← Book details Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai da idasa maganar Nanah ko rufe bakinta batai ba suka fara jin k'arar tashin Bindigogi tare da ihun jama'ar gari. Can kuma garin yayi tsin sai k'arar Bindigogin kawai kake ji. Banda kuka ba abunda y'an cikin Inna suke ita da Nanah. Kamin ka ce mi sun dunkule waje d'aya a d'aki, banda zufa babu abunda suke sharcewa.

Da kyar Inna ta samu bakin magana tana cewa "mun shiga uku Mlm fa bai shigo gida ba, shida Auta Innallihi wa'inna alaihir raju'on ke banga ta zama ba".

Ta k'are maganar had'e da k'ok'arin tashi.

Ai da sauri Nanah ta rik'e hannun Inna tana cewa "al'qur'an Inna bazan tab'a bari ki fita ba. Suma zasu nemi wajan b'oya ne"

"Ke wai Nanah mi yasa baki da hankali ne?, Autan ne zaki ce zai iya kare kansa. Yaron da bai kai shekara Sha uku bama, ta sha biyu yake. Kinga ki cika ni na ce ko?".

Duk abunda Inna ke fad'a hakan baisa Nanah sakin hannun tana ba. Suna haka suka ji an banko k'ofar gidan nasu. Su duka zabura sukai suna k'ara k'ank'ame junansu. Zaro ido sukai a tare duk zatonsu ko y'an Bindigar ne suka fad'o masu gida.

Sai dai muryar Auta da Mlm da sukaji ne yasa ba shiri suka Fito suna ware ido waje. Ganin yadda Mlm yake a hargitse ya kusa sa Inna da Nanah dariya amma sai suka maze. Domin Mlm hula daban babbar rigarsa ma daban takalmi kuwa k'ila akan hanya wajan gudu ya watsar da d'aya domin d'aya ne kawai sanye a k'afarsa.

Inna ce tayi saurin jawo Auta tana cewa "Mlm ina kuka tsaya haka?, kaida nasan ba cikin gari kuke kwana ba. Saboda irin haka, kun sanfa mutanan nan ba kyale garin nan zasuyi ba, ni dama nasan sai sun k'ara waiwayarsa. Mi zai sa Mlm bazamu tashi daga garin nan ba?".

Wata zufa Mlm ya sharce yana cewa "Kinga Binta ni banda arzik'in tashi daga garin nan, masu tashi kam sunata tashi, dan yanzu hakama shigowar nan da sukai ashe D'an Liti mai shigo suka zo d'auka, kuma sunyi nasarar d'aukar tasa. Domin yana isowa daga Kano yayo uwar sayayya ta shigonsa suka cafke sa. Sunma kusa halbin K'aninsa Jafaru Allah ne ya tak'aita, wai suke cewa ai ba kisa suka zo yi ba dama d'aukarsa ne kawai aka basu ajandar yi. Da badan haka ba ai sai su iya hallaka garin gaba d'aya kinga yawansu kuwa?".

Ba abunda zuciyar Inna take sai halbawa da k'arfi, cike da tausayawa Inna ta ce "amma Mlm kana gani suna d'auki d'ai-d'ai wata rana fa kar tazo kanmu muma, gara ace muma mu bar garin inaga hakan sai yafi mana kwanciyar hankali"

Zama Mlm yayi akan dankalin dake tsakar gidan yana k'ara cewa "Kinga Binta ba irinmu suke d'auka ba, mi nake dashi da har zasuyi sha'awar d'aukata babu uwar dana tsinana bare na aje wai a sunan dukiya sai wannan gidan. Ai irin su D'an Liti mai shigo sune ake d'auka ba irinmu ba".

Auta dake jikin Inna ya ce "Inna kinga yadda suke halba Bindigogi a bakin k'ofar shagon mutane sai gudu suke?. Kuma suna d'aukarsa suka tafi suka kuma kwashe komai na shagon masu tsadar suka d'iba"

"Kai Auta gidan ubanwa kaji Hakan"
Cewar Nanah dake tsaye.

