Sashe 7
So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ita dai Ruhaima a ranta tunani take to ya taga umaima ita kaɗai? Ina mijin nata ko dai ba zai zo bane? Tana son ta sani amma babu damar tambaya, jin horn acikin gidan ya tabbatar musu da zuwan wani baƙon,
"yawwa ga abbansu Abid ɗin nan ma ya ƙaraso hajiya" inji umaima, Wani sanyi Ruhaima taji acikin ranta,
Zuwan Alhaji sabo yayi daidai da fitowar Sameer daga part ɗinsa, sanye yake cikin ƙananan kaya farar t shirt ta polo sai blue ɗin wando jeans, gaisawa suka yi da Alhaji sabo sannan ya jagoranceshi zuwa ciki,
Bayan gaishe gaishe Sameer ya dubi hajiya wadda ke zaune É—an gaba dashi kaÉ—an,
"Hajiya Nifa inada uzuri.... Dan Allah ayi abinda za ayi"
Kallonsa Ruhaima tayi ta ƙasan ido ita dai a rayuwa ta rasa me tayiwa bawan Allahn nan da bata burgeshi tsakaninta dashi ko yaushe sai harara sai ɗaure fuska sannan babu wata magana mai daɗi da take shiga tsakaninsu dan ko gaishe shi tayi tun lokacin da yayansa yana nan a ciki ciki yake amsawa kai kamar ma a dole yake amsawar dama kuma bama zuwa gidan nata yake yiba sai da ƙwaƙƙwaran dalili,
"to ai Ruhaima ce ta taramu dan haka ita muke saurara...." maganar hajiya ta ratsa kunnuwanta nan ta dawo cikin hankalinta daga tunanin da take yi, gaba ɗaya kowa ita yake kallo kuma yake saurare banda Sameer wanda ko kallo bata isheshi ba dan wayar shi ma yake dannawa, shi kuwa alhaji sabo ido ya ƙura mata acikin ransa yana bakin ciki da takaicin rashin cikar burinsa yaso ya ɗanɗana kayannan yaji dan ya san zai samu cikakkiyar nutsuwar da yake so, amma yanzun ma bai haƙura ba kuma bai sare ba zai sake jarraba wata hanyar har sai ya dace,
"Kamar yadda kowa ya sani, ni marainiya ce na taso cikin maraici, cikin babu......"
"To sai me? Kowa ya san wannan, idan dan shi kika taramu muna da abin yi..." Sameer ya faÉ—a ta hanyar É—aga mata hannu alamar dakatarwa, bata kula shi ba taci gaba da faÉ—in abinda take da niyyar faÉ—a,
"Duk da na taso cikin babu, babu cin yau babu na gobe, babu suttura babu kayan ƙyale ƙyale ko more rayuwa hakan bai taɓa sani tunanin inyi sata ko in ɗauki abin wani ba, ban taɓa ji araina zan saci kayan wani ko in bada mutuncina dan in mallaki wani abu ba.... A koda yaushe kakata tana faɗa min cewa wadatar zuciya itace babban arziƙi koda mutum baida cin yau baida na gobe, nasha wahalar rayuwa iri iri a lokacin da nake tasowa saboda babu, amma haka na jure nayi hakuri har zuwa girmana, wallahi tallahi kayan wani ko dukiyar wani bata taɓa burgeni ba bare har inji araina zan iya ɗauka da sunan sata..... Abban Ajmal ya taɓa sanar dani sunyi haɗin gwiwa da Alhaji sabo wurin gina wani kasuwanci, nikuma a halin yanzu inada buƙatar kuɗi dan in gina rayuwar ɗana, lokacin da naje gida nemansa umaima tace yayi tafiya, ganin maganar ko a waya zan iya yi masa shiyasa na buƙaci da ta bani no wayarsa, shi da kansa yace bazan iya ganinsa ba a gida saboda yana da meeting amma zan iya samun ganinsa a guest house ɗinsa dan kusan gaba ɗaya harkokinsa yanzu acan yake gudanar dasu, wallahi zuciyata ɗaya na shirya naje ban taɓa tunanin wai da wata manufa ya gayyaceni can ba, lokacin da naje ya fito min da ƙudurinsa ban amince ba dan aganina wannan cin amana ne amma sai ya nemi da yayi min ta ƙarfi..... " wani kuka ne yaci ƙarfinta dama kuma tun lokacin da ta fara maganar hawaye ke bin kuncinta, duk jikin kowa yayi sanyi da kalamanta duk da wai basu gaskata cewa alhaji sabo yayi yunkurin yi mata fyaɗe ba,
" Ta yaya zamu yarda da abinda kike faɗa? Kina da wata shaida?" umaima ta faɗa a kufule saboda jin abin da ake faɗa akan mijinta, yayin da shi kuma alhaji sabo kallon Ruhaima kawai yake yana tunanin ta inda yakamata ya soma wanke kansa ya sake ɗaureta sannan ya ɓatata a idon kowa,
Handbag É—inta ta buÉ—e ta ciro wayarta tana goge hawaye,
"wannan itace maganar da muka yi awaya...." ta faÉ—a tana kunna recording É—in da tayi, bayan duk an gama saurara ta sake kunna wani tana cewa "wannan shine abinda ya faru a guest house É—insa"
Kowa nutsuwa yayi yana sauraren maganganun alhaji sabo wanda suke fita tar kamar yanzu yake yi, duk abinda ya faru tun daga zuwanta har lokacin da suka yi magana da mai gadi ya kirashi awaya har shigarta da yadda ya rinƙa hilatarta tana ƙi da kokawar da suka gwabza da komai kai har zuwan ƴansanda duk sai da kowa yaji, kunya ce ta lulluɓe alhaji sabo yaji kamar ƙasa ta buɗe ya shige dan tsabar kunya, bai taɓa jin kunya irin ta yau ba, da ya san wannan ranar zata zo tabbas da bai aikata abinda ya aikata ba, ita kuwa umaima kuka ta fashe dashi, babu wanda ya iya magana daga hajiya har Sameer, itama Ruhaima kukan take yi duk da bata so ta tona masa asiri ba amma bata da wani zaɓi illa hakan ko dan ta wanke kanta daga kallon da kowa ke yi mata, miƙewa tayi ta ciro kuɗin da ya bata dubu ɗari, ta ajiye a gabansa tace,
"waɗannan sune kuɗin da ka bani.... Bani da buƙatarsu a yanzu, gashi na dawo maka dashi...."
