Sashe 15
Soldiers Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin hakan yasa maheerah fad'ar karku tana da hankalinku insha Allah Babu abunda zaifaru muddin muna Raye bazamu Bari ahalin zaraah su to zartaba domin yanzu kunzamo ahali agareta....wannan tsohon Idan ya farka na,ajiye ruwan addu,a daza,abashi yasha saboda shekaru dayayi amatsayin sak'aho kamar Wanda baya duniya Kuma manta daku shine akayi ta yadda bazaku tab'a tunawa da shiba balle kuyi yunk'urin nemansa.
Alyasat da zaraah dolene su zauna acikin inuwa d'aya domin da temakon auren da ketsakanin sune muka karya wannan tsafin domin muddin suna tare baza,ataba cin galaba akansuba nasan yanzu mama zasu Hara itada mujinta sabida sune suka karya alkadarinsu Amma muddin suna tare hakan bazebasu nasara akansuba sabida hakan kukiyaye kurika addu,a danneman tsari agun Allah..suna gama fad'ar hakan du suka bace batt domin zancenne kawai sukeyi hankalinsu nakan yayarsu.
Shiru perlon yad'auka kamar ruwa ya cisu ko wada abunda ke ranshi sunrasa mai zasuyi farin ciki ko akasin hakan..sunjima awurin ba tare da kowa ya tab'ukawa kansa komaiba seda akayi Kiran sallar magarib kana duk mazan suka fita masallacin sake cikin stet d'in yayinda matan sukayi sallarsu anan cikin perlon
Mazan Basu dawo gidanba har akayi Isha,I seda sukayi sallar kana suka shigo Kuma har wannan lokacin su mama basu farka ba...ahakan suke zaune anan perlon har 10:00pm kana abbe da Abba suka nufi bedroom d'inda suke ciki...sukayi sa,a kuwa tashin Alyasat kenan Wanda mitsinshi ya tada mama sannu suka musu kana sukace sutashi suyi sallah
Seda sukayi sallar suka gama zasu fita kenan appey ya farka cikin sauri suka K'arasa gunshi suna mishi sannu...amsawa yayi Yana tambayar lafiya me sukeyi anan? Domin Shi gani yakeyi kamar baccine yayi ya farka... murmushi kawai sukayi tare da cemai ba komai Sam basu nunamai akwai wani abunba...ahakan suka rankaya zuwa perlon kowa yaji dad'in ganin sutashi cikin koshin lpyr su sedai bawanda ya nuna alamar komai sema cewa da Abba yayi kowa yajeya kwanta dasafe akwai meeting insha Allah zasu K'arasa Wanda sukeyi abbe yadawo kana zasuso suji yadda mama takasance matar alyasat...da hakan kowa yanufi part d'inshi inda mama abbe Alyasat Yusuf Lateep Alhassan da alhusain da ammy suka nufi pert d'in ammy...suko appey da habibbty se su sulaiman da najeeb Fahad suka nufi pert d'in habibbty kowada burin yaga wayewar garin gobe domin Jin abunda yashige musu duhu...!
Nima dai sai goben nan domin alkalamina yace atsaya yahuta gobe naji yadda wannan abun ya kasance☺️
*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk'atar complete kuma 700₦ ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124
Autar Alheri ✍️
*S F*
Page 31&32
__"ahakan suka kwana ko a part d'in ammy kowa da abunda keransa...washegari da safe bayan kowa ya fito, aka sake taruwa a part d'in habibbty a wannan karon gabaki d'aya stet d'in kowana wurin manya da Yara bayan anbuɗe taro da addu,a kana Jalaludeen ya fara basu labarin abunda yafaru A Ghana tin shigarsu k'asar har kawo abbe ya samu lafiya da labarin da gimbiya Halila tabasu na yadda suka samu abbe....kowa awurin yayi shiru yana saurarenshi har sai da yakai karshe
kana Abba yace, "Ikon Allah 🤔 lallai wannan abun ikon Allah ne kawai da buwayarsa tabbas wannan yarinyar alkhairi ce acikin ahalinmu, Allah yayi Miki albarka zaraah Allah yasaka miki da gidan aljannah.."
