← Book details Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce "eh man zasu sata mana, babu abunda zata nema ta rasa. Ai kaga gara ma taje can tayi mai dalili, kai ka huta da kashe kud'inka akanta. Kuma tazo karatun ta kasayi kayi asarar kud'i akanta, tunda kasan ai ba k'ok'ari gareta ba, asarar kud'i kawai zakai, gara can taje tayi karatun acan"

"Kuma fa hakane Hajara. Ai kawai na amince, ko gobe suka zo za'a iya d'aura auran babu wata damuwa"

Wani almurin murmushi ta saki. Tana cewa "yawwa Abbansu Maryam shi yasa fa nake k'ara sonka, akwai saurin fahimtar mutum. Bari naje wajan Asiyar na sanar da ita abunda ake ciki"

Tana gama maganar ta fice daga d'akin.

"Ahh ahh Asiya yada zama waje kuma?, ga d'aki"

Cewar Mama data fito daga d'akin Abba, ta iske Asiya zaune a waje.

Asiya ta ce "wallahi kawai zama nayi nida Maryam muna d'an tab'a fira, ina Khadija ne ni kam?, ban ganta ba"

Mama ta ce "wallahi Khadija sun fita ita da wadda zata aura sunje wata sayayya ne"

"Ahh kai Masha Allah, kice an samo mana siriki kenan?"

"Ai kuwa dai, na nunawa a sa'a kuwa"

"Ayyiririiii, kice mun kusa zuwa aikin hajji?".

Dariya Mama ta saki tana kamo hannun Asiya suka shige d'aki Mama na cewa "ai kuwa dai, gamu can a k'asa mai tsarki"

Zama Asiya tayi tana cire gyalanta ta k'ara natsuwa ta ce "kinga akwai fa magana a bakina sosai",

Dariya Mama ta saki tana cewa "tunkan kizo na riga da na gama da matsalar, domin nasan zancan daya kawo ki"

Cike da d'unbin mamaki Asiya ke duban Mama, ta kasa hakuri ta ce "kamarya ban fahimta ba?"

"Hmmm Asiya kenan, Malami na nasa yayi min duba, har ya sanar dani zuwanki, da abunda zaki zo min dashi, tunkan kizo, na riga da na sanar da Abbansu Maryam, akan wannan zancan, kuma na gama shawo kansa, kawai abunda zance miki shine su turo ayi auran kawai"

Rik'e baki kawai Asiya tayi tana kallon K'awar tata, shaid'aniya uwar shaid'anu. Yo idan ba shaid'aniya ba, waye zai haka?.

Kamo hannunta Mama tayi tana fiskewa ta ce "ke karkiyi wani mamaki fa, kamar kin manta wace ni?".

Ture komai Asiya tayi tana cewa "tunda kin gama da wannan, kema tukaicinki babba ne, idan abun ya kasance"

"Baki da damuwa komai zai kasance yadda muke so".

Dariya suka saki a tare harda tab'a hannu.

*Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria*

Waya ce manne a kunnan Momy suna waya da Asiya.

Daga cikin wayar Asiya ta ce "Hajiya an gama komai fa, yanzu haka wakilanku kawai zaku turo a d'aura auran, ku tafi da amarya"

"Da kyau, haka nake sonji. Zan turo miki naira million biyar, ki d'auki naira million biyu, kiba wacce tayi hanyar abun ya yiwu, naira million d'aya, shi kuma Abban yarinyar ki basa cik'on naira million biyun"

Wata shewa had'e bud'a Asiya ta saki tana cewa "saike Hajiyarmu, uwar gida, a gidan Alhaji Bin Muhammad daga ke ba k'ari, Allah dai ya biya".
Dariya kawai Momy ta saki tana kashe wayar. Ba'a jima ba kuwa saiga message na account number na Asiyar. Nan take ta tura mata kud'in gaba d'aya.

Zaune take a gaban Daddy bayan ta gama koro masa jawabin abunda take so ayi.
"Daddyn Salman, ina ganin yarinyar ita ce ta dace da zama da Salman, domin yarinyar tana da hankali da tunani, zata zauna dashi tsakani da Allah badan komai nasa na duniya ba, domin duk sauran da yake aura duk dan kud'insa ko kyansa ke rud'arsu".

