← Book details Soldiers Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Soldiers Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itako masifa kawai takeyi tana jifarsu wani sojane yahangeta tareda setata da bindiga yasako mata harbi akuma Dede wannan lokacin bibibo da k'awarta suka iso wurin domin dawowarsu kenan cikin azabar sauri maheerah ta gotarda ita yayinda maheer yacika yayi simtim sabida fishi atake yarikid'a yazama wani wurgegen maciji me azabar girma da tsawo wani irin k'ugi yafara tareda cilla jelarsa yakanannad'e jirginnan dashi tareda wutsiloshi k k'asa kad'an yarage ya isarda makasha kan wani dutse gimbiya halila tadakamai tsawa tana dakatardashi.

""Maheer kasaukoda jirginnan ahankali karkabari wani yacutu ajikinsu...shiru yayi Yana kallonta shibe ajiye jirginba Kuma be sakeshiba....suko su jalaludeen dasukaga mutuwa afili tinda sukayi Ido 4 da wannan shirgegen macijin suke salati tareda kalmar shahada cikin tashin hankali da firgicinda Basu tab'a riskar kansu acikiba ganin macijin bekashesuba Kuma be barsuba se kawai suka fara addu,a duk wadda tazo bakinsu...cikin bada umurni gimbiya halila tace kasaukesu nace zaraah tana lpy ba,abunda yasameta...se a lokacin yasauke wani huci me mugun zafi wanda da,akwai mutin akusanbakinshi a lokacin ba abunda ze Hana zafinnan kasheshi...walwale jelar yafarayi ahankali seda yasauke jirgin se kawai yaji muryar mama na fad'ar bibibo kada kasakesu sesun bitomunda Wanda ya hirbi abbana acikinsu domin bazan yafeba Sena dau fansa wlh...Ido duk suka k'walalo Jin wannan dadd'ar murya nafad'ar Kar asakesu captain Usman yace wannan akwai sheda niyar yarinya koma wacece muryarta da Dad'i Amma zuciyarta ba Iman...shiru yayi sabida hararar da jalaludeen ya zabga masa....shiko bibibo Jin abunda tace yasaka bayan saukesu seya Kara kanannad'e su da jelarsa ta yadda ba Wanda ze iya fita daga cikinsu....shuru wurin ya d'auka nawani Dan lokaci domin duka sauran jiragen sunfece ganin wannan tashin hankalin.

Gimbiya halila ce tadafa mama dake mak'ale jikin maheerah tace zaraan Abba kiyi hak'uri yasaukesu inyaso bawanda zebar jejennan acikinsu se abbanki yasamu lpy...shiru tayi batace komaiba seda maheerah tace k'awata kin yadda? Eh tafad'a ahnkali kamun bibibo yashiga zare jelarsa yasake jirgin.. rikid'a gimbiya halila tayi tadawo bil adama sak dashigar gidan sarauta kana ta umurci su bibibo suzo amatsayin mutane ba dabbobi ba hakako akayi Amma duk wannan abun da,akeyi su jalaludeen basa gani sedai sunajin maganar mama dawani sauti mekamada rugugi Amma basajin mi,akecewa seda duk suka zama mutane kana gimbiya halila tak'arasa Dede k'ofar jirgjn tace kufito daga waje...tana rufe bakinta wani soja yajanyo bindiga murmushi tayi kamun tace ba,anfaninda zatayima anan kawai kufito inkuwa kunfiso nabarku dasu shikenan Sena tafi....tinkamun tak'arasa duk suka shiga fitowa seda suka fito dukkansu kana sukaja suka tsaya suna kallon kyawawan mutanen dake gabansu...maheerah taja hannun mama suka K'arasa kusansu kana tace saka makon harbe harben dakukayi kun harbe abban wannan yarinyar itama kunso harbeta wannan dalilinne yasa Dan uwana yaso hallakaku Amma antynmu tanema muku alfarma sabida hakan doline yanzu kuzauna taredamu harya samu lpy inafatar kun fahimta?

Shiru duk sukayi secan jalaludeen yace afuwa muke nema Dan Allah kugafarcemu dudda cewa shigowa jije damukayi yanada dalilinshi Amma sam bamuyi tinanin zamu cutarda waniba Amma Dan kuyafe Mana duk acikin larabci yake zancen domin Sam besan dawane yare zeyi sumafimtaba yadda zasufi ganewa se Kuma akayi sa,a sunajin larabcib...murmushi gimbiya halila tayi kamun tace bakomai narigada nasan abunda kukazoyi Kuma zankaiku har inda way'anda kuke nema suka buya Amma kamunnan zaku D'an zauna Koda zuwa gobe ne muga yadda jikinshi yayi seku tafi...to mungode sosai cewar jalaludeen kamun Usman yace zamu iya ganin Wanda muka raunata kodan munemi yafiyarshi..."eh bakomai zaku iya gimbiya halila tafad'a tana kallon dija alamar tafitoda abban mama bukkarsu tashiga kamun tafitodashi kuwa tuni su mero sunbaza shimfidd'o Wanda su dai su jalaludeen basuga ta inda sukafitodasuba kawaidai sunga suna shimfid'awa....fitowa sukayi rik'edashi subuyu suka samu wuri suka zaunardashi kana maheerah tace gashinan....gabaki d'aya suka juya suna duban Dan kyakkyawa balaraben dake zaune awurin.

