Sashe 6
Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'arar tsayuwar motoci a cikin gidan yasa Momy tashi cike da fara'a kamar bakinta zai tsage tsabar makirci, harda fita k'ofar parlon gidan domin tarbar Salman.
Kande dake lab'e a kitchen tana lek'en Momy ta rake baki tana cewa a fili "keee duniya ina zaki damu?. Yanzu waye zai kalli matar can ya ce bak'ar muguwa ce?".
Ta idasa maganar tana kallon yadda Momy ta tarbi Salman ta rungumesa sai masa sannu da zuwa take, yadda kasan ta goyasa, baka tab'a kallonta lokacin d'aya kace ba d'anta bane.
"Ohhh My Son kasha hanya sannu kaji. Kaje ka watsa ruwa an gyara maka part naka, an had'a maka ruwan wanka ga abinci akan darning table kai kawai yake Jira".
Murmushi Salman yayi yana jin dad'in yadda Momy ke nuna masa so. Ya ce "Momy duk ni d'aya?. Ina Daddy ne?"
Murmushin itama ta sakar masa wadda bai kai zuci ba ta ce "Ohhh Daddynka yana wajan aiki, nasan yanzu haka yana kan hanyar dawowa domin ya san da dawowarka. Danma suna da wani mitin ai da harda shi wajan d'akko ka Airport ma".
Murmushi kawai ya saki yana juyawa ya nufi part nasa. Yana d'okin ganin Daddynsa.
Yana juya baya Momy tabi bayansa da harara. Tana maganar zuci "hmm haka kawai tunda na auri ubanka ko b'atan wata ban tab'a yi ba. Sai kawai na zuba maka ido ka gaje dukiyarsa, baccin kaima ga irin arzik'in da Allah yayi maka, wadda yama so yafi na uban naka. Ina ai bazan tab'a bari kaji dad'in dukiyar bama, bare ka tafiyar da ita yadda ya dace, saina ruguza rayuwarka Salman".
*8:00PM*
Zaune Daddy yake shida Salman suna cin abinci cike da hara da soyayya. Maganar kasuwanci suke da kuma kewar juna da sukai. Sai Momy dake zaune a gefensu tana ta k'ara zubama Salman duk wani abu da yake so tana ta washe baki kamar ta Allah.
Daddy ya kalleta yadda take ta nan nan d'ansa d'aya tilo abin sonsa ya ce "kai Momyn Salman anma manta dani kenan tunda anga Salman ya dawo ko?".
Dariyar yake ta saki tana cewa "yo ba dole ba, d'ana ya dawo ai dole na kasa zaune na kasa tsaye. Sai dai kayi hakuri Daddyn Salman wannan lokacin d'ana ne kawai".
Dariya suka saki a tare kamin Daddy ya aje cokalin dake hannunsa ya d'akko wayarsa yana cewa "abun y'ar hakane?. To shikenan kinci kyauta kawo account number naki yanzu kiji alart ai duk wadda ya kyautata ma Salman dole ne na basa kyauta"
Murtuke fuska Momy tayi tana b'ata rai ta ce "haba Daddyn Salman na d'auka Salman ai d'ana ne wadda nake d'aukarsa kamar ni ce na haifesa. Yanzu idan wani yaji ai sai ya d'auka dama ban isa haihuwarsa ba, ka nuna dama bani ce Mahaifiyarsa ba".
Da sauri Daddy ya ce "Ohh am sorry Momyn Salman ba haka nake nufi ba. Kyauta ce kawai zan baki, kin cancanta ne ba dan wani abu ba. Ni na isa na ce ba kece kika haifi Salman ba?".
Murmushin makirci ta saki tana sake cewa "Ohh yanzu naji bato koda na ce, to mun gode Daddyn Salman"
Dariya suka sake saki a tare Daddy na jin dad'in yadda Momy ke nunama Salman kulawa yana kallonta cike da so.
