← Book details Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna dake mata magana tun d'azo, ganinfa kamar bama jinta take ba, yasa Inna mamakin miye Nanah take tunani har haka ne?. Ace duk uwar maganar nan da take bata ma jinta ashe?.

Saida Innar ta dafa kafad'arta, ta d'ago a d'an zabure tana kallon Inna.

Inna tana kallonta, ta nisa ta ce "Nanah lafiyarki kuwa?"

Ai kawai Nanah saita fashe mata da kuka. Tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya.

Hankali a tashe Inna ta ce "Subhanallahi ke Nanah miye hakan kuma?",

"Inna tsoro nake ji wallahi. Inna ina tsoron mutuwa yanzu wallahi, bana son k'ara rasa kowa Inna"

Wani murmushin manya Inna ta saki tana cewa "haba ke kuwa Nanah ai mutuwa dole ce, ga duk mai rai. Ki kwantar da hankalinki insha Allahu sai Kinga y'ay'anki harma da jikoki, kinji bana son ganinki cikin wannan halin kinji?"

Goge hawayenta Inna tayi. Nanah ta sakar mata murmushin yak'i wadda bai kai zuci ba.

Cikin dare Nanah ta kasa runtsawa ko kad'an ga Auta dake kwance a jikinta, sai Inna dake gefensu. Tana baccinta hankalinta kwance.

Murd'awar da cikin Nanah yayi ne tasa ta sauk'e Auta daga jikinta, domin zuwa ban d'aki, haka nan taji wani zawo-zawo ya kamata.
Da sauri ta nufi ban d'aki.

Tayi mamaki ba abunda taci amma cikinta ya b'aci domin zawo tayi mai ruwa ma kuwa.

Bayan ta koma ta kwanta bata fi minti biyar da kwanciya ba, ta sake jin cikinta ya katsa.

Wani d'an tsaki taja tana dafe cikin nata. Fitowarta kenan zata d'auki buta, ba zato ba tsammani kawai taji K'arar halbe-halben Bindigogi kota ina suna tashi a tsakiyar garin nasu.

Cikin Nanah ne ya k'ara hautsinawa, ji tayi tana niyar sakin kashin a wando tsabar tashin hankali.

Zaro ido tayi hankalinta a mugun tashe tama k'asa koda motsawa a inda take. Sai da taji saukar maganar Inna itama hankalinta a tashe tana cewa "keee Nanah kinji abunda naji kuwa?, kodai kunne na ne kawai ke jiyo hayaniyar mutane da halbin Bindigogi?"

Nanah ji tayi kamar bacci take Inna ta farkar da ita. Bakinta na kyarma wajan cewa "mun shiga uku Innna, inama yau muka bar garin nan, na shiga ukuna, bana son mutuwa yanzu, bana son rasa kowa yanzu, wayyo Allah Inna ki taimaka mana, Inna ina zamu gudu?, Inna kina jifa gida-gida suke shiga".

Ai kawai Inna itama saita ji wasu zafafen hawaye na zubo mata. Auta dake gefen Inna ya rungumeta yayi shuru kamar wadda baida baki, shima kansa hankalinsa a tashe yake.

Banko k'ofar gidan da akai ce tasa Nanah da Inna zabura suna curewa waje d'aya. Ba abunda ke fita a bakinsu sai Addu'a, sosai Nanah ta rungume Inna da Auta.

Abunda ya shigo gidan nasu ne ya k'ara hargitse masu kwakwalwa.

Nanah kuwa zawon data ke rik'ewa ne ya samu damar kufce mata a wando. Zubewa kawai sukai a k'asa su duka. Ba abunda jikinsu yake sai rawa.

Ganin wasu Y'an Ta'adda sun kai su biyar fuskokinsu duk a rufe rik'e da wasu Bindigogi wadda tunda aka haifi Nanah bata tab'a ganinsu da idonta ba, kai hatta Inna ma, sai dai su kallesu a cikin Film.

Wata tsawa aka daka masu yasa su Inna runtse idonsu ba shiri suna fashewa da kuka.

"Keee ina mai gidan nan yake?"