"Yo ba dole Auta ya baku labarin yadda akai ba, tunda nida shi muna bakin hanyar abun ya faru Allah ne ya tak'aita inaga wa'innan y'an Ta'addar ba masu kashewar bane dan naji ance wai Daba Daba ce dama"

Inna ta nisa ta ce "to Mlm abunda nake gudu karfa wata rana marassa imanin su shigo mana gari, domin kasan basa kallon talaka da mai kud'i kawai jidar jama'a suke suyi cikin daji dasu".

Mlm da bai son maganar ace ya tashi daga garinsa inda yake mutuwar so, yasa yama mik'e ya shige turakarsa.

Ai yana shigewa Auta ya bud'e baki ya ce "Inna inama su sake dawowa, su ce zasu d'auki Baba, ai da, da gudu zaice mu koma birni, ina son mu tashi daga k'auye muma, kamar yadda abokina Ismail suka tashi suka koma katsina".

Da sauri Nanah ta bige bakin Auta tana zare masa ido tana cewa "kai baka da hankali ko?, kake mana irin wannan fatan"

Inna ta kalli Auta tana shafa kansa ta ce "kinga Nanah ba haka ya kamata kina masa fad'a ba, cikin hikima ake gayama yaro baiyi dai-dai ba. Kaga Auta babu kyau abunda ka ce, babu wadda zai so wa'innan mutanan su d'auki nasa, kuma daga yau karna sake jin irin haka ta fito daga bakinka kaji Auta na?".

D'an murmushi Auta ya saki yana d'aga kansa alamar yaji. Hararar Nanah yake yacce ta bige masa baki kuma yaji zafi, itama hararar ta b'alla masa. Tana komawa inda Inna ke daga ta barsa tsabar firgita har turmin ya kusa kifewa k'asa. Dakan Nanah ta ci gaba da yi tana son yin dariya ganin yadda Auta ya wani mak'ale Inna kamar wani mai shan nono................✍️

*SAUYIN YANAYI*

share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*

*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*

*EPISODE* 2

*Villa for sale in Dubai hills Estates*

Tsaye yake manne da waya a kunnansa. Ya juya baya gashin kansa kad'an daya sakko har bayansa ya d'ansa hannunsa yana shafawa.

Ya d'an d'auki lokaci yana wayar kamin ya sauke wayar yana jan lumfashi kad'an.

Turo k'ofar parlon da akai ne yasa shi juyowa gaba d'ayansa.

Jasmin dake tsaye ta zuba masa mayun idonunta ji take kamar ta cinyesa wani irin bala'in kyau taga ya k'ara mata na fitar hankali.

Wani irin miyau ta had'e tana k'ara binsa da kallo kamar idonta zasu fad'o.

Saukar muryarsa taji yana cewa "what look?, that's enough"

Sauke numfashi tayi tana k'ara takowa tsakiyar parlon tana binsa da mayan kallo har yanzu. Cike da yanga da iyayi ta ce "ai ka kai a kalle ka ne My Salman, babu macen da zata kalleka lokaci d'aya ta d'auke idonta daga kanka".

Tab'e bakinsa yayi wadda yake jawur kamar na jariri.Of course, he also knows that he should be looked at, but he is not in front of him. Ko wa'inda ake aura masa bada san ransa ake yin hakan ba, kuma da k'afafunsu suke guduwa saboda lalurar da yake fama da ita wacce take tashi akai-akai.

Muryar Jasmin ta katse masa tunanin daya fad'a.

"Ya kamata Salman izuwa yanzu ka amince dani, ka aure ni wallahi ina bala'in sonka"

Furzar da iska yayi yana bin Jasmin da kallo, kamin lokaci d'aya ya d'auke idonsa daga kanta. Kamar bazai magana ba, dan harta fidda rai da hakan, sai kuma taji muryarsa mai taushi da kaifi yana cewa "Jasmin nasha gaya miki nasha yin aure ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, duk wacce zan aure basa iya zama dani, because I can't curse those who have everything, even I have relieved the responsibility that God has placed on me. Dan haka please Jasmin ki manta da wannan maganar ta aure a tsakaninmu"

"Wallahi ko kashe ni zakai naji zan iya zama da kai nidai kawai ka amince ka aure ni dan Allah".

