← Book details So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

So Da Alaqa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi bai amsa ba, sannan cikin halin ko in kula ya kawar da kai,

"kayi maza ka shirya nace maka kaje, ko baka ji?" hajiya ta fada cikin faÉ—a,

"Naji"

Daga haka ya juya ciki, tsaki ya ja ya wuce gaban mirror ya fesa body spray sannan ya wuce gaban closet dinsa, farar jallabiya kar ya ciro yasaka yana jan tsaki, gefen gadonsa yaje ya É—auki wayar shi da key É—in mota ya fita yana ta faman ciccin magani,

Part É—in hajiya ya shiga, bai bi ta kan yaran dake ta faman guje guje ba a cikin babban falon gidan sannan da alama suma É—in babu wanda ya ankara da shigowar tashi,

Samun hajiya yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman safa da marwa take ta faman yi tana ta kaiwa da kawowa a falonta,

"Hajiya wanne division ne?" ya fada fuska ba fara'a, faɗa masa tayi ya juya ya fita yana ta ɓaɓɓata rai, tafiyar mintuna 30 ce ta kai shi division ɗin,

Lokacin da yaje iya DPO kaɗai da Alhaji sabo ya samu bai ga Ruhaima ba, kamar yadda Alhaji sabo ya tsare dpo ƙarya da gaskiya haka ya tsare Sameer wanda kusan gaba ɗaya ma zancensa ƙarya ne,

Sai da suka yi rubutu kowa yasa hannu daga ƙarshe aka shigo da Ruhaima dan itama ta saka hannu, kawar da kai Sameer yayi lokacin da take shigowa, fuskar ta jajur da idanuwanta saboda taci kuka har ta gaji, ɗankwalinta a hannu sai ko gyalenta dake kanta wanda ta yafa, hannu tasa Sameer yayi sallama dasu ya fita tabi bayansa, handbag ɗinta aka bata da takalminta, a hannu ta riƙe su dan tsabar baƙin ciki ko takalmin bata saka ba, tana biye dashi har gaban motarsa, ko Kallonta baiyi ba ya buɗe ya shiga itama ta shiga ranta a cunkushe kuma a dagule me yafi wannan tozarci da kunya? Ayi mata ƙazafin sata da bin maza? Yanzu ta san bata da wata hanya wacce zata wanke kanta sai abinda hali yayi, amma dai abinda ta yarda dashi shine Allah baya zalunci sannan baya bacci, ta san komai daren daɗewa Allah zai tona asirin alhaji sabo,

Tunda suka fito daga police station ɗin bata yi gigin kallon ko inda yake ba sai yanzu da suka hau titi sannan ta saci kallonsa ta gefen ido, sai da tayi danasanin kallonsa saboda yadda taga ya haɗe girar sama da ƙasa ya cika fam kaɗan yake jira ya fashe,

Tuƙi kawai yake yi gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa akai kamar babu wata halitta acikin motar sai shi ɗaya, ransa a ɓace yake tuƙin cikin tsananin baƙin ciki, kai tsaye gidanta ya wuce da ita, har cikin gidan ya tura hancin motarsa lokacin da mai gadi ya buɗe musu ƙofa, birki yaci da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan har sai da ta buge kanta amma bai ko kalleta ba, buɗe ƙofa tayi ta fita dan jikinta ya bata hakan kawai yake buƙata ahalin yanzu, tafiya kawai take bata ko sake marmarin juyowa ba taji alamun fitowarsa daga cikin motar shima, tana dab da hawa barandar falonta tajiyo amon muryarsa cikin kaushi yake yi mata magana,

"Be kamata ba sannan kuma ba daidai bane ki rinƙa bin mazajen mutane awaje ciki harda mijin ƙawarki, mijin ƙanwar mijinki dan kawai mijinki ya rasu, sannan saboda tsabar rashin tunani da toshewar basira harda sata..... Tirr.... Akwai mata da yawa da suka rasa mazajensu kuma suka daure suka yi hakuri suka kame kansu suka killace mutuncinsu, idan ba zaki iya haƙuri ba ki rungumi azumi a matsayin magani..... " daga haka ya juya ya nufi motarsa cikin tsananin fushi da ɓacin rai, tana tsaye tana kallonsa takalminta da jakarta da ɗankwalinta duk sun zame sun faɗi awurin saboda jinta take kamar ba ita ba, waɗannan baƙaƙen maganganun da Sameer ya faɗa mata su suka fi yi mata ciwo fiye da abinda Alhaji sabo yayi mata, yanzu ta san ba iya Sameer kaɗai ba kusan kowa kallon da zai rinƙa yi mata kenan, jarababbiya marar haƙuri ta kasa jure rashin mijinta tana neman wasu mazan, mai halin ɓera wadda Allah Allah take taga wasarere ta sata, tana nan tsaye kamar an dasata tana zubar da hawaye har motar Sameer ta fita, tafi mintuna 20 tsaye bayan tafiyarsa dan baƙin ciki dan har ƙafafuwanta saida suka yi tsami suka ƙage, daƙyar ta jasu ta shiga ciki sauran kayanta da ta zubar kuwa nan ta barsu ko bi ta kai bata yiba sai maigadi ne ya shigo mata dasu, zaman dirshan tayi a tsakiyar bedroom ɗinta tana kuka wiwi saboda baƙin ciki, daƙyar ta rarrashi zuciyarta bayan taci kuka ta ƙoshi, tana ƙoƙarin yin shirin bacci lokacin misalin ƙarfe 9:30 na dare taji wayar ta dake cikin jaka tana faman neman agaji sakamakon ƙarajinta da ya karade ko ina na cikin dakin.......✍🏻

*HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡

IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻

HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA,

*1.AYUSHER:-*
Writing by FERTYMERH XARAH

*2.ƘAZAFI NE:-*
Writing by RAHAMA NALELE

*3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-*
Writing by ZAINAB BAWA

*4 SO DA ALAƘA:-*
Writing by UMMI A'ISHA

WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘

Guda 4:- 1500
Guda 3:-1200
Guda 2:- 800
Guda 1:- 400

7033027658
Palmpay Bank
Aisha Muhammad Salis
+447894142004

Katin wayar MTN ta...
07044644433 da shaidar biya

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[15/08, 8:58 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*SO DA ALAƘA....!*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad:@Ummishatu*

Free page

5

***Driving yake amma tunaninsa na wani waje, shi gaba ɗaya lamarin mata yanzu tsoro yake bashi ba mamaki ba, banda lalacewar zamani ta yaya mace zata rinƙa ƙasƙantar da kanta tana ajiye darajar da Allah yayi mata tana cire kunyar da aka santa da ita tun tale tale tana kaiwa namiji kanta? Tsaki yaja a karo na ba adadi tun bayan da yabaro gidan Ruhaima, shi dai idan da abinda ya tsana a duniya to zina ce, yaƙi jinin zina sannan ya tsani duk wani mai aikatata amma yanzu yaga kamar tama zama ado dan idan mutum ba yayi wai gani ake bai waye ba, sannan masu yi basa kunyar bayyana kansu ya fahimci hakanne dalilin yawan kawo masa hari da mata keyi shi dai ya rasa wannan masifa ya rasa me suke gani atare dashi da suke yawan kawo masa farmaki, da zancen zucin da yake yi ya shiga unguwar su ransa a cunkushe kuma a ɓace, sallar ishah ya tsaya yayi sannan ya shiga gida, tun a hanya yaketa ganin kiran hajiya amma bai ɗaga ba.

Kamar yadda ya tafi yabarta hankali tashe yanzun ma haka ya sake dawowa ya sameta, duk bata da cikakkiyar nutsuwa, yana shiga ta miƙe daga zaunen da take bayan ta ajiye Ajmal a gefe wanda ada yake kwance a jikinta yana bacci,

"Ina Ruhaiman take? Me ya faru? Me ya hadata da ƴan sanda har ta kaisu ga zuwa police station? Yanzu ya aka ƙare?"

Duk da a cikin fushi yake sai da yayi murmushi jin irin tarin jerin tambayoyin da hajiya ta jero masa lokaci guda kuma ya san kowacce tambaya tana buƙatar amsarta,

" Sameer..... Kabani amsa mana "

" Hajiya ba wata matsala bace babba... Harma ai an kashe case É—in, tana can gidanta na sauketa..."

Daga haka ya wuce kitchen, zama hajiya tayi a ranta tana juya wannan al'amari, kwata kwata Sameer yaƙi wayar mata da kai ya sakata a duhu yaƙi ya bata gamsasshiyar amsar da take buƙata, kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take yi,

" Umaima....."

"Hajiya kinji badaƙalar da Ruhaima tayi ko? Wallahi sai na yi mata rashin mutunci sai na nuna mata true color ɗina.... Ta rasa wa zata bi sai mijina?"

Jin abin da Umaima ke faÉ—i yasa hajiya zaro ido cikin duburburcewa dan sam ma sai ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa,

" wai Umaima me kike faÉ—a hakane.... Meyake faruwa? "

" Hajiya Sameer bai sanar dake abinda yake faruwa ba?? "

" Bai sanar dani komai ba, kin ganshi shigowarshi kenan ya bani amsa a dunƙule yaƙi ya fayyace min komai...."

Daidai lokacin Sameer ɗin ya shigo cikin falon riƙe da filet wanda ya zubo abinci aciki, jin abin da hajiya ke faɗa a waya ya tabbatar masa da Umaima suke waya, ji yayi ransa ya kuma ɓaci, bai zauna ba ya wuce ya fita shi koma maganar fa ya tsana baya son yaji ana sake maimaitata dan hakan sake ƙona ransa yake yi, wannan wacce irin fitina ce ke damun Ruhaima? Koda yake kusan haka yanzu gaba ɗaya zamanin ya koma, wasu matan ma suna da auren amma hakan bai hanasu bibiyar wasu mazan ba a waje, shi kansa ba dan kariyar ubangiji ba matan aure nawa ne suka kawo masa hari? Kasa cin abincin yayi saboda damuwa.
Chapter 5 · 0% Book details