← Book details Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Taura Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai kusan qofar Khadija Nan sukaci karo da siyama ta fito afusace.,

'dauke Kai tayi zata wucewarta siyama tace,

I will never live peacefully with these three around,the great madam queen,the mental so called first wife and the stubborn son of great time mitswww...

Kasa qyaleta tayi ta kalleta a wulaqance tace,

And who are you calling mental?

You""""tafada Kai tsaye tana gyara tsayuwa.

Murmushi ayshah tasaki tareda kallonta up and down tace,

Do you know you're completely crazy and foolish?

Qara hasala siyama tayi zuciyarta ta rufe ta 'daga hannu zata sakarwa ayshar Mari taji anriqe hannunta ta baya.

Atared suka juyo Dan ganin waye dukkaninsu idanuwansu suka sauka kan mum.

Wurgar da hannun siyama tayi ta 'daga nata hannun zata Mari siyamar ayshah da idanuwanta suka ka'da Nan take sbd ganin mum 'din ta riqe hannun mum 'din idanuwanta na bayyana tsantsar qiyayyarta da mum cikin 'daga murya tace,

And who are you to interfere in this.?

A razane dukkaninsu suka kalli Ayshan sbd ba qaramin bazata zancenta yayi musuba.

'daure fuska ta sakeyi tareda 'dage gira 'daya tace,

This is between me and her and I can fight for myself I don't ask or need anyone's interference coz I don't tolerate crazy old ladies now.....

A matuqar zuciye ya 'daga hannu zai Mari ayshar mum tayi saurin riqeshi tana girgixa Masa Kai idanuwanta na kawo ruwa sbd ta tabbatarda abinda tayiwa ayshar Dole ta fuskanci haka.

Cikin 6acin Rai ya kallesu fuska a 'daure tareda daka musu tsawa yace su bar gurin.

Wani kallo ayshah ta watsa musu kafin tabar gurin tana cewa,

Dama me mutum ze tsayayi tunda masifa ta iso gidan.

Kasa kallon mum da jikinta yayi matuqar sanyi yayi yawuce part 'dinsa direct zuciyarsa na quna dan kuwa mummunan mataki zai 'dauka akansu duka indai akan mum ne.

Daf da zata shiga palonta taji anrungumeta ta baya da sauri ta juyo tana ganin Mahmud 'dinta ta 'daukesa da sauri tareda qanqamesa tana hawayen farin ciki koba komai ta yanke shawarar tafiya sbd har abada bazata iya Zama gida 'daya da mum ba 'dauke 'danta zatayi ta tafiyarta inda bamai Kuma jinsu bare yagansu.

Ranar da 'danta takwana cikin farin ciki da Jin 'dadin data Jima batayiba.,
Shikansa mahmud yayi kewar mummynsa sosai shiyasa Sai lafe Mata yake Yan shagwa6a.

Acikin Daren ta ha'da kayanta tsaf asuba nayi tayi sallah ta fa'da wanka jiki na rawa.

Daga masallaci direct part 'dinta ya nufo daf dazai shiga yaga fitowar wani qaton namiji da gudu riqeda rigarsa a hannu yayi bayan part 'din nata..

Mummunar fa'duwa gabansa yayi kansa ya Sara harsaida wani mugun jiri ya 'dibesa yayi saurin dafa bango.

What namiji cikin gidana?
Wani qarfi ne yazo Masa tareda 6acin Rai sa zafin zuciya yabi bayan mutumin Amma bai ganshiba gate yakoma da sauri yacewa securities karsu Bari kowa yafita Koda matansa ne kafin yadawo zuciyarsa na tafasa a zafafe ya banka qofar bedroom 'dinta dai dai fitowarta wanka 'daureda 'dan wani munafikin towel dayayi Mata ka'dan danko hadewa bayayi sosai.

Fa'duwa gabanta yayi jikinta ya'dan fara rawa Amma tafara qoqarin dakewa Dan ita tunaninta yagano guduwar dazatayi.

Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita
Ya rintse idanuwansa cikin zafi da karyewar zuciya ya damqota tareda matseta ya jijjigata da qarfi yace,

Why,why ayshah?
Duk abinda kikayi baya da aurena is not enough saikin kawomin cikin gidana,,,

Cikeda mamaki da tsoro take kallonsa tana qoqarin kwacewa sbd zafin riqon dayayi Mata,.

