← Book details Soldiers Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 30

Sashe 5

Soldiers Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri tsohonnan yace, "to shikenan yarnan tashimuje cikin gari ayimata suturar"...."kuje zanzo ta fad'a atak'aice"... Tun Bata rufe baki ba yace, "to shikenan sekin k'araso" Yana gama fad'ar hakan yabar wurin domin shikanshi da basin mama yayi ba Adan zaman da sukayi yasan ba muryartace ba tunda yanaji tana yiwa mamarta magana wani lokacin.!

Yana zuwa tasanarda Yan uwanshi Aiko suka d'auki eggo akayi cikin gari da ita duk da sunci bak'ar wuya kafin sufita saboda nisanda kenan...bayan sunfitone Allah yakawo musu wata mota babba kamar boss duk sukashi bayan sunyiwa memotar bayanin inda zekaisu..

Basu tsaya ko ina ba seki dan wani daga cikin dattijuwan suna Isa ba suka Sami mama zaune ak'ofar gidan ba wanda yayi mmkin ganinta Idan sukayi duba da abunda ya faru b'ata lokaci akashiga yiwa eggo sutura domin sadata da gidanta na gaskiya...sai da duk aka gama yimata komai za,afitada ita kana d'aya daga cikinsu yazo domin ya kira mama taganta kafin su fita da ita...Amma seya samu tana bacci mamaki sosai abun yabashi harzetafi yabarta sekuma sekuma wata zuciyar tace yatadata hakan yashiga tadata yad'an jima Yana Dan buga k'afarta kamun tayi firgigit tamik'e zaune tana rarraba Ido tareda doba inda take atake atake abunda yafaru yashiga dawo mata tun inda wannan mutumin yafincikota har hankad'e eggo dayayi wani irin zaro Ido mama tayi tareda mik'ewa tana fad'ar, "eggo eggo kina inane Ina mahaifiyata? Me mukeyi anan? Misuka Mata? Dan Allah Ina sukaimun eggo ta?" K'wallah wannan bawan Allah yashare kamun ya janyo hannunta izuwa inda gawar eggo take kwance..Yana zuwa wani ya bud'ewa mama fuskar eggo daketa fitadda anuri cikin suturarta kamarba matacciyaba...wani irin jaa baya mama tayi tana k'walalo duka idanuwanta kafin ta k'wall k'ara tana Kiran eggoooooo innalillahi wa innailaihhiraji un nashiga ukku 🙆 Ni mama sunkashemun mahaifiyata ba tare da takaini garinsu ba sun rabani da farin ciki na na shiga ukku Ni mama.... kuka takeyi sosai akan gawar eggo dakyar aka d'aga ta wata mata tayi cikin gida da ita kana aka tafi kai eggo gidanta na gaskiya....ansha fama da mama awannan wunin domin in banda kuka ba abunda takeyi ahakan har dare yayi duk me Imani Idan yakalli mama dolene ya tausaya mama Inka duba karancin shekarunta Babu uwa Babu uba bawani takamme ko jigo arayuwarta😥....cikin dare Mama nazaune tana rusar kuka kowa yayi bacci itace kawai Ido biyu...dafata taji anyi Koda tad'ago taga wata mata tayi shigar fararen Kaya da murmushi kwance a fuskarta...cikin kuka tafad'a jikinta tareda cewa k'awata Ina kikaje sunkashemun eggo ta sunkashet....kasa K'arasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta be hanata ba sai da tayime isarta kana yad'ago ta tana share Mata hawaye kamun tace ba k'awarki bace mama yayartace k'awarki da bibibo basanan sunyi tafiya me Nisan gaske domin cika umurnin me martaba nikaina bansan abunda kefaruwa dakeba sai da abokin bibibo d'inki yasanar dani kiyi hak'uri mama munkasa Baki farin ciki kamar yadda muka d'auke alkawari munkasa tare Miki faruwar wannan abunda yasameki Amma kiyi hak'uri komai na duniya me wucewa ne watarana sai labari, ki d'auka wannan abunda yasameki k'addara ce daga ubangiji insha Allah komai zai zo ya wuce kinji.

