eyes 'dinsa tareda kallon red lips 'dinta Yana Kai bakinsa kansu.

Kissing dinta yake cikin tsananin buqatarta..
Rigarta ya zame yana Kai hannunsa kan qirjinta yayi saurin zare bakinsa anata yakallesu sbd cikar dayaji sun qara da laushi.

Rintse idanuwa tayi cikin kunya yasaki murmushi tareda kwantarda ita a gadon yabita.

Saida komai ya lafa ya 'dauketa yakaita toilet sukayo wanka suka fito tana gyara zaman hijab 'dinta tace,

Deen there's a problem..

Saurin aje turaren dayake fesawa yayi ya riqota yace,

What is it my love.

Idonta na kawo ruwa tace,

It's about the wedding they've fixed for me and ya Umar,, the preparation for the wedding has started.

Jikinsa taga ya'dau rawa idanuwansa na canxa launi ya kalleta cikeda baqin ciki da takaicin zancen yace,

I'm sorry my love but I can't hide this anymore I will go and talk to them right away.

Riqosa tayi tana hawaye tace,

Deen please don't go let's find a solution first this is not gonna work.

Zama yayi tareda rintse idanuwansa Yana karanto adduar da shaikh ya koya Masa ta idan Rai ya 6aci.

Saida ya share kusan minti goma ahaka kafin yaji zuciyarsa ta rage quna suka fito Yana riqeda hannunta suka shiga mota sukabar gidan.

Shopping yakaita Amma Sam taqi yarda ta fita motar dole yashiga yayo Mata siyayya yakaita gidan anty zainab.
daqyar ya iya rabuwa da ita tashiga shikuma ya wuce.

Mamuh??

_dont forget to follow, vote and comment_
[7/18, 10:01 PM] ‪+234 803 314 9202‬: *_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_??
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*25*

Tun ranar Ba'a Kuma barinsu fitaba har tsawon kwana hudu duk inda hankalinta yake yayi mugun tashi musamman yanda taga shirye shiryen biki Sai da'da kankama suke Dan yanxu sati 'daya ne yarage kullum tana quryar 'daki a takure batada aiki Sai kuka ga wani mugun zazza6i da kullum dashi take kwana..

Duk hanyarda tabi danta samu ta fita batayi aikiba ga Yaya Umar da yanxu wata soyayya yakeji saima hakan yakuma sakata cikin babban tashin hankali..

A 6angaren Deen ma kusan haukacewa su mum yayi ya 'daga musu hankali yaqi ci yaqi Sha ga ciwon damuwa da yunwa daya bayyana qarara a tattare dashi Nan hankalin mum yayi mummunan tashi takasa zaune takasa tsaye Amma yaqi fa'da Mata damuwarsa.

Yau Kam daqyar yaga safiya yanayin sallar asuba ko wanka baiyiba ya zari mukullin mota ya fice.

Direct anguwarsu ayshah ya nufa yanayin parking ya fito ya doshi gidansu Kai tsaye ba tsoro ba fargaba.

Kasancewar da safe ne Babu kowa a qofar gidan dai Sai qarfe goma ake fara karatu.

Qofar gidan a bu'de take Kuma Yana jiyo sautin karatun alqur'ani da wani yakeyi a 'dakin dake kusa daga ciki.

Sallama yayi ahankali ba'ajiba ya 'dan 'daga murya yakumayi Yana cusa Kai cikin babban soron gidan.

Ya Ahmad dake 'dakinsa Yana karatun Qur'an ya aje ahankali tareda tasowa yafito Dan ganin wake sallama da sassafe haka.

Murza idonsa yayi yakuma kallon Wanda ke tsaye cikin doguwar farar jallabiya ya matso a zafafe zai cakumosa Deen ya riqe hannunsa tareda 'dago lazy eyes 'dinsa dasukai ja Kai tsaye yace,

I'm not here for this...I came to see my ayeeshah.

Uwarka zaka gani ba ayshah ba'''''sukaji anfa'da daga bayan Ahmad...

Umar ne tareda sani da baba alhaji..

Fixge hannun Ahmad baba alhaji yayi daga hannun Deen bai tsaya komaiba ya wankeshi da lafiyayyan Mari.

Rintse ido yayi da qarfi sbd Marin yashigesa Amma bayajin yau zai ja baya.

Nunasa da yatsa baba alhaji yayi cikin 6acin Rai yace,

Wannan Marin qoqarin 6ata Mana suna dakayine ta hanyar sace Mana 'ya dan sunanmu ya 6aci.,,Kuma inason maza tun kafin mutane su taru kabar Mana gida.