Ido jalaludeen yazaro Yana fad'ar *abbee* duk kallonshi sukamayi shiko se nuna wannan tsohon yakeyi Yama kasa magana Yana neman K'arasawa wurinshi asukwane

Usman ne yarikeshi Yana girgizamai Kai alamar karyaje shiko gabaki d'aya hankalinshi baya taredashi ganin hakan yasa gimbiya halila cewa Usman yasakeshi d'in Aiko Yana sakeshi yaruga aguje Yana fad'ar abbe dama kana Raye abbe miyazodakai k'asar Ghana mikakeyi anan abbe na kallanni kaga abbe jalaludeen D'inka nefa abbe nine jalal...ganin abbe nabinshida Ido kawai bece komaiba sema kwab'e fuska dayayi Yana duban mama...itako cikin sauri tazo wurinshi tareda Kama hannunshi da akaharba tana kallo tareda yimai sannnu Dan tuni su mero suncire masa harsashen.

Meda dubanshi yayiga gimbiya halila domin yaga tadanfi sauk'i sabida maheer dai kofuskar rahama babu ataredashi dama Dama ma maheerah cikin rauni yake fad'ar Dan Allah miyasamu abbe na? waya kawoshinan? suwayeku Dan Allah kufiddani aduhu please?

Ganin duk yarud'e yasa gimbiya halila fad'ar ""kwantarda hankalinka bawan Allah zamu gayama Amma dafari kagaya mana yakakedashi?

""Shid'in fa abbe nane k'anen mahaifinane uwa d'aya uba d'aya yab'ata shekaru da dama anata nemanshi Amma ba,asameshi Kuma tin daga Dubai abun mmki segashi a Ghana Dan Allah kunyimun bayani yadda Zan fahimta?

Shiru gimbiya halila tayi nad'an wani lokacin Ashe bincikene takeyi taga Idan abunda yafad'a gaskiya ne seda ta tabbatar da gaskiya yafad'a kana tace shikenan barakaji yadda muka sameshi Nan tabashi labarin tindaga had'uwar da su mama sukayi dashi har kawo yanzu kana tace dama Kuma way'annan ne muke jura kafin mukarya sihirin Kuma cikin ikon Allah gasu sundawo

kallonta tamaida ga maheer tace bibibon zaraah kaga aikinda zaraah tad'auko inafatar zaka amunce kuyi wannan jahadin kodan farin cikin zaraan ka...shiru bibibo yayi nadan wani lokacin kamun yadubi mama alamar neman K'arin bayani itako marairaice face d'inta tayi kamar zatayi kuka tace please bibibo inaso abbana yayi magana... shikenan zanyi bincike akan sihirin zuwa gobe Yana Kama fad'ar hakan yabar wurin... jalaludeen kuwa k'wallah yashafe kamun yadubi mama yace Allah yasaka Miki da aljannah k'anwata dakeda way'annan bayi nasa.. ameen y Allah Mama tace tana murmushi domin hakan kawai taji yakwanta Mata bakuma k'aramun dad'i tajiba d'aya kiratada k'anwarsa.!

Dubai

Anty Billy tuni tayiwa dady zancen auren muhibbat da alyasat Kuma yaji dad'in hakan sosai inda yasamu habibbty da zancen sedai tace bazatayiwa alyasat zancenba se lokacin daya bukaci aure Dan kanshi wannan dalilinne yasaka akarufe zancen izuwa lokacinda zezoda zancen auren.

Zaune yake a bedroom d'inshi Yana kallo a CCTV daya jona abaki d'aya ila ihirin pert d'in samarin gidan abubuwa yake gani kala2 wasu subashi mmki wasu Kuma subashi haushi zancendai najeeb na neman Mata hakanne domin baccin wannan yarinyar yak'ara zuwa dasu maban banta matan

yauko abunda yake kallone kebashi mmki matuk'a muhibbat ce kwance akan shareef tana wasada sumar kirjinshi shiko se wani lumshe Ido yakeyi Yana tura hannu cikin rigarta tareda damk'o breast d'inta Yana murzasu cikin shauk'i ganin abun nasu naneman zarta misaline yakashe dasauri Yana mek'ewa tsaye sintiri kawai yakeyi a bedroom d'inshi shin Mike shirin faruwada ahalinsu ne? Yaya dakanshi ze lalata k'anwarshi? aikoba mahaifansu d'aya ba ita d'in jininsuce miyasa shareef zeyi hakan? Dama muhibbat tasan maza kenan kumama yayunta innalillahi wa innailaihhiraji un abunda yaketa maimaitawa kenan kamun yakwashi wayoyinshi yafita.!