"Ameen Ya Allah" duk aka amsa kana habibbty tace, "lallai Zara kincika Yar baiwa samun yarinya irinki awannan lokacin abune me matuk'ar wahala kiyi abunda ko manyan mutane ba zasuyi ba Allah ya faranta miki yadda kikamana kema.."
Shiko Alyasat tunda aka fara bada labarinta abunda ya ɗaure mishi kai lallai wannan yarinyar ba abun wulakantawa bace agareshi ko dan soyayyar data kema abbenshi ba tare da tasan koshi waye ba gashi tabashi abubuwa ukku arayuwarshi da zuwanta ajiya Wanda kud'i ko muliki kowani muk'ami bazasu baduiba tadawomai da mahaifinshi mahaifiyarshi tasamu lafiya adalilinta kana tabashi budurcinta duk dan saboda iyayenshi shiko mai zai mata arayuwa yabiyata Yayiwa kanshi wannan tambayar!?
Shakka Babu yasan Ko da bayasanta bazai tab'a wulanta taba kuma tana da muhalli mai girma acikn zuciyarshi wanda bai tab'a bama wata maceshi ba...murmushi yasaki Wanda ya k'awata kyakkyawar fuskarshi yana mejin amsar da zuciyarshi ke bashi game da ita, maganar dady ce tadawo dashi daga duniyar tinanin da yaje
Inda yake cewa, "To ya,akayi takasance matar Alyasat Yaya Habeeb?
Nisawa Abbe yayi kana yafara magana kamar hakan, "Hak'ika zaraah matar Alyasat ce ta sunnah domin bayan nasamu lafiya na nemi sanin abunda zaraah keyi zaune acikin jeji Kuma tana rayuwa da aljanu a memakon mutane hakanne yasa gimbiya halila bani labarin zaraah atak'aice.
Wacece zaraah (mama)
A ƙauyen shinkafi akwai wani bawan Allah wanda akafi sani da malam mai lazimi shi wannan bawan Allah Babu abunda yakeyi arayuwarshi face karya sihiri da d'aure miyagun aljannu Kuma Yana bada taimakon akan duk wani ciyo daya shafi iska.
Shi wannan Malam yana da Mata biyu Yara 4 maza dukkansu magidanta domin duk ya surardasu isah shine babba sai bello kana sama,ila sai kuma autansu manniru
Malam mai lazimi bayanda wata Sana,adata wuce noma sai ba yadda taimako Wanda ta wannan hanyar yakan samu alherai da dama yanada dukiya sosai inda yaransa suke tafiyadda komai na dukiyarsa kuma daga gefe bello na nashi kasuwanci Daban wandaba na mahaifinsu ba hakan yasaka duk yafisu rufin asiri.
Ana hakan watarana malam mai lazimi yarasu mutuwar da tagirgiza ilahirin garin zamfara harmada kewaye bayan rasuwar mlm da kwana arba,in yaransa suka tada fitina se anraba gado ba yadda isah magajinsu bai yiba amma fir su Sala,ila sukace basusan zancenba
Hakan yasa yacewa bello yaraba yabasu tasu tinda dama shine k'arfin kula da dikiyar hakan kuwa akayi ya raba ya bawa kowa tashi harya Kara masu datashi tindasu suna da y'ay'a shiko bayada d'a ko d'aya bai tab'a haihuwa ba dagashi se matarsa d'aya Nana asama,u Yana kirantada Nana...hakan rayuwa taci gabada tafiya tsakaninsu basuda wani kyakkyawan zumunci daga mlm isah se Bello kawai ke zumuncin su tsakanin su da malam ila tsangwama ne da Gori shidai Malam Isah ba ya da cikakkiyar lafiya, shiko bello betab'a haihuwa ba.
A k'allah bello sai da yayi shekara 45 da aure be haihuba hakan yasa yad'ebe Rai daga samun haihuwar dagashi har matarsa Nana..watarana Nana tatashi da matsanan ciyar rashin lafiya Ko da aka kaita asibitin cikin Gusau akace cikine da ita, abunda ya bawa duka likitoci mamakin kenan domin ganin dattijuwa Yar shekara 59 da ciki maimakon suga tashin hankali agunta ko mujita sai suka ga sabanin hakan domin farin ciki marar misaltuwa suka nuna gidiyarsu ga Allah dasamun wannan rabon
Malam isah yayi murna sosai yayin da ila yaji wannan labari kamar sak'on mutuwarsa..ahakan Nana taci gabada renon cikinta har ya,isa haihuwa....watarana Nana na tafe kan hanya zatakaiwa Bello abinci agona tayi tafiya mai nisan gaske inda tarabu da cikin gari kuma Bata karasa gonar ba tana Jin jejine kawai senak'uda tataso Mata gadan gadan abunga jikin manyanci kai tsaye Nana tagala baita...tana cikin wannan halinne Allah ya jefo wannan twins d'in maheer da maheerah zasu wuce sai kawai sukaga halin da take ciki.
