← Book details Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Jamilu ne yace. "Eh Baba ɗazun da safe aka sallamaimu, daman kai muke jira kafin mu tafi, mungode Allah ya saka da alkhairy Baba" haka suka fito suna kara tautaunawa akan matsalar Mama, da yanda yazasu shawo kan matsalar ba tare da wani yaji ba har azo daga baya ana yi mana dariya, tunda ba wanda yasan nayi ciki sai yan'uwana sai kuma Alhaji Salahu da Mama taje ta gaya mashi, bayan sun dawo muka hada kayanmu sannan muka taho gida.

Koda muka koma gida kallon banza Mama tayi mana ta watsar, kallon da naga Mama tayi mana shi yasa jikina ya mutu take naji ban da lafiya dan ina tsoron abunda zatayi man, tunda ni daya za'a bari gidan nida ita zaunawa mukayi muka gaidata amman abun mamaki maimakon ta ansa gaisuwar sai ma ce masu tayi. "Wato ni zaku kai ƙara wajen Ali ko? Kunsa Ali ya isa yasani balle ya hanani? Kin nuna man ban isa da Khadija bako? Da har zaku kai ƙarata wajenshi dan nace zanyi ma Khadija... Katse ta Yaya Amina tayi tana cewa. "Mun isa mu kaiki ƙara wajen Baba wallahi Mama mudai ce mashi Khadija bata lafiya kema baki lafiya shine yace bari ya fara zuwa ganinki sannan yaje ya ga Khadija bamu ce mashi komai ba bayan nan ko Yaya Fatima."!? Cikin tsoro ta ida maganar tana kallon Yaya Fatima, take nasan ba lafiya mai Mama zatayi man wanda yasan yan'uwa suka kaita ƙara wajen Baba Ali, nidai kallonsu nike da tambaya a bakina dan inason nasan abunda Mama zatayi man wanda su Yaya basu son nasani, ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Auta tashi ki shiga ɗakinki ki huta dan naga kamar bacci kike ji, ke kuma Aisha shiga kitchen ki dafa mata ruwan sanyi wanda zata dan gasa jikinta mana." naso nayi gardama amman bani iya yi ma Yaya Jamilu gardama dama Yaya Aisha ce da sai nayi tunda nike bi mata daga ita sai ni, tashi nayi na shiga room din na, ina kallon sanda Yaya Amina ta leko taga mai nike sai akayi sa'a kwance ta tadda ni bisa gado na lumshe ido, ni kuma ina ganin haka nasan magana ta zasuyi amman basu sun naji, tasowa nayi na laɓe jikin kofa yanda zanji komai zasu ce.

Ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Mama dan Allah muna ƙara baki hakuri akan abunda Auta ta aikata insha Allah ba zata kuma ba, sannan kuma dan Allah karki aura mata Alhaji Salahu ki bata dama ta fiddo wanda take so sai a daura mata, amman aurar da ita ga Salahu da kike niyar yi shine barazanar lalacewar Auta Mama." ji nayi hawaye sun zuboman wai ni za'a daura ma wannan tsohon mutumin wanda ko gaidashi baniyi a unguwa tunda na lura da yanda yake kallona idan na fito zani islamiya ko kuma boko, ina cikin yin hawaye na naji Mama tace. "Duk ki tashi ku bani waje wanda basu da hankali sannan kuma sani wallahi sai na aura mata shi nan da kwana goma dan haka ku fita ku bar man gida kafin raina ya ɓaci." tashi naga sunyi nayi sauri komawa bisa gadona na share hawaye dan ban san na nuna masu naji abunda suke cewa haka suka shigo suka kara dubani suka ce na ringa tsarki da ruwan zafi ina gasa jikina dan naji kwari sannan suka tafi gida, ai suna fita naji tashin motocinsu na tashe da kuka mai cin rai, aiko Mama ta shigo ta fara yi man fada akan nayi shiru na tashi na shiga wanka yau bako zanyi.

Ba yanda zanyi haka nayi duk abunda Mama tace harda bani kayan kwaliya nayi , haka yazo ya gama yi man surutanshi ya tafi, ni kuma na fara shirya kayana cikin wata yar'karamar jikka ina jiran dare yayi na tafi na barma Mama gidan tayi yanda zatayi da shi, idan taga ban nan ai sai ta samu wanda zata aura ma tsoho haka na kama hidimata kamar ba abunda ke damuna ana kiran mangariba Mama ta shiga daki danyi sallah ni kuma na dauki jikka da wayata da komai nawa harda sarƙar zinarina guda biyu wanda Mama da Yaya Jamilu suka saya man sai kudi masu dan yawa na fitowata, ina fitowa naga mai naped nace ya kaini tasar jibia.

👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂

*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*

*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*

*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*

*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍

*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*

Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD

*Wannan page din nakine Phatermarh kankia Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Deey musy, my Dejja, ki sani nayi missing dinki sosai da sosai Allah ya maido man dake duniya social media lafiya sannan ya baki sa'ar karatun da kikeyi, ina maki fatan alkhairy ta wajena*

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14

Tunda suka shigo gida suka tadda Mama zaune tayi tagumi ga dukan alamu abun duniya duk ya bi ya isheta, da sauri Yaya Jamilu ya ida isa wajen Mama yana cire mata tagumi da tayi ɗaura kanshi yayi bisa cinyarta yana mata alamun lailashi, suma samun waje sukayi suka zauna duk sunyi shiru sun rasa abunda zakuce ma Mama, Yaya Fatima tayi karfin halin cewa. " Mama kin san dai mutum baya cika cikaken musulmi har sai yayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, itace ake kira da jarabawar rayuwa, Mama Allah kaɗai yasan irin kaddarar da Auta ta zano a rayuwarta kuma ba wanda ya isa ya wannan kaddarar, to mu mai zamuyi ma Auta Mama? Auta a halin yanzun tana bukatar Addu'armu muyi mata fatan faɗawa a hannun na gari." shiru tayi tana sauke numfashi dan halin da ta tadda Mama ta bata tausayi sosai kuma tabbas Mama tana son kula da ban magana mai dadi wanda zai sa hankalinta ya dan kwanta koda ba duka ba.

Kama hannunta Yaya Aisha tayi tana murzawa sannan tace. "Mama dan Allah ki yafe mana sannan ki yafe ma Auta, dan Auta ko tayi kuskure babba da tasa ƙafa ta gudu ta barmu ba tare da tayi wani tunani ba, kuma insha Allah zamu sa a nemo mana ita duk ind... "Aisha na yafe maku itama Khadija na yafe mata, amman ku sani ba wanda zaisa aje neman Khadija tunda ba wanda ya fidda sannan kuma ba'a aiketa ba, tabbas ba zanyi ma Khadija baki ba a halin sa take ciki sai dai nace Allah ya bata sa'a akan abunda tasa gaba nike na fita haƙinta a matsayin ta na marainiyar Allah ni kuma a matsayina na mahaifiyar ta mai son ganin farin cikinta, kuma da ta sani bata gudu ba da yau sai tayi dariya amman yanzun tunda har ta gudu ba baki ba watarana kuka zatayi da idanunta tana da nasani marar iyaka sai dai bani fatan Allah ya barni da rai na har wanann rana tazo, inalillahi wa'inna'alaihijirun Allah kana ganin halin da yarinyar ta samu ciki, ya Allah ka kareta daga sherin duk mai sheri, Allah karka ba wani damar kama ma ɗiya hannu da sunan yin fasiƙanci da ita koda kuwa ita ta kaimai kanta da kanta, ya Allah ka duba rayuwar marainiyarka wanda bata da uba sai uwa da yan'uwanta, Allah.... Kuka Mama ta fashe dashi kuka mai ciwo da ɗaci dan ita kaɗa tasan abunda takeji a zuciyarta.

Yaya Amina ce tayi karfin halin cewa. "Dan girman Allah kuyi hakuri addu'a dai zamu cigaba da yi kuma Mama kinsan jinin ya hau fa inji likita ya dace sausauta wannan damuwar, sannan Mama kika ce da yau zatayi dariya, wace dariya zatayi ko kin fasa aura mata Alhaji ne."? Girgiza kai Mama tayi sannan tace."Aa Amina ina bakata nayi mata aure, bayan Alhaji yazo zun gaisa da Auta sai na tafi nayi mashi rakiya zai koma gida, dan ita Auta suna gama magana ta tashi ta shiga ɗakinta, bayan mun gama ya tafi sai Aminu saurayin Auta yazo ya gaidani yace man ya shigo gari sannan yana ta kiran wayar Khadija a rufe shine yazo Allah yasa lafiya? Nan nace mashi yayi hakuri aure za'ayi mata take ya fara hawaye yana salati yana cewa maiye aibunshi da har Khadija ta fidda miji bata fidda shi ba, ni kuma tausayi ya bani sosai dan naga yana sonta sosai shine na gaya mashi abunda ya faru da ita da auren da zan mata da Alhaji ban boye mashi komai ba, amman abun mamaki maimakon yace bai aurenta sai yace man ai shi yana sonta a yanda take koda kuwa ta haifi cikin to zai aureta bayan ta gama shayar da abunda ta haifa sannan ya rike abunda ta haifa har yayi mashi aure, amman idan har na yarda a fasa auren da Alhaji shi zai aureta, amman sai nace mashi yaje ya dawo yau dan zanyi tunani, sannan ya shiga motarshi ya tafi bayan ya shigo da tsarabar da ya kawo mata, ni kuma ina dawo na tadda ta a parlour zaune, ban kai da yi mata maganar ba aka kira sallah na tashi na shiga dan yin sallah ina fitowa ban tadda ta a parlour ba sai na shiga kitchen na dafa mata abinci na haɗa mata ruwan wanka shigar da zanyi na tadda ta gudu, kuji abunda mukayi da Aminu."
Chapter 9 · 0% Book details