← Book details Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Sauyin Yanayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin wata sab'anin Salma yasa ya d'anbi Khady da kallon mamaki. Tana idasa k'arasowa inda yake yaji wani k'amshin turare kamar na bori yayi masa sallama a k'ofofin hancinsa. Kansa yaji ya fara juya masa, da k'arfe ya runtse idonsa. Sak'on d'aya biyu.......

Ya bud'e su akan Khady sai ya samu kansa da sakar mata murmushi. Wani irin dad'i Khady taji ganin tarkonsu ya kama.

Sallama tamai cike da iyayi da jan hankali. Saurayin a zuciyarsa yake cewa "kai wannan fa tayi Alaji ko ita na samu ai nayi sa'a"

Bayan sun gaisa Khady cike da makirci ta ce "hmm naji ance wai Salma kake nema ko?"

"Wacce Salma kuma?, ai ni ke na ce a kira ba wai wata Salma ba",

Dariya Khady ta saki tana sake cewa "uhum kad'ai fad'i gaskiya, ai na d'auka Salmar kake son gani na ce baka da labarin bata da tarbiyya ko kad'an duk gidanmu itace zakka, gata d'auke da ciwon Sikila ba wadda ya tab'a zuwa da sunan yana sonta".

Tab'e baki yayi kamin ya ce "mubar maganar wata Salma, baga ki yanzu ba kin maye gurbin duk wata mace a waje na yanzu. Ni sunana Jafar kefa?"

"Ni kuma Khadija"

"Wow so nice name"

Sun dad'e suna fira. Zasuyi sallama ya bata wata leda daya ciko da kayan ciye-ciye da dai sauran su. Hannun Khadija har kyarma yake wajan amsa tana rafka masa godiya.

Sai da tasa masa number wayarta shima ya amshi tata. Kamin ya shige cikin motar ya tayar yayi gaba.

Juyowar da zatai ta koma cikin gida ta hangi Ahmad dayayi parking motar Abba yazo d'aukar katin Salma na asibiti da suka manta a gida. Ya baro su Salma na jiran ganin likita.

K'arasowa yayi inda Khadija take yana cewa "keee dan Ubanki ba Abba ya hanaku zance ba?, har sai kun gama karatu koba haka ya ce ba?".

Yadda ya daka mata tsawa yasa Khadija zabura tayi cikin gida da gudu.

Bin bayanta yayi shima yana shiga cikin gidan.

Ganin yadda Khadija ta shigo a hargitse yasa Mama tashi ta jawota tana tabbayar "ke lafiya?"

Wani kukan makirci Khadija ta saki tana nuna k'ofar gida tana cewa "Mama ba Ahmed bane daga ya ganni ina zance shine yazo a gaban saurayina ya mare ni, wai ba Abba ya hanamu zance ba"

Wata uwar ashar Mama ta dark'ara, dai-dai shigowar Ahmed cikin gidan kuma a kunnansa duk yaji abunda Khadija ta fad'a.

Nunasa Mama tayi da yatsa tana cewa "kaiiii Ahmad ka fita ido na rufe bana son hassada da bak'in ciki, yo idan ba bak'in ciki kake data samu mai abun hannu ba uban mi kake mata?, saboda ba'a ce K'anwarka bace wacce kuke uwa d'aya, y'an ubanci zaka fara nunama Y'ay'ana. Shine zaka disgata a gaban saurayi saboda baka da kunya?".

"Amma Mama kin sanfa Abba ya ce baya son ganinsu da samari tun.......... "Kai dakata na ce, ina ruwanka da rayuwar y'ay'ana K'anwarka ce wacce kuke uwa d'aya ita ce kake da ikon mata haka, amma banda su Khadija babu ruwanka dasu nama gaya maka. Idan kunne yaji gangar jiki ya tsira"

Zai sake magana saiga Abba ya shigo gidan. Ai ganin haka yasa Khadija k'ara b'are baki tana sakin kuka.

Hajara ma saita kama matse hawaye tana kama bakin zaninta tana fyace majina, alamar tasha kuka ta gaji.