Daddy ya aje wani biro dake hannunsa yana rubutu a wasu takardu ya ce "kina ganin ita yarinyar ba'a danne mata hak'k'inta ba?, kin sanfa yadda rayuwar yaron nan take ciki"

Kamo hannun Daddy Momy tayi cike da kissa ta ce "ba wani danne hak'k'inta da akai. Hasalinma taimakonta akai, saboda ita kanta tasan ko a hanya bata isa ganin Salman ba, yaro mai kud'i ga kyau ga nasaba, komai ya had'a, kawai wannan ciwon ne ke basa matsala a rayuwa, kuma da sannu komai zai shige, idan komai ya wuce ita ce da riba nake gani ai"

Wani murmushin jin dad'i Daddy yayi, yaji dad'in yadda ta fahimtar dashi, kuma ya fahimta sosai. Inda daga k'arshe ya ce "to ita yarinyar y'ar ina ce?, yaushe kuma kike ganin za'aje domin tabbayo auran nata?"

"Y'ar Hadejia ce, kuma tabbayo aure duk bai taso ba, d'aurasa kawai za'ai, domin duk na gama da wannan, yanzu haka Abban yarinyar yasan da maganar, ku kawai yake jira"

"Ai shikenan tunda abu yazo gidan sauk'i. Zanje da kaina tare da wasu manya dana aminta dasu a d'auro auran zuwa gobe insha Allahu".

Cike da farin ciki Momy ta baro part d'in Daddy. Tafe take tana maganar zuci.
"Hmm Alhaji kenan, kaifa gani kake kamar son d'anka nake ko?, ina duk duniya ba abunda na tsana yanzu kamar shegen yaron can naka, amma da sannu zan kawo k'arshensa".

*NANAH* POV

Wani irin sansanin y'an Ta'adda ne su Auta suka tsinci kansu ciki. Auta ba abunda yake sai kuka yanata neman inda zai hangi Nanah.

An zube su wani waje duk ciyayi ga rana ta kwanyare.

Kowa ka gani wajan sab'anin y'an Ta'addar cike suke da tashin hankali.

Kamar ance Auta ya waiga ya hango Nanah dake d'aure a jikin wata bishiya har yanzu a sume take bata farka ba. Gashin kanta ya sakko ya rufe mata fuska.

Da gudu Auta ya nufi inda take, yana aikin kiran sunanta.

Wani d'an Ta'adda ne ya matso ya kwasa masa tsawa, yana cewa "kaiii ina zaka je haka?, koma inda kake kar yanzu na fasa maka kai da wannan Bindigar"

A tsorace ce Auta ya ke duban D'an Ta'addar. Amma duk da haka tsaye yake inda Nanah take ya rik'e tsintsiyar hannunta sai jijjigata yake.

A hankali Nanah ta fara motsa hannun nata, kamin komai nata ya fara dawowa dai-dai, dashi-dashi take ganin mutane, hatta muryar Auta sama-sama take iya jiyota, kamin ta ware idonta akan Auta.

Auta ko jin Nanah na motsa hannunta yasa shi sakin murmushin k'arfin hali yana sake kiran sunanta.

Kallon Auta take kamar wacce ta samu tab'in hankali. Kamin komai a hankali ya fara dawo mata, duk abubuwan da suka wakana a daran jiya.

Tana gama tunanowa ta fashe da wani irin kuka mai k'arfi jikinta na rawa, ta kama leb'en bakinta ta cije tana durzar kuka. Ganin yadda take kuka yasa Auta ma fashewa da kuka.

Wani daga cikin y'an Ta'addar ne ya k'ara matsowa inda suke, bai tsaya wata-wata ba, ya damk'e gashin kan Nanah ya jashi zuwa baya da k'arfi, har saida ta saki wata k'arar azaba. Fuskarta ce ta bayyana.

