← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 12

Sashe 1

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/08, 6:38 pm] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_

*SO DA ALAƘA....!*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad:@ummishatu*

Free page

*1*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI*

~~~Gudu take yi a hankali kaɗan kaɗan tana motsa jikinta cikin salon jan hankali da burgewa, shi ɗinma da yake biye da ita a hankalin yake yin nasa gudun inda yake ƙarewa halittar da ubangiji Allah yayi mata kallo, duk da cewa gudun tsere suke yi amma ya kasa zuwa ya wuceta saboda nishaɗin da yake samun zuciyarsa a ciki duk sa'ilin da yake kallonta,

Sake ƙurawa bayanta ido yayi sanye take cikin ƙananan kaya riga da wando blue black, rigar iyakacinta cibiyarta shi kuma wando a cinyarta ya tsaya sai dai kayan sun kamata matuƙa, shi kuma sanye yake da riga armless da wando boxer dukkaninsu kalar ruwan madara,

Sake rage gudun tayi tana ɗan numfarfashi cikin kissa da jan hankali, dariya yayi ya ƙarawa gudunsa mai yazo ya wuceta hakan da ta gani ya sata rakwarkwaɓe fuska tabi bayansa, kwance ta sameshi saman korayen ciyayin dake shimfide awurin kamar carpet ya wani baje yana shaƙar iska, kansa ta faɗa tana turo baki alamun yin fushi, hannu biyu yasa ya rungumeta yana faɗin,

"what's wrong with my baby?"

"Me yasa yau ka wuce ni?" ta faÉ—a cikin muryarta mai sanyi da rashin hayaniya,

"I told you kinyi ƙiba da yawa tun bayan da kika haifi Ajmal kika buɗe gaki nan daƙyar kike ɗaya ƙafa...."

Duka ta kai masa a ƙirji tana shusshura ƙafa kamar zata yi kuka, hannun ya riƙe bai barta ta dakeshi ba, a madadin hakanma sai ya soma sunbatar hannayen nata da lips ɗinshi masu tsananin taushi,

" Kin san ina son ki.... Babu ruwana da ƙibarki zan cigaba da sonki koda zaki ninka haka ƙiba sau goma..."

Murmushi tayi ta kwantar da kanta saman ƙirjinsa ta sake rungumeshi ƙam,

"thank you darling..... Thank you for making my heart smile and my eyes shine...."

"I love you..." ya faÉ—a yana sunbatar goshinta, mayar masa da martani tayi ta hanyar sunbatar wuyansa,

"Lokacin salla ya kusa, kuma na bar baby na shi kaÉ—ai a bedroom yana bacci may be yanzu ma ya tashi...."

"Za kiyi min wayo dai kawai.... Oya let's go" ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa riƙe da ita,

Maƙale kafaɗa tayi alamar ba zata tafi ba, ya san abinda take nufi shiyasa cikin salon so ya duƙa ta haye bayansa ya nufi ciki da ita bayan ya rufe garden ɗin. Kwantar da kanta tayi tana mai lumshe idanuwanta dan idan da akwai abinda ke sanyata nishadi a duniya bai wuce tajita kwance cikin jikinsa ko gadon bayansa ba. A hankali yake tafiya da ita har cikin bedroom ɗinsu, kan gado ya sauketa idanuwansa na kan ɗan ƙaramin gadon ɗansu Ajmal ɗan kimanin wata biyu wanda ke kwance yana bacci, wurin da yake kwance ya ƙarasa ya sunkuya ya manna masa kiss a kumatunsa sannan ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta,

"Ada kince dake Ajmal yake kama... Yanzu fa?"

"yanzun ma da ni É—in dai yake kamar" ta faÉ—a tana tashi zaune,

"To zo ki gani.... Wallahi yanzu da yake baccin nan dani yake kama, these days ma gaba É—aya kamanninshi sun koma nawa.... Ko jiya abinda hajiya ta faÉ—a kenan"