Bayan sun gama cin abincin kai tsaye part d'insa Salman ya nufa PA dake tsaye tare suka jera da wasu takardu a hannun PA d'in yadda yaga Mai gidan nasa na rik'e kansa yasa PA d'an shakkar rab'ar inda yake. Duk da PA na matuk'ar sonsa amma yana tsoro ciwonsa ya tashi yana kusa, ai kowa na tsoron abunda zai cutar dashi.
Sai dai addu'ar PA bata amso ba. Suna shiga parlon part d'in Salman kawai ba zato ba tsammani Salman ya zube a k'asa ba numfashi.
Wata irin zabura PA yayi yana waro ido waje tsoron tab'asa yake dan indai ciwon zai tashi dama haka yake, sai ya fara fad'uwa k'asa kamar wadda baida rai.
PA na tsaye a mugun tsorace shi bai fita ba shi bai idasa isa inda Salman yake ba.
Baiyi zaton tashinsa a d'an k'ank'anin lokaci ba, amma kawai idonsa ya gane masa Salman ya mik'e tsaye a haukace. Kalar idonsa ta sauya ta koma jawur kamar wuta. Wata irin kururuwa Salman ya saki kamar Zaki. Ya fara yaga suturar dake jikinsa, yana yagar fatar jikinsa kota ina kartar jikinsa yake, wasu irin farata zak'o-zak'o sun fito masa a hannu. Mutuwar tsaye PA yayi ido a waje jikinsa ba abunda yake sai kyarma.
Wani k'aton table dake gaban Salman ya wawuro, bai sauke sa a ko ina sai a akan PA wata irin zabura yayi had'e da sakin k'arar azabar data riskesa ba shiri.
Ai da mugun gudu yayi k'ofa yana fita ya jawo k'ofar ya gark'ame. Wata irin zufa ce ke ketoma PA sai zare ido yake yana dafe da goshinsa inda Salman ya fasa masa.
Da sauri PA yaje ya sanar dasu Daddy hankali a tashe suka nufo part d'in Salman d'in. Sai dai Momy ta rik'e Daddy ta hanasa shiga. Domin yadda suke ji Salman nata fashe-fashen abubuwa had'e da wasu irin surutai marassa kan gadu, kai da kaji yadda yake kasan baya cikin hankalinsa.
Wasu hawaye suka shiga zuboma Daddy na tausayin d'ansa. Ba irin maganin da ba'ai masa ba amma ina shuru kake ji. An d'auka ma ciwon ya tafi saboda yaushe rabon da ace ciwon ya tashi. Gashi idan ya tashi sai yayi kwana biyu yana cikin yanayin hauka tuburan.
Sai dai a kullesa shi d'aya hatta abinci sai dai a warga masa mudun yaga mutum to kuwa duka kawai yake kaiwa......
*Canada Bitor Estate*
Fitowarsa daga wanka kenan sauri-sauri yake ya shirya domin yau ma yana da aiki sosai a studio.
Bayan ya gama shiryawa k'ananun k'aya ne a jikinsa. Yana d'aure takalmin dake k'arfarsa, Amma ta shigo d'akin nasa. D'auke take da k'ofin shayi a hannunta, kallonsa tayi tana cewa "ba dai fita zakai baka ci komai ba?".
Dai-dai ya idasa d'aure igiyar takalminsa ya amshe k'ofin shayin ya kai bakinsa, d'an kurb'a yayi ya sauk'e yana cewa "Amma na makara ne yau wallahi idan na dawo zanci kawai"
Mik'a mata k'ofin shayin yayi wadda ba wani na kirki yasha ba. Yana kai mata kiss a goshi yana ce mata ya tafi.
Addu'a tayi masa tana binsa da murmushi kawai.
Yana cikin tafiya a motarsa kamar ance yabi wani titi ya hangi wasu dondozon y'an iska sunsha askin y'an iska daka kallesu zaka san basa jin magana ko kad'an ko miye zasu iya aikatawa.
Ci gaba yayi da binsu da kallo ata cikin gilashin mota, yana gaf giftasu gaya ashe macece suka tsare sunata ci mata zarafi.
