← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 12

Sashe 3

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ehh ya shigo baba" ta faɗa a taƙaice, juyawa yayi ya fita bayan fitarshi babu jimawa baƙon ya shigo kallo ɗaya tayi masa ta gane cewa daga cikin abokan Imran ne domin ba zai fishi ba ko a haife,da sallama a bakinsa ya shiga suka amsa atare ita da hajiya,

"Ya abunda ya faru kuma? Ubangiji Allah ya bayyana shi, ai Imran mutumina ne sosai akwai kyakkyawar alaƙa tsakanina dashi..."

"Allah sarki, mun gode madalla Allah ya bada lada" hajiya ta faɗa kuma kusan ma da hajiyan suke hira duk da gaba ɗaya hankalinsa yana kan Ruhaima wacce ke can duniyar tunani bata ma san yana yi ba, ita kanta hajiya ta fahimci hankalinsa yana ga Ruhaima amma dai bata nuna komai ba, kudi ya ajiye musu dami guda yayiwa hajiya sallama ya fita yana sake jaddada musu wai idan suna buƙatar wani abu a gaggauta sanar dashi...................... . ✍🏻

*HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡

IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻

HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA,

*1.AYUSHER:-*
Writing by FERTYMERH XARAH

*2.ƘAZAFI NE:-*
Writing by RAHAMA NALELE

*3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-*
Writing by ZAINAB BAWA

*4 SO DA ALAƘA:-*
Writing by UMMI A'ISHA

WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘

Guda 4:- 1500
Guda 3:-1200
Guda 2:- 800
Guda 1:- 400

7033027658
Palmpay Bank
Aisha Muhammad Salis

Katin wayar MTN ta...
07044644433 da shaidar biya

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[13/08, 7:08 am] Baby Aysher: ©️ *H. W.A*

