← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In banda salati babu abinda hajiya ke yi jin labarin abinda ya faru da Umaima ta kwashe ta sanar da ita yanzu kamar yadda itama Alhaji sabo mijinta ya sanar da ita babu abinda ta ragewa hajiya ta sanar da ita komai, jiki a sanyaye kuma a mace hajiya ta kashe wayar bayan ta gama jin abinda ya faru, tabbas ta san Ruhaima tana da nutsuwa da kunya da halin ƙwarai to amma yanzu ba a shaidar mutum shine matsalar, mutum yana iya canjawa akoda yaushe sannan kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, haka kuma wani abin ƙaddara ce wadda babu yadda mutum zai yi da ita, ita ta ɗauki Ruhaima tamkar ƴar da ta haifa ta cikinta ba wai sirika ba, duk abinda zata yiwa ɗan cikinta shi zata yiwa Ruhaima,wayarta ta sake ɗauka ta fara kiran layin Ruhaima,

Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban handbag ɗinta ta ciro wayar ganin hajiya ce me kiran yasata jin kunyar duniya ta lulluɓeta ta san Sameer yaje ya sanar da ita halin da ake ciki,

"Haba Ruhaima.... Ya ina yabon ki salla amma zaki kasa alwala.... Dan kina cikin wani hali Ruhaima sai ki kifara ƙoƙarin ɓata rawarki da tsalle?? Ai ko wani ne awaje Ruhaima bai dace ki kai masa kanki ba harda yunƙurin sata bare mijin Umaima....."

"Hajiya dan Allah ki fahimceni ke kadai na san zaki fahimceni akan wannan lamari wallahi yanda ake tunani ba haka abin yake ba...." ta faÉ—a cikin kuka,

"Wannan ai ya wuce Ruhaima sai dai a kiyaye gaba, dukkan ɗan adam ajizi ne amma ki kiyaye, dan Allah.... Ni tunda Sameer ya dawo naji yaƙi magana dama naji hankalina bai kwanta ba sai da Umaima ta kirani yanzu, Allah ya rufa asiri amma ki kiyaye dan Allah" daga haka taji hajiya ta katse wayar, take kuma wani kiran ya sake shigowa kamar dama jira ake, ganin Umaima ce sai da gabanta yai muguwar faɗuwa,

"Hello inlaw....."

"Karki fara... Karki kuskura ki sake kirana da haka Ruhaima... Ai baki É—aukeni a hakan ba tunda har kike bibiyar mijina, dama wannan shine dalilin da yasa kika zo har gida neman sa?"

"Dan Allah ki fahimceni Umaima, kema kin san wallahi ko a mafarki bazan taɓa aikata hakan ba...."

"Daga yau sai yau wallahi babu ke babu mijina, idan kika sake yunƙurin kusantar mijina zaki gane shayi ruwa ne......"

"Umaima karki bari shaidan ya shiga tsakaninmu dan All....." ƙitt taji Umaima ta datse kiran, wasu hawayen baƙin ciki ne suka sake ɓarke mata, daman ta san yanzu babu wanda zai yarda da ita kowa kallon mai laifi yake yi mata duk da irin kokarin da hajiya ke yi a kanta ace ta aikata haka ai da ta tabbata butulu, kukan nan dai shi take ta yi har tsawon wani lokaci da ita kanta bata sani ba.

Samun kansa yayi cikin wani ƙarin ɓacin ran a duk sa'ilin da ya tuna wayar da yaji hajiya suna yi da umaima, wato Alhaji sabo sai da ya kwashe duk abinda ya faru ya fadawa umaima kenan saboda tsabar rashin kara, Meyasa bazai rufa mata asiri ba sai ya sake zubar mata da mutunci acikin family? Haushi ne ya kamashi ya ja tsaki,

"Kawai salon ta jawowa mutane magana..... Sai da ta dauko mana magana dai hankalin ta ya kwanta" ya faɗa cikin ɓacin rai yana tashi daga kwancen da yake kan madaidaicin gadonsa,

