← Book details Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da tsananin tausayin kansu Baba ya ce "ashhsha yanzu muna ji muna gani garin nan zai dawo kamar mak'abarta?".

"Toya zamuyi gara mu matsa mu basu waje, domin tsira da rayuwarmu".

Cewar Balah. Baba ya ce "nidai gaskiya bani da inda zan kai Iyalaina wallahi, addu'a kawai zanyi Allah ya k'aremu gabaki d'aya. Sana yau can wajan gari zamuje mu kwanan?".

Balah ya ce "Baban Nanah yo ni nima ai babu inda zan kai nawa Iyalan. Kwana wajan gari kuma mu maza ai ta kama mu, domin kasan can baya indai suka shigo gari suka taradda namiji a gida kashesa suke nan take, shi yasa gaba d'ayanmu yau ba'a gida zamu kwana ba".

Ibro ma ya ce "Mai gari kuwa shi tuni ya kama gabansa shida Iyalansa an sai masa gida a cikin garin Jibia"

"Yanzu dan Allah miye wannan?, ace Mai gari guda na b'uya shida garinsa an hanasa zama a cikinsa"

Sosai suka tattaunawa kamin suyi sallama Baba bai koma cikin gida ba saida yaba su Balah kud'in harajinsa da y'an Dabar suka sa masu kowa saiya biya...

*Unguwar Dubantu Hadejia, Jigawa State Nigeria*

K'udundune take akan gado zazzafan zazzab'i ya rufeta. K'asusuwan jikinta sai kwankwatsa suke. Sosai take rawar sanyi yadda taji k'afarta na mata ciwo sosai, da cikin k'ashinta tasan ciwonta ne na Sikila zai tashi, hatta cikinta wani irin ciwo yake mata.

Hajiya ce ta shigo d'akin ganin halin da take ciki yasa hankalin Hajiya tashi ba shiri ta rungumo Salma tana cewa "haba Salma mi yasa tun d'azo baki sanar dani ciwon ki zai tashi ba?"

Da kyar Salma ta bud'e baki ta ce "Hajiya nima kawai ji nayi k'afata ta fara ciwo daga nan sai kwankwatsar k'ashi"

"Subhanallahi tashi yanzu nasa a mik'a mu asibiti bari nayi ma Abbanku magana Ahmad ya mik'a mu"

Hajiya na gama maganar ta fice daga d'akin.

Hajiya na fita tsakar gidan ta iske yaran gidan su Maryam tare da uwarsu Hajara duk sun dabaibaye ta tana rabon abincin rana. "Yara kamar wasu mayu". Cewar Hajiya a zuciyarta.

Wani kallon Mmn Maryam ta aikama Hajiya tare da su Maryam suna sakin shewa.
Duk da Hajiya tasan da ita suke hakan baisa yau ta tsaya ta maida martani ba, domin abunda Salma ke fama dashi ma kad'ai ya isheta.

B'angaran Abba ta shiga yana zaune yana jin redion sai Khadija dake zaune kusa dashi tana masa maganar kud'in karatunta, danta kusa komawa school. Hajiya na gani ya fiddo kud'i masu yawan gaske yaba Khadija, ta tashi rafka godiya take, ko kallon Hajiya bata yi ba, bare tasa ran gaida ita.

Hajiya cike da tak'aici ta kalli Abba ta ce "Fisbilillahi Abban yara kana ganin yarinyar nan ta ganni na ganta amma ta wuce bata gaida ni ba, saboda ban isa ba?, dama uwarsu ta gama hure masu kunne akaina yaran Hajara gaba d'aya sun raina ni a cikin gidan nan. Amma ni nawa yaran suna bata girmanta a matsayinta na matar Ubansu"

Abba dake danna y'ar k'aramar wayarsa bayan ya ajiye redion sai kuma ya sake aje wayar itama ya dawo da dubansa wajan Hajiya "Hajiya ya kike so nayi ne wai?, na tabbata akwai abunda ya kawoki, ba wannan ba ina sauraranki"

Wani abu mai d'aci Hajiya ta had'e a mak'oshinta ta cewa a ranta "lallai Rabe wato ma babu abunda zaiyi, yara sun gama rainata suna taya uwarsu kishi, ai ko wallahi zata san matakin da zata d'auka, bazata zauna yara y'an cikinta suna raina ta ba wallahi bac........ Abba ne ya katse ma Hajiya maganar zucin data keyi.

