← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 12

Sashe 8

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru motar tayi kamar babu kowa aciki wanda har hakan saida ya takurata, shi ɗinma kamar kusan hakan ƙila ma wannan dalilinne ya sanya shi kunna radion dake maƙale cikin motar, daga ita ita har shi ba wani sauraren radion suke yiba, ɗan satar kallonsa tayi ta gefen ido, fuskar shi yau babu yabo babu fallasa saɓanin irin yadda ta saba gani ko yaushe, a fisge dai yana yi mata kama da Imran sosai sai dai akwai ta inda suka bambanta da yawa, shi Imran fari ne dan za a iya saka shi cikin layin farare amma Sameer baƙi ne bawai chocolate color ba a'a baƙine sosai amma duk da hakan tana mamakin yadda mutane tun ba yanzu ba suke faɗin kyawun Sameer fiye da na Imran koda yake ita bata taɓa tsayawa tayi masa kallon ƙurulla ba sai dai ta kalleshi a sace shi ɗinma sau ɗaya take bata ƙarawa, amma dai ta san yanayin tsayinsu da jikinsu kusan duk iri ɗaya ne dan yanda Imran yake a tsaye shima haka Sameer ɗin yake sannan wani abu dake sake ruɗata shine muryarsu kusan iri ɗaya dan duk lokacin da taji yayi magana sai taji kamar Imran ne yayi,

Har suka isa gidanta babu wanda yace uffan, bayan yayi parking tana ƙoƙarin fita yayi ta maza wurin dakatar da ita bayan ya gama tattaro juriyarsa wuri guda dan shima kunyar ta yake ji na maganganun da ya fada mata ba tare da taunawa ba,

"amm.... Dama nace.... Kiyi haƙuri da abinda ya faru ranar nan..... Raina ne a ɓace shiyasa...... Kiyi hakuri"

"babu komai.... Ya wuce" daga haka ta fita ta rufe masa ƙofar motar, bai tafi ba saima fita da yayi domin yin sallar azahar yabar motar tashi nan cikin gidanta. Ita dai ciki ta shiga bata sanma yabar motarshi a gidan ba, ko ba komai yau dai ta samu nutsuwa cikin ranta sannan ta samu sauƙin halin da take ciki, alwala tayi tai salla bayan ta idar ta yiwa Allah godiya da ya kubutar da ita sannan kuma ya wanketa daga zargi, tana zaune kan abin sallar taga kiran mukhtar ya shigo cikin wayarta, mukhtar wani matashin magidanci ne dake rike da matsayin manager na wani babban store wanda yayi suna sannan yake kan shura har yanzu cikin wannan jaha mai albarka, tunda ya ƙyalla ido ya ganta lokacin da suka je shopping ita da Ajmal yabi ya liƙe mata, a zahiri dai ta san ba shida makusa duk da bai kai tsohon mijinta ba amma shi dinma zata iya sakashi sahun mazan ƙwarai sai dai da yake zahiri daban sannan baɗini daban haka kuma mutane yanzu sanin haƙiƙanin waye su sai ubangiji domin shi kaɗai ne masanin sirrin ɓoye da fili, ji tayi har cikin ranta ta gamsu da mukhtar yanzu sannan tana ganin lokaci yayi da zata bashi dama su sasanta su fahimci juna har su kai ga aure tunda dai yana mutuƙar ƙaunarta, gara dai kawaima tayi auren nan ta huta ko ba komai igiyar auren zata tare mata abubuwa da yawa, ayanda dai ya faɗa mata matarshi ɗaya wacce ta kasance cousin ɗinshi ce domin auren zumunci suka yi sai yaran su guda biyu mace ɗaya namiji ɗaya suna zaune a unguwar court road,

Da sallama a bakinta ta ɗauki wayar, ita sam bata saba da irin wannan hirarrakin ba da samari tun farko balle yanzu da take zawarci duk dai take jinta wata iri kamar sabuwar Ruhaima bawai waccan Ruhaiman ta asali ba, wani lokacin ma kunya ce ke hanata sukuni bare har ta tsaya ta saurari bazawari sai ta jita duk a takure dan bata saba ba, kai zata ma iya cewa tun tasowarta har tayi aure bata taɓa tsayawa da saurayi ba har shi kansa Imran ɗin basu taɓa tsayawa dashi ba, jin amsar da ta bashi wacce ya jima yana jira daga gareta ai bai san lokacin da yace mata gashi nan zuwa yanzu ba, murmushi kawai tayi ta kashe ranta acikin ranta amma wani irin raɗaɗi da ciwo take ji,tabbas babu abinda yafi mutuwa ciwo kuma a rashin uwa akanyi uwar ɗaki, ko a mafarki bata taba zaton irin wannan lokacin zai risketa ba domin ta gama shirya rayuwarta gaba ɗaya da mijinta amma da yake kana naka Allah na nashi sai gashi rayuwar ta juya mata, haƙura tayi da wannan zancen zucin da take ta tashi ta shiga wanka ta soma shiri, bata yi doguwar kwalliya ba amma dai ta shafa powder da kwalli sai man leɓe, baƙar doguwar riga ta saka ta yafa ƙaramin mayafin rigar akanta bayan ta saka pink ɗin hula mai ƴar tuta wacce aka yi ta kwalliya a jiki, turare ta ɗan feffesa sannan ta fita, kitchen ta wuce ta tsaya tana haɗa masa ɗan kayan motsa baki, fruits ta yanyanka sai drinks masu sanyi ta haɗa ta ɗauka ta fita, hakan yayi daidai da zuwan baƙon, a kunyace ta shigo dashi duk ta gagara sakewa shikuma sai faman kallon ta yake kamar yaga wata sabuwar halitta,

"yanzu dama ranki ya daɗe za a bani wannan damar amma shine aketa faman ja min rai? Yanzu to me kike shirya mana? Ina nufin zuwa nan da yaushe kike ganin yadace a ɗaura aure?" ya tambaya cikin zumuɗi yana kurɓar juice ɗin dake hannunsa,

"wannan kuma ai a hannunka yake Kaine zaka faɗa" ta faɗa cikin kunya kanta yana ƙasa tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta,

"ni ai ko yanzu kika ce nima a shirye nake sai in bada sadaki kawai a É—aura aure..."

