Sashe 11
So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata ce masa komai ba ta miƙe ta shiga ciki Ajmal yabita, wanka tayi masa gashi matsalar ko breakfast basu yi ba ga baba saude bata nan ita fa yau abin yayi mata yawa, shirya shi tayi cikin jeans da t shirt duka baƙake ta fesa masa turare kaɗan sannan ta saka masa baƙin combos,
Kamar yadda suka tafi suka barshi haka suka fito suka sameshi sai dai yanzu hankalinsa akan waya yake yana lallatsawa,
"zaku jira in haÉ—a breakfast ne?" ta tambayeshi tana gyarawa Ajmal belt É—in wandonshi,
"no.... Zan kaishi yaci abinci"
"to shikenan..."
Kiss Ajmal yayi mata a kumatu yana haddane dasu amma shi abin mamaki ya bashi ya aka yi yaron yasan kiss? Koda yake ta yuyu itace take yi masa amma duk da haka ya kasa mantawa shiyasa a hanya lokacin da suka tafi sai da ya tambayi yaron wai a ina ya gani,
"mommy ce take yi min" murmushi yayi dama yasan hakan mai yuyuwa ne. Kasancewar shima bai karya ba sai da ya fara biyawa dasu ta restaurant suka ci abinci sannan suka wuce makarantar sa zai saka Ajmal, makaranta ce mai tsada dan ta Æ´aÆ´an masu kuÉ—i ce kuma Æ´an gata dan babu students ma da yawa sosai, registration yayi masa sannan ya biya dukkan abubuwan da suka dace kuma bugu da kari makarantar haÉ—e take da islamiyya dan haka sai 5:30 ake tashi idan yaro ya tafi tun safe,
Koda suka gama gidan hajiya ya wuce da su kai tsaye dan sai gobe zai fara zuwa lokacin komai nasa ya zama ready kama daga kan uniform, school bag, lunch box, sandal da sauransu dan komai a makarantar ake badawa yana cikin kuɗin registration,lokacin da suka isa gidan sun samu umaima tana shirin komawa gidan mijinta bayan hajiya ta jajja masa kunne domin yazo shi dai Sameer har yau ya kasa daina ganin baƙin mutumin nan tun bayan da yaji irin aika aikar da yai niyyar yi Allah ya kare. Bai ce komai ba kawai ya wuce part ɗin shi yaje ya kwanta dan wani mashahurin bacci ke shamayarshi tunda safe amma ya daure bai yi ba wannan dalilin ne ma ya haddasa masa ciwon kai kadan kadan, baccin ya ɗan samu ya rage zuwa yamma lokacin da ya shiga wurin hajiya sai ita kaɗai ya samu da Ajmal domin su umaima sun tafi, abinci ya zubo ya zauna yana sauraren hirar da hajiya keyi masa wacce ta shafi matsalar umaima zuwa can ta ɗan sauya akalar hirar daga wacce take yi masa zuwa wata ta daban,
"wai Sameer har yanzu shiru baka samo budurwar ba?"
Sai da ya lumshe idanuwansa sannan ya buÉ—e kan filet É—in abincin da yake kan cinyarsa yana ci, ita dai hajiya ayita magana É—aya koda yaushe ba canji?
"Sameer baka jina ne?"
"hajiya ina jinki mana...... Ai maganar ce nakan rasa amsar da zan baki wani lokacin"
"ban gane kana rasa amsar da zaka bani ba?"
"to hajiya maganar budurwa yaƙi ƙarewa.... Ni har yanzu Allah bai nuna min wadda tayi min ba"
"kullum haka kake faÉ—a, koda yaushe maganar kenan baka ga wadda tayi maka ba....... Ni ina ganin tunda kai dubawar awurinka ta gagara ni inada idon da zan dubo maka, É—azu hajja Maimuna ta kirani wai Arfat ta samu admission anan BUK, wai zata zauna a hostel nikuma nace a'a ga gida yaushe zata zauna a hostel, kawai tazo nan ta zauna, to ni yanzu wani tunani ne ma yazo min, Sameer tunda ka rasa budurwa ni ina ganin kawai ka nemi Arfat..... "
Tunani yafara yi acikin ransa wacece ma Arfat? Idan bai manta ba tun yarinyar bata san kanta ba rabon da ya sake ɗora idanuwansa akanta, ƴar ƙanwar hajiya ce uwa ɗaya uba ɗaya domin hajja Maimuna itace autar su hajiya, yanzu haka tana can Gombe da yaranta, ji yayi ya tsani Arfat ɗin tun kafin ya ganta, shi kansa bai san me yake damunsa ba a duk lokacin da hajiya tayi yunƙurin haɗashi da wata sai yaji ya tsani yarinyar, ko wani ne ya kawo masa maganar wata haushi abin yake bashi, shi fa baya maraba da irin wannan haɗe haɗen,
"kaji abinda na faÉ—a maka ko?" muryar hajiya ta katse masa tunanin da yake yi,
"eh naji hajiya amma gaskiya wannan maganar a barta"
"koda yaushe abinda kake faÉ—a kenan... Sameer nima fa ina son inga iyalinka, ina son inga Æ´aÆ´anka"
"zaki gani hajiya Insha Allah amma sai lokacin yayi, har yanzu ni banga wacce tayi min ba kinga babu amfanin inyi auren favor daga baya inga irin type ɗina hankalina ya karkata can ta farkon ta rinƙa ganin kamar banyi mata adalci ba..."