*SO DA ALAƘA!*

*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

*Wattpad:@ummishatu*

Free page

3

~~~Rayuwa na tafiya, lokaci na wucewa, komai yana sauyawa, kullum sababbin al'amura ke sako kai sai dai hakan bai sauya rayuwar Ruhaima daga kan doron da take kai ba, addu'a yinta ake ba dare ba rana haka sadaka da sauran ayyukan alkhairi dan Imran ya bayyana amma Allah bai ƙadarta ba, lissafa adadin kuɗin da suka kashe wurin biyan malamai su yi addu'a ba zai lissafu ba domin malamai sun zo gidan babu adadi wasu ma tun daga uwa duniya, dan bata mantawa waɗannan malaman da suka tafi na ƙarshe tun daga ƙasar Mali suka zo, tayi kuka har ta gaji ta fawwalawa Allah lamarinsa.

BAYAN SHEKARA BAKWAI
***

Rayuwar Ruhaima ta sauya cikin waɗannan shekarun, ada tana cikin arziƙi dumu dumu amma yanzu rayuwar sai dai a lallaɓa domin ita ba aikin gwamnati take yiba, haka kuma bata da wata ƙwaƙƙwarar sana'a da zata taimaka mata ta riƙe kanta da Ajmal wanda yanzu yana buƙatar asakashi a makaranta,

Yau tun da garin Allah ya waye da tunanin neman mafita ta tashi, so take ta saka Ajmal a makaranta dan idan ta kalli yaron ma tausayi yake bata. Suna falo suna karyawa ita da Ajmal ɗin baba maigadi ya shigo yana sanar da ita wai tayi baƙi,cewa tayi su shigo,

Manta inda ta san fuskar mutumin tayi amma dai kamar ta sanshi, murmushi yake yi mata mai ma'anoni daban daban, hijabin jikinta ta gyara ta bar karyawar da take yi ta maida hankali ga mutumin suna gaisawa,

"Sai kuma naji ki shiru... Keda nace miki idan kuna da buƙatar wani abu asanar dani kuma sai inji shuru? Haba Madam.... Baki da buƙatar komai ne? Yau shekara nawa da ɓatan mijinki...."

Murmushin yaƙe tayi dan sam ita bata fahimci abinda yake nufi ba,

"Babu komai mun gode Allah ya saka da alkhairi..."

"Haba madam.... Menene abin godiya? Yaushe zaki cigaba da rayuwa cikin ƙunci da damuwa? Ki ajiye komai a gefe kiyi rayuwarki kiji daɗinki..... Kina da kyau, kin mallaki komai wanda ake buƙata a wurin ƴa mace, idan kika bada dama ba zaki ƙara kukan rashin mijinki ba.... "

Sai lokacinne ta fahimci inda maganar tasa ta dosa, nan take ta É—aure fuska ta kalleshi kamar yadda yake kallonta,

" Wannan ne ya kawoka? To mun gode zaka iya tafiya, sannan bana buƙatar sake ganinka acikin gidana idan kuma ba haka ba wallahi zaka ga abinda zai biyo baya"

Jiki babu ƙwari ya miƙe ya fita yana ƴan kame kame wanda hakan ya sake ɓata mata rai, wani dogon tsaki taja bayan fitarsa hawaye na bin kumatunsa, wai dama haka matan da suka rasa mazajensu ke fuskantar ƙalubale? Dama haka wannan zamanin namu ya lalace da butulci mai cike da tsantsar cin amana? Tashi tayi ta wuce cikin bedroom ɗinta ta kwanta kamar yadda ta saba kukan baƙin ciki a duk lokacin da wani yazo mata da magana makamanciyar wannan,

Kuka tayi wanda ita kanta bata san yawan lokacin da ta kwashe tana yinsa ba daga ƙarshe bacci ya kwasheta bayan ta tashi tayi wanka ta shirya shima Ajmal ta shiryashi ta kama hannunsa suka fita, gidan umaima ta nufa dake unguwar Sulaiman crescent, tana tuƙi tana tunanin rayuwa, a haka har Allah ya kaita gidan lafiya,

Rungume juna suka yi cike da murnar ganin juna,

"inlaw shine baki sanar dani zaki zo ba?" umaima ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukar Ajmal wanda ke sanye cikin jeans da farar t shirt,

"zo nan sweetheart, mommy bata kawoka kunyi wasa dasu Abid ba ko?"

"Na cema mommy zan dawo wurin su Abid"

Murmushi Ruhaima tayi tana sauraronsu, surutun Ajmal yafi gaban haka wannan dalilin ne yasa ta ƙagu ta sakashi a makaranta. Cikin mintuna kaɗan umaima ta cikasu da kayan motsa baki, dambun nama, cake, meat pie da sauran dangin kayan sanyi,da kallo Ruhaima ke bin ko ina na cikin falon saboda yanda gidan ya sake haɗuwa kuma ya ƙawatu da yake mijin umaiman mai kuɗi ne sosai kuma rayuwar tana gara masa daidai gwargwado,sai bayan da umaima ta dawo ta zauna sannan suka gaisa Ruhaima ta kalleta da murmushi tace,