Shi dai alhaji sabo kansa na sunkuye a ƙasa gumi sai yanko masa yake tako ina saboda tashin hankali,ganin ta juya tana ƙoƙarin barin falon tana kuka umaima tace,
" Ruhaima dan Allah ki yafe min.... Nabi daÉ—in bakin namiji na biyewa kishi idanuwana sun rufe na kasa fahimtarki... Wallahi koda wasa ban san mijina yana da irin wannan halin ba" tsayawa tayi cak tana sauraren maganganun umaima, kai kawai ta É—aga mata alamun gamsuwa amma daga haka bata iya cewa komai ba ta fita daga falon tana share hawaye......âœðŸ»
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
[17/08, 9:41 am] Baby Aysher: Â©ï¸ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*SO DA ALAƘA....!*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
Free page
7
***Ita kanta bata san a halin da take ciki ba ahalin yanzu dan ko shakka babu da za a tambayeta ba zata iya kwatanta yanayin da take ciki ba, baƙin ciki da farin ciki duk a lokaci guda duk da cewa dai baƙin cikin yafi yawa amma duk da haka taji daɗin yanda Allah ya kawo mata mafita har ta samu zarafin wanke kanta, dama ita gaskiya haka take duk daren daɗewa sai ta bayyana kanta sannan bata buƙatar taron dangi wurin bayyanarta saɓanin ƙarya, tana tafe tana share hawayenta har ta samu ta fita daga cikin gidan. Yanda Ruhaima ta fita ta barsu haka duk suke zaune kowa ya gaza koda ƙwaƙƙwaran motsi bama kamar ya alhaji sabo da gaba ɗaya yake jinsa kamar an dasa shi a wurin da yake zaune, shi yanzu koda magana zai yi baima san me zai ce ba, sannan ba zai yuyu ya tashi ya fita haka kawai ba tare da yace wani abu ba, bugu da kari baida koda kalma ɗaya da yake ganin zai iya amfani da ita wurin kare kansa, gaba ɗaya Ruhaima ta gama kunce masa zani acikin kasuwa, ta gama tona masa asirin da ya jima yana binnewa wannan fa shi ake kira da rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya, gaba ɗaya ilahirin falon yayi tsit baka jin komai sai shassheƙar kukan umaima wanda ya fara karaɗe falon,
"wallahi ka cuceni.... Amma ka sani kaima ka cuci kanka kuma na gama zama da kai dan bazan iya cigaba da zama da mazinaci ba....." daga haka ta yi ciki tana rusar kuka bata ko sake bi ta kansa ba,
Sameer kam kallonsa kawai yake a ƙule zuciya ta zo masa wuya amma dai bai yi magana ba dan ya san kome zai faɗa to ba mai daɗi bane a wannan lokacin shiyasa ya zaɓi yayi shiru, miƙewa ma kawai yayi ya fita, fitarsa babu jimawa itama hajiya ta shiga ciki ba tace da Alhaji sabo ko kanzil ba, nan ya sha zamansa ya gaji daga ƙarshe ya tashi yabar gidan.
Yanda ta fito daga gidan hajiya haka taci gaba da tafiyarta tana kuka duk da masu napep na tsaya mata wai ko zata shiga amma sam bata tanka su dan bata jin zata hau abin hawa, tana dab da fita daga cikin unguwar su hajiya taji alamar mota a bayanta ko juyawa bata yi ba duk da uban horn ɗin da ya addabi kunnuwanta da ƙara, har ya ƙaraso kusa da ita bata kalli motar ba sai da ta jiyo sautin muryarsa,
"Shigo in kaiki gida....."
Cak! ta tsaya kamar mai nazari, wai shi wannan wanne irin murɗaɗɗen mutum ne? Salon ta shiga yau ma ya yaɓa mata duk maganar da tazo ransa? Daurewa tayi ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shiga,
Tun bayan shigowarta taji ƙamshin turarensa wanda ita dai zata iya cewa tun ranar da ta fara ganinsa taji wannan ƙamshin kuma har yau bata ƙara jinsa awurin wani ba,