Tureta yayi da qarfi harsaida ta fa'di har kanta ya bugu goshinta ya fashe a zafafe zuciya na tafasa yace,

Ayshah Nima ayau na tabbatarda kece qaddarata,
Nasoki abaya so Mai tsanani,
Yanxuma Dana manta komai still zuciyata saidata kamu da sabon sonki nakuma tabbatarda dazan Kuma samun wani memory loss 'din I will still fall for you but wannan shine sakayyar....

Rintse idanuwansa yayi ga mamakinsa saiga hawaye na tsiyayo Masa ya girgixa Kai zuciyarsa na qara 'daci yace,

Ayshah go, leave, I don't want to see you again.

Tashi tsaye tayi cikin tsananin zafi da qunar Rai tana kallon tsakiyar idanuwansa hawaye na qoqarin sauko mata tace,

Deen me kake zargi dashi?

'dauke Kai yayi yace,

Just leave,.

Juyosa tayi da qarfi cikin kuka tace,

Deen ni kake zargi da wani?
Ni ayshah kana tunanin Zan iya rayuwa da wani namijin bayan kai.?
Deen do you really hate me that much da har kakemin wannan zargin after all the years danayi batareda kaiba Amma na tsare mutunci aurenka.?

Wannan shine nawa sakamakon?
Deen when will you stop hurting me and ruining my life?

Girgixa Kai tayi cikin hawaye idanuwanta na kadawa jajir sbd wannan shine Abu mafi Muni dayayi Mata arayuwa and this mark the end of their relationship.

Share hawayenta tayi tace,
Bazan ta6a manta wannan ranarba sbd itace ranarda na datse duk wani sauran hope na tsakanina dakai,
Nagama dakai Deen.

Juyawa yayi ya fice a fusace hawayensa na qara 6allewa.

Zubewa tayi bakin gado tareda sakin kuka ahankali zuciyarta na Kara karyewa tace,

Baba kuyi hkr gida Zan dawo wlh zuciyata fashewa zatayi Ina cikin tsananin rayuwa Ina buqatarku ku yafemin.

Har time 'din mahmud bai tashi bacci ba hakanan ta tadashi ta saka Masa Kaya ko wanka batayi masaba suka fito.

Mum da Khadija tagani bakin qofar palonta jiki asanyaye Khadija kuwa kuka takeyi sosai.

Kallon Khadija tayi itama idanuwanta na sake 6arewa da hawaye tace,

Khadija mum yau ta qara tabbatarminda Bata qaunata and she will never do sbd nasan she's behind all this,,, anyways dama I should be ready for even more of these since she's here Amma komai yariga ya qare...

Hawaye ne suka ganagarowa mum ta bu'de baki da zatayi magana ayshar tayi wucewarta riqeda hannun 'danta.

Ayshah na fita gidan kamar daga sama Khadija taga mutum bayan flowers 'din bayan windon 'dakin ayshah ta zaro idanuwa tayi cikin tsoro harzata gudu 'daki Sai tafasa ta nufi part 'dinsa da sauri jiki na rawa tafada Masa
A zafafe ya qaraso gurin tareda cakumosa siyama dake bayansu ta lalla6o da ta6aryarsu ta aiki ta 'daga da qarfi ta kwalawa Deen akai Nan take ya zube agurin Khadija ma na juyowa ta qwala Mata tasaki qara Mai qarfi itama ta zube qasa.

Hanya ta nuna Masa tareda basa kudin aikinsa da sauri ya fice haryana tuntu6e bayan ya maida uniform 'dinsa na aikin security agidan.

Ta6aryar ta maida kicin da sauri kafin tadawo gurin tareda daka kururuwa tana Kiran mum na mum ta qaraso tana ganin 'yayanta biyu zube qasa hankalinta yayi mumman tashi suka kwashesu Sai asibiti.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_
[7/29, 5:23 PM] prince_s_square: *_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*34*

Tafiya ka'dan tayi bayan tabar gidan taji takasa riqe kukan dake son fito Mata ta durqushe agurin tasaki kukan cikin qaramin sauti zuciyarta na neman tarwatsewa..

Zama kusada ita Mahmud yayi tareda 6ata fuska zai fashe da kukan shima yace,

Mummy who beat you?