*ZARAAH* d'agowa mama tayi dasauri tana kallan matar Jin ta fad'i asalin sunanta...itako murmushi kawai tayimata tare da shafa kanta tace nizan tafi kinji kirika yiwa mamarki addu,a kidena wannan kinjiko? Kai mama tad'aga cikin sauri kana tace zanbiki kikaini gun bibibo na bazan iya zama ananba Idan narufe Ido eggo nake gani kamar zata dawo tak'arasa zancen ciki kuka..."shikenan ya,Isa mama zanjeda ke Amma bibibo bayanan sedai Idan yadawo Zaki ganshi Zaki iya zama,inda nake? Daga matakai mama tayi cikin sauri..tace to shikenan rufe idonki...ba musu mama tarufe idanuwanta wannan matar ta b'ace b'at daga ita har mama kamar Basu tab'a wanzuwa awurinba..!

Tofa 🤔 wayannan bayin Allah wasukayiwa alkawarin zasu bawa mama farin ciki? Shin meyema had'inta dasu? Dasuka kasance wani gefe na rayuwarta?

Koda safiya tawaye mutanen gidan suka nemi mama sama da k'asa suka rasa abun kamar wasa har dare Babu mama abubu Alamarta megidanne yace sukwantarda hankalinsu kila mutanen datake taredasune suka d'auke ta tindadai ba wanda yashigo gidan balle ayi wani tunanin daban....sai a lokacin hankalinsu yad'an kwanta dudda basuji dad'iba Sam domin sunso rike mama tsakanida Allah domin tabasu tausayi matuk'a sai dai ba yadda za suyi da k'addarar rayuwarta..!

London

Wata baturiyace tsaye bakin k'ofar office d'in alyasat tana rike da wani abun ahannuta me kama da babyn roba (y'ar tsana) sedai kallo d'aya zakama abun kasan ba alkhairi a tare dashi duk'awa tayi wurin tana k'ok'arin daga carpet d'inda ke wurin sekawai muyar lateep Yana fad'ar leamtair mikijeyi ananne? Cikin sauri tatura abun cikin kasan wandonta tashiga k'ok'arin zuge igiyar takallminta tana fad'ar takalmanane yakwance Sr shine Zan d'ora.... kallonta yatsayayi kamar me nazarin wani abun domin Sam be yadda da itaba Kuma lateep be,iya b'oyoba Kuma nuk'u2 shiyasa yace ba gaskiya bane leamtair akwai dai wani abun Amma kasani ko miye nagani atare da brother na hummm....Yana gama fad'ar hakan yashige nashi office d'in...da kallo tabishi tana tinanin Hali irin nashi cikin ranta kuwa fad'ar takeyi koza,a mutu saita samu abunda takeso atareda alyasat..

Yau Thursday tun safe alyasat ke kiran k'annenshi domin suhashi da mahaifiyarsu Amma besamu ba kum. Ya tashi da k'ulafucin San yaganta domin hakan kawai gabanshi ke fad'uwa....wayarsa yajanyo tareda Kiran yusif Yana d'auka yace ""bro I will go to Dubai now? "What happened Satt?" Cewar Yusuf... nothing just I love see my mom...."ok wait I'm coming now....okay kawai yace tare da yanke wayar yatashi yashiga wanka bayan minti 15 yafito d'aure da towel akugunshi d'aya Kuma ahanunshi Yana tsane kanshi wurin mirror yanufa yashafa mayukanshi masu kamshin dad'i kana yafesa titare wurin kala ukku kamun yad'auko kayanahi yasaka kananun kayane wando blue Riga Marron gaskiya bakaramin kyau suka mishiba sufitida asalin kyawun farar fatarshi wayoyinshi yakwasa da jakar computer d'inshi kana yafita aperlo yaci karo da Yusuf da lateep suma duk cikin shigar kananun kayane ajikinsu Masha Allah dukkansu kyawawane ajin farko Amma alyasat yafisu kyau domin kyawunshi na dabanne Kuma da shi da Yusuf sun ɗan fi lateep tsayi shiko yafisu jiki... alyasat kuwa yafisu mird'ad'd'in jiki duk da suna ko wannensu ba baya ba...ahakan suka fita daga gidan cikin tafiya irinta majiya k'arfi masujida kansu way'anda hutu da nera suka gama ratsajinin jikinsu....suna fitowa kowanne yaranshi ya shiga suka taso tareda bud'e musu motocinsu suka shiga ahakan suma duk suka shiga tare da barin gidan tsiyace kamar yadda suka saba tare da d'aukar hanyar filin jirgi...!

