← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Driving yake amma hankalinsa na kan Ruhaima sufa mata zurfin tunaninsu kaɗanne shiyasa babu wahala an yaudaresu ko anyi musu wayo, abu kaɗan ke jan ra'ayinsu har su amince da mutum su bashi yarda ɗari bisa ɗari alhalin da yawa da suke yiwa kallon masoya ba masoyan nasu bane wanda suke kallon sune maƙiyansu a haƙiƙanin gaskiya sune masoyan nasu,

Bayan la'asar ya isa gida, sai da yaga umaima sannan ya tuna da abinda ya faru, shifa wallahi ko tuna maganar nan ma baya son yi bare maimaitata, bece uffan ba kan lamarin ya nemi wuri ya zauna yana kallon hajiya wacce ke yankewa Ajmal farce,

"hajiya nace ya dace a saka yaron nan a makaranta....."

Dakatawa daga abinda take yi hajiyan tayi ta zuba masa ido na É—an wasu lokuta sannan tace "wannan tunani ne mai kyau Sameer.... Ni É—inma abin yana raina dama kuma mune muka fi dacewa da cancanta wurin kula da gina tarbiyarsa ba wai iya mahaifiyarsa ba, mune zamu tallafa mata har ta cimma burinta wurin gina tarbiya da rayuwarsa..... Allah yayi maka albarka, wacce makaranta kake ganin ya dace a saka shi? "

" Amin hajiya..... Akwai wata nan kusa sai akaishi "

" to Allah ya bada sa'a "

Farin ciki yaji yana mamaye ilahirin zuciyarsa sakamakon ganin irin farin cikin da Ajmal ɗin ya shiga jin za asakashi a makaranta dan har ya garzaya ya tafi sanar dasu Abid. Daren ranar ya ɗauki Ajmal suka tafi shopping duk wani abu da ya san yaron zai buƙata ko mahaifiyarsa sai da ya siya daga nan suka wuce wurin Ruhaima, bai shiga ba iya Ajmal ɗinne ya shiga sai ko kayan da ya sissiyo musu wanda ya barwa mai gadi ya shigar mata dashi,

Tana kwance falo kan kujera lokacin da Ajmal É—in ya shigo, cemata yayi wai shi da uncle ne bakinsa ta É—an mara kaÉ—an tace,

"Daddy ne ba uncle ba, na faɗa maka daddy zaka rinƙa ce mishi...."

"yace zan fara zuwa school"

Murmushi tayi ta tashi zaune jin alamun buɗe ƙofa, ganin mai gadi da kayayyaki niƙi niƙi ya sata kallon Ajmal,

"ina kuka fara zuwa kafin ku zo nan?"

"shopping...."

Ba tace komai ba ta karɓi kayan duk da ta san ba dan ita yayi ba sai dai ko dan ɗan ɗan uwanshi,miƙewa tayi ta leƙa window nan ta hango shi tsaye shida mai gadi ko me suke cewa oho sai su sai Allah, yana sanye da ƙananan kaya jar t shirt da baƙin wando, komawa tayi ta zauna bata sake jin ɗuriyarsa ba dan bata ma san lokacin da ya tafi ba saboda ko shigowa baiyi ba. Haka ta kwana zuciyarta cunkushe da tunani kala kala, ta saka wancan ta kunce, duk ta rasa me ma ya dace tayi kan maganarsu da mukhtar, ita dai ta san ba wai sonshi take ba to ita yanzu ma ai babu batun wata soyayya a gabanta kawai dai zata yi aure ne aure irin na rufawa kai asiri bawai dan soyayya ba sannan har yanzu ta kasa jin nutsuwa a cikin ranta na ta amince ko karta amince, daren ranar dai sai bacci ɓarawo amma tajima tana juye juye.

Washe gari da safe misalin ƙarfe 11 ta gama shirya Ajmal bayan itama ta shirya cikin atamfa super Holland coffee color, ɗinkin riga da skirt ne, yau tunda garin Allah ya waye mukhtar ke faman turo mata saƙonni, jin yace wai yana nan zuwa anjima ya sata yin murmushi tare da mayar masa da amsa cewa unguwa zata je, kamar jira yake sai ga kira, a ƙagare ta ɗauka don kunya take ji duk sai ta rasa me zata ce,

"ayi min alfarma in zo inyi rakiya...."

Ɗan jim tayi kafin ta bashi amsa "ba wai naƙi bane amma...."

"dan Allah kar akatse min hanzari sannan kar a sace min gwiwa.... Idan kika ce a'a bazan ji daÉ—i ba"

"to shikenan sai ka zo...."

Sallama suka yi ta katse wayar tana jin aranta hakan bai dace ba, ta yaya zai kai ta gidansu abban Ajmal? Idan taƙi kuma shi yaji babu daɗi yaga kamar ko tana ɓoye masa wani abune, ita kuma zuwan nan da zata yi ma zata yi shi ne dan umaima so take taje ta rarrasheta tayi haƙuri ta koma ɗakin mijinta ko dan farin cikin yaranta,

Ita dai gaba ɗaya a ɗarare take da mukhtar ko hirar ma da Ajmal suke yi ita dai kunnene nata, har suka ƙarasa gidan hajiya maganarta bai fi a ƙirga ba, a waje ya ajiye su suka shiga shikuma ya tafi,iya hajiya kaɗai suka samu a falo ta gama karyawa bayan sun gaisa ta wuce bedroom wurin umaima, ganinta tayi kwance kamar marar lafiya duk idanuwanta kumbure saboda kuka,

Zaune ta tashi tana kallonta fuskarta asake,

"in law kune kuke tafe?"