Tashi tayi taje ta bayanshi ta rungumeshi ta karkatar da kanta ta leƙa dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba,

"Yanzu a hakane zaka ce kuna kama? Dan dai kawai kace hajiya ma ta faÉ—a ne shiyasa ba zan musa ba"

"Kalli idon shi ki kalli nawa...." ya faÉ—a yana juyo da ita gabanshi,

"Na san idon shi irin naka ne..."

"Hancin shi fa?"

"shima irin naka ne"

"Bakinshi fa?"

"irin nawa ne..."

Dariya yayi ya É—agata sama yana faÉ—in,

"kin dai faÉ—i son ranki kawai malama.... Muyi wanka ko tunda gashi can naji ana kiran salla"

Dariyar itama take tana harharba ƙafafu sakamakon cakulkulin da yake yi mata ta hanyar cusa kansa a cikinta. Cike da so da ƙauna suka yi wankan suka fito daidai lokacin Ajmal ya tashi, ɗaukarsa tayi tana daure da towel ta zauna gefen gado dan shayar dashi tana kallon gogan nata wanda yake tsaye gaban mirror yana goge jikinsa da ɗan ƙaramin farin towel body spray kaɗai ya feshe jikinsa dashi kusan kala biyar kasancewarshi ma'abocin ƙamshi daga bisani yawuce closet ya buɗe, juyowa yayi yana kallonta bayan ya riƙe ƙugunsa,ta gane nufinsa so yake ta shirya shi domin da haka ta sabar masa, langaɓar da kai tayi tana kallonsa,

"Ayya daddy kayi haƙuri ka shirya da kanka mana..... Ajmal yunwa yake ji"

Juyawa yayi yana kallon jerin tarin kayansa dake shirye cikin closet É—in, yafi mintuna biyu amma ya kasa ciro wanda zai saka,

"Ciro wannan blue É—in trouser É—in da maroon É—in t shirt pls" ta faÉ—a daga nan inda take zaune, hakan yayi kamar yadda tace sannan yazo gabanta ya shirya,

"zan je salla... Ki shirya kafin na dawo zamu fita dinner....."

"a dawo lafiya"

Kissing ɗin goshinta yayi ya juya ya fita yana balle botiran gaban rigar shi. Da murmushi ta rakashi har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta mayar da hankalinta kan Ajmal, bayan ya ƙoshi ta kwantar dashi ta miƙe, salla tayi bayan ta idar ta wuce gaban mirror ta soma shiryawa simple make up tayi dan iya powder kadai ta shafa sai gazal sannan ta shafa lips glow akan leɓenta, turarenta mai sanyin ƙamshi da daɗi na arabian oad ta shafa, doguwar riga ta saka baƙa ta sake komawa kan abun salla domin gabatar da sallar ishah dama shi kam ta san ba zai dawo yanzu ba har sai yayi sallar ishah kamar yadda ƙa'idarsa take,

Tana zaune kan prayer mat taji motsin shigowarsa, addu'ar da take yi ta shafa tare da miƙewa tsaye hakan yayi daidai da shigowarsa,

"Sannu da zuwa...."

Ta bayanta yayi hugging É—inta sannan ya sumbaci kumatunta kafin ya amsa da "Yawwa Darling"

Ajmal ya ɗauka ya fita tana biye dashi har gaban motarshi, sai da ya buɗe mata ta shiga ta zauna ya miƙa mata Ajmal sannan ya zagaya mazaunin driver ya zauna, a hankali yake tuƙin yana riƙe da hannunta guda ɗaya har suka isa wurin cin abincin, yanzunma shine ya buɗe mata ƙofar motar ta fito ya karɓi Ajmal sannan suka shiga cikin restaurant ɗin, da kanshi yayi musu order ɗin abinda zasu ci bayan sun kammala ya biya suka nufi gida.

Tare suka yi shirin bacci yana maƙale da ita a gefenshi laptop akan cinyarshi yana duba wasu ayyuka da zai yi, juyawa yayi ya kalleta idanuwanta a lumshe kanta bisa kafaɗarshi,

"Darling..... Kinyi bacci ne?"

Kai ta girgiza masa bayan ta buÉ—e manyan fararen idanuwanta,

"kwanakin baya na taɓa faɗa miki akwai wani aikin hanya da zan yi a Niger ko?"