'dagowa yayi da fuskarsa datayi ja sbd Marin ya kalli baban yace,

Ayshah is my wife and....

Naushi Umar yakai Masa a baki kafin ya cakumo wuyansa cikin zafin Rai Yana huci yace,

Idan kakuma fa'dar ko sunanta a wannan qazantaccen bakin naka saina fasa makashi da kwalba.

Sakinsa yayi tareda turasa baya da qarfi yana nuna Masa qofa da Ido yace,

Maza bar Nan tun kafin hakurina ya qare.

Gyara tsayuwa sukaga yayi yakuma kallon baba alhaji danko kallon Umar bayasonyi danji yake zuciyarsa zata iya bugawa idan Yana kallonsa...yace,

Baba please let me see her we have something to tell you all....

Ta baya Umar ya fixgosa jiyayi zuciyarsa ta 'dau zafi a hasale ya juyo ba zato ya saukewa Umar gigitaccen marinda Saida hancinsa bakinsa ya fashe..

Ahmad da sani na ganin haka suka rufesa da duka tako ina Nan hayaniya ta tashi kan kace me gabaki 'daya 'yan gidan sun fito Nansu abbakar suka da'du sukayi Masa mummunan duka.

Da qarfi nuratu tashigo 'dakin tana kallon qofa kamar munafuka tace,

Anty ayshah zasu kashesa gashican su Yaya na dukansa yaqi ko motsawa....

Tafi kwana biyu batada lpia ko qwaqwaran motsi batayi idanuwanta sun ko'de sbd kuka tanajin abinda nuratu ta fa'da Bata tsaya Jin sauran ba ta tashi tabar 'dakin da gudu..

Tundaga nesa Umar ya hangota yayi saurin cewa su anty su riqeta.

Riqeta sukayi ta qwace da qarfi ganin wani mugun dukan da Umar yakaiwa Deen 'din a baki.

Zubewa tayi gabansu tareda riqe qafafun baba malam cikin tsananin kukan fitar hankali tace,

Dan allah baba kace su daina,zasu kashesa wlh ya musulunta shima musulmi ne yanxu,,,,Ina tsananin sonsa Kuma da aurensa a.....

Wani lafiyayyan Mari taji ya sauka a fuskarta tana 'dagowa taga babanta tsaye ransa a matuqar 6ace
Umminta kuwa cikin gida ta koma da sauri sbd jiri da qirjinta dataji na neman bugawa.

Cikin wani irin yanayi na 6acin Rai baba malam ya juya baya yace,

Abbakar ku 'daukesa ku fitar dashi daga gidan Nan yanxu banason sake ganinsa.

Jansa sukayi sukayi suka Kai har bakin motarsa daidai Finn yabiyo ta anguwar yaga motar Nik ya tsaya saikuwa yagansa yashe cikin jini a rikice yafito yakira mum kafin ya 'daukesa yabar gurin da mugun speed.

Suna Isa asibitin akayi gaggawar kar6arsa kayi cikin emergency dashi sbd numfashinsa dayake qoqarin barin jikinta.

Ko ka'dan wannan karon ba sauqi cikin alamarin Dan kallo 'daya zakayi musu kasan Bata wani tashin hankali sukeba ta lapiyar 'dansu suke.

Zaune suke jigum jigum idanuwansu a ko'de da tsantsar damuwa da tashin hankali musamman mum da duk tayi wani mugun laushi Dan a yanda taga 'dan nata tasan yanada wuya yayi surviving..

Kuka takuma fashewa dashi tana fa'dawa jikin Finn.

Ba'a samu shawo kan matsalarba sai maraice sosai Kuma Yana farfadowa yafara qoqarin tashi mum da Finn sukayi saurin taresa yakalli mum da kumburarun idanuwansa saikuma ya fashe da kuka ahankali,

Jikinsu ne yayi sanyi gabaki 'dayansu ganin yanda yake kuka gashirban cikin tsuma zuciya.

Dafasa mum tayi tana tsiyayar hawayen tausayinsa Finn ma matsowa yayi ya dafasa shima zuciyarsa na karyewa.. Davina ma jikin Nik 'din ta kwanta tana kuka ahankali sbd Basu ta6a ganinsa cikin irin wannan yanayin ba.

Washe gari jikin nasa ya'dan samu sauqi ya tashi zaune dai dai shigowarsu mum 'dauke da breakfast cikin qaton basket.

Kallonsu yayi 'daya bayan 'daya da kumburarun idanuwansa kafin ya miqe ya tsaya gaban mum cikin shaqaqiyar murya yace,

Mum,,,
Chapter 13 · 0% Book details