Kukan magensa ne ya sake tunzura shi, dan shi yama manta da ita, ba dan ya so ba ya miƙe ya buɗe ƙofa, yana buɗewa ta shigo tana shinshina ƙafarsa sunkuyawa yayi ya ɗauketa yana shafata, ganin tana lasar baki yasa shi dafe kai,

"am sorry pretty.... Yau ban baki abinci ba sai sau ɗaya... Wallahi kaina ne a caje daren yau ɗinnan...." Saman gadonshi yaje ya ɗorata sannan ya fita, part ɗin hajiya ya sake komawa bai jima ba ya fito riƙe da glass cup cike da madarar kwali sai abinci a wani ɗan ƙaramin filet, part ɗinsa ya koma ya ɗauki magen ya ɗora akan cinyarsa ya soma bata abincin da madara tana ci,har ta cinye tas ya kwantar da ita kusa dashi, haka dama yake rayuwa da wannan magen wadda ya sakawa suna pretty tun tana yar ƙarama da ya tsinceta a lambun gidan ya ɗaukota, tare suke kwana.

Da ƙyar ta samu bacci daren ranar dan sai bacci ɓarawo, bayan asubah ta samu ta farka, amma tana farkawa abinda yafara zuwa ranta shine abinda ya faru jiya, take ta ji wani sabon bakin ciki ya sake turnuƙeta sai da ta share hawaye sannan ta shiga bathroom ta ɗauro alwala tazo tayi salla, bayan ta idar ta ɗauki alqur'aninta dake ajiye gefe ta karanta abinda ya sawwaƙa sannan ta rufe ta soma azkhar. Wunin ranar gaba ɗaya acikin ɗaki tayi shi duk da dama hakan ɗabi'arta ce yanzu amma na yau kam kamar na dabanne, shigowar baba saude mai aikinta wadda yanzu ita kaɗai ta rage acikin ma'aikatan gidan dan duk sauran ta sallamesu tun jimawa,shigowarta ne yasa ta tashi zaune da koɗaɗɗun idanuwanta take kallon baba sauden,

"Ruhaima... Lafiya kuwa yau duk baki fito ko falo ba? Ko wani wurin ke yi miki ciwo?"

"Wallahi lafiya lau baba saude.... Kawai dai akwai abinda ke damuna"

"Hakane.... Kowa ka gani dama akwai abinda ya dameshi sai dai hakuri, duk abinda yake damun bawa idan yayi hakuri zai wuce, na san kina cikin damuwa amma ki kara haƙuri akan wanda kikayi abaya Insha Allah ubangiji Allah zai baki mafita sannan yana tare dake a koda yaushe... Allah ya fiki sanin damuwarki Ruhaima kuma zai kawo miki ɗauki Insha Allah "

Duk da bata bayyanawa baba saude damuwarta ba amma kalaman na baba saude sun samar mata da nutsuwa kuma sun sanyaya mata zuciyarta haka kuma sun rage mata wani kaso mai yawa daga cikin damuwarta, ƙwarin gwiwa taji ta sake samu akan ƙudurinta da kuma nufinta,

Bata san lokacin da ta É—auki wayarta ta kira hajiya ba, da sallama hajiya ta É—auki wayar tata lokacin suna tare da Sameer acikin bedroom É—inta yana kwance kan gadonta Ajmal yana kan ruwan cikinshi yana doki dashi,

Saida ta gaida hajiya sannan cikin sanyin muryarta wanda ya gaurayu da damuwa tace "Hajiya dan Allah ina son magana da Umaima da Sameer da kuma ke harma da Alhaji sabo idan zai yuyu... Ma'ana dai ina so mu haɗu gaba ɗayanmu anan gidan ki kuma gabanki dan akwai wata sarƙaƙiya da nake son warwarewa....."

"To shikenan Ruhaima amma ni da sai nake ganin idan har akan waccar maganar ce ta abinda ya faru da kin barshi..."

"a'a hajiya a dai taimaka min a saurareni...."