Kai ta sake É—aga masa tana kallonsa,

"yawwa to yanzu maganar aikin ta taso.... Insha Allah zuwa Friday zan je inga ta yadda aikin zai kasance"

Sake ƙanƙameshi tayi ta shige cikin jikinsa,

"Zamu bika"

Dariya taga yayi kafin ya shafi fuskarta,

"Zan so hakan nima"

"Allah yasa kayi aikin ka gama cikin nasara"

"Amin Darling..... Me kike so in siya miki idan na gama wannan aikin"

"Mota" ta faÉ—a tana kissing hannunshi,

"Angama.... Nayi miki alƙawarin sabuwar mota insha Allah idan na dawo..."

"Yehhhh" ta faÉ—a tare da faÉ—awa kanshi gaba É—aya, janye laptop É—in yayi ya tureta can gefe yayi mata masauki a jikinsa sosai yana dariya.

Washe gari kamar yadda ya saba bayan ya gama shiryawa zai tafi office sai da ya fara biyawa ta gidan mahaifiyarshi domin ya gaisheta,

Ƴar kyakkyawar dattijuwar tana zaune saman sallaya da alama sallar walaha ta idar hannunta riƙe da carbi tana ja, har gabanta ya ƙarasa ya zauna yana murmushi,

"Hajiya barka da hutawa"

Murmushin itama take yi tana binsa da kallo,

"Imran..... An fito?"

"Allah ya nufa Hajiya.... Ina kwana?"

"Lafiya lau, ya iyalin, ina Angon nawa da alama rowarsa ake yimin ko?"

Dariya yayi har sai da haƙoransa suka bayyana kumatunsa suka lotsa ciki,

"Haba hajiya ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, idanma cewa kika yi ya dawo nan da zama gaba É—aya to hakan za ayi"

"A'a, har yanzu ku É—inma baku gama É—okinsa ba ai"

Murmushi ya sake yi ya sunkuyar da kanshi ƙasa kafin ya ɗago cike da farin ciki yace "Hajiya albishirinki...."

"Goro fari tas Imrana....."

"Hajiya wannan babbar kwangilar da zanyi ta samu.... Insha Allah zuwa nan da juma'a zan je Niger..... Bayan na kammala aikin zaki sake komawa umarah"

Faɗaɗa fara'arta tayi cikin murna da tsantsar farin ciki tace "Alhamdulillah..... Kai kai kai, Lallai kam dole a koma umarah ayiwa Allah godiya.... Allah yasa ayi lafiya agama da tarin nasarori Imran.... Allah ya sake ɗagaka, ya ƙarawa rayuwarka albarka"

"Amin hajiya... Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana"

Sallama yayi mata ya fita, tun yana hanya yake kiran gimbiyar tasa kamar yadda ya saba, wayar na dab da tsinkewa yaji ta É—aga a kasalance,

"Baccin ne?" Ya tambaya a hankali,

"uhmmmm"

"Ayya sorry na tasheki..."

"Dama ina son jin muryarka ai"

"An fara missing É—inane?"

"Over ma"

"To ko in dawo...?"

"uhmmmm uhmmmm kawai ina missing dinka ne fa"

Murmushi yayi kafin ya bata amsa da "I miss you more.... Ina Ajmal?"

"Yana bayan Dija ta goyashi.... Yana ta bacci"

"Ok, sai na dawo, I love you"

"I love you much more"

Ta faɗa tare da katse wayar, da farin ciki danƙare a zuciyarsa ya ƙarasa office, shi dai haka rayuwarshi take baya taɓa haɗa komai da iyalinsa, wani irin so yake yi musu mai tsanani wanda sam baki ba zai iya faɗarshi ba.

Cikin Æ´an kwanakin ya gama shirye shiryensa na tafiya amma sai ya fara zuwa birnin tarayya Abuja wanda daga can ne zai bi flight,

Yana maƙale da ita ajikinshi ya haɗasu ita da Ajmal ɗin gaba ɗaya ya rungume lokacin da ta iyo masa rakiya domin tafiya,

"Zaka biya ta gidan hajiya ne?"

"No, munyi sallama da ita tun daren jiya lokacin da naje, amma yanzu idan na fita zan kirata awaya"

"To Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya"
Chapter 1 · 0% Book details