Bakin Inna na rawa take cewa "mai gidan nan ya rasu da dad'ewa"

Zagaye gidan suka farayi suna bincika ganin babu wani namiji cikin gidan yasa wani Babba cikin y'an Ta'addar ya ce "kaiii Tajo, ka kashe min matar nan, yarinyar nan kuma ku taho min da ita, da wannan yaron"

Wata irin kururuwa Nanah ta saki tana ihu iya k'arfinta take cewa "na shiga ukuna, na lalace, dan Allah karku kashe min Innata, gara ni ku kashe ni, daku kashe ta, wayyo Allah dan Alla...... Maganar Nanah ta tsaya cakkk sak'on d'aya biyu...... Jin saukar k'arar Bindiga a kunnanta, kamin ta gama tantance waye aka halba, taga Inna ta zube a jikinta babu alamar sauran rai a tare da ita. Domin a saman kanta Tajo ya saita bindiga ya halbeta nan take.

Yadda kasan batun-batumi haka Nanah ta koma. Hatta da d'an yatsan hannunta baya motsi. Tana iya jiyo kukan Auta yana girgiza Gawar Inna dake yashe a k'asa.

Tana dai jin sadda wani ya sab'eta a bayansa, daga nan bata sake sanin mike faruwa ba.

Shima kansa Auta tasa k'eyar yaron sukai suna zaginsa suna turasa da bakin Bindiga.

Auta yana gani aka tasa su gaba aka bar gawar Inna. Auta yana ganin yadda y'an Ta'addar suka kaso mutane da yawa, dake cikin garin naso. Wasu suka d'ora su a Mashina, wasu a mota, wasu ma a k'asa, an d'aure su da igiya, kamar wasu dabbobi, yana gani akasa Nanah kan wani mashin, shima aka jefasa cikin wata bayan mota, suka fara tafiya cikin dokar daji mai duhun gaske, sunyi tafiya harta wuce hankali, tun yana iya gane ina suke har ya rasa ganewa, tun idonsa biyu suke tafiya har wani wahalallan bacci ya d'aukesa............

*SAUYIN YANAYI*

Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*

*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*

*EPISODE* 9-10 END OF FREE PAGES

*MAMA* POV

"Mlm so nake a lalata mata basirar rubuta littafin data fara. Ina so asa mata rashin kwanciyar hankali tare da farkai masu ban tsoro, ta yadda bata da wata natsuwar rubutun bare harta k'irkiri wani labari"

Mlm dake kallonta da jajayen idonsa, ya saki wani murmushi yana cewa "wani hanzari ba gudu ba Hajara"

"Ina jinka Mlm"

"Akwai wata k'awarki Asiya hakane?"

"Kware kuwa Mlm Asiya k'awarta ce Unguwa d'aya ma muka taso da ita ai"

"Yawwa to zata kawo miki ziyara a yau d'in nan. Zata zo da wani fahimmin zance, duk yadda zakiyi kiyi domin aba Asiya aurar Salma. Indai kina son ganin bayan Salma, to ki tabbatar Abbansu Maryam ya amince da abunda Asiya tazo dashi"

"Mlm na kasa fahimtarka fa?"

Murmushin gefen baki ya sake saki kamin ya d'akko wata kwarya cike da ruwa ya nuna cikinta, yana cewa "ki kalla tsakiyar kwaryar nan"
Da sauri Mama ta kai dubanta a cikin kwaryar abunda ta gani ne ya bata mamaki.

Da d'an mamaki take kallon Mlm.
Mlm ya ce "miye kika gani ciki?"

"To Mlm mutum na gani, kwance bashi da lafiya, kamar mai shirin komawa maciji, jifa fatar jikinsa yacce take komawa tana sabulewa kamarta aljanin maciji, masu komawa mutane, irin wadda nake kallo a cikin fina-finan India"

"To kinga wannan mutunin shine za'a aurama Salma shi, zata zauna da mahaukaci har rayuwarta ta lalace, bata tsinana komai a duniya ba, tazo a wahale zata koma a wahale".
Wata shewa Mama ta saki harda su bud'a tsabar dad'i.