"to shikenan sai mu barshi asabar ko saboda kinga suna zuwa aiki...."

"hakan yayi hajiya nagode Allah ya ƙara girma..."

Sallama suka yi, É—an tashi zaune Sameer yayi yana kallon hajiya,

"me kuma ya faru?"

"Ruhaima ke son Magana damu gaba É—aya.... Ina jin zata koma gida ne amma dai bata faÉ—i hakanba kawai hasashe na ne..."

"zata koma gida kuma? To amma hajiya ai bai kamata mu barta ta tafi ba..." ya fada cikin damuwa yana ƙarasa tashi zaune,

"to ya za ayi Sameer? Bari dai lokacin yayi sai muji me take tafe dashi"

Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya fita cikin damuwar dashi kansa bai san ko ta mecece ba, farfajiyar gidan ya fita ya samu ya jingina hannayensa cikin aljihun bakin trouser ɗin dake jikinsa..........✍🏻

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[16/08, 7:32 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*SO DA ALAƘA...!*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad:@Ummishatu*

Free page

6

****Rasa abinda zai yi yayi sai faman zancen zuci yake ta yi shi kaÉ—ai,

"to ko maganar da na fada mata ne ta ɓata mata rai? Na faɗa mata wani abu mai zafi ne?" ya tambayi kansa yana kallon harabar gidan,

"amma ni a iya sanina ai gaskiya na faɗa mata, bai kamata ta rinƙa ɗauko mana magana ba dan kawai tana missing mijinta...." ya sake bawa kansa amsa, "oho dai..." daga haka ya fita daga ma gidan baki ɗaya a ƙafa batare da ya ɗauki motar shi ba, sai dai duk da ya zurfafa tunaninsa ya kasa gano dalilin da yasa Ruhaima tace tana son ganinsu gaba ɗaya, tafiya yayi sosai acikin unguwar yana zagayawa daga ƙarshe ya yada zango a masallacin wani ƙofar gida dake da maƙotaka da unguwar tasu ganin lokacin sallar magariba yayi.

Sai da yayi salla sannan ya koma gida, sashensa ya wuce kai tsaye yayi wanka sannan ya fito riƙe da magensa pretty, lokacin da ya koma part ɗin hajiya samu yayi Ajmal yana tv game a falon hajiya nan ya biyeshi suka yita yi tare kamar wani sa'ansa har saida Ajmal ɗin yayi bacci. Washe gari itace ta kama ranar da Ruhaima zata zo domin ganawa dasu kamar yadda ta roƙa, duk da tana cikin tsananin fargaba da da tsoro amma ta dake ta daure tana ta addu'a da haka ta shirya, navy blue color na leshi ta saka mai duwatsu ɗinkin riga da skirt, turare kaɗan ta ɗan fesa sama sama sannan ta kawo blue ɗin mayafi ta yafa, sam bata ɓatawa kanta lokaci ba wurin yin kwalliya domin ko mai bata shafa ba saboda a haƙiƙanin gaskiya bata cikin nutsuwa da farin ciki tun daga ranar da Alhaji sabo yayi mata wannan sharrin,

Misalin ƙarfe 12 na rana ta isa gidan hajiya duk da dai gabanta sai faman faɗuwa yake, a falo ta tarar da hajiya da umaima wadda ko kallo bata isheta ba, duk sai ta sake jin babu daɗi ga kuma yaransu nan suna wasa tare wato su Abid tare da ɗanta Ajmal, daurewa tayi bayan ta gaisar da hajiya ta saki fuska tace,

"umaima ina wuni?"

Kamar ba zata amsa ba dan aciki ciki ta amsa gaisuwa, duk da hakan yayiwa Ruhaima ciwo amma sai ta basar ta danni zuciyarta, itama hajiya ganin haka yasata kiran Sameer awaya aganinta gara yazo su yi su yi abinda ya tarasu kowa ya koma gidansa bata son irin wannan zaman na doya da manja,
Chapter 6 · 0% Book details