Ta kallesa cike da damuwar rashin lafiyar dake damun Salma ta ce "Abban yara, Salma ce ciwon nan nata ya tashi, shine nake so ka bamu key d'in motarka Ahmed ya mik'a mu asibiti"

"Wato danta ji anyi maganar karatu shine zata wani ce ciwonta na Sikila ya tashi kenan?".

Kallon tak'aici Hajiya tabi Abba dashi kamin ta ce "ban gane miye kake nufi ba?. Ciwon y'arka ya tashi wadda kasan tana d'auke dashi, kuma dama akai-akai yake tashi zaka ce kuma wai danta ji ana maganar karatu zata ce bata da lafiya, kana nufin k'arya take kenan?".

"Ni bance ba, amma ta sani ko mutuwa zatai sai tayi karatu. Domin ita yanzu wannan ciwon da take fama dashi duk wadda zai aureta sai an sanar dashi, ba kowa ne zai iya auranta da ciwon nan ba".

Wani dogon salati Hajiya taja tana kallon Abba. Ita yanzu abunshi ya daina bata mamaki sai dai tsoro. Kwata-kwata an gama dashi duk Y'ay'anta bai damu da damuwarsu ba, sai dai Y'ay'an kishiyata Hajara. Ahhh lallai Hajara ta dace Bokaye, yo idan ba aikin Boka ba ko Mlm tasan haka nan dai kawai Uba ba zai k'i Y'ay'ansa har haka ba.

Shuru kawai Hajiya tayi tama kasa magana kwata-kwata. Ganin haka Abba ya mik'a mata key d'in motar kawai yana niyar tashi ya fice yabar mata d'akin. Da sauri Hajiya ta ce "baka bada kud'in magani, da za'a sai mata ba. Domin duk magungunan da take sha sun k'are gaskiya"

Dubu biyar ya mik'o ya bata. Amsa tayi tana bin kud'in da kallo kamin ta dawo da kallonta garesa ta ce "haba Abban yara, yanzu wa'innan kud'in miye zasu siya a cikin maganganun Salma?. Kasanfa magungunan data ke sha masu d'an tsada ne, saboda lafiyarta fa ake saya, wannan kud'in ai ko ganin likita da siyan kati bazasu isa ba bare ace ajega magani"

"Toni dai iya abunda nake dashi kenan"

"Amma naga kaba Khadija kud'i masu yawa, saboda ita boko zata ko?, ita koma Salma ta mutu kenan kake nufi?".

Ganin tana son sashi b'acin rai yasa ya idasa ficewa daga d'akin ya barta tsaye sake da baki.

Hajiya dake jin wani abo ya tokare mata mak'oshi, kwafa tayi kawai ta fice daga d'akin itama.

Tana shiga b'angaranta ta iske Ahmed rik'e da Salma. Da sauri Ahmed ya amshi key d'in yana kallon yanayin Hajiya fuskarta kamar akwai b'acin rai ya ce "yanzu haka Abba ya b'ata miki rai ko Hajiya?".

"Hmm Ahmad ai kasan duk sadda ciwon nan na Salma zai tashi to irin haka saita faru tsakani na da Mahaifinku".

"Kiyi hakuri Hajiya insha Allahu wata rana komai zai wuce. Nima yanzu nake shigowa na iske Salmar bata jin dad'i shine take gaya min kinje wajan Abba ya bada mota zan kaiku asibiti".

Hijabi Hajiya tasa tana amsar Salma daga hannun Ahmad ta ce "eh muje ko mun samu ganin likitan".

Suna tafiya Ahmad na cewa "insha Allah zamu samu ganinsa ai rana batai ba sosai duka sha d'aya yanzu".