Ta k'ara duba cikin kwaryar tana cewa "ai Mlm dole ma Abbansu Maryam ya amince da wannan batu. Abu d'aya zaka min kasa shi ya amince kawai idan na masa zancan, karma yayi min gaddama".

Mlm ya d'akko wani k'ulli ya mik'a ma Mama yana cewa "kinga wannan?, ki tabbatar kin sa masa a abinci yaci, kamin ki kai masa maganar, na tabbatar zai amsa bai shirya ba. Sana ita kuma zamu sa mata rashin natsuwar zuciya bata da lokacin ma rubuta wani littafi"

"Idan kamin haka Mlm ka gama min komai ai"

Mama ta fad'a tana bud'e jakarta ta fiddo da wasu kud'i, tana dank'ama Mlm sai washe baki yake.

*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*

"Hajiya yau ne fa na tura labarina na gasar Hikayata, kimin addu'a"

"D'iyar albarka Allah ya bada sa'a kinji"

"Amin Hajiyata"
Cewar Salma tana kallon Hajiya da murmushi kwance akan fuskarta.

Ahmad ne yayi sallama ya shigo hannunsa rik'e da wata leda.

Zama yayi kan d'aya daga cikin kujerun parlon yana kallon Salma dake mik'a masa gaisuwa, ya amsa yana cewa "Salma kina shan magungunan ki kuwa?"

Murmushi ta saki tana jin dad'in yadda Yayan nata yake bata kulawa sosai. Ta ce "eh man Y Ahmad Ina sha"

"To amma naga kwayar idonki ta canza kala tana son komawa d'orawa?"

"To nima ban sani ba, amma dai duk ina sha akan lokaci yadda ya dace"

"Abinci fa kina kiyaye cinsa?, kin san fa ba kowane abinci ne ya kamata ki rink'a ci ba?"

Hajiya ce tayi gyaran murya tana cewa "Ahmad kenan, kaima kasan ba komai take samu ta ci yadda ya dace ba, kai dai kawai Allah yasa mu dace ya bata lafiya kuma"

Shima ajiyar zuciya ya sauk'e yana mik'a ma Salma ledar hannunsa ya ce "anshi wannan ki samu kici, ki ajema Ismail sauran"
Da murmushi sallama ta amsa tana godiya.

Tashi yayi ya fice daga d'akin.
Bayan fitarsa Salma ta bud'a ledar tana kallon abunda Yayan nata ya sayo mata. Su kankana ne dasu Ayaba, da dai sauransu.
Sosai Hajiya tayi murna dan ya kamata Salmar ta rink'a shan abubuwa irinsu dama.

Sallamar da ake rafkawa a tsakar gidan ce, sawa Maryam fitowa daga d'akinsu.

Ganin k'awar Mama Asiya ce yasa ta cewa "Inna Asiya sannu da zuwa, ai ko yanzu Mamar ta dawo daga unguwa, Allah yasa zaki tadda ita, bari na kira miki ita, tana d'akin Abba"

"Yawwa y'ar albarka kira min ita, akwai magana yau ai",

Bata tsaya jiran jin sauran abunda Asiyar ke cewa ba tayi gaba ta shiga d'akin Abban.

Zaune ta iske Mama sai wani iyaye take ma Abba yana biye mata.

Ganin Maryam ta shigo d'akin yasa Mama dubanta tana jiran jin miya kawota?.

Maryam ta ce "dama Mama Inna Asiya ce tazo ",

"Kai ai ko nasan da zuwanta, bari jeki gani nan zuwa",

Maryam na fita Mama ta dawo da dubanta wajan Abba tana cewa "kaji abunda nake gaya maka ko?, dama na ce ma zata sake dawowa ne, domin tana so ayi abun da wuri"

Abba ya nisa ya ce "kin ce yaron bashi da lafiya zata je kula dashi ne, za'a d'aura auran domin gudun faruwar wani Abu?, to amma a can zatayi karatu ne ko kuwa?",

Kallon takaici Mama ke aikama Abba, yadda yake shirin mata musu, duk da ta basa abinci da abunda Malaminta ya bata, kuma ya ci, dan yana kanci ma.
Chapter 12 · 0% Book details