Murmushi tayi ta ɗan sake ƙasa da kanta kafin tace "Ahh da wuri haka?"

"to ai ni ba wasa nazo yiba Ruhaima.... Idan har kin amince ko nan da sati biyu sai kawai a É—aura aure"

"to bari dai mu ga abinda hali zai yi, zamu shawarta da manyan mu gani" ita kanta bata san dalilinta na faÉ—ar hakanba,

Gaba É—aya bata sake dashi ba shiyasa hirar sama sama suka yi ya tashi zai tafi dan dama daga office yake kuma office É—in zai koma, bin bayansa tayi domin yi masa rakiya, suna tafe suna É—an sake tattaunawa duk da ita dai babu abinda take cewa sai dai murmushi, shigowar Sameer ce tasa duk hankalinsu ya koma kansa, shima daga nesa yake kallonsu dan lokacin da yaje salla can tsallake sai ya gamu da wani abokinsa wanda suka yi B. U. K tare shine suka jima tare suna hirar yaushe gamo sai yanzu suka rabu bayan sunyi exchanging contact É—in juna,itama Ruhaima da mamaki akan fuskarta take kallonsa tana tambayar kanta wai dama wannan bai tafi ba?,

"shi kuma wancan waye?"

Tambayar da mukhtar yayi mata ta katse mata tunaninta,

"Ƙanin abban Ajmal ne...." ta bashi amsa tana kawar da kallon ta daga kan Sameer wanda ya nufi motarshi rannan a cunkushe,

"ayya Allah sarki.... To yayi bari in wuce" ya faɗa yana ƙwallawa mai gadi kira, nan ya taso a sukwane ya buɗe masa bayan mota ya soma fito da kaya kamar da gangan to masu abu da abunsu duk abinda ke faruwa akan idon Sameer wanda ke zaune yana cikin motarsu yana kallonsu ta mirror, ita dai juyawa tayi ta koma ciki yayin da mai gadi ya rinka shigar mata da kayan wanda duk na ciye ciye ne sai ko na shafe shafe da sabulan wanka, gel, da man wanke gashi da sauran tarkace irin na amfanin mata, akan idon Sameer mukhtar ɗin ya fita saida yaga fitarsa sannan ya fita daga motarsa yashiga ciki wanda rabonshi da shiga har ya manta, yana shiga da kayayyakin yafara arba a falo gasu nan kamar za a kasa a siyar dan yawa duk ledodin da kayan suke ciki suna ɗauke da tambarin store ɗin na su mukhtar, idonsa ne ya kai kan wata leda wadda ta tintsire nan ya hango tissue da pad,

"harda waɗannan abubuwan ya kawo mata? Wannan ai iskanci ne...." ya faɗa acikin zuciyarshi amma har lokacin idanuwanshi na kan ledar, sam bata san shigowarshi ba ta fito da zummar ganin kayan arziƙin da mukhtar ya kawo mata bayan ta tuɓe doguwar rigar da ta saka ta sake saka ƙaramar riga marar nauyi iya gwiwa kanta ko ɗan kwali babu, tana fitowa tayi arangama dashi tsaye ya riƙe ƙugunsa..............

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[18/08, 9:08 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*SO DA ALAƘA......!*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

TAURARI HUÆŠU
Free page

8

***Duk da ta san yaganta dan harma haɗa idanuwa suka yi ƙarewa amma hakan bai hanata komawa ba da baya da baya, cikin bedroom ɗinta ta shiga gabanta yana faɗuwa to shi wannan bawan Allahn me kuma ya sake dawowa yi? Wani dark blue ɗin dogon hijabinta ta ɗauka ta saka sannan ta sake fita, yana nan tsaye inda ta tafi ta barshi yanzun ma fuskarsa babu annuri ko kaɗan,

"waye wancan da ya fita?" taji ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba,

"baƙona ne...." ta bashi amsa acan ciki,

"ehh dama na san baƙonki ne.... Me yazo yi? Sannan wannan kayan kuma na menene?" ya sake tambayarta har lokacin idanuwanshi na kan kayan,

Shuru tayi masa bata amsa ba dan gaba ɗaya tambayoyin nasa sun fara bata haushi da ɓata mata rai, ya za ayi yazo ya wani tisata a gaba da tambaya yana titsiyeta kamar wani wan miji alhalin shi ƙanin miji ne,

"waÉ—annan kayan ki faÉ—a masa ya zo ya kwashe kayansa...."

Juyawa yayi ya fita bai jira amsarta ba kamar ya san dama bata da niyyar bashi amsar, zama tayi tabi bayanshi da kallo har ya fice mintuna kaɗan taji alamar fitar motarshi daga cikin gidan, tuɓe hijabinta tayi a ranta tana tunanin maganar da ya faɗa wai mukhtar yazo ya kwashe kayansa tab ai abinda bama zai taɓa yuyuwa ba kenan, kowacce leda sai da ta buɗe taga abubuwan da ke ciki daga bisani ta shisshigar dasu ciki kowanne ta kaishi inda yadace ta adana.
Chapter 8 · 0% Book details