Jin sukayi bazasu iya tafiya subartaba sai kawai maheerah ta taimaka mata harta haihu inda tahaifo yarta mace kyakkyawa San kowa kin Wanda ya rasa seda maheerah tayi Mata komai abunda yadace kana tarakata gida...ita Nana duk kallon takeyi wata mutunce irinta ta taimake ta batasan Sam abun ba hakan bane.
Ko da Bello ya dawo gida yasamu kawai Nana da yarta fad'in farin cikin da ya shiga awannan ranar bata lokaci ne domin duk wani Wanda yasan Bello yasan Yana cikin farin ciki...yayin da labarin haihuwa ya zamema ila tashin hankali da kiyayyar wannan yarinyar da,aka Haifa a cewarshi ta hanshi cin dikiyar Dan uwanshi..
Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar malam Bello wato fad'imatu Zara,u Kuma sunan mahaifiyar Nana...wannan dalilin ne yasa suke kiranta da *mama* uwar kowace acikinsu kenan..hakan rayuwa ta cigaba da tafiya har mama tafara rarrafe daga gefe d'aya Kuma kullun twins se sunzo sunga mama domin hakan kawai Allah yasaka musu Santa Kuma tanamusu kamasa wata sarauniya acan jinsinsu wadda takasance k'anwace ga mahaifiyarsu maheer na kiranta da uwar gijiyata wannan dalilin ne yasa yake Kiran mama da hakan
Tintana k'arama suke bayyana tana ganinsu kuma Basu tab'a Bata tsoro ba ko firgita ta har seda ta saba dasu hakan yasa duk abunda zasuyi Bata tsorata...duk wannan abun dake faruwa Nana Bata tab'a saniba domin basa Bari tagansu Kuma mama yarinyace mai shegen k'iriniya da tsiwa hakan yasa kowani abun nafariwada ita baza,ayi saurin saniba.
Akwana atashi Babu wuya awurin Allah yau mama nada shekara 4 aduniya Kuma yaune ila yasamu Bello da zancen beda gaba beda baya ya tai makamai jalinshi yakarye ga iyali...hakan Bello yad'auki Rabin dukiyarshi yabashi sa,annan yace yake da ita bashi yayi ba,aroba Amma yasani ko bayan ranshi sauran dukiyarshi ta mama ce domin akula da rayuwarta domin babban burinshi aduniya shine tayi karatu mezurfin...hakan suka rabuda ila Baki harkunne..duk wannan abun daya faru tsakanin ila da Bello sai da Bello ya fad'awa Nana kana ya fad'awa yayansu isah...bayan wata 3 dayin hakan wata rana Bello yaje gona da Mama ya barta shiko yaje Yana aikinshi Sega Nafee yaron malam ila ya kawomawa Bello fura mai shegen tsayi yace inji mamarshi tace yakawo musu shida babanshi...Bello najin hakan yakarb'a Yana godiya zama yayi Tasha furar sai da yak'oshi kana yashiga neman mama itamatasha yayi neman duniya begantaba se can Koda yaduba gun wata katuwar bushiyar mango suna zaune itada Maheer suna fira kamar yaya da k'anwa se dariya takeyi shiko Yana tsonarta... murmushi Bello yayi aranshi Yana fad'ar ko,Ina tasan wannan saurayin oho? Takawa ya shiga yi zuwa inda suke Amma ko rabi bai yiba zuciyarshi ta rike cikinshi yashiga ƙullawa sai kawai ya fad'i awurin tare da fara aman jini Babu kakkautawa..azabure sukayi kanshi itada Maheer din Dan ganin abunda yakeyi...!
*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk'atar complete kuma 700₦ idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07937092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124
Autar Alheri ✍️
*S F*
Page 33&34