Sake sakin Wani kukan tayi tana jawo 'danta jikinta.

Saida tayi iya Wanda zuciyarta ta 'dan rage nauyi kafin tafara qoqarin tashi taji ankira sunanta cikin sanyayar murya Mai taushi.

'dagowa tayi tareda miqewa tana juyowa idanuwanta suka sauka kan muh'd dake tsaye akansu yayi folding 'din hannuwansa a qirjinsa Yana kallonsu cikin tsananin sonta da tausayinta sbd mum takirasa tafada Masa Amma bayajin zaifara zuwa asibiti gurinsu Deen batareda yafara sanin inda ayshan da 'danta sukeba.

Sabbin Hawaye ne suka gangaro Mata cikin karyewar zuciya tace,

Murphy..

Lumshe idanu yayi zuciyarsa na tsananta tafasa da ganin yanda ayshan takoma.

Cikin kukan da baya fita sosai take kallonsa tace,

Where were you Murphy?
Deen has destroyed my life,,
I'm not dsame ayshah you used to know,,
I'm a shame now...... kukane ya qwace Mata ahankali tayi shiru tana rerowa zuciyarta na qara kaririyewa.

Matsowa yayi gabanta ya tsaya murya a karye yace,

Ayshah insha Allah wahalanki da kukanki ya qare,,
Girgixa Masa Kai tayi cikin kuka tana cewa,

I have no one to see or call my own..,I'm all alone..

Karki cire Kai daga rahamar ubangiji ayshah,
Have faith in Allah insha Allah everything will be alright again.

Kamo hannun Mahmud yayi tareda Jan akwatinta ya kalleta yace,

Let's go.

Kallonsa tayi saikuma ta sunkuyar dakai tabi bayansa ya bu'de musu motarsa suka shiga ya tada suka tafi.

Tunda taga sun fita garin Abuja ya gyara Zama tareda qarawa motar gudu sosai suka 'dau hanya ta rintse idanuwanta hawaye suka gangaro zuciyarta ta karye Dan kuwa kobai fa'daba tasan gida zai kaita.

********
Zaune suke suna sauraron abinda shaikh abdallah yake fa'da zuciyarsa ba da'di..

Tabbas malam babba kun Bari shai'dan dason zuciya sunyi galaba akan sani da kukedashi na addini,

Meye al'ada?
Al'ada fa ba musulunci bace hasalima gurarare da dama tayi hannun Riga da abinda musulunci yace ayi.,

Malam babba wannan al'ada da kuka 'dabbaqa gatanan Kuna gani tayi sanadin rushewar mutumci da girmanku a idon masu mutuntaku sbd yanzu meye amfanin wanna?""""yafada Yana 'daga jaridar hannunsa ta ayshah da aka bugo.

Gyara Zama yayi ransa na qara 'daci yace,

Wlh nayi baqin cikin rayuwar data samu ayshah sbd nida ban haifetaba nafi Jin zafin mummunar qaddarar data sameta,

Shi Wanda kuka wulaqanta 'yartaku akansa gashinan Kuna gani a tv da jaridu irin kyakkyawar rayuwar dayake yi duk sanadin 'yarku data Zama silar musuluntarsa.,

Maimakon da kuka gane komai ku gadewa Allah da aure sukayi ba zaman sa6on Allah ba saiku aje wata al'ada ku rufawa kanku asiri kubarsu.,
Idanma har hakan bazata yiyuba ku binciki 'yarku Mana ku gano ta inda Zaku warware matsalar cikin ilimi,

Cikin tsananin sanyin jiki baba qarami yace,

Tabbas ayshah taso bayani Amma sharrin zuciya da 6acin ran laifin datayi ya Hana a saurareta...

Wannan shine babban kuskuren da kuka tafka amatsayinku na masana addini,

Wlh Koda yaushe aikin zuciya Babu komai atareda dashi Sai nadama da kuka.,

Yanxu gashi duk masu zuwa 'daukar karatu da da'ira sun daina sbd ganin bakuyi aiki da alimin da kuke dashiba to maizasu cigaba da zuwa koya.?,

Da bahaushe,da yoruba,da kanuri,da buzu da Fulani da kowane yare 'daya agurin Allah matuqar musulmaine,
Chapter 20 · 0% Book details