"duk mace macece Sameer duk abinda zaka samu a wurin wadda kake kira da type ɗinka itama wannan ɗin zaka samu awurinta, Arfat yarinya ce mai nutsuwa mai hankali mai addini.... Insha Allah zaka ji daɗin zama da ita, sannan idan har nice na haife ka kuma na isa da kai to ita na zaɓa maka a matsayin mata "
" hmmm ji hajiya tana maganar wai duk mata ɗaya suke, wallahi mata suna suka tara especially ma matan yanzu " ya fada a cikin zuciyatarsa, shi dai yau yaga ta kansa wallahi da ya san irin abinda zai biyo baya kenan da baima shigo part ɗin hajiya yanzu ba, yana jinta taci gaba da yi masa ƴar nasiha akan ya sakawa zuciyarsa so da ƙaunar wannan zaɓin da tayi masa Insha Allah ba zai yi nadama ko dana sani ba, ji yayi abincin da yake ci ya fita daga ransa dan haka ya tashi ya fita ya kai abincin kitchen ya koma sashensa dan bashi da wurin zuwa, pretty ya ɗauka dama itace abokiyar wasan shi. Sai da yayi sallar magrib sannan ya tafi mayar da Ajmal gida, abin ya bashi mamaki mutuƙa sannan ya saka shi cikin tunani mai zurfi lokacin da yaga Ruhaima cikin kwalliya sosai a wannan daren,falonta sai ƙamshin turaren wuta yake yi ko ina da komai a gyare, banda gaisuwa babu abinda ya sake shiga tsakaninsu sai dai irin yanda yake kallon falon ta san akwai magana acikin zuciyarsa, miƙewa yayi dan tafiya amma sai ya zuba duka hannuwanshi cikin aljihu ba tare da ya kalleta ba yace,
"kiyi hankali da irin mutanen da kike kawowa gidan nan wai da sunan zawarci..... Sannan ki guji bin mutum da sunan kai ki unguwa"
Da kallo ta bishi ba tace masa komai ba kamar yadda shima bai so tace ɗinba dan yana gama faɗar abinda ke ransa ya juya ya fita, maida hankali tayi kan Ajmal wanda ke bata labarin irin abubuwan da suka faru a makaranta tun daga farko har ƙarshe, taji daɗi sosai dan dama wannan shine burinta taga ya samu ingantaccen ilmi wanda kowa zai yi alfahari dashi kuma zai amfana, kai ai Sameer halinsa sai shi haka kawai ya dage yayi ta kafa mata dokoki da sharuɗɗa kamar wani wanda yake aurenta, harda wani ta kiyayi bin mutane su kaita unguwa, lallai ma, duk waɗannan maganganun tana yin su ne cikin ranta.
Kamar yadda Ajmal ya sanar da ita wai yau zai fara zuwa makaranta tunda tayi sallar asuba bata koma ba, abincin da zai ci da wanda zai tafi makaranta duk ta haɗa tayi masa, 7 saura ta tashe shi tayi masa wanka ta shirya shi cikin kaya personal saboda uniform ɗin sai yau, suna falo yana yin breakfast duk sai murna yake ɗoki ya cika shi suka ji alamun shigowar Sameer, kayan bacci ne ajikinsa blue color daga waje ya tsaya bai shiga ba, tare suka fito da Ajmal ɗin tana riƙe da flask ɗin abincinsa, abun ya bata mamaki duk da ba sabon abu bane ganin tana gaida shi amma bai ko kalleta ba koda yake dama haka ya saba wannan halinshi ne sai dai ta bawa wani labari shan ƙamshi da ciki ciki ajininsa yake,
Sai da taga fitarsu daga gidan sannan ta koma ciki, bacci ta koma, haka ta wuni tana bacci daga ƙarshe ta rasa ma me zata yi gashi sunyi wayar har ta gaji da mukhtar, kallon ma ta kunna duk bai wani yi mata ba, kiran umaima ne ma ya ɗan ɗebe mata kewa dan ta kirata tana sanar da ita ta koma gidanta, sai da suka ɗan taɓa hira sannan take sanar da umaima Ajmal ya fara zuwa school yau, duk gidan babu daɗi yayi mata shuru ta rasa me zata yi dariya umaima tayi tace,
"haka abinfa yake, idan suna nan su dameka bakinka bazai huta ba idan basa nan kuma kaɗaici ya takura maka.... Kawai ki faɗa social media, zaki fi ɗebe kewa yanzun nan lokacin zai ɗan rinƙa tafiya, kije can kiyi ta kallon films da karance karancen novels"
Wannan shawarar tabi ta umaima kuma hakan ya taimaka mata dan tabbas tana cikin nishaɗi, ita social media bata taɓa burgeta ba dan akwai abubuwan da bata ma taɓa amfani dasu ba kuma suna kan wayarta dan ada gani take kamar ɓata lokacine ko kuma rashin aikin yi ne. Sai 6 na yamma Sameer ya dawo da Ajmal yanzun ma bai shigo ba, iya Ajmal ɗinne kaɗai ya shigo da kayansa a hannu kashi kashi dan an bashi komai yau sai murna yake tsabar ɗoki tun a daren ranar ya gwada kayan (uniform) bai bari gari ya waye ba, washe gari kam sai da tayi masa pics kafin Sameer yazo bayan ta shirya shi ya sha uniform ɗin shi wanda ya amshe shi yayi masa masifar kyau, milk color ɗin riga da necktie blue black sai blue black color ɗin wando, kamar jiya yau ma bai shigo ba itama bata fita ba sai iya Ajmal ɗin ta tura masa suka tafi.