"inlaw wurin mijinki na zo.... Ina son ganinsa kan wata muhimmiyar magana"

Ajiyar zuciya umaima ta sauke kafin ta kalleta tace "Gashi kuma kin daki gurbi.... Ina fata dai lafiya babu wata damuwa?"

"lafiya lau amma zuwa yaushe zai dawo?"

"A gaskiya inlaw zai yi 2 weeks kafin ya dawo dan aiki ya tafi kuma dazun nan yayi tafiyar"

Ɗan dafe goshinta tayi cikin rashin jin dadi da damuwa ƙarara wadda ta bayyana kan fuskarta,

"To shikenan babu matsala, sai ki bani phone no É—insa sai in kirashi kawai"

ÆŠan damm umaima tayi amma sai tayi murmushi tace "ok to ai babu problem bari na saka miki no É—in nasa"

Wayar hannunta ta bata ita kuma ta saka mata sannan ta mika mata ta karɓa tayi saving, sun jima a gidan suna hira Ajmal yana wasa da su Abid waɗanda suka dawo daga makaranta, sai magriba sannan tayi musu sallama suka tafi,

Sai bayan da ta idar da sallar ishah sannan ta samu zarafin kiran Alhaji Sabo wato mijin Umaima kuma abokin hulɗar mijinta Imran, har ta gama ringing ta tsinke bai ɗauka ba, nan ta sake kira amma har tayi ta gama ba a ɗauka ba, yanke shawarar tura masa saƙon karta kwana tayi, nan tayi masa sallama tace itace Ruhaima matar Imran tana son yin magana dashi dazu taje gidanshi bata sameshi ba,

Bai dawo mata da reply ba sai can misalin ƙarfe 10 na dare lokacin har ta gama shirin bacci sai ga kiran sa, kamar ba zata ɗauka ba amma sai wani ɓangare na zuciyarta ya shawarceta da ta ɗauka domin wataƙila da yuyuwar lokacin da ta kirashi har ta tura masa text massage yana can yana ganawa da mutane tunda matarsa tace mata aiki ya tafi,

"Assalamu alaikum....." ta faÉ—a cikin muryarta mai sanyi,

"Wa alaikumussalam..... Hajiya Ruhaima, yagida, ai sai yanzu naga kiranki da saƙonki.... Lokacin da kika kirani na shiga meeting ne wallahi"

"Ayya nima nayi wannan tunanin, dama dazu ma naje gidan sai umaima ke fada min kayi tafiya, kuma gashi ina son Magana da kai"

"To karki damu insha Allah da zarar na dawo zan sanar da ke, babu matsala"

"Ai babu wani abu koma awaya ne zamu iya maganar"

"a'a... Haba haba, ai idan nayi haka to ban mutuntaki ba kuma ban baki darajar da ta kamaceki ba Ruhaima.... Karki damu zamu tattauna face to face idan na dawo"

"to shikenan nagode, Allah ya kaimu, sai da safe" ta faɗa ataƙaice kuma bata jira cewarsa ba ta gintse wayar sannan ta kasheta gaba ɗaya,

Bata sake kiransa ba ko tura masa saƙo har sai bayan sati biyu ya kirata da kanshi yace mata ya dawo gari,

"ok to yaushe zan zo gida na sameka?"

"Ai matsalar bana zama a gida munata ayyuka tunda na dawo sai dai mu haÉ—u wurin aikin....."

Misalin ƙarfe uku na yamma ta kammala shirinta kamar yadda suka alƙawarta da Alhaji Sabo, doguwar riga ta saka ta atamfa purple color ta yafa milk ɗin mayafi kasancewar akwai ɗigon milk a jikin atamfar, bata yi wata doguwar kwalliya ba, iya gazal da lipstick kaɗai ta saka ta fita rataye da handbag ɗinta dama tun kwana biyu da suka wuce Ajmal yana gidan hajiya,

Drop ta ɗauka na napep har inda Alhaji sabo ya kwatanta mata, sauka tayi ta sallami mai napep ɗin sannan tayi knocking a ƙofar guest house ɗin, ɗaya daga cikin masu tsaron gidanne ya leƙo sannan ya buɗe mata,

"Dan Allah nazo ganin Alhaji sabo ne..."

"eh yana nan bari asanar dashi"

Sai da yakirashi a wayarshi ta hannu ya sanar dashi yace ta shiga sannan ya nuna mata hanya, cikin ƙarfin hali da kuma dakiya ta buɗe ta shiga, duk a tunaninta zata ga falon cike da mutane kamar yadda ya sanar da ita amma sai taga sai shi kaɗai sanye da ƙananan kaya,

"Barka da zuwa" yace da ita fuskarsa dauke da fara'a,

"Yawwa barka Alhaji"
Chapter 3 · 0% Book details