Ai ba shiri Faruk ya taka birki bai san sadda ya fito daga cikin motar ba yana nufar inda suke.
Duk da sanye yake da face mask hakan baisa wasu sun kasa shaida sa ba.
Wani daga cikin y'an iskan ya ce "kai guys wa nake gani kamar Faruk Galadima?"
Gaba d'ayansu suka waiga suna duban inda Faruk Galadima yake.
Budurwar dake sanye da wasu y'an iskan kaya ganin y'an iskan sun kyaleta yasa da sauri zata bar wajan wani ya kamo hannunta yana murzawa da k'arfi. K'ara ta saki tana shirin sakin kuka.
Da sauri Faruk ya k'araso wajan magana d'aya yayi masu suka kyaleta, wani na cewa "ai ranka ya dad'e ka wuce nan wallahi taci albarkacin ka".
"Ko zan iya sanin miye tayi maku?"
Cewar Faruk
"Kawai ka share y'ar wahala ce mutumina bashin Oga ta ci shine ya bamu umarnin mu keta mutumcinta. Amma tunda kayi magana an gama boss taci albarkacinka wallahi. Boss ko zamu iya d'aukar hoto?"
D'an murmushi ya saki yana cewa "zamu iya mana"
Bayan sun d'auki hoto a tare ya basu kud'in da suka ce Budurwar taci bashi. Zai shiga motarsa kenan, Budurwar ta matsu kusa da motar ta rik'e murfin motar tana kallonsa ta ce "nagode sosai d'an uwa"
Miskilin murmushi ya saki yana cewa "ba damuwa ai. Amma ya kamata ki rink'a kama kanki ba kowanne waje mace ya kamata ta rink'a shiga irin wacce kikai ba yanzu, mace tana da daraja ki kiyaye nan gaba"
Amsa mai kawai tayi da kai tana kallonsa har motarsa ta b'ace ma ganinta..........
*SAUYIN YANAYI*
Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
*EPISODE* 5
*Cottage Hospital: Kiri Kasama Road, Hadejia Jigawa State Nigeria*
Ahmed a sukwane ya koma asibitin, yana zuwa ya iske su Hajiya wani doctor ya tara su sun kai su goma yana masu jawabin micece ma Sikilar kanta. Da yawan wa'inda ke wajan duk y'an K'auye ne.
Duk da su Hajiya sunsan wasu abubuwa da doctor d'in yake fad'a amma bayanin da yake ya d'au hankalin mutane da dama. Shima Ahmad samun waje yayi ya zauna yana sauraron abunda doctor d'in ke fad'a, kamar haka.
(CUTAR SIKILA(SICKLE CELL DISEASE )
*"Yakamata* ace kowa yana da ilimi akan wannan cutar...
Mutane sun rabu gida uku(A sauqaqe amma)
*AA* =sune wanda basu da cutar kuma baza su iya yaɗa cutar ba
*AS* =Su ake kira da *Carriers,* ba suda cutar amma idan suka auri masu irin jinin su zasu iya haifar mai cutar
*SS* =Sune masu cutar
Kafin ku shaqu da wani wajen soyayya adalcin da kowa zayyi ma kanshi da yaran da zai haifa shine yasan wanne kalar jini ne dashi ta ɓangaren Genotype yaga ko zasu iya Aure
*AA+AA=* ✓Za su iyah aure
*AA+AS* =✓Za su iya aure
*AA+SS=* ✓Za su iya aure
*AS+AS* =×Ba a son suyi
*AS+SS* =×Ba a son suyi
*SS+SS* =×Ba a son suyi
Ciwon Sikila(Sickle cell disease) Wata cuta ce da ta take shafar sinadarin da yake ɗaukar iskar da ɗan adam yake shaqa lokacin numfashi
*Illolin da masu cutar suke fama dashi*
1-Ciwon gaɓoɓi mai tsanani
2-kamuwa da cututtukan infection Saboda garkuwar jikin su yana da rauni
3-Shanyewar jiki
4-Qonewar jinin jiki
5-mutuwar gaban namiji
6-Rashin girma sosai
Da sauransu