Kallon Jasmin kawai yake. Tausayi ma take basa wallahi, fad'a kawai take a fatar baki kyan nasa ne kawai yake rud'arta, bawai shi ainafin kansa ba. Shi yasa mata da yawa basa birgesa, da yawansu kud'insa da kyan da Allah yayi masa ne ke sawa su soshi ba wai wani abu ba.

Bai sake magana ba ya fiddo wayarsa ya kira PA d'insa Fahad.

Ba'a jima ba saiga Fahad ya shigo parlon.

Kallon Jasmin Fahad yayi yana watsa mata harara harga Allah shi haushi take basa. Yadda take iya zubar da darajarta ta mace take zuwa wajan Ogansa kullum cikin magiyar ya sota kuma duk a banza tunda yasan ba saurararta zaiyi ba.

Maganar Salman ce ta katse ma Fahad tunanin daya tafi.

"Fahad ka tabbatar komai ya gama kammaluwa na tafiyarmu?".

"Eh ranka ya dad'e k'arfe shidda jirginmu zai tashi"

Yana idasa fad'ar haka Salman ya fice daga parlon bai k'ara kallon koda inda Jasmin take ba.

Jasmin ji tayi kamar zata had'iye zuciya ta mutu tsabar yadda ya y'arfata, duk da ya saba mata hakan amma na yanzu tafi shik'a.

Da kyar ta samu ta fisgo magana daga bakinta ta kalli Fahad cikin jin haushinsa ta ce "ina kuma zaije?".

"Iska na wahalar da mai kayan kara. Kin san dai Mai gida ba mazauni bane, yana harkar kasuwancinsa k'asashe-k'asashe. Kuma koba wannan ba ai yana da dangi a Nigeria, ko baki san haka ba?, to zaije ganin gida ne".

"Hmmm PA kenan ba kaine sa'an yina ba, wadda ya ajeka shine dai-dai ni"

"Duk wannan haukan da kike hakan bazai sa Mai gida ya aureki ba. Saboda kyansa kika gani da dukiyarsa kike rud'e haka, amma ba dan Allah kike duk wannan haukan ba. Kuma na baki shawara Jasmin?. Mai gida koda yana da niyar aure yanzu to bazai tab'a auranki ba, domin baki dace dashi ba. Dube ki, dubi jikinki dubi kayan dake sanye a jikinki kwata-kwata kamar ba d'iyar hausawa ba. Kawai danki girma a ture sai akace ki yada al'adarki?".

Jikin Jasmin tsabar b'acin rai har wani rawa yake so take ta gaggaya ma Fahad magana itama amma wani abu ya tsaya mata a wuya.

Ganin bata da bakin magana yasa Fahad wucewa yana murmushi dan yasan ta shak'a iya shak'a. Ai wallahi baya fatan Mai gidansa ya auri irinsu Jasmin ai sai su lalata masa rayuwa gaba d'aya ma.

*Canada Studio Faruk Galadima*

Zaune yake a studios yana sauraran wak'ar da ya gama rerawa yanzu cikin harshan turanci. Dafasa akai ne yasa shi cire abunda ke manne a kunnansa yana duban Henry daya dafa k'afad'arsa.

Henry ya ce "Ohhh Faruk, you should rest like this and work hard today, I see that your phone is being called and you should check"

Sauk'e goran lumfashi Faruk yayi yana lumshe idonsa yana d'an murza dogon gashin kansa. Wadda daka kalla zaka san irin na Fulanin asali ne.

Muryarsa a gajiye ya mik'e yana cewa "by God, I'm also planning to leave the studio and go home. I know, Amma I'm waiting for me".

"You should do it because today we are working on this song"
Chapter 2 · 0% Book details