"in law ai ni fushi nake.... Ya za ayi ki ɗauki abu da zafi har haka? Wannan hukuncin da kika ɗauka baiyi ba gaskiya, kiyi haƙuri ki share komai ki koma gidanki..."

Ido umaima ta zuba mata har na tsawon wani lokaci kafin ta girgiza kai tace,

"Ruhaima kin san kuwa abinda nake ji? Kin san irin baƙin cikin da zuciyata ke ciki? Miji irin wannan babu amfanin cigaba da zama dashi..."

"wallahi na san yanda kike ji in law.... Karki faɗi haka, kiyi haƙuri ki koma gidanki kicigaba da addu'a Insha Allah wata rana sai labari.... Abubuwa da yawa kana haƙuri dasu ne kana shanyewa ba wai dan kanka ba a'a sai dan yaranka kar su shiga wani hali... "

Haka tacigaba da yi mata kalamai da faɗa mata maganganu masu daɗi har ta sauko ta yadda zata koma amma wai sai ta huta, dariya Ruhaima tayi tace hakanma ta gode, suna ƙule a ɗaki tana sanar da ita maganar mukhtar da kuma irin yanda ya matsa shi so yake ayi biki cikin ƙanƙanin lokaci har azahar tayi sai da hajiya ta aiko Abid wai yazo ya kira su suje suci abinci, fita suka yi suna dariya, hajiya suka hango saman dining kusa da ita Sameer ne suna cin abinci tare a faranti ɗaya,

"a'a yau ma ƙaunar ce ta motsa kenan..." umaima ta fada tana dariya,

"to ai dama koda yaushe wannan ƙaunar tana nan" hajiya ta bata amsa, ita dai Ruhaima ba tace komai ba, haka in banda gaisuwa babu abinda ya haɗasu da Sameer itama sama sama suka gaisa dan ta kula sai faman haɗe girar sama da ƙasa yake,a falo taja birki ta zauna nan umaima ta kawo musu abincin, jalop ɗin shinkafa da ɗanyen kifi amma su kuma su hajiya taga kamar macaroni suke ci,

"kin san shi waccan patient É—in baya cin kifi....." umaima ta faÉ—a lokacin da suka fara cin abincin,

"kuma ko ansaka bai ganiba sai ya gane?"

"ai tun daga nesa zai jiyo dan jaraba..."

Dariya suka yi gaba É—aya atare hakan ya janyo hankulan su hajiya gaba É—aya ya dawo garesu,

"ya aka yi kuma?" hajiya ta buƙata,

"hajiya in law ta samu bazawari, yanzu maganar aure ake"

Tunda yaji abinda umaima tace ya sake ɓata rai, ita kuma Ruhaima ji tayi kunya ta kamata. Tamkar wanda ya ƙware take ya soma tari mai rikitarwa harda faɗowa daga saman kujerar da yake zaune a kai, nan fa hankula suka tashi musamman na hajiya dan tafi kowa sanin irin baƙar azabar da yake sha a duk lokacin da wannan lalurar tashi ta motsa,

"yaya Sameer..... Yaya Sameer attack ka samu?" Umaima ta faɗa cikin tashin hankali, kai kawai ya iya ɗaga mata yana kokawa da numfashinsa wanda ke ƙoƙarin yankewa.........

*HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡

IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻

HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA,

*1.AYUSHER:-*
Writing by FERTYMERH XARAH

*2.ƘAZAFI NE:-*
Writing by RAHAMA NALELE

*3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-*
Writing by ZAINAB BAWA

*4 SO DA ALAƘA:-*
Writing by UMMI A'ISHA

WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘

Guda 4:- 1500
Guda 3:-1200
Guda 2:- 800
Guda 1:- 400

7033027658
Palmpay Bank
Aisha Muhammad Salis

Katin wayar MTN ta...
07044644433 da shaidar biya

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[19/08, 7:47 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*SO DA ALAƘA......!*

*NA*

*UMMI A'ISHA*

TAURARI HUÆŠU
free page

Wattpad:@Ummishatu

9

***Da taimakon umaima da na hajiya ya samu ya kai ga kan gadon hajiya domin bedroom É—inta shine mafi kusa daga inda ya samu attack É—in,

Ita dai Ruhaima gaba ɗaya ji tayi tausayinsa ya kamata lokaci guda, ita dai ta san sau da dama Imran ya kan ce mata Sameer ne baida lafiya ko kuma yasamu attack amma idanuwanta basu taɓa gani ba sai yau, wani irin kai komo taga numfashinsa nayi, lallai in dai hakane masu irin wannan lalurar suna buƙatar tsananin kulawa ta musamman,

Yanda su hajiya suka ruÉ—e ita É—inma a ruÉ—en take dan jikinta gaba É—aya in banda karkarwa babu abinda yake yi. Hankula basu kwanta ba har sai da aka yi masa allura bayan an kira likita, bacci ya É—an samu na tsawon wani lokaci,

Tagumi Ruhaima tayi tana kallon umaima wacce ke cin abincin da suka bari, ita kam gaba É—aya tama kasa ci,

"wai in law dama haka yake fama da wannan ciwon?"

"wallahi in law... Kuma kinga shi kaɗai keda shi duk familynmu,ƙaddara dai kawai"

"Allah sarki, Allah ya bashi lafiya ya yaye masa, amma maganin ba ayi masa na hausa?"
Chapter 9 · 0% Book details