Ahmad yana tsaye yana kallon ikon Allah, had'e da kallon makirci tsantsarsa wajan uwa da y'ay'anta.

Abba a d'an rud'e yake binsu da kallo kamin ya ce "mike faruwa ne?"

Khadija saita k'ara b'are baki tana cewa "yo Abba ba Ahmed bane daga na fita waje wani d'an ajinmu ya kawo min wani book nawa dana ara masa na makaranta, shine kawai ya kamani da duka wai zance nake, wai ka hanamu zance, kuma ni ba zance nake ba d'an ajinmu ne fa".

Ta k'are maganar tana matse hawaye.

Hajara ta amshe da cewa "kuma dan rashin kunya ina masa maganar miye tayi masa shine kawai ya kaima Khadija mari nima yana neman kai min marin, tunda dama ba kunya ce dashi ba".

Zaro ido Ahmad yayi kawai ya kama girgiza ma Abba kai, dake mai wani kallo na b'acin rai. Kai dama haka mata suke wasu?, haka suka iya kulla makirci, shi yanzu ko rantsuwa nawa zaiyi ma Abba to wallahi yasan bai isa ya iya kare kansa ba..... Tunaninsa ne ya katse jin saukar mari har biyu akan kumatunsa. Zaro ido yayi da mugun sauri ya dafe kumatun nasa. Yana kallon Abba daya sharara masa mari har biyu.

Cike da masifa Abba ke nuna Ahmed da yatsa yana cewa "wato uwarka ce ta turoka kayi ma mutane rashin kunya ko?, saboda kawai naki bata kud'in maganin Salma yadda zasu isa, shine kai kazo rasa kunya b'eran tanka, ka rama mata ko?. Ai ba'a kan Hajara da yaranta zaka sauk'e fushinka ba, gani ni ya kamata ka duka basu ba".

"A'a wallahi Abba ni Hajiya bata sanar dani komai ba, Allah ya baka hakuri".

"Idan nak'i hakurin fa?, bani key d'in motata"

"Abba suna asibiti fa suna jirana, kati nazo d'auka fa"

"Babu ruwa da inda kaje ka ajiye su, ka taro napep ku dawo kaja masu, bani key d'in motata kawai na ce"

Idon Ahmed jawur jijiyoyin kansa sun tashi tsabar b'acin rai, kawai ya mik'a ma Abba key d'in motar. Abba yasa hannu ya fisgesa da k'arfi ya juya ya fice daga gidan.

Yana fita Ahmed yabi su Khadija da kallo yadda suke sakin murmushin jin dad'i. Kwafa kawai yayi yana shigewa b'angaransu. Yana jin yadda Hajara ke sakin shewa da dariya tare dasu Maryam.........

*SAUYIN YANAYI*

Share Fisbilillahi
*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*

*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*

*EPISODE* 4

*Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja Nigeria*

A hankali yake sakkowa daga matakalar jirgi. Gilas ne manne a idonsa, wata irin iska ya shik'a ta k'asarsa Nigeria, wata irin nutsuwa na saukar masa a zuciya.

PA dake janye da akwatunan su na kaya. Wasu jifga-jifga motoci ne suka zo d'aukar Salman sun kai su biyar a jere.

Gaba d'aya Airport d'in kallo ne ya dawo garesa. Mata y'an gayu wa'inda suke ji da kyau da kud'i ko wacce na binsa da kallo kamar idonsu zasu fad'u, ko wacce mace dake wajan ji take inama ita ce matar bawan Allahn nan.

Yazo giftawa ya shiga motarsa PA daya bud'e masa gidan baya na tsaye yana jiran k'arasowarsa. Yaji wasu y'an mata na rad'a a hankali suna cewa "kaii K'awata kinga wani gaye?, wow wayyo Allah na, wannan ka same sa gidan duniya ai ka gama samun komai"
D'ayar dake kusa da wacce tayi maganar ta harareta tana cewa itama "to nan da kike ganinsa ba wani cikakken mai hankali bane, idan ciwonsa ya tashi cewa akai ko waye a kusa dashi mugun duka yake sha, da kyar ake kwace mutum a hannunsa. Sana auransa ya kai uku ko wacce bata iya zama dashi saboda baya iya tsinanama mace komai, nan da kike ganinsa bai cika namiji ba da'aAllah".