Har suka fita daga gidan mutanan tsakar gidan ba wacce ta d'aga kai ta ce dasu sannu ko ya mai jiki, duk da sun san ciwon Salman ne ya tashi.

Suna tafiya Hajara ta saki wani murmushin mugunta tana cewa "aikin banza kawai, ai ko wannan ciwon ya hana d'iyarki auruwa wallahi, ai indai ina raye Hajiya baki ba jin dad'i ko walwala a cikin gidan nan".

Khadija data fito daga d'aki ta ce "hmm Mama ai kina min dai-dai abunda kike sa Abba yana masu. D'azo fa naje amso kud'in school, ta shigo d'akin karki so ganin yadda ta nuna bak'in cikinta da kud'in da Abba ya bani"

"Tayi ta gama, kad'an ma ta gani. Kuma d'iyarta ita da karatu sai dai idan anayi a lahira zatayi. Amma ni ce nan nasa Mlm ya toshema shegiya kwakwalwa"

Maryam ta zaro ido dake kusa da uwarta, ta dafa Hajara ta ce "kee Mama dama kice silar maida Salma marar k'ok'ari?"

Harara Mama ta banka ma Maryam ta ce "kee kiyaye ni, nasan halinki da shegen surutun tsiya, na sake naji maganar nan a bakin wani to wallahi sai nayi miki abunda baki tunani"

Zaro ido Maryam tayi tana sakin dariya kamin ta ce "haba Mama ya za'ai na tona miki asiri ai kema kin san bazai tab'a yiwuba, kawai abunne yaban mamaki"

Khadija ta kalli Mama ta ce "amma gaskiya Mama kin nakasata da yawa, kuma kin kyauta mana. Da yanzu shegiyar ta fimu komai wallahi dan daga gani ba k'aramar mai basirar karatu za'ai ba can"

Mama ta saki dariya ta ce "yo ai dama sai da Mlm ya ce min haka, ni ko na ce a dod'e kwakwalwata, ta daina gane komai, yo ina zaune zan bari tazo ta kere yarana ku biyu da nake dasu duk duniya ai bazan tab'a bari ba. Ita d'aya da kuke gani zata iya zama wani abu wadda ku kuna ku biyu ko kwatarta baza ku kamo ba, ni kuma ina ji ina gani bazan tab'a bari hakan ta faru ba".

Wani yaro ne yayi sallama yasa su duka suka bisa da kallo jin abunda yaron ya ce ne yasa Mama tashi tana cewa "kai mi naji kace?"

Yaro ya sake cewa "ance wai ana sallama da Salma wani mai mota ne yana waje"

Ai da sauri Mama ta ce ma yaron yaje gata nan zuwa.

Khadija da bakinta ke kyarma wajan magana ta ce "kan uba can. Mai mota ne yazo neman wancan yarinyar mai d'auke da cutar Sikila?"

Tashi Maryam tayi da sauri tana cewa "Mama kinyi shuru?",

"Kin san mi za'ai?, ke Khadija zan baki wani turare ki fesa sa kamin kije wajan wadda yazo neman Salma. Idan kika je ki tabbatar ya shak'i turaran. Sana ki b'ata Salma a wajansa, na tabbata zai dawo wajanki "

Maryam ta tab'e baki cike da jin haushin Khadija ta ce "haba Mama wai komai za'ai sai dai ace Khadija ni kuma fa?".

"Ke kinga ki kwantar da hankalinki kema naki na nan zuwa"

Duk da haka Maryam sai kunbure-kunbure take ta koma ta zauna kamar zata fashe da kuka, taso ace ita ce zataje taga waye ba Khadija ba. Dama ita ba wani samarin arzik'i ne da ita ba, duk na banza ne masu zuwa a soshale, a school d'insu.

Kamin a rufe minti biyar saiga Khadija an fito ance uban gayu ana taku dai-dai. Harara Maryam tabi bayan Khadija dashi, ji take kamar ta fisgota ta dawo da ita.

Khady na fita ta iske matashin saurayi a k'ofar gidansu. Jingine jikin wata mota sai kyalli take.
Chapter 4 · 0% Book details