Hawaye duk sun b'ata mata fuska. Cike da rashin imani yake kallonta ya ce "zakiyi mana shuru a wajan nan, ko sai na kashe wannan bakin naki, maima mutane kukan banza?"

Wani irin bak'in ciki ne ya rufe Nanah, data na dama wallahi saita kashe duk wani d'an Ta'adda dake wajan yanzu, to amma bata da damar hakan.

Sakinta yayi yana maido dubansa inda Auta yake.

Ya wani k'ankance ido ya ce "ni wai miye ma anfanin tahowa da wannan yaron?, ai da an rage masa wahalar duniya, an aikasa can kiyama".

Zare ido Nanah tayi tana jin wani sabon tashin hankali na saukar mata.

Tafiya suka farayi suka bar wajan da Nanah take. Suna magana, ganin haka yasa Auta rungume Nanah dake d'aure kamar wata akuya.

Ba abunda y'an Ta'addar suke sai shan tab'a da giya. Ga y'an matan da suka dad'e da satowa suna faman dafa masu abinci, wasu ma sun maida su k'aruwan k'arfi da yaji, sun maida su kamar wasu matansu.

K'iri-k'iri sai kaga k'aton gardi, daya ji sha'awar mace, zai d'auki mace kamar kayan wanki yayi cikin wata rufma da ita, ya biya ma kansa buk'ata, ya kuma tashi ya zuge wandonsa. Yadda suke afka masu kamar wasu dabbobi.

Yadda Nanah ta lura da yawan matan wajan suna sato sune kawai dan su rink'a masu bauta, da biyan buk'atarsu kawai. Hakan yasa Nanah shiga wani sabon tashin hankali marar musaltuwa.

Motsi kad'an tana nanik'e da Auta, wadda ji take kamar ta mayar dashi ciki.

Wata irin yinwa ta fara addabar wa'inda suka sato, ciki harda Auta, ya fara kuka, yana gaya ma Nanah yinwa yake ji. Dan rabonsa da abinci tun jiya cikin dare gashi har gare ya waye rana na neman fad'uwa.

Wasu hawaye ne suka shiga zuboma Nanah na tausayin Auta, ita dan ita zata iya zama a haka, zata iya jurewa na d'an wani lokaci, kai zama ta iya hakura har zuwa wata safiyar. Shifa?, yaro ne.

Gashi anbi an wani d'aure mata hannu, tana son rarrashin Auta, tama rasa wacce kalma zata fara basa hakuri da ita.

Kukan da Auta yake ne ya fara isar y'an Ta'addar. Hakan yasa wadda Nanah bazata tab'a manta sunansa ba, Mai suna Tajo ya nufo inda suke.

Duk duniya idan akwai wadda ta tsana to bazai wace wannan Tajo ba, shine ya rabata da farin cikin rayuwarta, wato Innarta, shine ya ruguza masu rayuwa, shine ya rabasu da jigwan rayuwarsu. Da tana da dama saita kashe Tajo kamar yadda ya kashe Inna.

Da jajayen idonsa yake kallon su Nanah, ganin irin kallon da Nanah ke aika masa dashi, na tsananin tsana da fusata, yasa Tajo shekewa da wata dariya yana nuna Nanah da hannunsa.

Can ya tsagaita dariyar yana kallon Nanah da ba alamar tsoro yanzu a cikin idonta. Ya ce "keee uban mi yaron nan yake so ya ishemu da kuka?".

Shuru tayi bata da niyar magana ga Auta daya k'ara balun d'in kukansa.

Haushi abun ya bama Tajo, hakan yasa ya d'auke Nanah da wani gigitaccan mari. Wadda yasa taga giftawar wasu taurari. Duk da haka taji zafin marin daya kai mata, amma tayi shuru tana kallonsa da jajeyen idonta da suka kad'a sukai jawur.

Ganin fa bazata tanka masa ba, yasa Tajo jawo Auta ya daka masa tsawa yana cewa "kaii kayi ma mutane shuru ko yanzu nasa wuk'a na yanka maka wuya wallahi"

Auta bai daina kuka ba, majina da hawaye duk sun b'ata masa fuska.
Chapter 13 · 0% Book details