Wani abu mai d'aci ne ya tukare ma Salman wuya idonsa ya kad'a yayi jawur danma a cikin gilas ne baka tab'a ganewa. Shi kad'ai yaji miye y'an matan ke cewa. Saboda Allah yayosa da mugun sauri jin magana, koda rad'a kuke zaiyi wuya baiji miye kuka cewa ba, indai tazarar ba wata bace. To yanzu ma a d'an kusa suke dashi koma a hakan wai rad'a suke suna galmarsa.

Shigewa kawai motar yayi PA dake tsaye ya maida murfin motar ya rufe. Yana tunanin mike damun Mai gidansa?. Da alama ciwonsa kwanakin nan na gaf da tashi dama a Nigeria indai zai zo to kuwa sai ciwon ya tashi.

*Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria*

"Kande ki tabbatar kin jera komai yadda ya kamata"

Kande dake wajan darning table ta d'an tab'e baki tana maganar zuci "kaji makirar mata, a waje ta Allah a zuci shaid'aniya. Yanzu Fisbilillahi duk wannan rawar kan da take akan Salman zai dawo da za'a bata wuk'a a b'oye zata iya hallaka bawan Allah ko?".

"Keee Kande ubanmi kike tunani ina miki magana?, kin mayar dani y'ar iska"

A tsorace Kande ta kai dubanta wajan Momy dake jefo mata kallon wulakanci bakinta na kyarma ta ce "kiyi hakuri Hajiya wallahi banji bane. An gama jera komai ai"

Tsaki kawai Momy tayi tana zama d'aya daga cikin kujerun parlon tana d'aukar wayarta. Wata number ta kira bugu d'aya aka d'auka.

"Kinga Asiya abunda kike so fa bai zai tab'a yiwuba"

Daga cikin wayar aka ce "haba Hajiya kinsan fa yarinyata Sakina tana mutuwar son Salman, mi yasa zaki ce bazai yuwu ba?. Bayan nasan komai na gidan Alhaji Bin Muhammad na k'ark'ashin ikonki ne"

D'an sauk'e lumfashi Hajiya tayi kamin ta ce "bana son rayuwar d'iyarki ta salwanta ne, bana so ta zama k'aramar bazawara ne, domin bazata iya zama da nakashashshan yaron nan Salman ba, abunda nake so dake shine Asiya ina so a samomin yarinya wacce iyayenta suke da son kud'in tsiya wacce a gidansu anfi tsanarta wacce bata da gata gaba da baya, irinta nake son k'ara aura masa, wacce zatayi sanadiyar nakasa masa rayuwa. Boka ya ce min dole a samo yarinya wacce bata da galihu shine kad'ai zai iya zama da ita wacce koya bigeta tasha wuya babu inda zata iya guduwa dole dai ta zauna dashi. Danni burina kawai ace yau Salman ya kashe matarsa dole yaje gidan yari, duk wa'inda yake aure ba sonsu nakeyi ba, saboda suna da galihu Y'ay'an masu hannu da shuni ne. Kuma dama suma ba dan Allah suke sonsa ba, dan kyansa ne da dukiyarsa ke rud'arsu. Dasun zo kuma sunga ya yake sai su gujesa".

Sauk'e goran lumfashi Asiya tayi dake cikin wayar kamin ta nisa ta ce "tabbas na gane ina kika dosa Hajiya, na gane nufinki kin iya taku gaskiya, komai a hankali kike binsa a sannu-sannu ta yadda wani mutum bazai tab'a gane ke muguwa bace, dole sai idan kice kikai niyar ya sani. Lallai na jinjina miki kuma insha Allahu a nan Hadejia zan bincika miki yarinyar data dace".

Murmushi kawai Momy ta saki tana sauk'e wayar bayan sunyi sallama.
Chapter 5 · 0% Book details