*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk'atar complete kuma 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07037092176 kokuma kikira wannan number 👉 08107819124

Autar Alheri ✍️

🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)

*By Dr Yasmeen Ahmed*

Autar alheri ✍️

Page 11&12

__"suna Isa jirginsu yatashi zuwa Dubai..Koda suka sauka sunsamu mota samada 10 najiran saukarsu domin lateep yasarda dazuwansu wa yaransu dakenan sojojine cinjim a wurin suna jira karasowar iyayen gidan nasu...cikin takonsu na izza da tak'ama suka sauko daga jirgin zuwa cikin motocinsu Amma kamun suk'arasa duk inda sukawuce se an busu da kallon birgewa musamman Mata jikake kawai ana fad'ar wow abun gwanin Sha,awa....mota d'aya suka shiga su duka ukku inda sauran zugar mitocin suka take musu baya tareda halbawa akan kwalta.

Acan gida kuwa perlon ammy cike yake da matasan gidan musamman yaranta dake kewaye da ita suna kuka domin yau sunwayi garida wani abun mmki atareda ita Wanda yak'ara daga hankalinsu...zaune take kawai ba ko motsi numfashinta kawai zakaji ka tabbar tana Raye Dan murmushin datakeyi yanzu Babu idanuwanta sun kafe wuri d'aya...wannan abun baƙaramin daga hankalin ahalin gidan yayiba....tinda suka doso gidan gabanshi kek'ara tsananta fad'uwa zuciyarshi se tsinkewa takeyi Amma bazaka iya gane hakanba sabida bebari abun ya bayyana a face d'inshi ba....da mugun gudu motocin suka yanko babban titin stet d'in suna rabka uwar jiniya wadda kebada shedar zaratan samarin gidan sukawo ziyara.

Cikin tashin hankali daya bayyana a fuskar kowa dake wurin habibbty takalli suhaif tareda fad'ar kid'auketa amarda ita bedroom d'inta Kuma kuyi k'ok'arin Dede face d'insu karsu fahimci wani abun kamun musan abunyi Dan Allah kundai San waye alyasat basena gaya mukuba...Aiko cikin sauri alhassan yad'auketa kamar yad'auki baby yawuce da ita yayinda sadam yayi saurin Kuna tv kana kowanne yayi k'ok'arin dedeta natsuwarshi.... najeeb yace mukirkirin wani abun Wanda baze Bari yagano akwai wata matsalar ba... gaskiya kam domin dasun gammu hakan sesunyi tinanin wani abun cewar Fahad... suhaif yashare k'wallar idonshi kana yace kawai Idan suntambaya ma,iya cewa Muna meeting ne akan auren su yaya sadeeq..."eh to hakan ma yayi cewar sulaiman Wanda ko Baki berufeba suka shigo perlon.

Mik'ewa duk sukayi suna tin k'arar Yan uwannasu tareda shiga rungumarsu suna musu sannu dazuwa...Amma alyasat kamun wani yasamu zarafin ganinshi yawuce bedroom d'in ammy acikin sauri batareda yagaisada kowaba Kuma ba Wanda ya lura da hakan se Yusuf da Kuma habibbty sekuma Al, Hussain dayaje rungumarshi yakauce...Amma dai bawanda yace komi acikinsu.

Zama sukayi dukkansu anan perlon kamun lateep yace lpy kuwa naganku duka part d'in ammy? Mike faruwa ne? Murmushi ya shareef yayi Yana fad'ar bakomai fa kawai muna ɗan tattaunawa ne...da Ido yakafeshi kamun yace Anya kunada gaskiya kuwa? "Eh munada gaskiya Mana Yaya lateep suka had'a baki wurin fad'ar hakan...kallan juna akayi tsakanin yusif da lateep kana suka girgiza kansu irin akwai wata ak'asa d'innan kamun yusif yace akanme kuke tattaunawar?

Akan bikinsu Yaya shareef Mana suka koma fad'a atare kamar masu jiran tambayar? "Humm yy kyau suka fad'a atare suma domin Basu yadda ba.....alyasat kuwa yanashiga yaganta kwance alrufeta da blanket yaje yashafa fuskarta tareda Kura Mata Ido nawani Dan lokaci kana yamanna mata kiss agoshi yafito dudda jikinshi nabashi wannan bacci bana lpy bane Amma koba komai yad'an samu sauk'i aranshi tinda yaganta..
Chapter 5 · 0% Book details