Ghana

Zaune suke dukkansu afilin inda bukkarsu mama take sunacin abunci dudda basusan daga Ina yafitoba amma karamcin way'annan bayin Allah yayi musu dad'i sosai...mama kuwa tana zaune tana bawa abbanta abaki Yana kallonta itako se murmushi takeyi jalaludeen ma yakasa cin nashi kallonsu kawai yakeyi tareda tsananin mmki aranshi... Maherr da tind'azu yake tsaye awunrin Yana kallon yadda mamarsa ke farin ciki sekawai abun yayi masa dad'i se yanzu yayi gyaran murya tareda K'arasawa wurinsu d'auke da sallama abakinshi..!

*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk'atar complete 700 idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08107819124

Autar alheri ✍️

🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)

*By Dr Yasmeen Ahmed*

Autar alheri ✍️

Page 19&20

Free page yak'are daga wannan kiyi hanzari kinemi naki domin karki Bari abaki lbr

__"amsawa sukayi duk suna kallanshi kana yasamu wuri yazauna kusan mama yace""uwar gijiyata nayi bince akan sihirin sedai kamar yadda anty halila tace doline sedake zamu karyashi nisawa yayi kamun yasake cewa aikin Yana cikin ruwa acan akajefashi Kuma gudu yakeyi yadda wannan sihirin ke gudu hakan abbanki zeyita yawo aduniya batareda sanin takamammen inda zashiba ajiya nasaka antsayarda aikin inda zamu samu sauk'in kamashi sedaifa bawanda ze iya fiddashi acikin ruwannan se bil adama sabida hakan Idan kinshirya semuje.....kamun tayi magana jalaludeen yayi saurin cewa aa kabari Ni muje ai wannan tayi k'arama kartasaka kanta ahad'ari...murmushi gimbiya halila tayi kamun tace ba Wanda ze iya wannan se ita domin tana tattareda abunda bakadashi sabida hakan kabari suje kawai kaide kayi musu fatan nasara...nisawa yayi kamun yace shikenan Allah yabasu sa,a akan abunda zasuje nema... ameen y Allah duk suka amsa kana mama tamik'e tana cewa bibibo suje mik'ewa shima yayi kana maheerah ma tamik'e sukabar wurin seya rage daga gimbiya halila sesu mero datawagar sojojinsu jalaludeen..!

Dubai

Alyasat nafita yawuce part d'in yusif aperlo yasameshi zaune Yana aiki a computer d'inshi zama yayi kusadashi tareda jingina bayanshi jikin kujerar batareda yace komaiba tinanin yake aranshi wannan wanne irin Bala,I ne ace y'ay'a family d'aya Amma suna neman junansu Idan son muhibbat shareef keyi baze auretaba itako dake fad'ar tana sanshi Ashe duka karyace Aiko zeyi maganinsu....tinaninshi ne yakatse lokacinda yaji yusif nakiran sunanshi yad'ago shima Yana dubanshi..."Miyake faruwa ne bro Naga kayi shiru se tinani kakeyi? Dan yamutsa face d'inshi yayi kamun yace no bakomai kawai inasan komawa London ne kamun mudawo bikinnan daza,ayi kaga daganan semu dawo aikinan Baki d'aya ko?

Shiru yusif yayi nadan wani lokacin kana yace hakan zeyu kuwa? "Eh mana kodama bazeyuba nibazan cigabada zama acanba domin gidannan namu akwai matsaloli sosai gaskiya doline murik'a saka Ido gudun faruwar wani mummunan abun...nisawa yusif yayi yace hakane bro to kodai kaga abunda kefaruwa ne acikin stet d'innan?

Da mmki alyasat ke dubanshi kamun yace wani abunne yafaru?

"Humm zokaga yusif yafad'a Yana nuna masa abunda ke cikin computer d'inshi...Ido alyasat yad'an bud'e kamun yadafe kanshi domin abunda yagani yabashi mmki sosai dudda yaga wani shima Amma beyi tinanin abun yake hakanba...ganin yayi shiru bece komaiba ne yasa yusif fad'ar yanzu minene abunyi?
Chapter 9 · 0% Book details